Showing 9001 words to 12000 words out of 55369 words
Chapter 4 - MAZAN JIYA Littafi Na Farko Rubuta Labari Abdul'aziz Madakin Gini.txt
haddasa haka ban face tunda sarki maharaz suke tare da hibru bai taba ganin ya harare shiba sai ayau bayan shigar sarki maharaz cikin gidan sarauta fada ta watse babu kowa face and wadansu dakaru 300 wadda suke tsaron imnal.
Shiko hibru saiya tafi can nesa kadan da filin fadan yayi sumfuda ya zauna inda yana iya hango imnal, nan fah hibru ya shiga sakar zuci wata zuciyar tace dashi ya afkawa wayennan dakarun dake tsaron imnal ya kashe su sannan ya kunce imnal ya tafi dashi in yaso subar kasar gabadayan su, wata zuciyar kuma sai tace dashi ai bai kamata yayi hakan ba tunda shima yayi imani da darbuza zaifi kyau ya bari sai antafi yaki sannan sukama gabansu haka dai hibru ya cigabada zancen zuci ya kulla wannan ya kunce wancan har yamma tayi likis bai gusa daga inda yake zaune ba kuma bai nemi abinci koh abin sha ba har dare ya raba hibru nanan zaune a inda yake bai gusa ba cikin halin damuwa da bakin ciki kuma koh alamar bacci a idanunsa babu a lokacin ne hibru yaji tsani sarki maharaz da darbuza domin baiga amfanin biyayyar dayake mishi ba. Adaidai wannan lokacin ne iska mai sanyi ta soma kadawa wadda ta zoma sanadin farfadowar imnal daga doguwar suman da yayi, imnal ya bude idanunsa da kyar yana gani dishi-dishi sai kawai yaji wata irin izababbiyar ishirwa nan fah ya fara kiran ruwa! ruwa!! tun yana fadi a hankali harya bude makokoron sa yana fadi da karfi koda hibru ya jiyo sautin muryar imnal yana kiran ruwa saiya mike zumbur a firgice ya lalubi sulkar sa ya yunkura da sauri da nufin ya ruga zuwa inda imnal yake kawai sai yaga matarsa wato marigayiya mahaifiyar imnal ta bayyana a gabansa cikin tsananin tsoro hibru ya fadi kasa ya kama ja da baya yana mai nunata da dan yatsa yana karkarwa. Koda ganin haka sai marigayiyar ta dube shi cikin murmushi tace kwantar da hankalin ka yakai sadaukin zamani kayi sani cewa niba matarka bace na kasance cikin jinsin aljanu sunana luzaira yar salbas, nazone gareka acikin suffar matarka domin nasamu damar hanaka abinda kake son yi domin idan ka kaiwa imnal agaji wannan lokaci tamkar ka ruguza cigaban rayuwar sane, cikin rashin yadda hibru ya dubi luzaira yace ta yaya zan yarda dake kuma akan wani dalili zaki min wannan taimako shin bakya ganin halin da dana yake ciki ne sakamon kishirwar dake addabarsa.
Koda aljani luzaira taji wannan batu sai tayi murmushi tace duk irin wahalar da imnal zaisha bazai mutu ba bincike ya tabbatar da cewa danka zai girma ya shahara a duniya nan gaba lallai ya zamo wajibi ka yarda Dani idan har kana son ka cika burinka na rayuwa inko kaki acikin bautar sarki maharaz zaka mutu, ina sanar dakai cewa a duniya darbuza bashida wani makiya wadda yawuce ubana sarki salbas mai mulkin birnin Shulai a kullum suna farautar juna Kuma wannen so yake ya kama dayan su a raye domin samun sinadarin da zasu cika burinsu, nazone sbd mu taimaki juna zan taimake ku kusamu yancin kanku daga sarki maharaz da aljani darbuza, ni kuma da taimakon kadai zan iya taimakawa mahaifina domin mu kama darbuza a raye sa'adda aljana luzaira taxo nan a zancen ta sai hibru ya sake rudewa kuma ya cika da mamaki yace yanzu kina nufin darbuzan da muke bautawa aljani ne kamarki?
Luzaira tace ko shakka babu tace ai dayawan ku bil'adama mu kuke bautawa sbd kuna ganin munayin abunda ku bazaku iyaba hibru yayi ajiyar zuciya yace to yanxu tayaya zan iya taimakonki ke kuma tayaya zaki iya taimakona?
Aljana luzaira tayi murmushi tace har abada bazaka taba kubuta daga cikin bautawa sarki maharaz ba sai an karya wani asiri daya maka shidai wannan asiri anyi shine silin gashin kirjinka guda daya kuma an bunne shine a cikin wata tsohuwa rijiya gaba-dubu (1000) dake can karkashin wani kogi dake birnin sin, itadai wannan rijiya duk duniya babu mahalukin dazai iya shigarta sai ni da abbana mu kadai, tabbas zanje na tono wannan asiri amma sai idan kayi alkwarin cewa zaka hada karfi da karfe dakai da danka imnal ku dauko takobin saiful lujara da mashin galilul haras da kuma hular lamsara kun bani su a hanuna, ina tabbatar maka dacewa bincikena ya nuna min cewa sarki dujalu da sarki maharaz bazasu iya dauko wayennan makaman ba amma kaida imnal zaku iya, lokacin da aljana luzaira tazo nan a zancen ta sai hankalin hibru ya dugunzuma daga can saiya dago kai ya dubi luzaira yace wato de yanxu bangare ukune suke son mallakar wayan nan kayan yaki na #mazan jiya bangare na farko shine sarki dujalu sai sarki maharaz sai na uku kuma keda abban ki, abinda na fahimta shine idan muka samu nasarar dauko wadannan makamai nida dana muka damka miki zaki rikesu ne amfanin kanki ke kadai koko zaki kaiwa abban ki? Kuma tambaya ta biyu agareki itane shin kina nufin mai girma darbuza bai san da zuwanki ba, kuma baisan duk abun dake faruwa tsakanin mu? yayin da aljana luzaira taji wadannan tambayoyi saita bushe da dariya sannan ta murtuke fuska tace yakai sadaukin zamani kayi sani cewa duk wani boka da amsa sunan sa bashida wani burin da yuce ya mallaki wadannan makamai na Mazan JIYA, karshe kuma batun aljani darbuza shin yana gani koh yana jin mu bai tasoba sbd idan yanada ikon ganina da banxo ba domin bazai taba bari nayi hulda dakuba.
Sa'adda aljana luzaira taxo nan a zancen ta sai sadauki hibru yayi shiru yana tinani kansa a sunkuwe sannan ya dubi can inda ke daure a sama yaga ya sake suma na biyu, sai takaici da bakin ciki yasake mamaye zuciyar sa cikin karfin hali ya dubi aljana luzaira yace ki tafi sai bayan mun fito daga wannan yaki ki dawo izuwa gareni kiji amsar dazan baki idan zakizo kijo min acikin tsakar dare, koda fadin haka sai ya mike tsaye ya kwashe shimfidar sa ya nufi hanyar dazata kaishi gidan shi ko sau daya bai sake waiwayowaba balle yaga halin da imnal ke ciki. Bayan tafiyan hibru sai aljana luzaira ta tashi sama taje daidan fuskar imnal ta hura mishi iska a bakin ta wadda tasa gashin kansa ya tarwatse yana kadawa acikin iska tamkar ana guguwa mai karfi take imnal ya farfado yana mai ajiyar numfashi aiko yana bude idanun shi sai yayi arba da luzaira ta kura masa idanu tana murmushi babban abun mamaki shine duk ciwon dayakeji ajikinsa ya gushe haka yunwa da ishirwa ma duk sun gushe batare da fargabar komai ba imnal ya dubi aljana luzaira yace wacece ke? kuma menene ya kawoki wajena? ina mai rokonki da kadakiyi kokarin fitar dani daga cikin wannan halin danake ciki.
Koda jin haka sai aljana luzaira ta bushe da dariya ta tankwashe kafafunta tamkar tana zaune a kasa bisa buzu ta fiskanci imnal sosai sannan tace yakai jarumin gobe kayi sani cewa lbrn yana tsawo amma idan kanaso kasan ni wacece ka tambayi abbanka bayan ka kubuta ka tambayeshi lallai ni mai amfani ne ga cigabar rayuwar Ku ina mai yimaka sallama yakai jarumin gobe sai gani na biyu in mun sake saduwa, gama fadin hakan keda wuya sai aljana luzaira ta bace bat kaman bata wanzuwaba awajen.
Bayan Kwanaki uku fadar sarki maharaz ta cika ta batse bakomai ne ya haddasa haka ba face ayau ne za'a dugunzuma bakidaya dakarun birnin dana sauran kasashe makwabta wadanda aka gayyato saboda yin gagarumar tafiya izuwa kogin bahar sufiya don dauko takobin Saiful lujara saboda yawan jama'ah da kyar sadauki hibru ya kutsa ta cikin jama'ah ya isa inda aka daure imnal da zuwa sai ya iske imnal lafiya kalau acikin hayyacin sa, kuma babu yunwa ko ishi atare dashi cikin hanzari hibru ya hau kan wannan dogon mumbari ya kunce igiyar data daure hannayen imnal sannan ya sabo shi a kafada ya sauko kasa, gabadaya dandazon jama'ar dake wajen suka zubawa hibru idanu duk inda yabi sai kaga ana darewa ana bashi hanya ana masa jinjina da kirari domin ansan yaune rana irin tasa wato ranan dazai jogaranci rundunar mayaka izuwa yaki, dayawa daga cikin mutanen garin sunyi bakin cikin hukuncin da aka yankewa imnal dan hibru kuma sun san cewa imnal gwarzon mayaki ne wanda ake takama dashi yanzu gashi raunata shi a lokacinkirari daza tafi yaki a lokacin da akewa hibru da dansa kirari ne sarki maharaz da yar sa suka fito daga gidan sarauta, nan fah kallo ya koma kansu kowa ya zuba musu ido cikin matukar mamaki bakomai ne ya haddasa mamakin ba sai ganin irin shigar da sarki maharaz yayi dakuma irin wacce mulaifa tayi dukansu sun sanya jajayen sulke sun rataye takuba a bayansu komai na jikin su jane hatta dawakansu kowa yasan sarki da mulaifa basu kasance mayaka ba amma ansan cewa sarki maharaz kasurgumin matsafi ne, lokacin da hibru ya isa inda dokin sa yake saiya zaunar da imnal a kasa ya jingina bayansa a jikin gini ya bude wata jaka ya fiddo da garin magani ya mika masa sannan yace karbi wannan ka shanye ya kai dana domin raunukan sudaina maka zogi, imnal ya dubi hibru cikin murmushi yace ya abbana ai babu inda yake min ciwo a jikina kuma ko kadan bana jin kishirwa da yunwa koda jin haka sai hibru ya dubi imnal cikin mamaki yace menene ya kawo maka agaji a tsakanin dare uku zuwa wayewar gari?
Imnal yace wata aljana ce mai suffa wadda kasha kwatantamin data mahaifiyata kuma tazomin a cikin suffar mutane ba aljanu ba tace a wajen ka zan samu labarin ta wacece wannar aljana ya abbana? Hibru yayi ajiyar zuciya yace kabar wannan magana tukunna har sai bayan kasamu lafiya gama fadin hakan keda wuya sai hibru yaji an busa algeta alamar sarki ya tsaya a gaban jama'ah zaiyi bayani da hanzari hibru ya mike tsaye imnal ya riko hannun hibru yace shin gimbiya mulaifa ma tafito kodajin wannan sai hibru ya dubi imnal a fusace yace na rabaka da gimbiya mulaifa amma ka ki to kasani cewa idan ka kara min maganar ta ko kuma kanuna min kana kaunar ta zamu raba hanya yayin imnal yaji wannan batu sai idanunsa suka ciko da kwalla ya dubi hibru yace ka gafarceni yakai abbana naimaka alkawari daga yau bazan sake maka magar gimbiya ba kuma bazan sake nuna kauna agareta ba.
Cikin farin ciki hibru ya sumbaci goshin imnal yace ubangijin daya halicci darbuza ya albarkace ka gama fadin haka keda wuya ya nufi inda karagar sarki take har saida yaje dab da sarki ya tsaya sarki ya dubi gabas da yamma, kudu da arewa a lokacin da filin fadar yayi tsit tamkar babu mai rai a wurin sannan yayi gyaran murya yace yaku jama'ar birnin darul mahabur tare da jama'ar sauran kasashe makwabta a wannan nahiya tamu ina mai yiwa kowa barka dazuwa fadata kuma ina gdy dakuka amsa gaiyatata domin nuna kishin kasar Ku dakuma dukiyar ku data jama'ar ku Kamar yadda kuka sani cewa gagarumar masifa da bala'i na tunkarar mu idan bamu fita wannan yaki ba ina mai kira agaremu damu jajirce iya karfin mu dan ganin munje mun riski babban abokin gabar mu a can tekun bahar sufiya domin hanashi dauko takobin saiful lujara a can ne zamu yake shi don tserar da rayuwar mu da jama'ar mu kafin yasami nasarar mallakan kayan yakin mazan jiya kamar yadda kuke gani a yanzu nida yata munyi gagarumar shigar yaki alhali bamu kasance mayaka ba ko sadaukai kuyi sani cewa ayau munfito ne da dukkan karfin sihirin mu don tunkarar masafi dujalu a halin yanzu na baiwa yata mulaifa dukkan sihirina na tsafi guda dari tara da casa'in da Tara(999) na cikon dubun ne ban bata ba SBD wani dalili mai karfi na bata wadannan sirruka ne sbd ta taimaka min awannan yakin domin abokan gabanmu yawansu ya wuce misali ina mai sanar daku cewa yanzu haka sarki dujalu tareda miliyoyin dakarunsa sunyi nisa a tafiyar su ta zuwa tekun bahar sufiya kuma suna amfani da alkaluman tsafi wajen gajarce nisan tafiya muma zamuyi amfani da namu sihirin don gajarce nisan tafiyan yanzu nabaiwa dukkan ninku sa'a daya daku gama kimtsawa domin sa'a dayar na cika hadiman zasu iso daga karshe ina mai kira ga sarki yaki na hibru bn imlas dayazo yanzu ya sameni a cikin dakin gani domin muyi tattaunawa na musamma akan yadda yaka mata mu bullo wa wannan yaki koda sarki maharaz maharaz yazo nan a zancen sa sai filin fadar nan ya rude da sowa. Nan de sarki maharaz ya kama hannun gimbiya mulaifa suka wuce izuwa cikin dakin gani shiko sadauki hibru saida ya koma wajen imnal ya sanar dashi cewa zaije wajen sarki su gana..
Kuyi haƙuri kwana biyu kun jini shiru ko, wallaahi laifin Hadejawa ne dan kawai munje bakunta garinsu sai bari dai nayi shiru da bakina🤔🤔🤔
Shin kana bukatar wani littafi na yaki kawai tuntubeni ta wannan Number ko kuma kayi mani magana da profile dina 08138873799.
MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part E
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Lokaci da hibru ya shiga dakin gani sai ya cika da tsananin mamaki domin sarki Maharaz kawai ya gani da gimbiya Mulaifa babu sauran yan majalisa, kuma maimakon yaga sarki akan kujerar daya saba zama akai sai yaganshi a kasa bama akan kujara ba, ita Mulaifa a dab dashi, koda hibru ya hada idanu da sarki sai yaga idanunsa acike suke da kwalla, al'amarin da yayi matukar girgiza hibru kenan, ya karasa gurin su sarki Maharaz jikinsa a sanyaye shima saiya zauna a kasa suka fuskanci juna, maganar farko da ta fito daga bakin sarki Maharaz itace yaya jikin Dana imnal?
Kodajin wannan tambaya sai ran hibru ya baci bai san sa'adda ya dubi sarki a fusace ba yace ya shugabana kayi magana akan abun dayake gaban mu amma ba batun imnal ba, Yace domin ina ganin bashida wani amfani a wannan yakin da zamu je, mu barshi anan gida saboda yayi jinyar jikinsa.
Koda gama fadan haka sai Hibru yaga hawaye ya zubo daga cikin idanun sarki Maharaz cikin razani Hibru yace ka gafarceni yakai shugabana idan har wannan furuci nawa ya kona maka rai.
Koda jin haka sai sarki Maharaz ya tsam daga inda gimbiya Mulaifa ke zaune sannan ya dawo dab da Hibru ya dafa kafadunsa suka kurawa juna ido sannan yace yakai babban aminina kuma abokina, ayau ina mai neman gafara agareka duk abin dakaga nayi maka ko nayi ma danka ba'a kan kiyayya bane sai domin soyayya da kuma bin umarnin mai girma darbuza dana marigayi sarki hubaru, a halin yanzu baka kaunata acikin zuciyar ka, yakai abokina kayi tinani zuwa shekarun baya da suka gabata tun sa'adda muna yara kanana kawo izuwa girman mu da yadda akayi nazamo sarkin birnin nan da kuma yadda akayi kazamo sarkin yakina, lallai ayau ne zan fada maka wani sirri daban taba gaya maka shiba, amma sai bayan ka bawa Mulaifa labarin rayuwar mu ta baya da yadda akayi na auri mahaifiyarta, da kuma yadda na shiga tashin hankali bisa rashin samun haihuwa.
Lokacin da sarki Maharaz yazo nan a zancensa sai idanun Hibru suka cika sharkaf da hawaye ya dubi Mulaifa cikin tsananin tausayi yace yake 'yarmu ki saurara da kyau kiji wannan labari mai dauke da dimbin abun tausayi da ban alajabi, kuma kisan irin dangartakar dake tsakani na da mahaifinki.
Koda jin haka sai Mulaifa ta tattara hankalinta waje daya ta kurawa Hibru idanu.
Shi kuma saiya shiga bata labari kamar haka "A wasu shekarun baya da suka gabata zamanin da sarki Ruzba ke mulki a wannan birni Darul Mahabur, nida mahaifinki mun kasance fadawan sarki ruzba wadanda aikin mu kawai tsaron lafiyar sarki, duk inda sarki zaije muna tare dashi kuma ko kuda bama bari ya sauka a jikinsa, mahaifin sarki ya kasance kasurgumin matsafi dan haka ya gaji tsafi kuma ya shahara, bisa wannan dama daya samune sarki ya zabe shi acikin dakaru masu tsaron lafiyar sa, niko mahaifina shine sarkin yaki birnin Darul Mahabur, a wannan lokaci tsufa ya riske shi har yakai baya iya fita yaƙi, awannan lokaci ban wuce shekaru sha biyar ba don haka ni nake wakiltar mahaifina a yakuna, sau uku muna tseratar da rayuwar sarki ruzba a lokacin da wani babban abokin gabarsa yake kawo masa hari don ya halaka shi, hari na farko a wani yammaci ne da sarki ruzba ya fita rangadi izuwa bayan gari inda muka shiga wani daji da ake kira Furuz, a rayuwar sarki ruzba babu abunda yake sha'awa kamar yin suu acikin kogi kuma dakan shi yakan shiga kogi yayi kamun kifi.
Acikin dajin Furuz akwai wani babban kogi da ake kira bahar zur, shidai wannan kogi yana da girman gaske da muggan halittun ruwa a cikin sa, lokacin da mukazo zamu gifta ta gaban kogin tare da tawagar mu, sai sarki ruzba yace a tsaya a bakin kogin.
Kodajin haka sai hankalin dakarun mu ya dugunzuma domin sun san halin sarki zai iya cewa sai an shiga cikin kogin yayi suuu. Nida maharaz ne kawai hankulanmu basu tashiba domin mun yarda da kanmu, kawai sai sarki ya dubeni ya dubi maharaz yace inaso na shiga cikin kogin nan nayi suuu. Don haka sai Ku biyoni ciki domin nasan cewa Ku kadai ne zaku iya biyoni.
Nan take sarki ya sauko daga kan dokin sa ya dauki fatsarsa ya fada cikin kogi, cikin sauri nida maharaz muka bishi. A duk dakika biyar sai Maharaz ya dubi hannunsa domin ajiki yake ganin abinda ke karkashin kogin, da zarar yaga wani mugun abu ya tafo inda sarki yake saiya sanar dani sai nayi nitso a kasa na tarar da abun komai hazarinsa na kashe shi, acikin abinda bai kai rabin sa'a ba na kashe manyan kadodi biyar saida sarki ruzba ya shafe sa'a guda amma ko kifi daya bai kama ba, har ya hakuri da nufin ya daina ya fita da cikin kogin sai yaji fatsar sa tayi nauyi matuka ta yadda bazai iya dago