Showing 12001 words to 15000 words out of 55369 words
Chapter 5 - MAZAN JIYA Littafi Na Farko Rubuta Labari Abdul'aziz Madakin Gini.txt
taba, cikin mamaki ya dubi Maharaz yace yakai boka dan boka wai shin wani irin kifine na kamo mai girma da nauyi da har na kasa dago shi sama?
Maharaz ya dubi tafin hanunsa yaga babu komai acikin fatsar cikin kaduwa da zaro idanu maharaz ya dubi sarki yace nikam banga komai acikin fatsar nan ba, tabbas muna cikin tashin hankali, duk yadda akayi wani abune mai mugun sihiri ya shiga fatsar ka, kafin ni koh sarki ruzba muce wani abu sai mukaga an fisgi sarki ruzba anyi kasa dashi izuwa karkashin kogin, ba shiri muma mukayi nitso izuwa karshin kogin, kawai sai mukayi arba dawani wani katon mutum ya shake sarki ruzba da hannu biyu har sarki ya fara kakarin mutuwa, cikin zafin nama na kafa hannayen wannan maridi na fara kokarin banbaresu daga wuyan sarki, nan kwanjin maridin ya kumbura idanun sarki ruzba sun kumbura ga kuma rashin numfashi shima Maharaz yana kokarin kashe maridin da karfin tsafi, amma duk abinda ya watsa mishi basa tasiri, kawai sai maridin ya juya baya ya gabzawa Maharaz naushi a fuska take Maharaz ya sulela sumamme ya tafi izuwa karkashin ruwa.
Al'amarin daya dugunzuma hankalina kenan na tattara karfina gabadaya na gabzawa maridin naushi a kunnensa na hagu, sbd karfin naushin saida jini yayi tsartuwa ta kunnensa na hagu, ba shiri ya saki wuyan sarki ya kwarara ihu cikin zafin nama na kamo sarki ruzba sannan nayi kasa na kamo Maharaz sannan nayiyo sama, kafin maridin ya dawo hayyacinsa tuni na fito dasu bakin kogin muka zube wanwar a gabar kogin duk mu ukun muna cikin mugun hali, ni ina numfashi sama sama Sarki da Maharaz kuwa duk a sume suke, cikin gaggawa aka shiga yi musu fifita.
Koda na mike tsaye sai naga wannan basamuden katon yayi fitar burgu tamkar an chillo shi daga cikin baka, take ya dira akan turba ya tsaya kyam kawai yana murmushi, har asannan jini na diga daga kunnensa, koda sauran dakaru sukayi arba dashi sai suka razana suka dinga fantamawa cikin daji, mutumin ya dubeni ya bushe da mahaukaciyar dariya wadda amsa kuwarta ya cika dajin, daga can sai murtuke fuska cikin kakkausar murya yace kai yaro kayi kuskure da kake zaton cewa zaka kare sarki ruzba, tabbas sai nayiwa sarki ruzba kisan wulakanci a gabanka kuma kaima sai nayi filla filla da sassan jikinka..
Kodajin wannan batu sai zuciyata ta kekashe gabarin tsoro na dubeshi a fusace nace karyarka tasha karya yakai wannan azzalumi, kai waye dakake tinanin zakayi mana kisan gilla.
Maridin ya sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan yace sunana Gilzam sadaukin sadaukai na maridan duniya, musamman sarki darbuza na birnin kailus ya dauko hayata domin na kashe sarki Hubru ayau, bisa yarjejeniya aduk kwanaki bakwai zai dinga bamu mutum dari nida iyalina muna cinyewa, domin naman mutane ne abincin mu, babu wani bala'i dazai hanani kashe sarki hubru ayanzu, idan kuma kuna gani zaku iya toh ku jaraba.
Kafin na bude baki nace wani abu tuni gilzam ya zare wadansu zabga zabgan takubba guda biyu ya durfafo mu, girman kowace takobi ya wuce misali, nauyin ta kuwa saidai karti ashirin su dauka, dama tuni jikin sarki hubru dana Maharaz ya fara karkarwa sbd tsananin razanar da sukayi bisa ganin gilzam da kalamansa, amma sbd tsabar tsoro sun kasa mikewa ma su gudu. Cikin matukar karfin hali na zare tawa takobin na tunkari gilzam duk dayake ni kaina nasani gilzam yafi karfina nesa ba kusaba amma saina tari aradu daka...
Gilzam ya nufo kaina gadam gadam nima na nufeshi acikin dakewar zuciya, takun sawun gilzam tamkar na toron giwa ne amma hakan batasa na razana ba, koda muka hadu ya kawo min wawan sara da takuba biyu da nufin ya fille min kai da kafafu saina goce da dukkan zafin nama na, takobin farko saita samu wata bishiyar dibino mai tsawo take bishiyar ta rabe gida biyu ta ratattake akasa, takobi ta biyu kuwa sai ta karci kasa, nan take ta haifar da girgizar kasa da zabtarewar ta, koda ganin faruwa wannan alamari sai hankalina ya dugunzuma na tabbatar dacewa yaufa na gamu da gamona.
Sarki Hubaru da Maharaz kuwa sai suka sake tsurewa domin sun gama saduda sun san mutuwa tazo, niko danaga haka ban karaya ba sai na dada durfafan gilzam, shi kansa gilzam yayi mamaki dan bai taba haduwa da mutumin dabai taba razana akan shiba sai ni, abinda yafi daure mashi kaima shine na kasance yaro mai kuruciwa dan shekaru goma sha, cikin matukar fusata gilzam ya tasomin da dukkan karfin sa yana mai kawomin sara da suka da muggan makaman sa, nikuma ina gocewa amma ko kadan na gagara maida martani saboda karfin harinsa da zafin namansa ya ninka nawa, kaini kaina nayi mamakin yadda ma nake gocewa harinsa nan gilzam ya tashi hankalin dajin gabadaya ya haddasa kamawar wuta da girgixar kasa. Sai da muka shafe sa'a guda cif nida gilzam muna fafatawa shi baisami nasarar hallakani ba balle ya koma Kansu sarki hubru.
Bayan ansamu sa'a gudan ne naji na fara gajiya, shiko Gilzam kamar a lokacin nema ya fara gumurzun, alamarin daya dugunzuma hankalina kenan na tabbatar dacewa saura kiris tawa ta kare. kwatsam! sai muka jiyo kururuwan mazaje daga bayan mu cikin sauri muka waiga sai naga ashe dakarun da muka fito rangadi dasune sukaje suna neman daukin sauran dakarun darul mahabur, sama da mutum miliyan biyu ne suka durfafo mu suna ihu da karaji, karar sukuwar dawakan suma kawai ta isa ta razana mutum ya dauka yakin duniya akeyi.
Koda Gilzam ya hango wannan runduna ta durfafo shi sai yayi murmushi ya ruga garesu, tun gabanin su riske shi. Kaico!! yayin da Gilzam ya ratsa ta cikin dakarun saiya dinga zubar dasu tamkar yana shara, sai dai kaga takobinsa na datsa mutane tana raba dawakansu gida biyu, nanfa ya bude kasuwar daukar rai sai hangowa nayi jini na tsartuwa yana malala akasa, kafin na ankara tini gilzam ya kashe sama da dakaru miliyan daya da rabi da dawakansu.
Ko da na hango wannan barna saina fusata ainun na falfala da matsanacin gudu Irin wadda bantaba yin irinsa ba, domin har ji nake kamar zantashi sama, na nufi inda gilzam yake wannan barna, yayin daya rage saura taku uku na isa gareshi sai na daka tsalle sama na sauka akan wuyansa, kafin yasa takobinsa ya kadoni tuni na soka masa wuka a kunnensa na hagu take wukar ta lume acikin kunnensa ya bullo ta daya kunnen. Gilzam ya kwarara uban ihu alokacin da jini yake shatata daga cikin kunnensa kawai sai yasa hannunsa guda ya kawomin wawura, niko na goce amma saida ya chakumo rigata, sai kawai ya cillani sama saida nayi tafiyar taku dari a sama sannan na maku akan wata bishiya na fado kasa a matukar galabaice, awannan lokacin ne naji Gilzam yana kururuwa mai matukar razanarwa bashiri sauran dakarun dabasu mutuba suka farfado sukayita faduwa daga kan dawakansu saida gilzam ya shafe dakika dari da arba'in yana kururuwa kuma yana kokarin zare wannan wuka dake cikin kunnensa amma ya kasa, daga can sai akaji yayi tsitt kuma sai ya sulale kasa ya durkushe bisa guiyoyin sa ya kame tamkar gunki, wato yayi mutuwa irin ta manyan mazaje.
Koda ganin haka sai sarki hubru ya mike zumbur ya rugo da gudu zuwa inda nake kwance ya tasheni zaune ya rungumeni yana mai tsananin farin ciki da godiya a gareni.
A iya rayuwar mu nida maharaz bamu taba shiga cikin harabar gidan sarautaba kullum saidai mujira sarki inya isa fada sannan mukuma aikin muna tsaron lafiyarsa amma awannan rana saida sarki hubru ya shigar damu har cikin turakarshi inda muka zamo yan kauye muka dinga kalle kalle.
Nan take yasa aka kawo mana abinci da abun sha iri-iri wato dai ya shirya mana walima saboda farin cikin mun ceto rayuwarsa muna cikin more walimar ne muka hango abinda yasa muka tsaya cak gabarin ci da sha, duk gabadayan mu muka kame tamkar babu mai rai acikin mu.
A lokacin da muka kame kamar babu rai ajikin mu bawani abu muka gani ba face wata kyakkyawar mace ta gaban kwatance ta nufo mu tana sanye da doguwar riga, wadda aka yiwa ado da zinare shekarunta basu haura goma sha uku ba, koda sarki ya hango wannan kyakkyawar budurwa saiya mike da sauri yaje ya taro ta sannan ya kariso da ita ya zaunar da ita abisa kujerar datake fuskartar tamu nida maharaz muka kura mata idanu muka kasa kauda kai har saida sarki hubru ya tabo mu muka dawo hayyacin mu kyakkyawar bata kalli daya daga cikin muba saita sunkuyar dakai tana mai murmushi kawai. Sarki hubru yayi gyaran murya yace yaku amintattun dakaru na kuyi sani cewa tunda na zama sarki awannan birnin babu wani da na miji da ya taba shigowa har cikin turaka ta sai ku, saboda muhimmanci aikin daku kayi min ayau dinnan na ceton rayuwata daga sharrin babban abokin gabata wato sarki dumbazu na birnin Kailus. Wannan kyakkyawar budurwar da kuke gani a gabanku 'yatace ta cikina, sunanta Sahira, tunda aka haifeta bata taba fitowa daga harabar gidan nan ba, kuma jama'ar gari basu san an haifeta ba, kai hatta hadiman cikin gidan nan basu san da haifuwarta ba kune mutane na farko da ta fara gani a rayuwarta banda nida mahaifiyarta.
Tuntuni bincike awajen bokaye na ya tabbatar min dacewa, acikin bayina zan samu mutum biyu zarata wadda zasu kareni daga sharrin makiya, kuma daya daga cikinsu zai gaji sarauta ta, dayan kuma zai auri wannan kyakkyawar yata, kusani cewa ba'a son raina hakan zai faru ba, kuma banaso ace wani ya auri Yata wanda ba basarake ba amma babu yadda zanyi kaddara tariga fata.
Koda sarki yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa sannan ya cigaba bayani...
To nima jin wannan kalamai na Sarki Hubaru yasa nayi kikam Kasancewar na kamu da soyayyar Gimbiya Sahira kuma naji yana ikirarin ba zai bazai baiwa talaka yarsa ba 😢😢😢
Shin kana bukatar wani littafi na yaki kawai tuntubeni ta wannan Number ko kuma kayi mani magana da profile dina 08138873799.
Koda sarki yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa sannan ya cigaba bayani inaso kusani cewa a duniyar nan babu abinda nakeso sama da yata sahira, to amma inaji ina gani zan rabu da ita domin bincike ya tabbatar min dacewa rayuwata gajeriyace abune mawuyaci na kara shekara biyar nan gaba a duniya, daga yau na damka muka sahira a hannunku na sani cewa a halin yanzu duk biyun kun kamu da kaunar sahira, to amma fa kusani cewa dole daya daga cikin ku ya hakura yabarwa dayan wadda duk ya auri sahira acikin ku bazai tabayin sarauta ba kuma zai sota samada komai a rayuwar sa, kuma saita rigashi mutuwa wanda yarasa sahira acikin ku shine zai gaji sarauta ta kuma zaiyi tsawon rai a rayuwarsa har yabar duniya haihuwa daya zaiyi sannan ya mutu yabar abunda ya haifa, babu wani tsafi ko wani kokari dazai sauya wannan kaddara akan mu inaso ku kwantar da hankalinku akan fitar da zuciyoyin ku bisa samun mulki koh auren yata domin lokacin ne zai banbanta komai da wannan kalami nake muku sallama daku tashi kutafi gidajen ku amma kafin sannan akwai kyauta ta mussamman yacce zan baku koda gama fadin haka sai sarki hubru ya dubi yarsa gimbiya sahira yace jeki ki dauko musu kyautarsu cikin fara'a sahira ta mike tsaye ta shiga wani daki tana tafiyar kasaita tamkar dawisu jim kadan sai gata tafito da wadansu jakukkunan fata guda biyu sahira ta matso gabanmu tabawa kowa jaka guda koda muka karba muka bude ashe zinare ne acike makil nan take muka zube kasa muna gdy sarki hubru ko kallon mu baiyiba saiya kama hannun gimbiya sahira yashige da ita izuwa cikin wannan dakin data dauko kudin shigewarsa keda wuya sai maharaz ya rude ya rikice sbd ganin wadannan kudade niko sai naji sam kudin basu dameni niba.
Daga wannan rana wani abu sake faruwa ba sai bayan kwanaki goma sha bakwai da wata safiya sa'adda tafiya takama Sarki hubru izuwa wani kauwe da ake kira zumur domin yaje ya dubo wani tsohon abokinsa wadda ya kwanta ciwo tsawon wata uku, shidai wannan aboki na Sarki Hibru sunan sa abul husnu, kuma tun kuruciwa suka taso da sarki hubru abinda yasa yayi zamansa a zumur shine ya samu nasibi matuka a harkokin kasuwanci domin mutanen garin suna matukar kaunarsa sbd yawan taimakon sa da kuma kyautatawa ga talakawa, akarshe ma saida suka matsa mishi ya karbi shugaban cin birnin Sarki hubru ne dakanshi yazo ya nada shi a matsayin shugaban birnin akaxo akayi gagarumin biki bayan wata daya dayin bikin ne ciwo mai tsanani ya kama abul husuna lokacin da lbr ya riski sarki hubru sai hankalinsa ya dugunzuma aka nemi likitoti suyi masa magani saida likitoci sukai kwana goma suna lura da abul husuna basu gane irin cutar datake damunsa ba, bisa dole duka debi nasu da nasu sukaje suka sanarwa sarki hubru halin da ake ciki dajin bayanin likitocin sai hankalin Sarki ya kara dugunzuma akan hanyane sarki hubru ya tafi wajen wani amintaccen bokansa ya sanarda dashi halin da ake ciki, nan take bokan yayi bincike nan take yayi murmushi ya duvi Sarki yace ai wannan cuta ta abokin ka sharrin sihiri ne ba wani bane yayiwa abul husuna asiri sai tsohon shugaban kauyen zuhur sbd bakin cikin an sauke shi daga mukaminsa andaura abul husuna, shi dai wannan asiri an bunne shine a kofar gidan abul husuna.
Abul husuna bazai taba warkewaba sai an tono asirin kuma idan an tonoshi take wanda yayishi zai mutu babu mai iya tono wannan asiri sai Sarki mai karfin mulki kamarka. Ya shugaba yazama dole kaje dakan ka kaje ka tono wannan asiri amma kada kaje sai randa asirin ya cika kwana casa'in da binnewa domin idan ka tonoshi kafin cikar kwana casa'in da wanda yayi asirin da wanda aka yiwa duk mutuwa zasuyi.
Lokacin da bokan yaxonan azancen sa sai sarki hubru ya cika da mamaki daga can kuma sai ya dubi bokan yace toh yanzu idan naje kofar gidan abul husuna yaza'ayi nagane daidai inda aka bunne asirin boka yayi murmushi yace dazarar kaje kofar gidan kadaga kwagirinka na sarauta sama kasake shi, a duk inda kwagirin ya fado to daidai wajen zaka saka a tone kodajin wannan batu sai sarki hubru yadauko dukiya mai yawa yabawa bokan nasa yana mai matukar farin ciki sannan sukayi sallama sarki ya tafi gida. A ranar da abul husuna ya cika kwana casa'in a kwance yana jinya mukayi shiri tareda dakaru dubu arba'in muka tafi kauyen zumur saida mukaci rabin tafiya mun shigo cikin wata sahara inda babu gida gaba babu gida baya babu bishiyoyi ko duwatsu babu ruwa sai kawai mukaji wani irin tsananin zafi yana fesowa, nan da nan dawakanmu suka dimauce suka kama tutsu suna yada mahayan su suna fita da gudu wata irin gagarumar iska ta taso ta dinga daga mutane da dawakai suna yawo akan iska al'amarin daya dugunzuma hankalin kowa kenan keken dokin sarki maharaz saida ya rabu da kasa zaiyi sama kenan na rikoshi da karfin tsiya amma sai karfin iskar yafara rinjayata saida maharaz ya taimaka min sannan muka sauke shi kasa ni kaina inda badan maharaz ya taimaka min ba da tuni iska tayi sama dani munaji muna gani gagarumar iskar tayi sama da dukkanin abokan tafiyar mu tayita lulukawa dasu tun muna iya hango su har saida suka bace bat ya rage saura mu uku bisa turba wato ni da sarki hubaru wanda cikin keken doki bayan lafawar guguwar ne sarki hubaru ya fito daga cikin keken dokin ya tsaya a tsakiyar mu nan take na zare takobi na kama kallon gabas da yamma kudu da arewa ina jiran tsammani. Shiko maharaz sai yafara kallon tafin hannunsa yana karanta wadansu dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya sai mukaga wata katuwar inuwa ta lullube mu koda muka daga kawunan mu sama sai mukaga wata katuwar halitta tana saukowa daga sama mai tsananin muni da rashin son gani sannu ahankali halittar ta iso kasa-kasa yadda kana iya ganin cikakkiwar fuskarta koda mukayi arba da halittar sai duk mu ukun muka firgice ainun kamar zamu zabura da gudu dayake ita dai wannan halitta bakomai bace face wata sihirtarciyar dodanniya mai kawuna takwas kowani kanta guda girmansa yakaina katon dutse gabadaya kawunan takwas ajikin wuya daya yake shiko wuyan nata dogo ne har karawa kanshi tsayi yakeyi kamar yadda wuyan take kara tsawo haka hannayen tama ke kara tsawo ga dukkan alamu dai idanta mike hannunta guda daga inda take zata iya dauko abindake can bayan duniya daga kowace kusurwa kawai sai mukaga dodanniyar nan ta wangame bakinta guda ta kama gabadaya dakarun namun nan guda dubu arba'in harda dawakansu sunata zubowa kasa a mace anan tayita amarsu suna zubowa tamkar an dafa su acikin tukunya har tururin zafi ne ke fita daga jikinsu SBD tsananin zafin dake jikin dodanniyar bayan dodanniyar tagama amayarda abunda cikinta saita dube mu da idanunta kwala-kwala ta tuntsire da mahaukaciyar dariya maikama da saukar aradu, muka kara firgicewa muka hau kakumar junanmu lokaci guda ta turbune fuska tace kaicon yaku wadannan kananan halittu yau kun gamu da uwar dodannin duniya dayan ku bazai tsira daga bala'i naba duk saina zare muku ruhun numfashi, kuyi sani cewa sarki dumbazu na birnin kailas ne ya aikoni na hallaka sarki hubaru, labari ya riske ni cewa anturo gilzam kun hallaka shi to kusani cewa nina gagari dukkan sadaukan duniya da duk matsafan duniya, yau shekarata dubu tara ina tare mutane da aljanu a can dajin sarbusa ina cinyewa ankasa ganin bayana yanzu Sarki dumbazu yayi min alkawari cewa in dai na hallaka sarki hubaru zai dinga bani mutane dubu ina cinyewa basai nayi wahalar farautar suba, burina shine naci adadin mutane miliyan dubu saba'in a sannan ne zan iya haifan yayana wadanda bazasu bazama ko inaba a duniya sai sun cinye komai da kowa a kwana tara yazamana cewa babu wani abu mai rai a doron kasa saini dasu kawai.
***********************
Mazan Jiya Part 11
#Cigaba
Koda uwar dodanni