Showing 3001 words to 6000 words out of 55369 words

Chapter 2 - MAZAN JIYA Littafi Na Farko Rubuta Labari Abdul'aziz Madakin Gini.txt

wajen yin wannan tafiya kuma koda akan aljanu za su tafi dole su shafe sama da shekara guda kafin su isa tsakiyar tekun bahar sufiya. Neman takobin saiful lujara a cikin kogin kuwa dai_dai yake da neman jaki mai qaho, wato dai mace ce da ciki zata iya haihuwa lafiya kuma zata iya rasa rayuwarta. A taqaice al'amari ne na sa'a da rabo, amma dai sai babbar sa'a sannan za'a dace. Idan har aka sami nasarar dauko takobin saiful lujara to lallai sauran makaman biyu ba za suyi wahalar samu ba sosai. Duk mutumin da ya hada wadannan makamai a jikinsa shi kadai tabbas ya cika GAGARABADAU kuma sai ya mulki duniyar na n gaba dayanta. Ba wai mutane kadai zai mulka ba hatta aljanu, dabbobi da dukkanin halittu sai ya iya sarrafa su har tsuntsaye kuma babu halittar da ba zai iya yin magana da ita ba, kuma ya bata umarni ta bi dole.
Ya ku ahalin darul mahabur ku sani cewa ba mu ga ta zama ba, dole ne mu mike tsaye mu zage damtse don ganin mun riga sarki dujalu samo wadannan makamai guda uku. Idan kuwa mukayi sakaki ya riga mu samunsu to muna ji muna gani zai zo ya baje qasarmu ya kashe mazajen mu sannan ya gaje matan mu da 'ya'yan mu da dukiyoyin mu.
Ya zama wajibi mu aika da wannan sako ga sauran kasashen da ke karkashin wannan nahiya tamu domin mu sanar da su halin da ake ciki kuma mu nemi gudunmawar su bisa wannan gagarumar tafiya".
Sa'adda sarki maharaz yazo nan a zancen sa sai dakin yayi tsit tamkar babu kowa a cikin sa.
Nan take dakin bautar ya watse jama'a suka tafi suna tattauna wannan lamari a cikin firgici da matukar damuwa. A wannan rana dai mutane ba su da hirar da tafi ba2n shirin sarki dujalu. Nan da nan labarin al'amarin ya fara bazuwa sauran garuruwa birane da qauyuka da kuma sauran qasashen maqofta. Duk jama'ar da ta ji wannan labari sa ta rude ta shiga shirye shiryen kare kai da bayar da dakarun gudunmawa izuwa birnin darul mahabur.
Tun a wannan rana ne sarki maharaz ya aiki wasu zakwakuran hadiman sa na jinsin aljanu suka kai wasika zuwa dukkanin sarakunan da ke muli a nahiyar. A cikin sa'o'i kadan labarin ya riski ko in da ina sarakai suka firgice ainun kuma suka miqe tsaye wajen fara shirye shiryen tafiya.
Wannan shine abin da ya faru a fadar sarki maharaz bayan ya sanar da jama'ar sa jawabin gunkin darbuza wanda aka saba yi a duk qarshen shekara a lokacin bauta.

☼☼☼ ☼☼☼ ☼

Al'amarin imnal da mahafin sa sarkin yaki hibru kuwa, tun da suka baro dakin bauta suka nufi hanyar gida sai duk suka yi shiru suna tunani a cikin zukatan su ba tare da sun ce kala ba.
Shi dai sarkin yaki hibru ba komai ya ke tunani ba face kiyasta rayukan da za'a yi asara yayin wannan tafiyar gami da irin dukiyar da za'a 6arnatar. Haka kuma yana jimamin tafiyar da za.ayi abar mata yara da tsofaffi kawai a birnin ba tare da an bar musu dakarun tsaro ba wanda hakan na iya janyo komai ya faru, duk da cewar sadauki hibru ya san cewa bashi da mata, kuma bashi da sauran dangi a fadin kasar gaba daya sai yaji takaici da baqin ciki suka mamaye zuciyar sa saboda ya san cewa wannan gagarumin yaki da za'a fita ba karamar masiba bace da koma bayan ci gaban nahiyar gaba daya domin zai janyo karyewar tattalin arziqi kuma masoya za su rasa masoyan su, iyaye za su rasa 'ya'yansu 'yan uwa zasu rasa 'yan uwansu.
Koda hibru yazo nan a zancen sa sai idanunsa suka ciko da qwalla saboda tausayin halin da jama.a za su shiga.
Shi kuwa sadauki imnal ko kadan tunaninsa ba irin na mahaifin sa bane. Abin da yafara fado masa a rai shine wai shin ya za.ayi ya mallaki wadannan kayan yaki guda 3 na MAZAN JIYA?
Koda ya gama aiyana hakan a zuciyarsa sai ya yiwa kansa dariya ya ce Amma fa bani da hankali akan wane dalili ne ma zan nemi abin da ya gagari manyan sarakunan duniya masu taqama da komai.
Gama aiyana hakan ke da wuya sai gimbiya mulaifa ta fado masa a rai ya ce to wai shin yanzu za'ayi tafiyar nan tare da gimbiya mulaifa kuwa? Lallai zan kasance mai tsananin baqin ciki idan ba a tafi da ita ba. Idan kuwa aka tafi da ita sai na fi kowa farin ciki a fadin duniya.
Haka dai imnal yayi ta saqe saqe a zuciyar sa har suka isa qofar gida. Dama imnal ne akan gaba har ya sanya qafar sa a cikin qofar gidan sai ya dakata ya waigo ya dubi hibru fuskar sa cikda alamun damuwa koda ganin haka sai hibru ya tsaya cak ya kura masa idanu sannan ya ce mene ne ya faru?
Imnal ya ce ka gafarceni ya abba na nayi babbar mantawa dazu a dakin bauta sarki ya ce min na fada maka muzo ni da kai yana neman mu a fada da yammacin gobe.
Ko da jin wannan batu sai hankalin hibru ya tashi yai shiru ya sunkui da kansa qas .daga can kuma sai ya dubi imnal ya ce ka gaya min gaskiya shin kayi wani laifi dazu a dakin bauta???
Jin wannan tambaya sai imnal ya sunkui da kanasa alamun rashin gaskiya ya ce qwarai kuwa nayi laifi. Domin na tashi daga inda nake zaune naje wajen gimbiya Mulaifa....
Koda jin haka sai hibru ya dafe kai yana mai ajiyar numfashi, sa'annan ya ce tabbas na san cewa ruwa baya tsami banza. Ni dai a sani na sarki bai ta6a neman shawarata ba sai dai kawai a gaya min cewa za'a fita domin naya shiri.
Tabbas ka aikata babban laifi don haka dole ne ka fuskanci mai tsanani saboda wannan laifi don haka ni babu ruwana, tsuntsun da yaja ruwa shi yake duka. Koda jin wannan magana sai imnal yayi murmushi ya ce indai akana soyaiya ta ga gimbiya Mulaifa ne a shirye na ke don na kar6i horo koda kuwa na mutuwa ne, cikin tsananin takaici hibri ya dube shi a fusace, kawai sai ya wuce zuwa turakar sa ya bar imnal tsaye a kofar gida.
Da yammaci kuwa fadar sarki maharaz ta cika makil da jama.a masu amsa gaiyatar tafiya yaki, duk da cewa adadin jama.ar da suka taru bai kai daya bisa goman masu tafiya yaqin ba sai da fadar ta cika ta batse sai da ya zamana duk inda ka duba kawunan bil'adama ne rututu.
Tun a farkon yammacin ne sarkin yaqi tare da dansa suka amsa kiran sarki suka hallara a fadar, shi kuwa sarki maharaz bai fito ba sai da kowa ya gama zuwa. Da fitowar sarki kowa ya miqe tsaye don girmamawa a gare shi har sai da ya zauna sannan kowa ya zauna.
Sarki ya dubi dubun mutane da suka amsa kiran sa sai ya cika da farin ciki, da ya duba 6angaren da su imnal suke tsaye sai ya murtuke fuska ya 6ata rai.
Bayan fadawa sun zube sun kwashi gaisuwa ya rage sauran sarkin yaki hibru da dansa Imnal, kawai sarki yayi nuni da hannun sa izuwa ga wani badakare yana maiyi masa nuni da yazo da imnal gabansa, nan take badakare ya tasa keyar sa yazo da imnal gaban sarki.
A wannan lokaci gimbiya Mulaifa na zaune daf da sarki. Koda taga an tasa keyar Imnal anzo dashi gaban sarki sai hankalinta ya tashi domin ta tabbatar da cewa lallai hukunci za'ayi masa. Gaba daya jama'ar dake fadar kuwa sai suka cika da mamaki suka zuba ido don su ga irin hukuncin da za'a yiwa Imnal yaron da ba.a ta6a ganin yayi wani laifa ba. A kullum shi da mahaifin sa ba su da wani abin da ya wuce biyaiya ga sarki, Sarki maharaz ya mike tsaye daga kan karagar mulkin sa ya dubi jama'a ya ce ya ku ahalin darul mahabur ku sani cewa wannan yaro Imnal d'a ga sarkin yakin mu hibru ya kasance mai ladabi da biyayya a garemu kamar yadda mahaifin sa ya kasance, kuma bamu ta6a kamashi da wani laifi ba, amma sai gashi a jiya ya aikata wani babban laifi
wanda bamu ta6a zaton zai aikata shi ba. Laifin kuwa shine a jiya sa'adda kowa ya sunkui da kansa kas a dakin bauta sai shi ya miqe yaje inda nake zaune ya zauna kusa damu. Wannan shine karo na farko da wani mahaluki ya karya dokar maigirma darbuza a cikin kasar nan, don haka dole ne ayi masa hukunci gwargwadon laifin sa.
Mai girma darbuza ya ce a daure imnal a sama jikin katako kuma a cikin rana tun daga hudowar ta har zuwa faduwar ta ba tare da an bashi ruwa koda makwarwa daya ba har tsawon kwana uku. Idan kuma ya sake aikata irin wannan laifi hukuncinsa zai zamo kisa ne.
Koda sarki maharaz ya zo nan a zancensa sai idanun Mulaifa suka ciko da qwalla suka fara zubar da hawaye. Hibru da imnal kuwa ko a jikin su maimakon ma hankalinsu ya tashi sai suka kama murmushi domin sun san cewa wannan horo ba komai bane akan irin horon da hibru ya bashi tun yana dan karami. Sarki Maharaz yaci gaba da bayani .. Sai gobe za'a fara wannan horo ga Imnal, kuma washe garin ranar da aka gama horon ne zamu dunguma gaba dayan mu mu tafi izuwa gagarumin yaki da ke gaban mu. Domin mu riga sarki dujalu dauko takobin saiful lujara. Ina mai kira ga dukkanin jama'ar mu da a ci gaba da shirye-shirye babu sassauci domin tuni dakarun gudunmawa sunzo da yawan su mu kawai suke jira a tafi...
Ko da gama wannan jawabi sai sarki Maharaz da Mulaifa suka shiga gida sannan jama'a kowa ya kama gabansa.
Lokacin da imnal da hibru suka isa gida sai hibru ya aika imnal kasuwa don ya sayo masa zugazugi na wutar Qira sabo da nasa ya lalace. Imnal ya hau doki ya tafi kasuwa tun kafin ya isa kasuwar sai yaga duk inda ya ratsa jama'a na kallonsa suna magana akan hukuncin da sarki zai yimasa.
Kafin ya isa kasuwar ne ya hadu da wadansu kuyangin gidan sarki suna tafe suna hira. Koda suka ganshi sai suka sha gabansa suka shiga yi masa kirari suna kodashi. Al'amarin da ya matukar bashi mamaki kenan ya dubesu ya ce ya ku wadannan kuyangi ku kuwa mai yasa kuke kodani haka alhali kuwa banyi wani abin al'ajabi ba? Suka ce ai kuwa kai ne kayi babban abin al'ajabi tunda har ka siye zuciyar gimbiya Mulaifa a halin bata ta6a nuna tana son wani da namiji ba face kai. A yanzu haka tana can gida tana kuka sabo da jin za'ayi maka horo na kwana uku bisa laifin da ka aikata.
Babu irin rokon da gimbiya ba tayi wa sarki ba akan ya janye wannan horo amma yaki, saboda bakin ciki ne shi yasa ta kasa ci ta kasa sha kuma ga dukkan alamu haka zata kwana a wannan hali yau.
Sa'adda kuyanga ta zo nan a zancenta sai hankalin Imnal ya dugunzuma ainun ya rasa abin da ke masa dadi a duniya, sai kawai ya dubi kuyangin ya ce da su idan kun koma gida ku shaidawa gimbiya cewa wanda take kuka dominsa yana bakin ciki bisa zubar hawayenta da kuma rashin ci da shanta.. Lallai shi ma ba zai ci kuma ba zai sha ba a yau har sai yazo ya ganta ta kowane hali...
Jin wannan batu sai kuyangin suka zazzaro idanu cikin tsananin mamaki wacce tayi magana dashi tace taya zaka iya shiga gidan sarauta har ka ganta ahalin akwai tsananin doka da tsaro?
Imnal yai murmushi ya ce ko mutuwa ke tsaro a yau sai na ga gimbiya Mulaifa kuje ku gaya mata cewa komai dare ina nan tafe a yau. Koda gama fadin haka sai imnal ya kada linzamin dokin sa ya wuce izuwa kasuwa ya siyo zugazugin ya koma gida sannan ya ci gaba da taya hibru kera wasu sababbin makaman yaki tamkar babu wani abu da ke sosa zuciyarsa.

Nima zan so ganin yadda Jarumi Imnal zai iya ratsawa ta cikin wannan tsaro na gidan sarautar birnin darul mahabur har yaje ya sadu da Gimbiya Mulaifa, masu karatu ko zan samu dan rakiya kuwa?

Da fatan kuna hutun karshen mako lafiya, sannan duk wanda yake son complete na Littattafan yaki harma da na soyayya zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 whatsapp kadai pls banda kira 🥺

MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part C
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey


Da tsakar dare lokacin da gari yayi tsit ba kajin komai face kukan gyare. Da daidaikun sautin tsuntsaye, imnal ya miqe tsaye dama ko runtse ido bai yi ba bare yayi barci. Cikin sanda ya debo wadansu bakaken kaya ya sanya sannan ya rufe fuskar sa da bakin rawani, takalmin da ya sa kuwa na fata ne kasansa gashi ne yadda duk abin da ya taka ba za.aji sautin komai ba.
Ko allura bai dauka ba a matsayin makami, ya bude kofar dakin sa ya fita ba tare da hibru ya ji motsin sa ba, maimakon ya bude kofar gidan sai kawai ya daka tsalle kamar dan biri ya dira akan katangar gidan, duk da cewa tsawon katangar ya kai kamu sittin. Kafin ya tafi ya tanadi kayam da ya cire daga jikinsa a cikin 'yar qaramar jaka kuma shifidar da ya kwanta sai yatara tsummokarara yai musu siffar mutum ya lullu6esu tamkar mutum ne a kwance.
Dama tuni ya daure dokinsa a kofar gida bai shiga da shi ciki ba saboda dama yasan cewa zai yi amfani da shi yayin da dare ya raba. Koda imnal ya dirgo daka kasa daga kan katangar sai yaje ya kwance dokin ya haye kansa ya zabureshi ya nufi hanyar da zata kai shi gidan sarki tuni ya aiyana a ransa ba zai wuce rabin sa.a ba zaije ya dawo.
Cikin matsanancin gudu imnal ya ci gaba da tunkarar gidan sarautar sai ya sauya hanya domin ya 6ullo ta bayan katangar gidan, cikin kakanin lokaci ya hango katangar gidan da sauri ya sauko daga kan dokinsa ya daureshi a cikin bishiyoyi masu duhuwa sannan ya 6uya a cikin duhuwar, ya kurawa katangar idanu yana kallon dakaru kuma yana nazarin hanyar da zai bi ya shiga gidan ba tare da wani ya ganshi ba.
Al'amarin da ya qara tayar da hankalinsa kenan domin bai ga ta yadda hakan zata iya faruwa ba.
Sai imnal ya dan jima yana nazari sannan dabara ta fado masa.
Nan take ya hau kan bishiya ya karyo itatuwa sannan ya sauko ya daddaure itatuwan da 6awon bishiya yayi siffar mutum mutumi ya dora shi kan dokin sa ya kora shi, dokin ya fita da gudu ya wuce ta gaban wadannan dakaru dake tsaitsaye a bayan katangar.
Ko da suka ga mutum a sukwane ya wuce ta gaban su sai suka bi shi gaba daya da gudu domin su kure masa gudu, damar da imnal ya samu kenan ya fito da gudu daga cikin duhuwar da ya 6uya.. Ko da ya rage saura taku uku ya riski katangar sai ya daga tsalle yai sama tamkar tsuntsu ya kama karshen katangar, yana kama katangar sai ya ji ta da tsananin santsi har hannun sa ya su6uce zai fado sai ya sake jefa daya hannun nasa ya kamo katangar ya dafa kafafun sa sama ya dirga akan katangar, koda ya leqa qasan katangar izuwa cikin gidan sai ya ga akwai tsawo sosai in yace zai fada zai iya karyewa.
A dai dai wannan lokacin ne ya jiyo dawowar dakarun da suka bi dokin sa sun dawo da gudun tsiya. Nan fa zuciyar imnal ta buga da karfi domin ya san cewa babu mamaki sun bi dokin ba su ga kowa a kan sa ba sai itatuwa, sai baban su ya ce lallai ma ko waye mai dokin nan ya raina mana wayo, sai ya daka ma sauran dakarun tsawa ya ce kowa ya koma malafar sa ya ci gaba da aiki don akwai alamar zuwan baki gidan nan.
Imnal ya ringa bin katangar har ya hango wani tafki a jikin katangar daga cikin gidan sai yayi sauri zuwa wajen keda wuya sai yaga bakin tafkin 12dakaru ne suke kaiwa da komowa, amma sai yayi ta maza ya daka wawan tsalle sai ya fada cikin tafkin nan ji kake Zundum..
Al'amarin da ya juyo da hankalin kwamandan dakarun nan sai ya umarce su da su shiga cikin tafkin su lalubo abin da ya fada su fito da shi.
Nan take suka bi umarninsa suka shiga tafkin nan.. Koda imnal ya ji dakarun nan sun shigo cikin ruwan, cikin zafin nama ya samu guda daga cikin dakarun nan ya suburbudeshi ya bishi da mazga, nan take ya suma sai ya cire kayan jikin sa ya sanya masa shi kuma ya sanya nasa, sakamakon dakarun duk kayan su iri daya ne. Can sai gaba daya suka yo sama su shaida ma sugaban ba su ga kowa ba, sai ya ce kowa ya koma ma6uyar sa imnal ne na karshe ya fito daga cikin tafkin ya ruga izuwa cikin wani sashen gidan sarautar. A lokacin da imnal ya fito daga ruwan ne ya ruga akayi akasi shugaban dakarun ya waigo kawai sai ya hango imnal ya ganshi dan karami kamar wada. Al'amarin da ya ba shi mamaki kenan domin ya san cewa duk cikin
yaran sa babu gajere ko wada. To ya ya akayi aka samu wannan? .
A gigice shugaban dakarun ya ruga izuwa bakin tafkin kawai sai yaga nasa badakaren a saman ruwa a sume.Shugaban dakarun yayi sauri ya kwala wa yaransa kira suka firfito daga malafar su a guje suka taru a gaban tafkin. Ya dubesu yace lallai muna da baqo a cikin gidan nan ku bazama neman sa.
Nan take dakarun suka bazu izuwa kowanne sashe na gidan sunan dube dube.
Lokacin da imnal ya ruga cikin gidan sarautar yana la6e la6e sai ya rasa hanyar da ya kamata ya bi saboda bai san 6angaren turakar gimbiya mulaifa ba. Kawai sai ya bi kan wata matattakalar bene da gudu. Da zuwa ya ga dakaru za su gan shi sai ya nemi wuri ya 6uya. A haka ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login