Showing 45001 words to 48000 words out of 55369 words
Chapter 16 - MAZAN JIYA Littafi Na Farko Rubuta Labari Abdul'aziz Madakin Gini.txt
tsit tamkar mutuwa ta gifta, sarki ya dubi sauran jama'a ya ce sakamakon wannan gasa shine anyi ragas tsakanin Sadauki Rabbasu mai wakiltar zuri'ar mafarauta da Sadauki Hantaru mai wakiltar zuri'ar makera, saboda haka za a sake yin wannan gasa a shekara mai zuwa.
Da jin haka sai jama'a suka barke da shewa gami da murna.
Al'amarin Sadauki Rabbasu da zuri'arsa kuwa sai suka cika da tsananin bakin cika, Rabbasu bai san lokacin da hawaye ya zubo masa ba saboda tsananin takaici ya durkushe kasa ya kafa kansa a kasa.
Shi kuwa Hantaru dama yasan cewa babu wanda zai samu nasara a wannan gasa tsakanin shi da Rabbasu, domin boka Sulbaini ya fada masa cewa sai sunyi wannan gasa sau uku babu mai nasara, wanda a karshe dole ne a tura su neman takobin Saiful Lujara dan kawo karshen gasar gabadaya a birnin na Darul Habur.
Nan take Hantaru ya yanke jiki ya fadi kasa saboda tsananin galabaita, cikin gaggawa aka zo aka dauek shi aka sanya shi cikin kekn doki aka tafi da shi, saboda kumburin jiki da duruwar jini sai da aka kwana uku ana jinyar Hantaru sai a sannan jinin daya taru a fuskarsa da kuma jikinsa ya bace.
Salimat ce tayita gasa masa jiki da ruwan dumi, kuma tana dafa masa magani yana sha, kafin jikin Hantaru ya dawo daidai a kullum idan ta dubw shi sai ta fashe da kuka saboda ganin irin tsananin wahalar da ya sha, hakan ne ma yasa ta tubure akan ba zata yarda a sake yin wannan gasa da Hantaru ba, sai dai su tattara yanasu-ya nasu su koma can birnin Kisra gidan mijinta. Da kyar d sidin goshi su Shuraim suka lallabata ta yard zata sake zama a garin har shekara ta zagayo.
Wannan shine abinda ya faru a can birnin Darul Habur bayan anyi gasar tseren gudun barewa ta neman aure da aka saba yi duk shekara.
MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part R
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
*******
Acan birnin Kisra kuwa tun daga ranar da Shamilat da Hantaru suka bar gari sai sarki kusaidu ya shiga cikin wani mugun hali da bakin ciki, sannan yana yawan kuka bisa yawan begen yarima Hantaru da yake yi, abu kamar wasa sai sarki kusaidu ya kwanta ciwo kuma aka rasa abinda ke damunsa, domin sam bai fada wa kowa abinda ke damunsa ba.
Lokacin da ya fahimci cewa idn ya kara jimawa a wannan hali to tabbas rayuwarsa zata salwanta, sai ya kira wadansu amintattun bayinsa su uku ya basu wasika yace suyi shiri su tafi can birnin darul Habur su kai wa matarshi wannan wasika.
Nan da nan kuwa suk yi shiri suka kama hanya a sirrance ba tare da kowa ya sani ba, dalilin da yasa sarki Kusaidu bai yi shawara da boka Ardusa ba wannan karon shine yaga wani abu da yayi matukar daure masa kai, har yaji cewar ba zai kara yarda da shi ba har sai ya tabbatar da abinda yake zargi.
Masu iya magana sunce shi laifi kuikuyo ne har abada yana bin mai shi, duk abinda mutum ke yi a boye komai daren dadewa sai asirinsa ya tonu, musamman abinda ya shafi cin amana da danne hakkin wani.
Wata rana da tsakar dare sarki kusaidu na kwance a dakin uwar gidansa suna bacci, sai kawai wani dan mitsitsin tsuntsu ya shigo turakar ya tsaya a saman taga daidai saitin Zarifa yayi wani irin kuka tamkar yana raira waka. Koda jin wannan tsutsun sai Zarifa ta farka daga baccin da take yi kamar dama can idonta biyu ba baccin take yi ba, da mikewarta zaune sai ta dubi sarki Kusaidu ta tabbatar dda cewa bacci yake tunda gashi har yana sharar munshari, a hankali cikin sanda ta sakko daga saman gadon ta cire rigar baccin dake jikinta sannan ta saka tufafinta masu kyau ta nufi bakin kofa.
Ashe sarki Kusaidu ba bacci yake ba, domin tun daga ranar da su Hantaru suka tafi birnin Darul Habur bai sake samun damar yin bacci daddare ba, sai dai kawai ya kwanta yayi lamo kamar mai yin baccin amman ba baccin yake iya wa ba, zuciyarsa cike da tunanin gami da begen dansa yarima Hantaru da kuma matarsa Salimat. Duk motsin da Zarifa ta ke yi yana jinta, kuma wani lokaci har bude idonsa yake yi kadan ya kalleta, da zarar yaga ta juyo sai yayi maza ya rufe idon nasa.
Lokacin da Zarifa ta isa bakin kofar turakar, sai ta tsaya cak, ta juyo ta kura wa fuskar sarki Kusaidu idanu ta sake tabbatar da cewa bacci yake yi, sai da ta bata dakika sama da dari shida a kofr sannan daga bisani ta bude kofar a hankali ta fice daga cikin turakar gabadaya.
A lokacin ne shima wannan mitsitsin tsuntsun da ya shigo wannan turakar ya fice da sauri, koda jin ficewar tsuntsun sai sarki kusaidu ya leka waje ta cikin taga, duk da cewa dare ne gari yayi duhu amman duk da haka sarki kusaidu ya samu damar hango wannan mitsitsin tsuntsun ta cikin ragowar hasken farin wata, lokacin da mitsitsin tsuntsun ya rikide ya zama wani aljani, bisa ga mamakinsa kuma sai yaga matarsa Zarifa ta haye bayan aljanin ya bude fuka fukansa ya tashi da ita sama, kafin kifta ido sun kule a sararin samaniya sun bace bat!
Koda ganin wannan al'amari sai sarki kusaidu ya cika da tsananin mamaki, kuma hankalinsa ya dugunzuma ainun ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa ya ce ina matata Zarifa ta tafi a cikin wannan dare, sannan wane ne ya turo wannan aljanin daya dauketa? Sarki Kusaidu ya kasa baiwa kansa amsar wadannan tambayoyi dan haka sai yayi shiru ya shiga sabon tunani, daga can sai yayi ajiyar zuciya ce hakika duk yadda aka yo matata Zarifa tana cin amanata ne, alhalin ni ina zaune da ita da zuciya daya, kuma ina kaunarta bilhakki, amman babu komai, koma mene ne take aikatawa a boye da sannu zan sani.
Haka dai sarki Kusaidu ya koma ya kwanta ya ci gaba da tunanin su Hantaru da Salimat, bayan kamar rabin sa'a da kwnaciyarsa sai yaji an bude kofar an shigo, bai bude idanunsa ba, kuma bai yi wani motsi ba sai kawai ya ci gaba da kwarara munshari. A lokacin ne yaji an hawo gadon an kwanta, kamshin turaren data saba sakawa a jikinta ne ya sa ya gane matarsa ce Zarifa ta dawo.
Nan take sarki Kusaidu yaji wani azabben bakin ciki ya shigeshi tamkar ya hadiyi zuciya ya mutu, amman sai ya danne zuciyar tasa ya hakura.
Kashegari da safe sarki kusaidu bai nuna wa Zarifa wata damuwa ba, sai ma ya tashi da farin ciki yana mai cewa zarifa shi fa yau ya tashi da sha'awar fita rangadi.
Koda jin haka sai Zarifa ta yi caraf ta ce aiko nima ina sha'awar fita rangadi sai mu fita tare kenan?
Sarki Kusaidu ya dubeta cikin damuwa ya ce a'a gwara dai kiyi zamanki a gida domin wannan rangadin da zan fita ni kadai zan fita ba tare da dakaru ba, kuma zan iya yin nisan zango, kinga Kenan bani da tabbacin zan iya kare lafiyarki idan kika biyo ni.
Cikin matukar mamaki Zarifa ta ce kai kuwa saboda me zaka fita rangadi kao kadai, shin ka mnta ne cewa kai sarki ne? Baka tsoron magauta su kawo maka hari?
Sarki Kusaidu yayi dariya ya ce ai ni bana tsoron harin magauta domin na tabbatar da cewa ina tare da tsarin boka Ardusa, ke nake ji saboda baki da tsari irin nawa.
Koda jin wannan batu sai Zarifa ta yi shiru bata kara tankawa ba.
Ba tare da bata wani lokaci ba, sarki Kusaidu ayi shiri shi kadai, cikin batar da kammani ya fice daga cikin birnin Kisra. Sarki Kusaidu ya durfafi wata hanya da zata sadashi da wani kauye da ake kira da Raufal, daga cikin birnin Kisra zuwa kauyen Raufal tafiya ce ta rabin sa'a kacal, amman sai sarki ya zaburi dokinsa da sauri domin yana son ya isa kauyen cikin kakanin lokaci. Da isarsa kauyen kai tsaye ya wuce zuwa wajen wani bakon boka wanda bai wuce kwana uku da sauka a kauyen ana kiransa da suna Hulubul Auzar.
Yau kwana biyu kenan rak da sarki Kusaidu ya samu labarin saukar boka Hulubul auzar, kuma ya samu labarin bokan ne a wajen wani amintaccen yaronsa da yake masa fatauci mai suna Ramzal.
Ramzal ya tabbatar wa da sarki kusaidu cewa yaga bokan da ya fi boka Ardusa karfin sihiri, domin a gabansa boka Hulubul auzar ya warkr da wani mara lafiyya wanda ya shekara ashirin a kwance sakamakon wani asiri da aka yi masa, wanda yasa ya makance kuma ya kuturce, babu irin kokarin da boka Ardusa bai yi ba akan yaga cewa ya warkar da wannan mara lafiya amman ya kasa, sai ga shi a dare daya boka Hulubul auzar ya zo ya warkar da shi
Lokacin da sarki Kusaidu ya iso kofar gidan da aka sauki boka Hulubul auzar sai ya iske bakan a tsaye ya zubo masa idanu fuskarsa cike da annuri.
Tun kafin sarki Kusaidu ya karasa gareshi sai boka Hulubul auzar ya rugo da gudu izuwa ga sarki Kusaidu yana mai yi masa lale marhabun, kuma ya kama mashi dokin ya sauko, nan take suka shiga cikin gida suka kadaita a cikin wani daki.
Har sarki Kusaidu ya bude baki zai ce wani abu sai boka Kusaidu ya tari numfashinsa ybace ya kai wannan sarki kada ka bata yawun bakinka wajen yi mani bayanin abinda ke tafe da kai, nasan kazo wajena ne domin nayi maka bincike bisa zargin da kake yi akan matarka Zarifa ko ba haka bane?
Cikin tsananin mamaki sarki Kusaidu yace zancen ka dutse ya kai wannan boka mai daraja.
Hulubul auzar ya dubi Sarki Kusaidu yace ya kai wannan arki mai daraja kayi sani cewa sau tari wadanda muka dauka a matsayin masoyanmu, kuma abokan shawararmu sune manyan abokan gabarmu masu son ganin bayanmu, mafi akasarin mutanen da muaka yi wa rana su kuma sai suyi mana dare, in mai bakin cikin sanar da kai cewa fiye da shekaru ashirin baya, boka Ardusa da matarka Zarifa suna cin amanarka ta hanyar lalata da junansu, kuma dan da matarka Salimat ta haifa Hantaru ba danka bane dan boka Ardusa ne da Zarifa.
Ko da jin wannan batu sai sarki kusaidu ya dubi bokan cikin tsananin mamaki da rsahin gasgata zancen shi yace to amman ta yaya aka yi wannan abu ya faru haka?
Maimakon boka Hulubul auzar ya bashi amsa sai kawai yayi nuni da hannunsa izuwa jikin bango, nan take hoton dukkan abunda ya faru tsakanin boka Ardusa da Zarifa ya bayyana akai, tun daga ranar da suka fara cin amanar shi kawo izuwa ranar da zarifa ta haifi Hantaru ta ajiye wa Salimat, yayin da Salimat ke nakudar sihiri wanda boka Ardusa ya sanya mata ba tare da ta sani ba.
Koda ganin wannan al'amari sai sarki kusaidu ya fashe da kukan bakin ciki, yaji duniyar gaba daya ta yi masa zafi, kawai sai ya zabura ya zare wuka daga jikinsa ya daga sama zai burma a cikinsa, cikin hanzari boka Hulubul auzar ya rike hannunsa ya fisge wukar ya ce haba ya shugabana, ai idan ka kashe kanka makiyanka sun samu nasara akanka cikin ruwan sanyi, inason ka dauki dangana ka koma gida ka kuma cigaba da rayuwarka kamar yadda ka saba yi a kullum, sannan kada ka nuna wa zarifa sauyin komai, kada ka raba shimfida da ita, daga nan har izuwa ranar da amaryarka da kuma danka Hantaru zasu dawo gida, a sannan ne ido zai raina fata ayi maka ramuwar gayya, wacce tafi ta gayya ciwo.
Kada kace zaia dauki wani mataki a yanzu akan Zarifa da Ardusa, domin ba zaka iya ganin bayansu ba, kuma idan ka matsa zasu kawar da kai ne su gaje mulkinka da dukiyarka a banza. Ko ni dinnan ban isa na kareka daga sharrin su ba. Ina mai tabbatar maka da cewa boka Ardusa ba karamin hatsabibi bane ni kaina ba zan iya da shi ba duk da cewa na fishi karfin sihiri.
Alkawarin da zan maka shine zan cigaba da kare lafiyarka da kuma rufe sirrinka bazai taba sanin cewa ka san sirrin abinda yayi maka ba a yanzu har sai lokacin da Hantaru zai dawo gida. Tabbas Hantaru ne zai yi masu hukunci daidai da abinda suka aikata, domin har abada bazai taba karbar ba a matsayin iyaye, kuma ya tsanesu tamkar yadda ya tsani mutuwarsa.
Daga wannan rana sarki Kusaidu ya cigaba da rayuwa mara dadi, ciwo kuma ya kara tsananta a jikinsa, kullum sai dai a kwantar a kuma tayar baya iya yiwa kansa komai, a duk sa'ad da boka ardusa yazo duba shi inya dubi fuskarsa sai yga kamar kura yake gani, ita kuwa Zarifa a duk sa'ad da tazo kusa da shi sai yaga kamar bakar macijiya ce take fasa kai zata sareshi, baban qbnida ya kara susuta sarki shine aminttatun bayinsa da ya tura zuwa birnin Darul Habur dan kai wasika ga matarsa Salimat tunda suka tafi basu dawowa ba har tsawon wata shida babu su babu duriyarsu.
Al'amarin da ya kara jefa matsanancin ciwo kenan ga sarki Kusaidu, ya zamana cewar kullum fadawansa ma jira suke kawai ace rai yayi halinsa su san wanda zasu dora akan karagarsa.
Babu abin takaici face kullum boka ardusa a turakar Sarki yake yini, shine mai nuna wa sarki kauna fiye da kowa, hatta masu baiwa sarki magani bai yarda da su ba, sai ya tabbatar da ingancin maganin sannan yake yarda a baiwa sarki maganin ya sha.
Wannan hali da sarki Kusaidu ya shiga sai ya zamo tamkar samun dama a wajen Ardusa da Zarifa suka shagala da more rayuwarsu wajen cin amanarsa.
A duk sa'ad da Zarifa ta bukaci boka Ardusa yayi bincike akan halin da Yarima Hantaru ke ciki sai ya kwantar mata da hankali yace ai yarima Hantaru yana nan lafiya lau, kuma zai dawo birnin Kisra a lokacin da sarki kusaidu zai mutu ya haye karagar mulkinsa.
Lallai a wannan lokaci ne zamu sanar da yarima cewar mune iyayensa na gaskiya, kuma babu yadda zai yi dole ne ya karbemu a matsayin iyayen nasa, kuma ya girmamamu. Wannan kalamai na boka Ardusa ba karamin faranta wa Zarifa rai yake yi ba, sai kawai ta rungume boka Ardusa su ci gaba da sharholiyarsu.
A zahirin gaskiya boka Ardusa yayi iyakar kokarinsa wajen gano halin da Hantaru yake ciki a cikin hallarar tsafi da mahaifiyarsa acan birnin darul habur amman abu ya gagara, duk sa'ad da ya matsa akan bincike sai madubin tsafinsa yayi bindiga ya tarwatse. Al'amarin daya dugunzuma hankalinsa kenan ya gane cewa lallai akwai wani babban bokan dake boye sirrin yarima acan birnin Darul Habur, abinda bai sani ba shine ba wani boka bnae face malaminsa a harkar bokanci wanda tuni ya dade d yin gaba har ma ya baiwa yan bayansa sirrinsa wato boka Sulbaini.
Abinda boka Ardusa ya gano a cikin bincikensa kawai shine nan da shekaru uku masu zuwa yarina Hantaru zai dawo gida, wannan shine abinda yasa hankalinsa ya kwanta, ya amince da cewar zai cigaba da jiran dawowar yarima Hantaru.
Kash! Hakika rashin sani yafi dare duhu, domin inda boka Ardusa yasan abinda zai biyo baya idan yarima hantaru ya dawo gida da ya kashe kansa saboda munin abin takaicin da zai samesu shi da farkarsa Zarifa.
Acan kuwa birnin Darul Habur bayan kimanin wata daya da yin gasar neman auren gimbiya Larziyya, sai bangarorin biyu suka shiga shirye shirye gasar da za a yi nan da watanni goma sha daya masu zuwa, ya zamana cewa sun dage ainun dan ganin cewa idan lokaci yayi su samu nasara. Dare da rana kuma kullum Hantaru da Rabbasu cikin basu horo ake na kara wa jikinsu juriya da zafin nama gami da tsananin gudu, sai da takai cewa kowannensu na iya yin azabben gudu wanda a cikin rabin sa'a zai shafe tafiyar yini guda.
Haka suka cigaba da baiwa jikinsu horo har tsawon wata goma sha daya, a tsawon wannan watanni tsakanin Hantaru da Rabbasu Babu wanda ya kara ganin fuskar gimbiya Larziyya saboda sarki ya sa an tsareta a gidan sarauta, babu wani mahalukin da ya isa yaje inda take, kuma itama bata isa taje ko ina ba.
Da kyar da sidin goshi kuma a sirrance Gimbiya Larziyya ta samu damar aika wa da Sadauki Hantaru wasikar soayayya a cikin kwana talatin, duk sa'ad da wasikar ta riski Hantaru baya ganin komai a cikin takardar face kalaman kuka da bakin ciki bisa dalilin rashin saduwarsu, gami da baitocin waka na kara kaimi da kuma shawara kan lallai ya kara kaimi wajen ganin cewa ya samu nasara lashe wannan gasa da za'a yi ta neman aurenta a karo na biyu.
Baya ga haka kuma a koyaushe tana yi masa tuni bisa alkawarin daya daukar mata guda uku, alkawari na farko;
Shine komai rintsi ba zai janye ba, alƙawari na biyu kuwa shine duk alfarmar data nema a wajensa zai yi mata, alkawari na karshe wanda shine cikon na uku kuwa shine a duk halin da suka cintsi kansu a ciki ba zasu guji juna ba.
Ko sau daya Hantaru bai taba saba wa aika wa da Gimbiya Larziyya amsar wasikarta ba, kuma a koyaushe yana kara tabbatar mata da cewa alkawarinsu yana nan babu abind zai tashe shi har abada.
Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a je ba, hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce rana bata karya sai dai uwar diya ta ji kunya, a kwana a tashi sai ranar gasa karo na biyu ta dawo.
Ai kuwa a wannan rana sai da hankalin gabadaya mutanen birnin Darul Habur ya dugunzuma saboda tsananin yawan al'ummar da suka cika wannan gari, tamkar mutane duniya ne suka hallara.
A wannan rana anyi muguwar bakar gasa ta tashin hankali, wacce ta zamo sanadiyyar ajalin gaba daya dakarun gasar face na mutum biyu rak wato Hantaru da Rabbasu, suma din sai da kowannensu ya suma sau uku, kuma a karshe suka sake yin ragas kamar yadda al'amarin ya faru a gasar farko, wato a lokaci guda suka kama barewar gasa kuma suka tsinkata gida biyu. A wannan rana Sadauki Rabbasu kwana yayi yana kukan bakin ciki,