Showing 27001 words to 30000 words out of 55369 words
Chapter 10 - MAZAN JIYA Littafi Na Farko Rubuta Labari Abdul'aziz Madakin Gini.txt
tana da wata kariya a jikinta wadda mahaifinta ya shayar da ita tun tana jaririya, kuma babu abinda za a iya yi dan lalata wannan kariya.
Koda ganin wannan al'amari sai bakin ciki ya turnuke boka Ardusa, domin ya fahimci cewa har abada Hantaru bai yi sarautar birnin Kisra ba muddin baiyi watsi da harkokin farauta ba ya kama na fada ba.
Al'amarin sarki Kusaidu kuwa da amarya Shamilat hankalinsu yafi na kowa dugunzuma bisa ganin yadda dansu yaki damu da komai face harkar farauta da kuma yaki, ko kadan Hantaru bai shaku da sarki ba sai dai mahaifiyarsa Shamilat, kuma yana bata mafi yawa daga lokitansa a gidan abokansa yayan mafarauta na birnin, sai da sarki Kusaidu ya gana da boka Ardusa sau 10 akan wannan matsala, amman ko yaushe sai dai boka Ardusa yace da sarki ai sai dai ayi hakuri amma babu abinda za a iya yi.
Boka Ardusa bai fada wa Shamilat dalilin da yasa tsafi baya tasiri a jikin Yarima Hantaru ba, dalili kuwa shine idan tasan da hakan hankalinta zai dugunzuma ta bazama neman taimako a wajen wasu bokayen kuma a haka asirinsa na iya tonuwa har sarki Kusaidu ya gane cin amanar da suke masa.
Wata rana amarya Shamilat na zaune tare da sarki Kusaidu suna fira sai ta ce da shi ya kai mijina ka sani cewa tunda ka aureni ka raboni da kasarmu ban taba kaiwa iyayena ziyara ba sai dai su sukawo mani, ina son kayinmani izinin zuwa a wannan karon, nayi kokari nayi shiri na je. Idan da hali ma zan so na tafi da yarima domin yaga dukkanin danginsa na can.
Yayin da sarki Kusaidu yaji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya Ya ce yake mata ta kiyi sani cewa b laifina bane ki kai wannan ziyara, ina tsoron dazuzxukan dake kan wannan hanyar ne kafin a isa birninku, ni kaina sau daya nabi wannan hanyar lokacin da naje neman aurenki. Lokacin da zanje sai da akayi gagarumin shirin yaki na dakaru masu yawan gaske, kuma sai da Boka Ardusa yayi mani rakiya dan tabbatar da tsaro.
Yayin da shamilat haka sai ta yi murmushi ta ce ya kai mijina indai dan tsautsayin hanya ne ka kwantar da hankalinka, ina mai tabbatar maka da cewa babu abinda zai samemu, domin tun ina yarinya karama iyayena suka bani tsari na musamman, bama ni ba hatta dana da ya sha nono na ya samu wannan tsari, kaima daka aureni ka samu wannan tsari, indai kana cikin hayyacinka to babu wani mahaluki daya isa ya cutar da kai. Ni nasan cewa baka son rabuwa da yarima daidai da rana daya shiyasa baka son nayi wannan tafiya
Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubo wa sarki Kusaidu ya ce Tabbatas kin fadi gaskiya yake mata ta, amman ki sani a halin yanzu babu abinda ke damuna sama da rashin shakuwata da Yarima, ko kadan bai damu da ni ba tamkar ba ni na haifeshi ba, duk shawarar dana bashi baya amfani da ita, har gwara ma ke naga yana matukar kaunarki, kuma baya son yaga bacin ranki.
Sa'adda sarki Kusaidu yazo nan a zancensa sai tausayinsa ya kama Shamilat, ta dafa kafarsa ta ce kada ka damu ya kai mijina nayi maka alƙawari da zarar munje garinmu mun dawo zakaga sauyi a tare da Yarima zai kaunaceka kamar yadda ko wane da yake kaunar ubansa Hakazalika zai shaku da kai, sannan zai ajiye harkokin farauta ya rungumi na sarauta.
Da jin haka sai sarki Kusaidu ya dubi Shamilat cikin tsananin mamaki ya ce Ta yaya hakan zata faru?
Shamilat ta ce kakana shahararren boka ne wanda babu kamarsa a nahiyarmu, ina mai tabbatar maka da cewa ko Boka Ardusa aka sai dai suyi kunnen doki a karfin sihiri, kai ina da tabbacin kakana yafi Ardusa tarin ilimin tsafi, lallai nasan zai taimakemu ya juyo da hankalin yarima zuwa kan tafarkin da muke so.
Yayin da sarki Kusaidu ya ji wannan batu sai ya cika da farin ciki kuma ya amince da batun tafiyar Shamilat. Tun kafin dare yayi Shamilat ta tura aka kira mata Yarima Hantaru tayi masa albishir da tafiyar da zasu yi a gobe ita da shi izuwa can mahaifarta ta darul maabur.
Koda jin haka sai Hantaru ya cika da tsananin farin ciki domin a rayuwarsq bashi da wani buri da ya wuce yayi doguwar tafiya wacce zai ratsa ta cikin dazuka masu ababan hadari, kamar yan fashi da muggan dabbobin daji, ba dan komai ba sai don ya jaraba iyakar tsawagaron ku riyarsa da kuma shan wahalarsa, ya kuma ga iyakar karfin damtsensa, tunda ya ke sau daya ya taba halartar yaki a birnin Kisra kuma lokacin da yaje filin yakin ma saura kiris a gama da abokan gaba, a takaice dai Yarima Hantaru yana so yayi doguwar fafatawa da aboka gaba. Saboda tsananin dokin da yarima Hantaru yake saboda tafiyar da zasu yi tun a daren ya kimtsa kayansa sannan ya daura wa dokinsa sirdi sannan ya tanadi kayan yakinsa. Lokacin daya kwanta bacci sai idanunsa suka bushe ya kasa bacci saboda tunanin tafiyar ta gobe. Bisa wannan dalili ne yasa ya tafi dakin mahaifiyarsa Shamilat, da shigarsa cikin turakar sai ya isketa a zaune tayibshiru tana tunani sai faman murmushi take yi kamar wacce take magana da wani. Har Hantaru ya zauna kusa da ita amman bata san ya shigo ba, sai da ya dafa hannunta sannan tayi firgigit kamar wacce ta farka daga bacci, Hantaru ya dubi Shamilat cikin mamaki ya ce ya ke ummina tunanin me kike yi ne haka wanda har ya hanaki ki kwanta kiyi bacci.
Sa'adda Shamilat ta ji wannan tambaya sai ta yi murmushi sannan ta ce Ya kai dana kayi sani cewa tsananin murna ce ta hanani na kwanta nayi bacci, saboda ina murnar cewa zanje naga kakana wanda ya haifi ubana Boka Sulbaini Bn Ukash. Kayi sani cewa a hannun Sulbaini na girma har nayi wayo, daga baya da za a yi mani aure aka rabani da shi, a ranar da za'a rabamu da shi munsha kuka tamkar ranmu zai fita saboda sabo da juna, rabona da shi yau shekara 16 kenan, nasan cewa yanzu ya kara tsufa ainun babban burina shine na sake saduwa da shi kafin rai yayi halinsa.
Koda Shamilat ta zo nan a zanjenta sai hawaye ya zubo mata, take Hantaru yaji tausayinta ya kamashi har shima kwalla ta zubo masa, Hantaru ya rungume Shamilat gana mai cewa ya ke ummina ki kwantar da hankalinki domin naji a jikina cewar wannan kaka naki na nan a raye kuma tabbas zamu je mu riskeshi.
Tsawon yan dakiku duk su biyu suka yi shiru babu wabda ya ce kala, daga can sai yarima ya janye jikinsa daga jikin nata suka dubi juna sannan ya ce Ya ke ummina shin ba kya bani labarin yadda rayuwar mutanen birninku take ba?
Lokacin da shamilat ta ji wannan tambaya sai ta yi murmushi sannan ta gyara zamanta ta ce Mafi akasarin mutanen birninmu mafarauta ne da kuma makera, mahaifina shine sarkin makera kuma shine galadiman sarkinmu ana kiransa da suna Shuraim Bn Alkas. Tsakanin zuri'armu ta makera data mafarauta babu kyakkyawar fahimta ko zumunci mai karfi, kuma babu auratayya mai yawa. Babu abinda yafi burgeni a garinmu face wata al'ada da aka saba yi duk karshen shekara, al'adarvita ce za'a zabo budurwar data fi dukkanin yan matan garin kyau a sa gasar neman aurenta a tsakanin jaruman samari, masu ji da sadaukantaka. Yanayin gasar shine za a saki barewa a daji a kasa tsere duk saurayin da yafi kowa gudu ya kamonwannan barewa to shi zai auri wannan kyakkyawar budurwa. A lokacin da ake tseren gudun an yarda samarin su dinga bangaje juna duk wanda ya fadi kasa to ya fita daga cikin gasr kenan.
Gabadaya mutanen garin banda al'karan gasar suna hawa kna wani dogon tsauni ne su tsitsaya dan su hango abinda ke faruwa, su kuwa alkalan gasar suna bin bayan mahayan ne, lokacin da shamilat ta zo nan a zancenta sai Yarima Hantaru yaji soyayyar darul maabur ta lullubeshi domin ya fahimci cewa can ne ya dace da yanayin rayuwarsa, dan haka sai ya sake cika da tsananin farin ciki.
Yadda yarima yaga rana haka yaga dare, wato har gari ya waye bai runtsu ba, washegari da sassafe ya tashi tunma kafin alfijir ya keto yayi wanka ya kuma sanya tufafinsa, yana gama kimtsawa kuyanga ta kawo masa abincin kalaci, amman yana yin lokamar farko sai yaji ya koshi dan haka sai ya mike ya bar abincin ya tafi dakin Shamilat, yana zuwa ya iske ta, tuni itama ta gama shiryawa shi take jira kawai.
Nan take kuyangi suka fito da kayayyakin Shamilat har da guzurin da zasu tafi da shi da kuma tsaraba, duk wannan abu da ke faruwa Zarifa bata sani ba sai a lokacin da sarki ya fito daga cikin turakarsa ya riski Shamilat da hantaru tsaye cikin turakarsa, kawai sai ta riske sarki Kusaidu yana bankwana da shamilat har yana rungume yarima Hantaru yana zubar da hawaye.
A gigice zarifa ta taho da gudu ta karaso garesu ta kama hannu Yarima Hantaru ta rike tana mai cewa ya kai dana ina zaku tafi haka amman baku fada mani ba?
Yarima ya dubi Zarifa a wulakance ya ce zamu tafi garin kakannina ni da mahaifiyata.
Koda jin haka sai Zarifa ta ji zuciyarta ta buga da karfin gaske, har bata san sa'adda ta kama surutai ba tana cewa ai bai kamata ku tafi yanzu ba, zai fi kau ku bari ayi maku shiri na musamman.
Yarima Hantaru yq ce ai babu abinda zai hana mu wannan tafiya a yau, sai dai fitar ruhi daga cikin gangar jiki. Gama fadin hakan keda wuya sai Hantaru ya kama hannun Shamilat ya ja ta suka tafi, barori ba biye da su da kaya niki-niki.
Koda ganin haka sai Zarifa ta sulale tq fice daga cikin gidan sarautar ba tare da kowa ya sani ba. Cikin hanzari Zarifa ta haye bisa doki ta ruga izuwa gidan Boka Ardusa domin ta sanar da shi halin da ake ciki dan yasan matakin da zai dauka kada asirinsu ya tonu.
Boka Ardusa na zaune shi kadai a cikin harabar gidansa ya zuba wasu alkaraman sihiri a gabansa yana nazari sai kawai yaga Zarifa ta shigo da gudu kuma a gigice har tana tuntube zata fadi kasa. Koda ta iso gabansa sai ta zube kasa tana mai faman haki, kuma ta bude baki zata yi magana sai kawai Boka Ardusa ya daga mata hannu yana mai yi mata nuni ta yi shiru.
Bisa dole zarifa tayi shiru bata ce komai ba, kuma ta kura sama idanu har sai da ya gama yan tsubbace-tsubbacensa. Boka Ardusa ya juyo ya dubi Zarifa ya ce da ita ai nasan abinda ke tafe da ke, kuma tun a jiya nasan da batun tafiyar amarya Shamilat da danmu Yarima. Ki kwantar da hankalinki tamkar tsumma a randa domin babu abinda zai faru. Ina mai tabbatar maki da cewa muddin ina numfashi a doron kasa har abada asirinmu bazai tonu ba. Ki saki ranki kije kita bacci harda munshari, da sannu burinmu zai cika danmu ya zama sarkin birnin darul maabur.
Koda jin wannan batu sai Zarifa ta kyalkkyale da dariya, can kuma sai ta hade fuska ta yi shiru kamar tana nazari.
Boka Ardusa ya dubeta cikin damuwa ya ce tunanin me kuma kike yi, alhalin na fada maki cewar babu abinda zai faru?
Zarifa ta yi ajiyar zuciya ta ce ni abinda nake tsoro shine kada yarima yayi zamansa acan birnin darul mahabur yaki dawowa nan gida, abu na biyu ni fa yanzu na shiga matsananciyar damuwa saboda dana yarima bai san cewa nice mahaifiyarsa ta gaske ba, shin kana tsammanin cewa nan gaba zai karbeni ne a matsayin uwa ?
Boka Ardusa ya ce kwarai kuwa, kuma sai ya kaunace mu fiye da kowa a rayuwarsa nayi maki wannan alkawari, kedai ki ci gaba da hakuri al'amarine na lokaci, idan muka ce zamu yi wa lamarin gaggawa to fa lallai burinmu ba zai cika ba.
Haka dai Boka Ardusa yayita lallamin Zarifa har hankalinta ya kwanta, suka aikata cin amanar da suka saba sannan ta tafi.
Mazan Jiya Part 15
#Cigaba
A lokacin da shumilat da yarima hantaru suka fita kofar gari sai suka kama hanya batareda fargabar komaiba su kwana nan su tashi chan saida suka bar birnin darul maabur da shiga su daji na fark6 wanda ake kira sujud sai shamilat taja linzamin dokinta ta tsaya shima sadauki hantaru saiya tsaida dokin nashin, shamilat ta kasa kunnenta bataji motsin komai ba sai tayiwa yarima hantaru magana cikin rada tace akwai muggan yan fashi a wannan daji kuma sun iya nada muggan tarkuna sai mun kula da kyau koda jin wannan magana sai hantaru yayi mata nuni data sauka daga kan dokinta batareda wata gardama b shamilat ta sauko shima saiya sauko daga kan nashi. kawai sai yasaki dokin nasa yayi gaba koda dokin nasa yayi tafiyar kamar taku talatin saiya zurma cikin wani wawakeken rami mai zurfin gaske saiga wadansu samudawan yan fashi suna mai rugowa daga cikin maboya suna zuwa bakin ramin suna tsayawa adadin yan fashin ya haura 300 dukkaninsu sun kasance majiya karfi kuma suna daukeda muggao makaman yaki sun shafe fuskokinsu da bakin shuni bayan yan fashin sun gama yiwa wawakeken ramin kawanya rai suka fuskanci cewa yaufa karensu bai kama zomo ba domin doki ne kawai ya fada cikin ramin babu mahayi akan dokin babu dukia cikin tsananin fushi shugaban yan fashi ya dubi sauran dakarun ya daka musu tsawa yace tsayuwar me kuke maza ku baxama neman mai wannan dokin kafin yagama rufe bakinshi sun tarwatse sun rarrabu acikin dajin, ashe dvk abin da akeyi hantaru da shamilat na labe acikin wani duhuwa suna hangowa koda hantaru yaga yan fashin nan sun rarrabu suna farautarsu sai ya cewa shamilat ta dada buya acikin wannan duhuwa shi kuma sai yakama wata doguwar bishia yakama hawa samanta hantaru yayi lamo acikin ganyen bishiyar duk dan fashin dayaxo inda shamilat ke boye sai hantaru ya diro ta bayansa ya masa mangara daya ya fadi sumamme sannan ya kwashe makanshi yayi sama dasu a haka saida ya sumarda sama da yan fashi 50 koda yaga zasu gano inda shamilat ke boye saiya sauko kasa ya dauke ta daga wajen ya ruga zuwa inda wawakeken ramin nan yake wanda dokinsa ya fada ciki!! wohohoh nan take hantaru ya shiga cikin ramin nan ya dauko dokinshi kafin hantaru ya juya ya daura shamilat akan dokinsa sai yaga yan fashin sun masu kawanya kimanin su 300 da doriya tuni shugaban yan fashin dora wata wuka mai tsananin kaifi akan wuyan shumilat cikin firgici hantaru ya dubeshi yana mai daka mishi tsawa yace ku kwashi duk abinda kuke so daga dukiya amma inamai gargadinku da kadaku kuskura ku tuba lafiyar mahaifiyata koda jin haka sai shugaban yan fashin yace aiko sai mun dauki fansar yan uwanmu daka sumar ka kwashe musu makamai yanxu xan kashe mahaifiyartaka sannan kaima nayi maka kisan gilla na kwashe dukiyar taku kafin hantaru ya budi baki yace wani abu tuni shugaban yan fashin nan ya dadara wukar nashin akan wuyan shumilat bisa mamaki sai yaji kamar akan dutse ya dadara cikin zafin nama hantaru ya zare wata wuka ajikin shi Cikin zafin nama hantaru ya zare wata wuka ajikinshi ya cillata ta cake a goshin shugaban yan fashin ya sulale kasa matacce koda ganin haka sai sauran yan fashin suka afkawa hantaru suna masu kai mishi sara da suka ta koina kaicoh! inda yan fashin nan sun san abinda zai biyo baya da dukkaninsu sun nemi gudu tsira. koda sukayiwa hantaru kawanya kawai sai yayi wuf yakama kafar daya acikinsu ya maidashi makaminshi da kuma garkuwanshi ya dinga tare sara dashi kuma yana maida martani dashh nan danan suka daddatsa dan uwan nasu duk wanda hantaru ya makawa dan uwan nasu sai kaga ya fadi sumamme koh matacce nan fah akarasa mutum daya daga cikinsu wanda zai iya koda lakutar jikin hantaru saboda tsananin zafin namanshi da karfin bugunshi kafin cikar sa'a dari biu duk ya bazar dasu akasa mattatu a sannane ne hantaru ya dubi shumilat cikin matukar mamaki yace yake ummina yaya akayi wuka ta kasa yanka ki? shamilat tayi murmushi tace shin kamanta cewa ubana
sarkin makerane babu wani karfe dazai iya huda jikina koda kaima kanka karfe bazai cinkaba saboda kasha a nono shin kataba jarba karfe acikin ka? hantaru yace Aah amma barina jarraba yanxu nagani nan take hantaru ya zare takobinsa ya yanki dantsen hannunsa aiko sai yaga ko kortsanuwa bai yiba kawai sai ya cika da tsananin mamaki. batareda bata lokaci ba suka hau dawakansu suka cigaba da tafiya suna masu kada dawakan gaba suka bar yan fashin a zube a kasa matattu ru hantaru suka cigaba da tafia har tsawon kwana sha daya basu sake haduwa da wani mugun abuba da tsakar ranar kwana na shadayan ne suka shigo cikin wani bakin daji mai ban tsoro domin babu komai acikin shi tsaunuka masu tsawo da kwazazzabai da shigarsu cikin dajin hantaru ya aiyana a ranshi lallai baza'a rasa muggan halittu acikin shiba koda gama aina haka sai ya zare takobinshi yaceda shamilat ta dawo nashi dokin shamilat batayi wani gardama ba tayi yadda ya umarceta yin hakan keda wuya sai sukaga wadansu manyan gwaggon biri sunata fitowa daga cikin
kogunan dutsen nan suka cigaba da bullowaa kamar bazasu kare ba koda ganin gwaggunan birin sai hankalin shumila da hantaru ya dugunxuma domin basu taba ganin birrai masu girma da muniba kuma koba komai sarkin yawa yafi sarkin karfi hantaru yasake kankame takobinshi dakyau yana ainawa arranshi cewa yau komin rintsi da tsanani baxai bari a taba lfy mahaifiyarshi ba adaidai wannan lokacin ne shamilat taji nadama tazo mata abisa wannan tafia zuwa birnin iyayenta nan take ta tunoda zancenda mijinta a lokacin da yake fadamata hadarin dayake kan wannan hanya. sannu a hankali birurrukannan suka cigabada matsowa suna yiwa dawakansu hantaru kawanya sukansu dawakan saida suka kama ruri da haniniya bisa gani birurrukan,shiko hantaru koh gizo baiyiba yaci gaba da rike linzamin dokinshi da hannu daya dayan hannun kuma