Showing 24001 words to 27000 words out of 55369 words

Chapter 9 - MAZAN JIYA Littafi Na Farko Rubuta Labari Abdul'aziz Madakin Gini.txt

miliyan dubu daya.
Wohoho! Hakika tashin hankali ba a samasa rana zuwa yake ba sallama, idan mutum yayi arba da wannan zuga ta rundunar sarki Dujalu zai iya haukacewa koma zuciyarsa ta buga fat daya, saboda tsananin kwarjininsu gami da bna tsoro, idan aka ce zasu iya tashin duniyar nan kaf a cikin sa'a daya su baje kaf biranen to ba za ayi mamaki ba, idan suna tafiya a kasa bisa turba aka hangosu daga nesa kamar zango dari sai mutum ya jiyo takun sawayensu wnda ke haddasa girgizar kasa, idan kuwa a sama suke tafiya sai kaga sun haddasa gagarumar guguwa wadda ke haddasa bishiyoyi su kama rangaji suna karyewa da zubewa kasa, koguna kuwa su kuma tambal-tambal suna zubewa kasa.
Sarki Dujalu na da matan aure guda dari da goma sha daya, amman bai taba samun haihuwa ba, bashi da iyaye kuma bashi da sauran dangi face wata kanwarsa guda daya wacce ta kasance kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance wacce suke uwa daya uba daya ana kiranta da suna Hursiyya. A duniya babu abinda sarki Dujalu ke tsantseni sama da kanwarsa Hursiyya, domin ko kadan baya kaunar abinda zai sosa zuciyarta ko kuma ya taba lafiyarta, duk inda kaga sarki Dujalu to fa sai kaga Hursiyya a damansa sam basa rabuwa da juna dare da rana sai dai kwanciyar bacci, kai wani lokaci ma akan cinyar sarki Dujalu Hursiyya ke bacci yana shafa gashin knta gami da raira mata wakoki masu dadin sauraro ko kuma yana bata 'abarai masu dadi da debe kewa, ko kadan Hursiyya bata da sadaukantaka kuma sarki Dujalu bai bata sihirin tsafin sa ba ko guda daya, wani babban abin mamaki a tare da ita shine gabadaya halayenta da ra'ayainta ya sha banban dana dan uwanta sarki Dujalu domin bata son zalunci sannan tana da yawon tausayi. A fagen kyautavkuwa tamkar indararo dan ko yaushe hannunta a bude ya ke, bisa wannan halayya tata ne yasa ta samu daukaka da farin jini a wajen talakawan kasar, har addu'a suke a boye suna fatan Sarki Dujalu ya mutu ta haye kan karagarsa saboda sun san cewa zasu samu yancin kansu. A rayuwar Hursiyya babu abinda ta fi so sama sauraron dadadan labarai, jarumtaka da kuma na abubuwan al'ajabi. Bisa halayen Hursiyya na jin kai da tausayi ne yasa sarki Dujalu ya tsani yin tafiya tare da ita, domin ita ce kadai mahalukiyar da take take masa burki wajen tafiyar da zalunci a harkokin mulkinsa. Kai sau tari ma ko zaman fada baya son yi tare da ita saboda tana yawan katse masa hanzari, kasancewar baya son ganin bacin ransa duk alfarmar data nema baya fasa yi mata, sau tari idan sarki Dujalu ya fusata saboda irin katse masa hanzari da take yi, ko yayi yunkurin dukanta sai ya kasa saboda alkawari daya daukar wa mahaifiyarsu kafin ta mutu, alkawarin kuwa shine ya rike mata Hursiyya bisa amana, kuma komai ta yi bazai hukunta ta ba, sannan zai kula da lafiyarta fiye da yadda zai kula da tasa lafiyar. A duk sa'adda Dujalu ya tuno da wannan alkawari sai ya cizi yatsa kwallar takaici ta zubo masa.
A ranar da su sarki Dujalu suka shafe kwanaki goma sha takwas suna tafiya ne izuwa tekun bahar Suffiyya, sai suka yada xango a cikin wani kyakkyawan daji mai yawan ni'ima, Kasancewar yana dauke da koramai, bishiyoyi da kuma kananun dabbobin daji masu saukin farauta gami da kyawawan tsuntsaye, duk irin masifar dake cikin daji da zarar rundunar su sarki Dujalu ta ratso cikin daji sai masifar ta nemi mabuya saboda taga sa gudu maganin ki gudu.
Bayan an kafa tantuna a cikin wannan daji mai ni'ima an ci abinci an huta sai Hursiyya taga sarki Dujalu ya kwanta yayi shiru ya shiga zurfin tunani, al'amari daya sosa Zuciyarta kenan ta dube shi ta ce ya kai dan uwana ina dalilin wannan tunanin naka haka mai zurfi, shin kana wasi-wasi ne akan samun nasarar mu ne akan wannan yaki da muka fito ko kuma kana tunanin yadda zuwa nan gaba zaka mulki duniya ne?
Yayin da sarki Dujalu yaji wadannan tambayoyi daga bakin yar uwarsa Hursiyya ai yayi murmushi sannan ya sake gyara kwanciyarsa a saman lallausar shinfidarsa irin tasu ta sarakai, ya dubi Hursiyya cikin natsuwa yace da ita ya ke yar uwata kiyi sani cewa duk abinda ika fada ba shi nake tunani ba, ina naxari ne akan yadda soyayya takai Mazan Jiya zuwa ga halaka, har suka rasa komai na duniya, bisa wannan dalili ne nayi alƙawarin cewa bazan taba yarda naso mace fiye da kima ba, domin ita soyayya siradin mutuwa ce, duk wanda ya taka siradin ba makawa sau ya hallaka, haka nan kaidin mace yafi tsinin allura tsini kuma yafi kaifin zabira kaifi, komai jarumtakar mutum kuma komai karfin mulkinsa da karfin arzikinsa mace na iya maida shi rago, fakiri kuma bawa kamar yadda ta faru ga Mazan Jiya irin su Sadauki Hantaru.
Koda jin wannan batu sai Hursiyya ta gyara zama sannan ta ce ya kai dan uwana na rokeka bisa darajar mahaifiyarmu ka bani labarin Mazan Jiya da yadda aka yi soyayya ta jefa su ga halaka.
Dujalu ya gyada kai tare d cewa ai kin tambayeni labari mai tsawo, wanda in muka farashi ban san ranar gamawa ba, sai dai yana dauke da darasi mai yawa a cikinsa domin zaki samu ilimin zaman duniya, za kuma kiji yadda ake yaudara ta rashin mutunci gami da mummunan cin amana, sannan kuma zaki ji abin tausayi wanda nasan dole ne ki zubar da hawaye, ke idan kika ji wannan labari kin daina yarda da kowa a duniya koda kuwa iyayen da suka haifeki ne.
Hursiyya ta sake gyara zama ta ce dan darajar tsafinka da darajar mulkinka ka gaggauta far banu wannan kasaitaccen labarin, ina mai tabbatar maka da cewa ko ina mai tabbatar maka da cewa koda zamu kwana kana jawabi bazan gaji ba, kuma bazan ji bacci ba.
Sa'adda da sarki Dujalu yaji haka sai ya bushe da dariya sannan ya ce to shikenan bari na jarabaki na gani idan har zaki iya jurewa, Dujalu yayi gyaran murya sannan ya fara bada labarin da cewa:
Kimanin shekara tamanin da suka shude, anyi wani adalin sarki mai suna Kusaidu a birnin Kisra, Sarki Kusaidu ya mallaki dukiya mai tsananin yawa, sannan yana da tarin mayaka Hakazalika akwai manya manyan birane a karkashinsa kimanin guda 40, sarkin Kusaidu nada matar aure guda daya jal wadda suka yi auren saurayi da budurwa ana kiranta Bazira, har bayan shekaru oma da aurensu amman nasu taba samun haihuwa ba, ko kadan wannan matsala bata damu Bazira ba. Amman shi sarki Kusaidu duk sa'adda ya kalli yawan dukiyarsa d kuma karfin mulkinsa ya kuma tuna cewa bashi da magaji sai yayi ta kuka, babu irin neman maganin da sarki Kusaidu baiyi ba amman abu ya gagara, domin saida ya ziyarci ko wanne bangare na duniya dan ganawa da manyan bokaye amman abu ya cutura.
Lokacin da Fazira taga hankalin sarki ya ki kwanciya bisa ga matsalar rashin haihuwa, sai ta kadaita da shi ta ce ya kai mijina ka yi sani cewa a duniya bani da farin ciki sai naka, kuma bakin cikinka nawa ne, ni a tawa shawarar tunda dai ni ban haihu da kai ba me zai hana ka kara aure, ko a dace a samu biyan bukata?
Koda jin wannan batu sai Sarki Kusaidu ya cika da tsananin mamaki ya ce da ita Kaicon ki ya ke mata ta, tun kafin muyi aure kika kafa mani dokar cewa daga kanki bazan kara ba, kuma na amince da haka ko kin manta ne?
Da jin haka sai hawaye ya zubo wa Fazira ta ce ai wata larurar tana kawar da wata, nidai a halin yanzu na janye wannan sharadin in har soyayyata da taka ka tabbata gaskiya ce to ka yi aiki d wannan shawara tawa.
Yayin da Sarki Kusaidu ya ji hkaa sai yayi shiru yana tunani ba tare da yace da ita komai ba har izuwa lokaci mai tsawo, daga can kum sia ya dago kai ya dubi Fazira ya ce ki dan bani kwanaki uku zan yi shawara tukunna.
Koda jin haka sai Fazira ta cika da farin ciki kuma ta rungume sarki Kusaidu tare da sumbatar goshinsa kna daga bisani ta fice daga cikin turakar tana tsalle gami da murna, ba kaomai ne yasa Fazira farin ciki ba, sai sanin cewa sarki Kusaidu bashi da wani abokin shawara wanda ya wuce bokansa mai suna Boka Ardusa Bn Zabbar. Fiye da shekaru talatin sarki Kusaidu ake harka da boka Ardusa kuma ya yard da shi dari bisa dari, babu wani sirri nasa wanda bai sni ba. Sai dai abin bakin ciki da takaici shine duk tsawon wadannna shekaru boka Ardusa na cin amanar sarki Kusaidu ba tare da ya sani ba. Domin Ardusa ya mayar da Fazira matarsa ta sirri, wannan cin amana ya samo asaline tun daga lokacin Fazira ta so ta auri Sarki Kusaidu, kasancewarta yar wazirin mahaifinsa amma sai sarki Kusaidu ya nuna ko kadan baya sonta da aure, domin ya dauketa kamar kanwarsa ta jini, dalili kuwa shine a gidan su Fazira sarki Kusaidu yayi wasan kasa saboda akwai yayan Fazira sa'ansa ne, kuma abokinsa wanda suka shaku ainun har ya zamana cewa basa rabuwa dare da rana sunansa Asharab. Tun Fazira na karama jininta ya hadu dana Sarki Kusaidu take matukar kaunarsa, lokacin da Fazira ta cika budurwa sai masoyanta suka yi mata ca! Sabida ta kasance kyakkyawar gaske, ita kuwa sai ta tubure ta ce babu wanda take so face yarima Kusaidu.
A wannan lokaci mahaifin sarki Kusaidu ne yake mulkin birnin Kisra, kwatsam! Sai aka wayi gari Asharab ya kamu da rashin lafiya har ta kaishi ga kwanciya, al'amarin daya dugunzuma hankalin Yarima kusaidu kenan ya koma gidan su Asharab ana jinyarsa kenan dare da rana ya zamana cewar yayi wa gidan sarki kaura gabadaya, a ranar da Asharab ya kwana tara yana jinya ne sai rai yayi halinsa, bakin ciki a wajen Kusaidu bazai fadu ba, domin sai da ya kwana uku bai ci abinci ba, kuka kuwa dare da rana haka ya dinga yi babu sassauci, nan da nan ya rame ya kuma lalace da kyar aka samu ya dawo daidai ya ci gaba da rayuwa kamar yadda ya saba, tun daga lokacin da Asharab ya rasu sai Kusaidu ya dauke kafarsa daga gidansu Fazira gabadaya ya daina zuwa, hakan ne ya tada hankalin Fazira ta dinga biyoshi har gida tana nuna masa soyayya, shiko ya dinga nuna mata cewa shifa kanwa ya dauketa ba masoyiya ba, har Fazira ta girma ta cika ya mace nan fa ta cigaba da kokarin janye hankalin Yarima Kusaidu amman ya ki amincewa da ita.
Sai bayan da mahaifin Kusaidu ya rasune ya gaji sarauta sannan ta soma samun yardarsa albarkacin boka Ardusa. Shidai boka Ardusa hadimin mahaufin sarki Kusaidu ne, ganin haka ne yasa shima Kusaidu ya aminta da shi.
A ranar farko da Fazira ta je wajen boka Ardusa da bukatarta ta son auren satki kusaidu, sai ya nuna mata bukatarta mai sauki ce amman fa sai idan ta yarda ta bashi kanta. Sai da Fazira ta shafe wata uku tana nazarin wannan sharadi a karshe dai taga cewa in har bata amince da sharadin boka Ardusa ba, to fa bazata taba samun damar auren sarki Kusaidu ba. Kawai sai ta abince d shi din, a ranar da abin ya faru ne Sarki Kusaidu ya amince da batun aurenta, da mako ya dawo aka daura auren amman duk da cewa Fazira ta auri sarki bata daina zuwa wajen Ardusa ba sun lalatrsu a sirrance, ita kanta Fazira ta yi mamakin yadda ak yi ta cigaba da yarda da boka Ardusa, abinda bata sani ba shine, ya asirceta ne babu yadda za'a yi ya bukaceta ta ki yarda. Haka dai Fazira da Ardusa suka cigaba da cin amanar sarki Kusaidu har tsawon shekaru sirinsu bai taba tonuwa ba.
Bayan Fazira taji cewar sarki Kusaidu zai yi shawara sai ta saci jiki ta wuce zuwa gidan boka Ardusa nan ta sanar d shi abinda ya faru da sarki, ta kuma ce lallai ya baiwa sarki shawarar ya kara aure.
Boka Ardusa ya kyalkkyale da dare tare da cewa amman ke meye hikimarki akan bashi wannan shawara?
Fazira ta dubi boka Ardusa cikin nutsuwa ta ce da shi ka yi sani cewa har abada sarkk ba zai taba haihuwa ba, tunda matsalar rashin haihuwar daga gareshi ta ke, ni kuwa zan iya haihuwa, idan ya auro wata matar ina so kayi aikinka na bokaye kaga ta samu juna biyu, inyaso cikinka da nake dauke da shi a yanzu in na haifeshi sai ya tashi a matsayin dan amaryar sarki, kaga kenan danmu ne zai gaji sarautar, nasan tabbas zaka iya boye nawa cikin har na haihu ba tare da mutane sun sani ba.
Lokacin da Fazira tazo daidai nan a batunta sai boka Ardusa ayi shiru, ya fada dogon tunani gami da nazari, daga can sai ya bushe da dariya harda buga kafa a kasa yana mai cewa Hakika ku mata ababan tsorone, ta yaya kika iya kulla wannan dogon makircin acikin dakiku kadan? Nikam tunda nazo duniya ban taba ji ko ganin yaudara da makirci irin wannan ba.
Fazira ta bushe da dariyar murna tare da cewa ai bakaga komai ba sai nan gaba tukunna sannan ne zaka gane mu mata mune muke sarrafa duniya da duk abinda ke cikinta, muke haddasa zaman lafiya da rashinsa, kai ko yaki idan kaga ya barke ba zato ba tsammani idan ka yi bincike zakaga snadinsa mune.
Koda gama fadin haka sai Fazira ta mike da sauri, tayi wa boka Ardusa sallama domin a wannan lokacin yamma ta yi likis, ta tashi tayi tafiyarta, kuma a wannan lokaci an kusa tashi daga fada, tana tsoron kada sarki ya nemeta bata nan.
Kamar yadda Fazira ta shirya makircinta haka al'amuran suka kasance, wato sarki Kusaidu ya auro wata kyakkyawar budurwa jinin sarauta mai suna Shamilat acan wata kasa dake makwabtaka da birnin Kisra mai suna Darul Maabur. Wata uku da tarewar amarya Shamilat sai ga ciki ya bayyana, amman abin mamaki shine ko kadan amarya bata ji wani sauyi a jikinta ba, kuma bata yin wata lalura irin ta masu ciki.
Sannu a hankali ciki ya rika girma har ya cika wata tara rana daya sai nakuda tazo wa Shamilat, mata suka taru akanta amman saida Shamilat ta kwana ta wuni tana nakudar bata haihuba. Al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin sarki kenan ya kasa zaune ko tsaye.
A lokacin da shamilat ta samu juna biyu irin farin cikin da sarki Kusaidu yayi ya wuce gaba tunani, domin sai da ya kusa zaucewa saboda tsananin farin ciki, ya rika kyautar dukiyarsa dare da rana, kai sai da takai hatta suturar dake jikinsa yana cirewa gami da baiwa barorin dake gidan sarautar, har sai da aka kulleshi a daki kuma aka hanashi fita.
Yayin da nakudar amarya Fazira ta ki cinyewa sai ga uwargida Shamilat ta zo dakin haihuwa, da zuwanta sai ta kuri duk matan dake baiwa Shamilat agaji ta ce duk basu san aikinsu ba ma, kawai sai ta kulle kofar dakin ya zama cewa daga ita sai mai nakudar a cikin dakin, nan take ta shafa cikin amarya Shamilat ai kuwa sai hankalinta ya gushe ta suma, Fazira ta shafi nata cikin kawai sai ga tsohon cikinta ya bayyana kuma nan take nakuda ta zo mata, bayan kamar rabin sa'a Fazira ta haifo santalelen yaro kyakkyawan gaske, cikin hanzari ta gyara jikinta sannan ta gyara jaririn ta ajiyeshi daf da amarya, daga nan ta sake shafar cikin anarya a karo na biyu sai ga jinin haihuwa na zubo wa daga jikinta. Jim kadan amarya ta farfaɗo aiko sai ta ji jariri na tsala kuka a kusa da ita.
Koda sauran mutanen gida suka jiyo kukan jariri sai suka rugo izuwa dakin haihuwar suna shewa gami da murna, cikin matukar mamaki. Ai kuwa labari na riskar sarki sai kuwa ya fito daga cikin turakarsa tare da fadawa dakin haihuwar ya dauki jaririn ya rungumeshi yana kukan farin ciki.
Sai da aka kwana talatin ana bukukuwa da walimar farin ciki a birnin Kisra saboda murnar wannan haihuwa da akayi wa sarki Kusaidu.
A kwana a tashi dan da amarya ta haifa mai suna Hantaru ya fara girma ya cikq shekaru biyar, Hantaru ya taso yaro kyakkyawa mai jarumtaka tq ban al'ajabi, domin tun yana da shekaru iyar yake iya daukar abubuwa masu nauyin gaske, idan kuwa yana wasan kokawa a cikin sa'anninsa babu mai iya kada shi. Kai sai da takai cewa yaran da suka girmeshi ma kada su yake yi. Lokacin da Hantaru ya cika shekaru tara sai ya zama cewa yana satar jiki ya shiga daji yin farauta shi kadai b tare da ya dauki makami ba, sai dai aka ya kamo damisa ko bauna ya shigo da ita gari a mace bisa kafadarsa.
Nan da nan jarumtakar Hantaru ya bazu a ko ina a nahiyar, har aka dinga zuwa kallonsa ana mamakin sa, wani abin mamaki a tattare da Hantaru shine ko kadan bai damu da harkar sarauta ba, babu yadda sarki Kusaidu bai yi da shi ba akan ya rinka zuwa fada sun zama tare amman sai ya sulale ya tafi farauta. Baya ga farauta abu abinda Hantaru ke so sama da koyon yaki, dan haka sai ya like wa Sarki yakin birnin Kisra ya zamana cewa kullum yana gidansa yana koyon yaki. Aiko a cikin shekaru bakwai Hantaru ya zama gagarumin mayaki har ma yafi sarkin yaki shahara.
Tun sa'ar da Fazira da boka Ardusa suka fa cewar gaba daya hankalin Yarima Hantaru baya kan sarauta sai hankalinsu ya dugunzuma suka shiga kokarin asirce zuciyara domin yayi watsi da harkar farauta data koyon yakin nan. Amman sai suka sha ruwan mamaki domin asirin da suke masa yaki yayi tasiri akansa. Ganin haka ne yasa Boka Ardusa ya dukufa akan binciken gano dalilin faruwar hakan, a cikin binciken nasa ne ya gano cewa nonon da Hantaru ya sha na amarya shine yya janyo ashin tasirin tsafi a jikinsa, domin ita amarya Shamilat

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login