Showing 6001 words to 9000 words out of 55369 words
Chapter 3 - MAZAN JIYA Littafi Na Farko Rubuta Labari Abdul'aziz Madakin Gini.txt
yayi ta wuce dakuna barkatar yane leke leke ta cikin tagoginsu. Wani lokacin sai kaga saura kiris a ganshi sai kuma ya duka kasa ko ya shige cikin wani lokon ya 6uya.
Yana cikin haka ne ya hango wani daki kofar sa a bude kuma fitila a kunne. Koda ya leqa tagar dakin sai ya hango kuyangin nan guda biyu a zaune cikin tararrabi idanun su a bushe babu alamar sunyi barci ko suna jin sa, cikin zafin nama imnal ya fada dakin ya rufo kofa. Koda kuyangin nan biyu suka ganshi sai sukayi sauri su kashe fitilar dakin, cikin rada daya daga cikin su ta matso dab da shi ta ce hakika ka cika mai sa.a yaya akayi ka shigo cikin gidan nan ka tsallake duk tsaron waje da na ciki?
Imnal yayi ajiyar zuciya ya ce ni dai yanzu bani da lokacin amsa tambaya ,abin da nakeso da ku kawai kuyi mini jagora izuwa inda turakar gimbiya take.
Cikin hadin baki suka ce"ta6dijan ka rufa mana asiri indai ba so kake a hallakamu ba shin ba ka jin guje gujen dakarun tsaro ne? Nan din nan ma da kake ciki hadari ne ga rayuwar mu idan aka shigo aka ganka. Abin da zamu iya yi maka kawai shine mu baka zanen taswirar gidan nan mai dauke da nunin inda gimbiya take" Imnal ya ce na gode da hakan ma maza ku bani.
Cikin rawar jiki daya daga cikin kuyangin ta dauko taswirar wadda ke zane akan wata busasshiyar fata ta miqa masa ta ce "Wannan ita ce gudummawar mu a cikin soyaiyarku kai da gimbiya"
Koda jin haka sai murna ta kama imnal yace "Ni kuwa nayi muku alqawari duk ranar da burin mu ya cika ni da gimbiya sai na 'yantaku na ba ku kyautar dukiya irin wacce ba.a ta6a baiwa wani ba"
Gama fadin hakan keda wuya sai suka ji ana kwankwasa kofar dakin da qarfi ana yi musu tsawar su bude.
Kafin kuyangin suyi wani yi wani yunkuri sai suka ga imnal ya daka tsalle sama kamar dan biri ya naushi saman rufin dakin wanda akayi shi da katako mai kaurin gaske. Take saman ya 6urma ya fice fit ta cikin sa. Koda imnal ya tsinci kan sa a saman rufi sai ya ci gaba da gudu akan dakuna. Ba zato sai yaji ana harbo masa kibiyoyi cul cul cul ! In ba don karfin gudun sa ba da tuni an sameshi, sai da yayi tafiya mai tsayi a sama sannan ya hango wani tafkeken tafkin wanka mai dauke da ruwa garai garai gunin ban sha.awa.kwatsam sai ya hango gimbiya Mulaifa a tsaye a gaban tafkinkwatsam sai ya hango gimbiya mulaifa a tsaye a gaban tafkin ta daga kai sama tana duba madubi.
Koda imnal yaga babu kowa a kusada ita sai ya yadako tsalle ya fado cikin tafkin kafin ya fito daga tafkin tuni itama ta daka tsalle ta biyoshi ciki kawai saita danna shi izuwa kasan tafkin sukayi nutso ta wuce gaba yana biye da ita sai gasu sun biyo wani kwararo sun fito saman wani sabon tafkin wadda yake tsakiyar cikin turakarta babu kowa awajen face kuyangi fitowar keda wuya daga cikin tafkin sai kuyangi 2 suka rugo suka yafa musu mayafan goge jiki har izuwa wannan lokaci mulaifa bata dubi fuskar imnal ba balle tace dashi wani abu kuma fuskarta a murtuke take tamkar wadda aka aikowa sakon mutuwa.
Al'amarin daya jefa imnal cikin mamaki kenan amma sai yayi shiru baice komai ba bayan an gama tsame lemar dake cikinsu sai Mulaifa ta sake kama hannun imnal zuwa dakin baccinta da zuwa sai dukkanin kuyangin da suke ciki suka fito waje suka rufo kofa nan take Mulaifa ta sharawa imnal mari ta fashe da kuka ta rungumeshi tana mai cewa saboda mai zaka saida rayuwarka kace sai kazo ka ganni a wannan dare, shin mun rabune har abada baxamu sake saduwa ba inda tsautsayi yasa ka hallaka da tuni nima na kashe kaina.
Sa'adda imnal yaji wannan batu na mulaifa sai gabadaya jikin shi yayi sanyi nan take yaji kaunar mulaifa ta kara mamaye zuciyarsa kawai saiya janye jikinsa suna masu fuskantar juna yace yake abin begena kiyi sani cewa sa'adda na samu labarin halin da kika shiga sbd hukuncin da aka yanke min sai hankalina ya dugunzuma, naji bazan iya yin komai ba sai nazo na ganki burina na ganki da idanuna koda kibiyoyi dubu zasu nutse a cikin gangar jikina, sa'adda imnal yazo nan a zancen sai mulaifa ta sake rungumeshi cikin tsananin farin ciki tana mai cewa tabbas kaine zaka zamo abokin rayuwata gama fadin hakan keda wuya sai sukaji Sarki Maharaz na kwankwasa kofa yana cewa a bude alamarin daya dugunzuma hankalin imnal da kuyangun ita kuwa mulaifa ko a jikin ta kawai saita dafa imnal da dan yatsanta guda na hagu take imnal ya rikide yazamo kofin zinare irin wadda ake saka furanyi aciki faruwar hakan keda wuya sai mulaifa ta umarci kuyangin nata su bude kofar. Sarki maharaz ya shigo a fusace yana haki nan take ya kama kalle-kalle yana nazarin ko wace kusurwa batareda yace komai ba. daga can sai Mulaifa ta duci sarki tace babu wani bako daya shigo wajena koda jin haka sai sarki maharaz yayi murmushi ya matsa dab da Mulaifa ya dafa kafadunta yace yake yata a iya sanina baki taba min karya ba ashe za'a wayi garin ranar da zaki min karya saboda soyayya inaso kisani cewa na fahimci akwai soyayya tsakanin ki da imnal dan sarkin yaki tabbas shina nake zargi da shigowa gidan nan ahalin yanzu na tura dakaru zuwa gidan sarkin yaki idan sukaje suka iske baya nan tabbas toh shine yazo... hukuncin kisane zai tabbata akan shi maimakon horo.
Koda mulaifa taji haka sai hankalinta ya dugunzuma amma saita dubi sarki maharaz batare da nuna wani damuwa ba tace ina mai tabbatarka imnal na gida a kwance, sarki maharaz yayi murmushi har ya juya zai fita sai idanunsa suka kai kan wannan kofin zinaren sarki maharaz ya kura kofin kurawa kofin idanu yana nazarinsa, a lokaci ne zuciyar Mulaifa ta fara bugawa.
Lokacin da sarki maharaz ya kurawa kofin zinaren nan idanu yana nazarin sa a lokacin zuciyar Mulaifa ta fara bugawa da karfi bayan sarki maharaz ya gama nazarin wannan kofin saiya juyo ya dubi mulaifa yace yaushe kika samu wannan kofin? Nide asanina bantaba sayo irinsa ba mulaifa tayi murmushi tace ai musamman na aika birnin shamrun aka kera mini shi koda jin haka sai sarki maharaz ya karisa inda kofin yake ya daukeshi yana mai jujjuya shi a hanun shi yace amma fah ya bani sha'awa sosai shin zaki iya bani kyautarsa mulaifa tayi murmushi tace ya abbana ai komai kake so daga gareni basai ka tambaya ba dauka yakamata kayi kawai amma akwai wanda zaifi dacewa dakai nasa akera maka shi zaizo nan da kwana Bakwai, yayin da sarki maharaz yaji wannan magana sai jikinsa yayi sanyi kuma ya kasayin gardama kawai saiya ajiye kofin sannan ya sumbaci goshin gimbiya mulaifa ya fice daga cikin turakar. Fitarsa keda wuya sai kuyangi suka rufe kofar turakar. ita kuma mulaifa saita ruga ta dauko wannan kofin zinare nan take ta karanta wadansu dalamisan tsafi ta tofa akan kofin faruwar hakan keda wuya sai kofin ya tarwatse kamar an watsa hoda, sannu a hankali hodar ta dinga disashewa ta bace bat kawai sai gimbia mulaifa ta tafi izuwa kan gadonta ta kwanta domin sai a sannan ne hankalinta ya kwanta.
Al'amarin imnal kuwa shide kawai ya tsinci kansa ne kan gadon cikin dakinsa kawai sai yaji ana magana da mahaifinsa hibru a kofar dakin ga dukkan alamu ran hibru a bace yake domin yana magana ne cikin daga murya da fushi maganar da imnal ya fara ji daga mahaifinsa itace, yanzu niza ayiwa haka to kusani cewa tun safe ina tareda dana kuma yanxu haka yana cikin dakinsa yana barci wata kakkausar murya tace "Ya shugabana kayi hakuri mu yan aiken sarki ne dan haka bai kamata kaga laifin mu ba saboda bin umarni ne, yanzu dolene ka bude mana mugani idan yana ciki musan amsar daza muje mugayawa sarki, idan kuma bazaka bude ba dolene mu bude da kanmu".
Koda jin haka sai hibru yayi ajiyar zuciya yace ai bama sai takai haka ba.
Nan take ya bude kofar dakin aiko saiga imnal yanata sharar barci abunsa kamar ma baisan abinda akeyiba sai jikin dakarun sarki yayi sanyi babban cikinsu mai kakkausar murya ya dubi hibru yace ka huta lafiya ya shugabana kawai saiya juya ya fita daga cikin dakin sauran dakarun kuma suka rufa masa baya, cikin hanzari hibru yaje ya kullo kofar gidan sannan yadawo cikin dakin imnal ya dubi imnal yace yakai dana tashi muyi magana nasan idanunka biu kuma tabbas ka fita daga cikin gidan nan cikin dare.
Koda jin haka sai imnal ya mike zumbur ya kurawa hibru idanu cikin mamaki sannan ya sunkuyar da kanshi kasa cikin alamun kunya da rashin gaskiya.
Koda ganin haka sai hibru yace yakai dana kayi sani cewa duk wanda ya rigaka kwana dolene ya rigaka tashi a ka'idar rayuwata duk tsakar dare nakan farka na duba ko'ina na gidan nan kuma na fita kofar gida na kwanta, tun kafin a haifeka nake wannan al'ada kuma mahaifiyar ka batasan inayi ba, yauma kamar kullum hakan tafaru kuma dana duba cikin dakinka sai naga baka nan kuma dana duba waje sai naga babu dokinka, hakan ya tabbatar min dacewa ka fita cikin daren nan abinda bansani ba ina katafi? yanzu na samu amsar inda kaje tunda dakarun sarki sunzo don su tabbatar da cewa ko kaine kaje gidan sarki yakai dana mai yasa kake jefa kanka cikin rigima da tashin hankali mai kajeyi gidan sarki shin kamanta ne cewa kanada babban kaifi kuma a gobene za'ayi maka hukuncinsa.
Sa'adda hibru yazo nan a zancensa sai jikin imnal yayi sanyi, daga can sai yadago kai cikin alamun nadama yace yakai abbana ka gafarceni kayi sani wannan kuskuren danayi bayin kaina bane zuciya ce ta ribance ni ina mai tabbatar maka ayanzu nida gimbiya mulaifa bazamu iya rayuwa ba idan bama tare da juna.
Koda jin wannan batu sai hankalin hibru ya dugunzuma ya mike tsaye ya juyawa imnal baya lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla, imnal ya mike tsaye ya zagayo gaban hibru ya tsaya kawai saiya durkusa bisa gwuiwoyinsa ya kama tuba da neman gafara hibru kuma kama kafadan imnal yayi suka fuskanci juna a lokacin da hawaye ke zuba da idanunsu hibru yace yakai dana bakayi min laifin komai ba kayi sani cewa in bah soyayya ba da nine sarkin wannan birni namu, amma saboda na zabi soyayya nayi watsi da mulki in badan soyayya ba da maxan jiya guda uku wato jarumi hulkas mai hular Lamsara, Kaura Shaddadu na birnin Kufa mai mashin galilul haras da sadauki Hantaru mai takobin Saiful Lujara da basu mutu a banza ba tabbas soyayya tushen wahala ce sai mai sa'a da rabo ke tsallake shaukin cikinta ina tsoron kada rayuwar ka ta kare irin yadda tawa takare da kuma yadda ta mazan jiya takare, ya kai dana kayi sani cewa na ziyarci bokaye da dama kuma sun tabbatar min dacewa zaka samu daukaka anan gaba. Da wannan furuci nake maka sallama sai ka je ka kwanta ka rintsa muga abinda zai faru dakai gobe, gama fadin hakan keda wuya sai hibru yaja kofar dakin ya rufe Imnal ya koma kan gadonsa ya kwanta.
Tab! Gaskiya nima fa na fara tsorata da sha'anin soyayya dan haka zan ajiye dukkan wasu kalamaina na soyayya a wajen guda tunda ga jarumai ma masu dakakkiyar zuciya sun mutu a banza saboda tafarkin soyayya ballantana mu 🤔, amman dai wace irin shawara zaku bani shin na cigaba da soyayya ko kuma na hakura da ita gudun kada abinda ya faru da mazan jiya ya faru da ni.
Shin kana bukatar wani littafi na yaki kawai tuntubeni ta wannan Number ko kuma kayi mani magana da profile dina 08138873799.
Zan ci gaba.
MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part D
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Al'amarin sarki hibru kuwa tunda duku dukun safiya ya shirya abincin kalaci ya shiga dakin imnal sai ya iske shi acikin mafarki har yana surutai a fili, ba komai yake ambato ba face sunan gimbiya Mulaifa yana fadan kalamomin soyayya. Hibru ya daki kafar imnal yana mai daka mishi tsawa yace mai kakeyi har yanzu baka tashi ba, to kasani saura kiris mu makara zuwa fada, kashirya ka sameni a falo muyi kalaci, gama fadin hakan keda wuya sai hibru ya juya ya fita, shiko imnal sai yayi sauri ya kimtsa ya riski hibru a falo sukayi kalace sannan suka fita kofar gida domin su tafi izuwa fada. Da fitowarsu sai hibru ya shiga cikin bsuma ya kamo dokinsa da nufin su hau tunda na imnal baya nan, har sun yunkara zasu hau sai imnal ya hango nashi dokin ya tafo da gudu shi kadai, cikin gaggawa imnal ya rugo ya riske shi kawai sai yaga wasika a karkashin siddin dokin cikin zafin nama ya zare wasikar ya boyeta acikin rigar sa saboda kar hibru ya gani, nan take imnal ya hau kan dokin shi shima hibru hau kan nashi suka tafi fada.
Fada ta cika makil babu abunda mutum zai gani sai kawunan bil'adama lokacin da hibru da imnal suka shigo cikin fadan kowa ya gama halatta har sarki kuwa sai da yazo, kuma a wannnan lokaci shi ake jira a hankali suka cigaba da tafiya bisa kafafunsu suka durfafi inda sarki yake. Sarki maharaz da gimbiya Mulaifa na zanne sun zubawa su hibru idanu shi dai sarki maharaz fuskar sa acike takeda murmushi amma na mugunta ita kuwa gimbiya Mulaifa fuskarta acike take da tsananin damuwa kamar zata fashe da kuka. Koda hibru da imnal suka zo dab da karagar sarki sai suka zube kasa suka kwashi gaisuwa. Sarki maharaz ya amsa gaisuwan cikin murmushi yana mai kauda kai ga kallon su kawai saiya dubi wadansu karti biyu majiya karfi da suke tsaye a gefe daya yayi musu inkiyar su cika aikin su, nan take kartin biyu suka kama imnal suka daure shi ajikin wani murtukeken ice mai gwafa dake kasa sannan sai suka yayyage rigar jikin imnal da karfin tsiya suka daga murtukeken icen sama suka soke shi acikin rami mai zurfi saiga imnal a sama.
Koda kammala haka sai sarki maharaz ya miki ya fiskanci gabadayan jama'ar da suke fadan yace yaku jama'ar darul mahabur, kamar yadda kuka sani fiye da shekaru talatin da suka gabata muna bautan mai girma darbuza a kasar nan, ba ataba samun wanda ya karya doka ba, sai a wannan karon da imnal dan hibru ya aikata wannan laifi kusani mai girma darbuza shiya yanke hukunci dakansa hukuncin kuwa shine za ayita shara masa bulala har sai fatar jikinsa da kwoilewa kuma ana zuba mishi gishiri acikin shi har sai ya suma. Ba za'a kunce shiba sai ya kwana, kuma babu ci babu sha har na tsawon kwana uku.
Koda sarki maharaz yazo nan a zancensa sai gimbiya Mulaifa ta fashe da kuka ta kama rokon sarki maharaz da ayi wa imnal afuwa, sarki maharaz ya dakawa mulaifa tsawa yace kinaso nima nayi laifi ne ga mai girma darbuza, lallai ni mai biyayyane ga mai girma darbuza idan kikaga ba ayiwai imnal wannan hukuncin ba to tabbas bana nunfashi ne, nan take sarki maharaz ya sake duban karti guda biyu kawai sai suka daiki bulala da gishiri acikin wani katon kasko suka hau kan wani dogon munbari mai matattakala, Wanda yake dab da inda aka daure imnal suka fara cika aikinsu, yazama cewa daya ya fara zabgawa imnal bulala shi kuma dayan yana manna mishi gishiri a fatar jikinshi, maimakon jama'ah suji imnal na ihu da kuka sai sukaga ya kurawa gimbiya mulaifa idanu yana mai murmushi, ita kuma mulaifa in banda kuka babu abunda takeyi awannan lokaci a sannan jamma'ar dake wajen suka tabbatar da cewa akwai soyaya tsakanin imnal da gimbiya Mulaifa.
Kafin ajima bayan imnal yayi kaca kaca da jini, komin rashin imanin mutum idan yaga yadda akewa imnal dolene ya tausaya mishi, lokacin da Mulaifa taga azabar da akewa imnal ta wuce ta hankali sai ta mike zumbur ta ruga izuwa gidan sarauta kash!! inda gimbiya Mulaifa tasan muhimmancin zamanta awajen da bazata tashiba domin kallon fuskarta da imnal keyi shi ya hana shi jin zafin azaban da akeyi mishi, aiko tana shigewa gidan sarauta imnal yaji tamkar numfashinsa zai dauke sbd azaba amma saboda juriya da jarumtaka saida imnal ya shafe sa'a uku acikin wannan hali sannan ya suma, duk abinda ke faruwa sarki yaki hibru na tsaye a gefe yana kallo yana murmushi tamkar zuciyar sa bata sosuwa akan abinda ke faruwa, a badine zuciyar hibru a tafasa take kamar zata kone saboda takaicin da bakin cikin ganin yadda sarki ya rufe Ido yake horar da dansa, babban takaicin dake damunshi shine yasha bakar wahala awajen taimakon sarki maharaz harma ya kusa rasa ranshi a lokacin da sarki maharaz yake neman haihuwa ruwa ajallo yau gashi sarki bai damu danashi danba. hibru ya tambayi kanshi wai menene amfanin biyayyar dana kewa sarki, akan wani dalili zan cigaba dayin bauta ga Wanda baisan halacci ba, na kubutar da rayuwar yar shi amma shi gashi yana so ya salwantar da dana hakika lokaci yayi dazan daina wannan bauta a yayin da muka bar gida don tafiya wannan gagarumin yakin, adaidai wannan lokacin da sadauki hibru yazo nan azancensa imnal ya suma saboda azabar da'ake masa.
Koda kartin biyu sukaga ya suma sai suka daina masa azaban suka sauko daga mumbarin a sannan ne sarki maharaz ya sake mikewa cikin farin ciki yace yanzu mun cika umarnin mai girma darbuza hankali ya kwanta dan haka da sallami kowa, shiko mai laifi za'a bar dakaru masu tsaronsa don karwani yakawo masa dauki lallai ahaka zai kwana uku batare daci ko shaba koda gama sai sarki ya juya da nufin ya shiga gidan sarauta kawai saiya hada idanu da sarki yaki hibru nan take maharaz yaji zuciyar shi ta buga da karfi, bakomai ne