Showing 21001 words to 24000 words out of 55369 words

Chapter 8 - MAZAN JIYA Littafi Na Farko Rubuta Labari Abdul'aziz Madakin Gini.txt

har na mayar masa da martani.
Sai da muka shafe sa'a tara muna wannan bakin Artabu Dumbazu ya kasa samun nasara a kain ni ma na kasa maida mashi da martani koda sau daya ne kuwa, hakika duk wanda ya fika jarumta to fa ya fika har abada, domin baka isa ka kamoshi ba.
Koda sa'a tara ta cika muna wannan gumurzu sai gajiya ta riskeni har ya zamana cewa da kyar nake iya daga takobina na kare saran da Dumbazu yake kawo mani, shikuwa ko kadan bai gajiba domin kmar ma a sannan ne ya fara gumurzun. Yayi da yaga na fara sarewa sai ya cika da murna ya ci gaba da kawo mani hari a sannu yana murmushin mugunta, sai da ya kaini jikin bango ya tareni sannan ya buge takobina ta fadi kasa sannan ya labta mani wawan sara a cinya, ban san sa'ar da na kwarara uban ihu ba tare da durkushewa a kasa ba cinyata na zubar da jini.
Dumbazu ya sake dankara mani wani saran a dayar cinyar tawa na zube kasa wanwar a matukar galabaice nan fa idanuna suka fara gani dishi-dishi. Dumbazu ya sake dag takobinsa da nufin ya fille mani kai, amman kawai sai naga hannun nashi ya sandare ya kasa labta mani saran, da kyar da sidin goshi na juya baya kawai sai naga wuka ta nutse a tsakiyar gdon bayansa jini na burbulowa ta tsakiyar girjinsa, tsaye a gaban Dumbazu gimbiya Sahira ce jikinta na karkarwa, a sannna ne na gane cewa ita ce tayi ta maza ta rugo ta caka wa Dumbazu uka a gadon bayansa. Nan take Dumbazu ya sullae kasa matacce ko shurawa bai yi ba, a sannan ne nima idanuna suka rufe na sume a wajen.
Lokacin dana farfaɗo sai nayi arba da gimbiya Sahira tsugunne a gabana ta rusar kuka, raunikan dake jikin cinyoyina an saka masu magani, a gefe daya kusa da ni kuma Maharaz ne a kwance har wannan lokaci yana numfashi da yar duk da cewa an sa masa magank a jikin raunikan nasa.
Koda na daga kina na dubi gabas da yamma, kudu da arewa sai naga ashe gaba daya mutanen birnin Karlus ne suka rufemu sun tsura mana idanu suna kallonmu kawai, a gefe daya kuma fadawan Sarki Dumbazu ne a tsaitsaye sunyi tsuru-tsuru kamar ace kyet su fice da gudu. Ashe duk mamakinmu suke yi yadda akayi har muka iya ffaatawa da sarkinsu, har ma kuma muka samu nasarar hallaka shi.
Saida muka yi kwana arba'in muna jiyyar raunikan mu a birnin Karlus ni da Maharaz sannan muka warware, amman duk da haka bamu warke sumul ba, sai a sannan hankulanmu suka dawo jikinmu har na samu damar baiwa gimbiya Sahira llabarin dukkan abinda ya faru tsaninmu da mahaifinta gami da wasiyar da ya bamu mu shaida mata.
Koda gimbiya Sahira ta gama jin bayanina sai ta fashe da matsanancin kuka kuma ta rungumeni tana mai ci gana da kuka. Da kyar na lallasheta daga can sai ta dubeni ta ce da ni tana so tayi wata magana ta sirri da Maharaz.
Cikin matukar mamaki na dubeta nace da ita "Ke kuwa wace irin magana ce wannan da zaki yi da abokina wacce bakya so na ji?
Koda taji wannan tambaya ai hawaye ya zubo mata ta ce ka yi hakuri ya kai mijina na gobe, wannan magana da zanyi da maharaz sakone daga mahaifina zuwa gareshi, kuma ya gargadeni da cewa komai rintsi da tsanani kada na kuskura na sanar d kai.
Koda gama fadin haka sai gimbiya Sahira ta tafi wajen maharaz tayi masa rada a kunnensa, gabadaya jama'ar dake wajen babu wanda yaji abinda ta ce masa, faruwar hakan keda wuya sai kawai muka ga Aljani Mara'il Labarus ya sakko daga sama tare da tsirga a gabanmu, al'amarin da yayi matukar bamu mamaki kenan domin mu a zatonmu ya dade da mutuwa, hakan yasa ko neman inda gawarsa take ba muyi ba.
Yayin da Aljani mara'il labarus yaga muna mamaki da ganinsa a raye sai ya bmau labarin cewar ai dama dogon suma yayi, lokacin daya farfado sai yaga babu kowa a wannan fada ta farko da muka fara shiga, dan haka sai ya tashi da yar ya tafi can bayan birnin Karlus ya boye knsa a cikin daji yayita jinya har saida ya warke.
Koda jin wannan labari sai muka cika da farin ciki, a daidai wannan lokaci ne wazirin sarki Dumbazu ya zo gaba ya tsaya tare da cewa ya kai wannan sadauki mai abun mamaki, tunda har ka samu nasarar kashe sarkinmu, yanzu abinda ya kamata kayi shine ka maye mana girbinsa. Da jin wannan batu sai nayi murmushi n ce ai ni bnai da bukatar mulki ko dukiya, abinda nazo nema na samu, kuma ba komai bane face masoyiyata kawai, sai nayi nuni izuwa ga gimbiya Sahira, ita kuwa sai ta rugo gareni cikin farin ciki gami da murna ta rungume ni. Daga nan sai na dubi wazirin Dumbazu nace da shi mukam yanzu mun kammala aikin da aka turomu yi a birninku, saboda haka muna yi maku sallama sai ku zabi shugabanku a tsakaninku.
Gama fadin hakan keda wuya sai Aljani mara'il labarus ya rankwafa bayansa muka hau mu uku muka zauna, sannan ya bude fuka fukansa guda 18 yayi sama da mu, kafin kiftawar idanu mun bace bat a cikin gajimare. Tun daga wannan rana sai naga abokina Maharaz ya daina sakin jiki da ni, ya daina yin hira da ni, hatta abinci baya yarda muci tare, al'amarin daya dugunzuma hankalina kenan na rasa binda ke mani dadi a duniya, a duk sa'ar dana tambayeshi shin ko nayi masa wani laifi ne? Sai yayi murmushi ya ce sam banyi masa laifin komai ba.
Tsawon kwanaki 17 da muka shafe muna tafiya a sararin samaniya daga birnin Karlus zuwa birninmu na darul mahabur bamu yi hirar rabin sa'a ba nida Maharaz. Muna isa birnin darul mahabur muka iske sarki Hubaru da boka karlus sun mutu an binne su, muna kuka muka isa inda kabarinsu yake, sai da muka shafe sa'a uku cur muna a gaban karin muna kuka sannan da kyar aka kawar damu daga bakin kabarin aka tafi da mu izuwa fada.
Kashegari da safe aka dora Maharaz akan karagar sarki Hubaru kuma aka daura aurensa da Husuna yar sarki Hubaru, bayan an gama bikin nadin Sarki Maharaz ne aka daura aurena da gimbiya Sahira sannan ya bani sarautar sarkin yakinsa, na cigaba da yin bauta gami da biyayya ga sarki Maharaz tsawon shekaru, kuma duk bukatar da ya zo mani da ita ina binta ga dukkan iyakar karfina ban taba nuna masa cewa na gajiya ba, na sha bakar wahala akan biyan bukatunsa musamman a lokacin da suka rasa haihuwa shida matarsa Husuna, domin sai da na kusa rasa rayuwata a kakarina na nemo masu maganin haihuwa. Duk wannan iyayya da bauta da nake yiwa sarki Maharaz bai taba yi mnai godiya ko sau daya ba, kuma gabadaya abotarmu da kusancinmu sai ya yanke su, ko magana bana samun damar yi da shi face in mun zauna dakin gani tare da sauran fadawa idan bukatar hakan ta taso. Har yau har gobe ban san dalilin da yasa sarki Maharaz ya nisanta da ni ba. Yake gimbiya Mulaifa wannan shine tarihin rayuwata data mahaifinki da kuma dangantakar dake tsakanina da shi. Masu iya magana suna cewa ranar wanka ba'a boyon cibi, yanzu dai gani ga shi kuma yace zai fada mani wani sirri wanda bai taba fada mani ba a yanzu, wanda shine sanadin da yasa ya nisanta abotarmu.
Lokacin da Hibru ya zo nan a labarinsa sai hawaye ya zubowa sarki Maharaz ya matso daf da shi yadda suna iya jin numfashin juna sannan ya ce ya kai abokina hakika abinda kake zargi tabbas haka yake, idan baka manta ba a ranar da gimbiya Sahira ta kashe sarki Dumbazu acan birnin Karlus ta fada mnai wani sako a cikin kunne na cikin rada ko ba haka ba? To wannan sako ba wani abu bane face wasiyya daga mahaifinta wacce ya sanar da ita tun kafin sarki Dumbazu ya zo ya saceta, abinda ya fada mata shine, lallai ta sanar da ni cewar dole ne na nisnta da kai tun daga ranar da n zama Sarki birninmu na darul mahabur, idan kuwa naki to tabbas mulkina zai rushe, kaima kuma burinka bazai cika ba, domin ba zaka zama Sarkin yaki ba, kuma duk mu biyun ba zamu samu haihuwa ba har abada, bisa wannan alilai ne yasa na yanke abotarmu kuma na nisanta kaina daga gareka, amman a kullum sai na shiga turakata na kulle kaina nayi ta kukan bakin ciki ba tare da kowa ya sani ba. Ya kai abokina ka gafarceni inaso ka fahimta cewa dole ce tasa na aikata hakan a gareka bawai a son raina bane kuma dama ance kada na sanar da kai gaskiyar al'amarin sai a lokacin da naga gagarumin yaki ya taso wanda bamu da tabbacin samun nasara akan shi. Sa'adda Sarki Maharaz ya zo daidai nan a jawabinsa sai Hibru ya rungumeshi, take duk su biyun suka rushe da matsanancin kuka suna masu daɗa kwakumar juna.
Mulaifa dake tsaye tana kallonsu sai ta kamu da tsananin tausayinsu, itama sai ta fashe da kukan aka rasa wanda zai rarrashi wani a tsakaninsu. Bayan sun jima a cikin wannan hali sai Sarki Maharaz ya janye jikinsa daga na Hibru suka sake kallon juna a karo na biyu sannan ya ce ya kai abokina kayi sani cewa abotarmu ta zama samu kamar yau muka fara ta, kuma ina neman alfarma guda daya a wajenka.
Cikin murmushi Hibru ya ce fadi duk abinda kake so zanyi maka shi, sarki Maharaz ya ce ina so kabar yata Mulaifa tayi jinyar Sadauki Imnal a cikin wannan tafiya da zamu yi, lallai tare da ita za a yi wannan tafiya. N sani cewa Imnal yana matukar kaunar Mulaifa idan har tana tare d shi sai ya fi saurin warkewa, samun kafiyarsa da wuri shine samun kwanciyar hankalinmu, domin bincike ya tabbatar da cewa rawar da Imnal zai taka a wannan yaki ko ni da kai ba zamuyi rabinta ba.
Da jin haka sai Hibru ya yi murmushi tare da cewa na amince da haka. Nan take farin ciki ya lullube Mulaifa da sarki Maharaz, har suka rungume juna tare.
Sadauki Imnal na kwance a cikin dandazon mayakan da zasu fita yaki izuwa tekun Bahar Suffiyya, sai kawai akaga kuyangi da dakarun sarki Maharaz sun rako gimbiya Mulaifa suna masu ratsowa ta sansanin dakarun yakin, nan fa aka zuba ido aga wajen wa kuma gimbiya ta zo, kunyangin dake yi wa gimbiya Mulaifa su 12 ne, 6 na dauke da faratin abinci da abinsha iri-iri, ragowar 6 kuwa suna dauke da magunguna, shimfidu da kuma tanti. Kai tsaye gimbiya Mulaifa ta durfafi inda Sadauki Imnal yyake kwance, al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan a wajen, da isowar Mulaifa gaban Imnal sai ta durkusa daf da shi, ta dubeshi tare da sakar masa wani tattausan murmushi ta ce da shi nice baiwar daka bukaci mahaifinka ya samo domin yin jinyarka.
Koda jin haka sai Imnal ya yunkura da nufin ya mike tsaye, amman sai Mulaifa tayi sauri ta danne kafadarsa ta maida shi kwance, Imnal ya ce wane ni na kalleki a matsayin baiwa, ai nine bawanki, haba ya shugabata ki kula fa domin kina gaban talakawanki kike kada kije kiyi abin kunya.
Koda jin haka sai Mulaifa ta bushe da dariya tare da cewa ya kai masoyina, kayi sni cewa shi so makahone kuma kurma ne, wanda duk yayi zurfi a cikin kogin so to baya ji kuma baya gani, nayi nisa a cikin kogin kaunarka dan haka babu abinda zai sa naji kunyar wani mahaluki yayi kyautata maka. Ina son k saki jikinka ka daina dari-dari da shakkar komai, domin mahaifina ne ya turoni gareka da kansa kuma ya umarceni da nayi jinyar ka a yayin wannan gagarumar tafiya da zamu yi har izuwa lokacin da zaka samu lafiya ka warke sumul. Ina mai dada yi maka albishir da cewa a halin yanzu abotar mahaifinka da abbana ta dawo sabuwa kamar da. Nan take Mulaifa ta baiwa Imnal labarin duk abinda ya faru a dakin gani tsakaninta da sarki Maharaz da kuma sarkin yaki Hibru.
Koda ta gama bashi labarin sai nan take yaji wani irin farin ciki ya lullube shi irin wanda bai taba jin kamarsa ba, kwatsam! Sai suka ji an fara busa algaita gami da kida tambura alamar cewa sarki ya fito daga cikin gida domin a fara wannan gagarumar tafiyar.
Nan take kowa ya nutsu aka mimmike tsaye, masu dibar kya na diba, masu hawa dawakai suna hawa, wasu kuma ana tattara dukiya da guzuri ana laftawa rakuma, dawakai da kuma keken doki.
Koda sarki Maharaz ya fito daga gidan sarauta sai aka ganshi tare da abokinsa sarkin yaki Hibru bisa kan fararen dawakai biyu, duk sunyi gagarumar shigar yaki kala daya suna tafe suna fira cikin nishadi abin gwanin ban sha'awa.
Gabadaya jama'ar dake filin fadar sai suka cika da matuƙar mamaki, domin rabon da aga Maharaz da Hibru a haka tun kafin su samu sarauta, maimakon sarki Maharaz da Hibru su tsaya gaban jama'a suyi bayanin karshe na wannan tafiya, sai suka wuce kai tsaye wata hanya da zata kaisu zuwa dakin gunki darzuba. Da isarsu kofar dakin bautar sai suka sakko daga bisa dawaknsu, bayin dake biye da su sukayi sauri suka kama dawakan suka rike. Maharaz da Hibru suka shige cikin dakin bautar rike da hannun juna, a haka har saida suka isa inda gunki darzuba yake, isarsu keda wuya sai suka durkusa bisa gwiywoyinsu sannan suka suddar da kawunansu kas, kuma suka rufe idanunsu.
Bayan sun dan jima a haka kawai sai suka yunkura da nufin su fece daga cikin dakin bautar, ba zato sai suk ji muryar darzuba yana mai cewa "Ku dakata mana tukunna yaku abokan asali, kuma masoyan gaskiya, sannan aminan zahiri. Cikin hanzari suka koma suka durkusa kamar yadd suka yi a farko.
Darbuza ya ce hakika a yau ina mai matukar farin ciki da dawowar abotarku, domin kuwa kunyi hakuri da dukkanin kunci gami da takaicin da muka jarabceku da shi, domin inganta rayuwarku da nuna amincewarmu bisa karbar bautarmu da kuke yi ba dare ba rana. Nayi maku alkawari zan tsare rayukanku daga dukkanin irin masifun da zaku shiga a cikin wannan gagarumar tafiyar, kuma lallaı duk irin wahalar da zaku sha karshe kune zaku yi nasara, abinda bni da tabbacin yi maku alkawarinsa shine kare lafiyarku, dalili kuwa shine wanda kuke bautawa da wanda su sarki duzalu ke bautawa ya kasance mai karfi kamata kuma shine babban makiyina a duniya, tabbatas muna yi gaba mai tsanani kwatankwacin irin wadda sarki huburu da sarki darzuba suka yi kafin mutuwarsu. Ina mai sanar da ku cewa nima ina nan ina gagarumin shirin yaki domin tunkarar abokan gaba acan tekun bahar Suffiyya, wanda kokarinsa shine ya kare sarki dujalu kuma ya bashi ikon da nasarar dauko takobin saiful lujara, kmar yadda nima zan kareku kuma na baku nasara, wannan yaki da za a yi a bakin kogin bahar Suffiyya ba a taba yin kamarsa ba a tarihin duniya ba, domin sai anyi asarar dubun nan rayukan miliyoyin aljanu da biladama da kuma dukiya mara adadi. Dole ne cikin biyu ayi daya, kodai su halakamu ko kuma mu mu halakasu, amman ina da yakinin cewa mune da nasara domin nayi bincike har sau dubu dari amman banga komai ba sai nasara a garemu, da wannan kalami ne nake sallamarku sai mun hadu a bakin kogin bahar Suffiyya, lallai zamu gajarce maku tafiyar daga kwanaki masu yawa zuwa kwanaki kadan.
Sa'adda darzuba yazo nan a jawabinsa sai Sarki Maharaz ya bude baki yayi godiya, shiko Hibru sai yayi shiru bai ce komai ba, tun sa'ar da darzuba yayi nisa a cikin jawabinsa sai zuciyar Hibru tta cika da wasiwasi ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa ya ce wai shin wannan wane irin abune muke bautawa, wane ne haka muke bautawa wanda basji da cikekken yakini, ai bai kamata ace abinda ake bautawa yana shakkar wani abu ba, kai ni a ganina ma kamar akwai wani guda daya wanda yafi dukkaninsu karfi da iko, inya so sai ya yake su ya kawar da su dukkaninsu ya zamana cewa shi kadai ake bautawa. Nikam dama can zuciyata ta dade tana rawa akan wannan abin bautar na mu, domin sau tari yana barinmu muna shan bakar wahala, da kyar muke tsira da rayuwarmu, to yanzu kuma gashi shi da bakinshi yake cewa yana da kishiya gami da abokin gaba amman muje zuwa sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba'a je ba.
Nan dai Maharaz da Hibru suka mike tsaye suka fice daga cikin dakin bautar, kai tsaye suk koma bakin kofar fada suka sake tsayawa, bayan sun sauka daga kan dawakai sai sarki Maharaz ya wuce zuwa kan mimbari yayin da Hibru ke take masa baya, bayan sun hau kan mimbarin ne sun tsaya sun masu fuskantar jama'a sai Sarki Maharaz ya bayanin godiya ga jama'a uma yayi gaisuwa ga baki wadanda suka zo daga sauran makwabtan kasashe domin kawo agajin yaki bisa kare mutuncin nahiyar gabadaya. Daga nan sai yayi bayani ga jama'a inda ya kara masu kwarin gwiywa da karfafesu bisa mahimmancin wannan yaki da za'a fita. Yana gama wannan jawabi ne jama'a suka barke da shewa aka hau yi masa kirari.
Nan take sarki Maharaz da sarkin yaki Hibru suka yi wa gabadaya jama'ar jagora, wato suka wuce gaba aka bisu duw a baya. Inda ace mutum na nan tsaye a wajen yaga wannan rundunar ke fitowa daga cikin birnin darul mahabur sahu sahu bisa rakuma, dawakai da alfadarai sai yayi tsammanin cewa gaba daya mutanen duniya ne suka fitowa saboda yawansu.
Wannan shine abinda ya faru a birnin darul mahabur bayan kasashen dake nahiyar gaba daya sun hada kai sun fita gagarumin yaki dan kare buranensu daga sharrin sarki dujalu.

**********************

Al'amarin Sarki Dujalu kuwa lokacin daya durfafi hanyar kofin bahar Suffiyya tare da dandazon dakarunsa na yaki mutum miliyan dubu daya da suke tafiya bisa wasu zaratan dakarun aljanu suma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login