Showing 15001 words to 18000 words out of 55369 words

Chapter 6 - MAZAN JIYA Littafi Na Farko Rubuta Labari Abdul'aziz Madakin Gini.txt

tazo nan a zancen ta sai naji dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyata kawai saina dubi sarki hubru da maharaz nayi musu inkiya dasu fada cikin keken doki aikuwa sai sukayi wuf suka fada suka rufe kansu niko saina zare takobi na, na fuskanci uwar dodanni nace ai saiki fara gamawa dani kafin ki gamada sarki hubaru koh! nikaina nasan bakin rijiya yafi gaban wasan yara dan haka tsaurin ido kawai dakuma jarraba sa'a nayi amma ko kadan banasa ran cewa zan iya tabuka wani abu saidai nasan ance mai rai baya rasa motsi watakila nadan iya bata mata lokaci.
Lokacin da uwar dodanni taji nayi wannan lafaji a gabanta saita sake bushewa da mahaukaciyar dariya a karo na biyu wadda har zaida walkiya tayita fita daga bakinta tartsatsin wuta yadinga fita cikin dacin rai da shammata ta mangareni da hannunta guda sbd karfin dukkan saida nayi sama na gwara baya ajikin wata bishiya ita kanta bishiyar saida ta tunbuko har jijiyoyin ta daga cikin karkashin kasa muka fadi kasa tare na baje wanwar a sume koh shurawa ban sake yiba azaton uwar dodanni kasusuwan bayana sun karye na mutu don haka saita zuro hannun ta a hankali ta balle kofar dakin keken dokin dasu sarki hubru ke ciki sukayi arba da fuskarta kawai saita kama musu dariya alamarin daya firgita su kenan mussan da suka hango a can gefe daya a kwance a mace ana cikin wannan haline na farfado akayi sa'a kuwa banyi yunkurin mikewa ba yadda hankalin uwar dodanni zai dawo kaina, a sannan ne tazuro hannun ta cikin keken dokin ta damko sarki hubru da maharaz tayi sama dasu da nufin takai kawunan cikin bakinta ta gutsure su kwatsam sai uwar dodanni taji motsi akan jelar ta abinda bata saniba shine nine na ruga na hau kan jelar naketa tsala matsanacin gudu domin na isa kan kafadarta kafin hannunta yakai bakinta, koda uwar dodanni taji motsin yana karuwa saita fara kai duka faruwar hakan ne tasa uwar dodanni tasamu jinkirin kai hannunta izuwa cikin bakinta ta gutsure kawunan su sarki hubaru koda taga motsin yaki karewa saita maida hankalinta wajen kai hannunta cikin bakinta guda saura kiris ta zuro kawunan su sarki hubaru a bakinta na iso kan kafadar ta aikuwa saina daka tsalle daga kan kafadarta nakaiwa hannunta sara wanda ke dauke dasu sarki hubaru take takobi na ya zabtare hannun nata ya fado kasa su hubaru suna cikin yankekken hannun nan kuwa ya kama tsartuwa da feshi daga cikin dulgul min hannun tamkar magudanar ruwa ta balle tsananin zafi da zogine da uwar dodanni tajine yasa tahaukace ta makance tahau kaiwa iska duka tana ruri da kururuwa mai tsananin firgitarwa, koda naga ta dimauce saina dinga saran sassan jikinta da takobina nikaina nayi mamakin yadda nasamu wannan nasara cikin gaggawa haka bayan sassan jikin uwar dodanni ya gama faduwa kasa sai sarki hubaru da maharaz suka fito daga cikin keken doki suka kuramin ido kawai suna mai matukar mamaki na sarki hubaru ya dube ni yace wai shin wannan yaro anya kuwa kai mutum ne tayaya kake yin wadan nan abubuwan alajabi wadanda sunwuce gaban tsammani. Koda jin haka sainayi murmushi na goge jinin dake jikin takobina na sumbaci takobin nace ya shugabana kaga wannan takobin inhar dai ina tare da ita bana shakkar tarar kowani irin bala'i asalinta ta kaka nane na uku indai kaga an cini da yaki to bana tarene takobin nan nayi imani da haka sarki hubaru ya kurawa takobin nawa ido dakyau ya girgiza kai baice komi ba.

ayi hakuri da wannan zancigaba zuwa anjima.
**********************
Mazan Jiya Part 12

#Cigaba

A sannan ne muka dubi gawarwakin dakarun mu dake zube a kasa sai takaici ya turnuke mu bamu san sa'adda idanunmu suka ciko da kwalla ba nan take muka cinnawa gawarwakin wuta sannan muka hau keken dokin sarki hubru muka cigaba da tafiya har muka isa kauyen zumur bamu sake haduwa da wani tashin hankaliba kamar yadda bokan sarki hubru ya fadi haka alamura suka kasance da isarmu kofar gidan yadaga kwagirin sa na sarauta sannan ya sake shi ya fado kasa aiko sai kwagirin ya cake a karkashin kasa bai fadi kasa ba koda ganin haka sai sarki hubaru ya dubeni yace maza ka tone daidai inda kwagirin ya cake, nan take na cika umarni koda nayi rami mai zurfi kamu uku saiga wadansu layu ina fito dasu sai maharaz yayi nuni ga hannunsa akan layun take suka kone kurmus faruwar hakan keda wuya said juyo shewar mata acikin gidan take abul husuna ya fito daga cikin gida ya takawa da kafafunsa cikin koshin lafiya, koda yayi arba da sarki hubru sai yacika da tsananin farin ciki ya rugo gareshi suka rungumi juna abul husuna yace lale marhabin da aminina dama nayi mafarki zan warke daga wannan cuta a ranar daka kawomin ziyara.
Koda jin haka sai sarki hubaru yayi murmushi yace aiko mafarkinka gaskiya ne tunda gashi ya tabbata nan take sarki hubaru yabawa abul husuna duk abunda yafaru tsakaninsa da bokansa akan rashin lafiyansa koda jin haka sai abul husuna ya cika da tsananin mamaki yace aiko shi makiyi bashida kama domin aduk fadin garin nan babu mai nuna min kauna samada tsohon shugaba ashe kaunar ta karyace da yaudara, rufe bakin abul husuna keda wuya saiga matar tsohon shugaban da yayan sa sun rugo da gudu suna kuka da zuwa sai suka zube a gaban abul husuna suka bada lbr cewa ga maigidan su can yayi wata irin mutuwa mai ban tsoro, koda jin haka sai sarki hubru ya dubesu yace kuje ku kone gawar maigidanku domin sharrin dayaso yayi abokina abul husuna ne ya koma kansa, koda jama'ah sukaji lafazin da sarki hubaru ya fada akan tsohon shugabansu sai duka hai tsine masa da murna akan muturwar sa, nan take abul husuna ya shigar damu cikin gidansa ya kaimu har izuwa turakarsa zaman mu keda wuya sai wata tsaleleliyar budurwa wadda muka gani tamkar hussainar gimbiya sahira ce sbd tsananin kyawu shi kansa sarki hubru baisan sa'adda ya kura mata idanu ba dan tsananin alajabi itadai wannan budurwa bambamcinta da sahira kawai tafita shekaru ne akalla zata girmeta kamar da shekaru biyu budurwa ta nufo mu da farantin abinci sannan ta durkusa har kasa ta gaisheda sarki hubru sannan muma ta gaishe mu sannan ta koma cikin gida har sarki hubaru ya bude baki zaice wani abu sai abul husuna yace kada kace komai yakai abokina wannan budurwa dakuka gani yata ce ta cikina sunanta husna kamar yadda ka boye yarka ga jama'ar kasar nan haka nima na boye tawa kuma bokan da yamaka bayanin cutata shine yasa na boye tawa yar kuma ya gayamun cewa duk ranar daka kawo min ziyara tare da matasa biyu masu tsaron lafiyar ka to acikin sune yata zata samu mijin aure sa'adda abul husuna yazo nan azancensa sai sarki hubaru ya cika da tsananin mamaki. Daga can sai sarki hubaru ya kallemu yace ku tashi ku fita inason ganawa da abokina.
Haka muka tashi muka fice duk kuwa da cewa muna matukar jin yunwa kuma ga abinci mai rai da lafiya an kawo. Bayan fitarmu daga gidan Abul Husuna sai muka samu waje muka zauna muka yi shiru dayanmu bai ce uffan ba, daga can sai na dubi Maharaz nace da shi ya kai abokina nifa abubuwan nan dake faruwa da mu suna jefamu cikin rudani da rikittarwa, kaga dai ance dole a cikinmu ne daya zai auri Gimbiya Sahira sannan ance a cikin mune daya zai auri wannan budurwa Husuna, ina ganin tun yanzu ynaa da kyau kowanne daga cikinmu ya banbance zabinsa, kai yanzu a cikin yan matan nan biyu wacce ta kwanta maka a rai.
Yayin da Maharaz ya ji wannan tambaya sai yayi murmushi yace ya kai abokina kayi sani cewa ai ni bani da zabi sai abinda ka zaba, dan kada na zabi wacce kake so a ranka, nikam duk wacce na samu babu matsala.
Da jin wannan batu sai hankalin ya dugunzuma nace da shi a'a ba za a yi haka ba, inaso ka yi sani cewa idan ka auri gimbiya Sahira ba zaka yi arziki ba, kuma ba zaka yi sarauta ba, alhalin tun tasowarka baka da wani buri da ya wuce ka zama attajiri kuma ka yi sarauta, amman idan ka auri Husuna tabbas wannan burika naka zasu cika, saboda haka ka yarda ka auri Husuna ko dan ka cika wadannan urika naka.
Koda Maharaz ya ji wannan batu sai ya rungumeni ya kuma fashe da kuka yana mai cewa lale maraba da abokin na gari wanda ke son ganin cikar burin abokinsa.
Cikin kaduwa na janye jikin daga nasa muka fuskanci juna nace da shi "Ya kai abokina ina dalilin wannan kuka naka?"
Maharaz ya sunkuyar da kansa kas y ce ban taba sanin cewa kana kaunata fiye da yadda kake kaunar kanka ba sai yau, tabbas ka dakusar da taka rayuwar dan daga tawa, tuni nima nayi bincike a wajen bokan mahaifina ya tabbatar mani da cewa kaine kadai zaka iya taimaka mani domin cimma burikana, idan kwa ka ki tofa sai dai na mutu a matsayin bawa, amman idan ka taimaka mani to kai zaka mutu ne a cikin bauta.
Koda naji haka sai nayi murmushi nace na gwammace na mutu a cikin bauta muddin burinka zai cika, kuma nima nasan nawa burin zai cika tunda nasan zan gaji mahaifina sarautar Sarkin yaki.
Maharaz yayi murmushi farin ciki sannan yace tabbas zaka gaji mahaifinka.
Saida mukayi kwana biyu acikin kauyen zumur sannan mukayi shiri muka koma birnin darul mabur mu uku kacal, Sarki hubru bai yarda abul husuna yabamu yan rakiya ba mun isa gida lafiya amma sai muka iski wani babban abun bakin ciki wadda har izuwa karshen rayuwata bazan taba mantawa dashiba abunda muka iske shine tundaga komar gidan sarauta muka dinga arba da gawawwaki duk inda muka duba saidai muga jini na malala sai tarin gawa, a dimauce muka ruga izuwa gidan sarauta sarki hubru na kwalawa yarsa kira amma baiji ta amsaba gabadaya hadiman gidan ma babu wanda muka riska a raye a cikin turakar sarki hubru ne mukaga wata wasika akan gadonsa sarki hubru ya sunkuya yadauki wasikar, a lokacinda hannayen sa suke karkarwa cikin karfin hali yafara karanta wasikar kamar haka takarda daga sarki uban sarakai gwarzon sarki dodon mazaje wato sarki dumbazu na birnin kailus zuwaga kaskantaccen sarki mai taurin kai, babban abokin gabata hubru Ibn salkas ina mai sanar dakai cewa ruwa ba sa'ar kondo bane tabbas ina sama dakai, kodayake ka cancanci yabo domin yau shekara goma ina kokarin kasheka amma na kasa ayanzu na aiko gilzam da maridai yaranka sun hallaka su na turo uwar dodannin duniya itama sun hallakata toka sani zuciyar maza ta tafasa dan haka na taso dakaina na shigo har cikin masarautarka domin in halakaka da hanuna amma sai akayi rashin dace baka nan, abinda ya hanani na biyo bayanka shine binciken danayi a tsafi in nabiyoka ragas zanyi da yaranka, don hakane na yanke shawarar na dauke yarka sahira na tafi da ita izuwa fadata idan ka isa kai ubane mai son yarsa kazo har fadata ka karbi yarka idan bakazo ba zan yanke kan yarka na turo maka shi nan da kwanaki talatin idan kuma kana son yarka ta tsira toh kasa a yanko min kanka akawo min nan fadata koda sarki hubru yazo nan a karatun wasika saiya yanke jiki ya fadi a kasa sumamme.
*********************
Mazan Jiya Part 13

#Cigaba

A lokacin da sarki hubru ya fadi a kasa sume a dimauce muka rugo kansa munayi masa fifita sannan yadawo haiyacinsa koda ya bude idanunsa yayi arba damu saiya fashe da matsanacin kuka yana mai cewa narasa yata! narasa yata!! har abada, yaku wadannan mazajen fama na umarce ku daku gaggauta fille kaina sannan ku dauki kan kuje dashi wajen bokana shabulus Ibn mukaibar domin yabaku aljanin dazai iya kaiku fadar sarki dumbazu kafin cikar kwanaki talatin, lallai ku damka kaina ga sarki dumbazu domin yabaku yata sahira ku tafo da ita nan birnin darul mahabur.
Sa'adda Sarki hubru yazo nan a zancensa sai tausayin sa yakama mu har idanuwan mu suka ciko da kwalla tsowon yan dakiku mukayi shiru bamuce komai ba kuma bamu birnin sarki hubru ba, koda ganin haka saiya daka mini tsawa yace shin bakuda kunne ne bakuji abunda nace ba, cikin tattausan harshe na dubi sarki hubru nace ya shugabana ai basai mun fille maka kai mun kaiwa sarki dumbazu ba inaso kabamu izini muje har can fadarsa mu yake shi mu kawar dashi, kuma mu dauko maka yarka mukawo maka ita nan fadar ka a cikin koshin lafiya.
Koda jin wannan batu sai sarki hubru ya kwarara ihu ya tsalle ya tumu da kasa SBD tsananin fusata da tashin hankali har saida muka rikeshi yadawo cikin hayyacinsa saida kimanin dakiku dari uku da sittin suka shude sannan yayi ajiyar zuciya ya dubemu yace yaku manyan gobe inda kunsan masifar datake can fadar sarki dumbazu dakuma karfin sihirinsa da bakuce zakuje ku yakeshi ba ina tabbatar muku dacewa a halin yanzu kuma a wannan zamani duk duniya babu wani sadauki mai tsananin karfi tamkar sarki dumbazu kuma babu matsafin daya kaishi karfin tsafi hatta bokaye da aljanu shakkar sa sukeyi abinda yasa kukaga ya gagara hallakani a tsawon shekaru goma shine duk duniya babu wanda yasan sirrinsa sama dani kuma inada wani kambun tsafi wadda indai yana jikina dumbazu bazai taba haduwa daniba balle yasamu daman hallakani duk duniya mutum biyu ne rak masu irin wannan kambu daga ni sai shi sarki dumbazu asalin sarki dumbazu almajirin mahaifina ne shiko mahaifina gawurtaccen matsafine Wanda ya shahara a can wata kasa da ake kira mulubiya wato a takaice de niba dan asalin wannan birni bane yawon duniya ne yakawo ni nan har nasamu shiga awajen sarkin garin ya amintar dani harya aura min yarsa bayan ya mutu ne na hau karagar sa albarkacin wannan kambun tsafin da ubana yabani.
Babban abinda ya haddasa gaba tsakanina da sarki dumbazu shine dumbazu yayi shekara ashirin yana yiwa ubana bauta har yasamu ya yarda dashi ya bashi sirrukan tsafi dayawa dumbazu yarike amanar amanar mahaifina hanu biyu har takai cewa mahaifina yadau keshi tamkar dan cikinsa don haka sai wata rana saiya kebe dashi cikin sirri yace dashi yakai dumbazu kayi sani cewa duk a cikin almajirai na babu wadda na yarda dashi dama dakai, kuma gashi yanzu tsufa ta riske ni bisa binciken danayi inada karancin kwanaki a duniya sbd haka zan baka wani sirri na karshe wadda kaine mutum na biyu dazai mallake shi bawani bane mutum na farkon face dana hubru wannan sirri dazan baka wani kambun tsafine wadda indai kana tare dashi babu wani mahaluki daya isa ya hallakaka komai jarumta karsa da karfin tsafinsa mutum ko aljan aduk sa'arda makiyinka ya tafi farautar ka bazai taba haduwa dakai ba saidai ku yita sabani babu wani tsautsayi dazai sameka muddin kana tareda wannan kambu, duk tsananin yaki ko matsifa zaka iya ratsawa ka wuce a yanzu haka tuni na daurawa dana hubru wannan kambu kuma kaima ga naka. Koda gama wannan jawabi sai mahaifina ya bude wata tsohuwar akwati ya dauko wannan kambu ya mikawa dumbazu hannun dumbazu na rawa ya karbi kambun ya daura shi a hannunsa na dama faruwar hakan keda wuya sai mahaifina ya dubeshi cikin tsananin damuwa yace kash! kayi babban kuskure sbd me kadaura wannan kambu a hannun ka na dama shin kamanta cewa komai na tsafi da hannun hagu ake yinsa inda kadaura wannan kambu a hannun ka na hagu da har abada baza a iya rabaka dashi ba amma yanxu bakin alkalami ya bushe a koda yaushe makiyanka na iya rabaka da wannan kambu.
Koda mahaifina yazo nan a zancen sa sai ran dumbazu ya baci zuciyar sa takama tafarfasa yace tur!! dakai yakai wannan tsohon banza hakika kacika tsinanne kuma la'ananne meyasa tun farko bakace min karna daura kambun nan a hannun dama ba, wato na fuskanci cewa kana sane kamun wannan mugunta saboda danka ya fifita akaina, yau shekara ashirin kenan ina maka wahala amma shi danka baisan wahalan kaba ko guda tabbas ka cuceni kuma kaci amanata sbd haka nima dole naci amanarka yanzu take zan kashe ka kuma komai daren dadewa saina kashe wannan dan naka na cire kambun nasa, nasa a hanuna na hagu. Kodajin wannan batu sai mahaifina ya yunkura da sauri domin ya bude wannan tsohuwar akwatin nasa amma kafin hannunsa yakai kan akwatin tuni dumbazu ya zare takobinsa ya fille mishi kai nan take mahaifina ya sulale kasa matacce. Batareda bata lokaci ba dumbazu ya dauki wannan tsohuwar akwatin sihirin mahaifina ya tafi ya bazama gari nema na amma duk inda yaje sai ace dashi yanzun nan nabar wajen wato mukayita sabani kenan lokacin dana koma gida na iske gawar mahaifina saina sulale kasa sumamme nan take daya daga cikin almajiran mahaifina mai suna Kusad ya zuba min ruwa na farfado kodana bude idanu na nayi arba da Kusad saina tambaye shi a fusace nace wanene yayiwa uban nan nawa kisan gilla? nan take Kusad ya gayamin cewa shide yaga sa'adda mahaifina ya kira dumbazu cikin turakarsa suka kadaita kuma daga karshe ya jiyo dumbazu na daga murya cikin fushi daga can kuma sai yaji sautin sarar takobi kodajin haka sai kusad ya la6e a bayan kofar turakar kawai sai yaga dumbazu ya fito daga cikin turakar da sauri rikeda akwatin sihirin mahaifina dakuma takobin sa jini na diga a jikin ta.
*********************
Mazan Jiya Part 14

#Cigaba

Koda gama jin wannan batu saina rushe da matsanacin kuka domin nasamu tabbacin cewa dumbazu ne ya kashe min mahaifina babban abun bakin cikina shine nasan cewa har abada bazan iya daukar fansa ba akan dumbazu domin akwai ranar da mahaifina yace dani yakai dana ko a bayan raina kada ka kuskura kace zakayi kokarin ganin bayan dumbazu domin bazaka taba samun nasara a kansa ba saboda yafika karfin sihiri, kai baka samu komai ba daga cikin ilmina amma zan baka wata kariya wadda babu wani mahaluki dazai iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login