Showing 48001 words to 51000 words out of 55369 words
Chapter 17 - MAZAN JIYA Littafi Na Farko Rubuta Labari Abdul'aziz Madakin Gini.txt
haka dai ya rungumi kaddara bisa dole ya cigaba da hankoro zuwan Shekarar gaba.
A takaice dai sai da aka yi gasa sau uku ba zakara sai ragas ake yi tsakanin Hantaru da Rabbasu, a ranar da akayi gasar ta uku ne shugaban alkalan gasar wato sarkin birnin Darul Habur wato mahaifin Gimbiya Larziyya ya yi bayanin cewa tunda dai wadannan zaratan jarumai sunyi ragas har sau uku akan gasar neman auren yarsa, to yanzu za suyi gasa ta karshe mai tsananin wahalar da ko dayansu yayi nasara ko kuma duk su biyun su hallaka, idan kuma suna ganin cewa b zasu iya yin gasar ba to sai dai duk su biyun su hakura da neman auren Gimbiya.
Sarki yayi gyaran murya sannan ya cigaba da cewa ita dai wannan gasa ta karshe bata komai bace sai ta tafiya izuwa kogon mazabatul hirsham dake can karshen dajin hayatul Maut dan dauko takobin Saiful Lujara.
Koda sarki ya zo nan a jawabinsa sai filin gasar ya rude da hayaniya da ka-ce-na-ce saboda sanin masifun dake dajin hayatul Maut.
Dajin hayatul Maut yayi kaurin suna a ko ina a wannan zamani, domin dajine fiye da shekaru dubu da suka gabata babu wata halitta da ta taba shigarsa ta fito, duk abinda ya shiga cikinsa ya shiga kenan, har abada b za a sake jin duriyarsa ba, walau mutum ko aljan ko dabba ko tsuntsu, kai bama cikin dajin hayatul Maut ba, hatta gefen dajin ba a bi.
Lokacin da filin gasar ya rudu da ka-ce-na-ce sai sarki yasa aka busa kaho kowa yayi tsit tamkar mutuwa ce ta gifta. A sannan ne sarki ya dubi Hantaru da Rabbasu wadanda ke duke a gabansa cikin mugun yanayi na galabaita mai kama da suma y ce Ya ku wadannan manyan zakuna ababan kwatance, kuyi sani d cewa daga yau har duniya ta nade ba za a manta da jaruntakarku ba, to amman fa ba zaku cika mazan jiya ba sai idan kunyi wannan gasa ta karshe, dayanku ya samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara, shin kun amince zaku siyar da rayuwarku domin neman suna da neman auren yata?
Koda jin wannan tambaya sai Sadauki Rabbasu yayi farat ya ce ya shugabana kayi sani cewa rayuwata bata da wani amfani muddin ban mallaki gimbiya Larziyya ba, kuma ban kare martabar zuri'ata ba ta mafarautan wannan Birni, saboda haka na amince na siyar da raina domin cikar burina da burin zuri'ata.
Koda jin wannan batu sai jama'a suka sake barkewa da sowa, aka hau buga tambura da ganguna ana yiwa Rabbasu kirari da jinjina, sai da sarki yasa aka sake busa kaho sannan jama'a suka yi tsit a karo na biyu.
Sarki ya dubi Sadauki Hantaru ya ce ya kai wannan namijin duniya ka ji abinda abokin gasarka ya fada, kai kuma me zaka iya cewa?
Hnataru yayi ajiyar zuciya ya ce ya kai wannan sarki mai daraja, ka yi sani cewa a duniya babu wani abu mai daraja wanda yakai faranta rab masoyi, lallaı bani da masoyi wanda ya kai mahaifiyata da kuma abar begena Gimbiya Larziyya, mahaifinta bata da wani buri face ace yau kambun gasa ya dawo hannun zuri'arsu ta makeran wannan birnin, haka kuma masoyiyata bata da wani buri da ya fi ace yau nine zakaran gasar neman aurenta, bisa wannan dalilai dana wassafa na amince na sallama rayuwata domin faranta ran zuciyoyin wannan masoya nawa guda biyu.
Koda jin haka sai jama'a suka sake barkewa da shewa gami da ihu, masu buga ganga nayi, masu busa algaita da tambura ma nayi. Sai da aka dan jima ana cashewa sannna aka busa kaho kow yayi shiru, saannan sarki yayi gyaran murya ya ce to jama'a kunji abinda zaratan jarumanmu suka fada, saboda haka kofa a bude take ga dukkanin jarumi wadanda suka ga zasu iya shiga wannan gasa wato su bi su Rabbasu izuwa dajin hayatul Maut dan shiga kogon Mazabatul Darshal a dauko takobin Saiful Lujara. Ko da mutum bai yi nasara ba, zai yi suna, idan kuma suna bai samu ba rayuwa zata salwanta, wanda duk yake ganin zai iya bin wadannan Sadaukai ya bayyana kansa yanzu.
Koda gama fadin haka sai sarki yayi shiru ya kama kalle kalle yana mai duban gabas da yamma kuma kudu da arewa ko zaiga wani jarumin da zai fito ya kawo kansa, tsawon lokaci ba asamu mutum daya da ya fito ba.
Ko da ganin haka sai sarki yace na sallami kowa da kowa, domin ta tabbata cewa wadannan zaratan jaruman guda biyu sune kadai zasu yi wannan tafiya, da wannan furuci nake sallamar kowa, sai kuma bayan kwana talatin zamu yi sallama da jarumanmu biyu domin su tafi dajin hayatul Maut, zamu ba jaruman mu adadin kwanaki arba'in wanda duk ya dawo daga dajin hayatul Maut dauke da takobin Saiful Lujara a cikin kwanaki arba'in din a cikinsu to shine zai zamo mijin ya ta gimbiya Larziyya, kuma ya cika namijin duniya Sarkin Sadaukai wanda har abada tarihin jarumtakarsa ba zata taba gushewa ba, kuma idan yaso zai iya mulkar duniya gabadayanta saboda sihirin dake jikin wannan takobi da ya mallaka ta Saiful Lujara.
Koda jin wannan batu sai jama'a suka cika da tsananin al'ajabi kowa ma yaji inama zai iya saida rayuwarsa ya tafi neman wannan takobi. Nan dai mutane suka yita fadar albarkacin bakinsu, aka kwashi Hantaru da Rabbasu a matukar galabaice tamkar wadanda suka shekara suna jinyar cuta aka tafi da su gida, haka yasa taro ya watse kowa ya kama gabansa.
A wannan karon ma Samilat ce ta yi jinyar Hantaru har tsawon kwanaki ashirin, sannan jikinsa y dawo daidai ya samu lafiya. A kullum dan Salimat ta dubi Hantaru ta tuna saura kwanaki kadan su rabu, Rabuwar da babu tabbacin su sake saduwa sai ta fashe da matsanancin kuka. Da kyar da sidin goshi Hantaru yake rarrashinta ya kuma bata baki sannan take daina kukan. A koyaushe Hantaru yana kara kara mata gwarin guiwa da cewa ya ke ummina kiyi sani cewa da zarar na dawo ne zamu koma can birnin Kisra tare da amarayata Gimbiya Larziyya ki sadu da mijinki, mu cigaba da sabuwar rayuwa, kuma a sannan ne zanyi wa boka Ardusa da mahaifiyata larifa hukunci da ya dace dasu bisa cin amanar mijinki da suka yi.
A duk sa'ad da Hantaru yayi wannan furuci a gareta sai ta sake fashewa da kuka ta ce ya kai dana ka yi sani cewa har abada komi lalacewar iyaye, iyaye ne. Kada ka kuskura kace zaka hallaka Ardusa da Larifa bisa cin amanar d suka yi wa mijina, kai dai kawai ka tona masu asiri domin su zamo abin kwatance ga al'umma kuma darasi ga al'umma, ni dai bukatata a gareka ita ce, duk matsayin da ka kai a duniya kada ka gujeni, domin bani da wani face kai, duk da cewa banice na haifeka ba, ina jin a raina cewa ko a nan gaba bazan so dan da zan haifa kamar yadda na so ka ba. Ya kai Hantaru ka rike ni a matsayin uwa mahaifiya, kuma ka sani kamar yadda kowanne da ke son uwarsa, burina shine koda mai rabawa zata rabamu mu rabu da soyayyar juna.
Yayin da Hantaru ya ji wannan batu sai ya rungumeta kuma ya fashe da kuka yana mai cewa har abada bazan gujeki ba yake ummina, kece uwata a zahiri, kuma kece uwata a badini.
Kaico! Hakika kowa ya rasa masoyi yayi kuka, a duniya kaf babu abinda yafi farin ciki kamar samun masoyi, inda ace mutum na nan a lokacin da wadannan masoya suka rungume junansu sun kuka dan alhinin rabuwar da zasu yi nan bada daddewa ba, dole ne tausayinsu ya kmashi har ya zubar da hawaye, domin shakuwar dake tsakaninsu da sabo da juna ya wuce ayi misali face abinda zuciya ta kintata.
A ranar da kwanaki talatin suka cika ne Hantaru ya gama shirya kayansa domin tafiya izuwa dajin hayatul Maut dan dauko takobin Saiful Lujara, lokacin da yazo yin bankawana da Salimat da kuma iyayenta, sai zuciyarsa ta karaya ya fashe da kuka ya kasa cewa komai a garesu, koda ganin haka sai duk su ukun suka fashe da kuka suma suka rungumeshi suna masu kankame shi a jikinsu tamkar ba zasu barshi yayi wannan tafiya ba.
Kwatsam sai suka ji alamar motsin tafiya ana shigowa cikin gidan, cikin hanzari suka wauga suka yi arba da wanda ya shigo, ba kowa bane sai boka Sulbaini mahaifin Shuraim.
Sulbaini ya tsaya cak yana kallon Hantaru shi kadai, a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla sannan sai ya dubi Salimat ya fara zubar da hawaye.
Koda ganin haka sai Salimat da Hantaru suka ruga gareshi suka rungumeshi shi tare da fashewa da matsanancin kuka har zuwa lokaci mai dan tsawo, daga can sai Salimat ta janye jikinta daga nasa, suka fuskanci juna sosai sannan ta ce ya kai kakana mene ne dalilin da yasa kake kuka a yanzu, alhalin kaine ya kamata ka karfafi zukatanmu bisa wannan tafiya da dana zai yi.
Sa'ad da Sulbaini ya ji wannan tambaya sai ya kama hannu Salimat ya jaya gefe guda inda babu wanda zai ji abinda zasu tattauna da ita, ya shiga yo mata wadansu bayanai, tunda ya fara bayanan Salimat ta fara kuka, aiko yana gamawa sai ta rushe da matsanancin kuka, kuma ta rungumeshi tana mai kankameshi a jikinta kamar wani zai kwace mata shi, da kyar Sulbaini ya cire jikinsa daga nata sannan ya taho gaba hantaru ya tsaya daf da shi har suna iya jin numfashin juna, Sulbaini yayi murmushi mai taushi ga Hantaru sannan ya ce ya kai namijin duniya kayi sani cewa nazo ne domin muyi bankwana, kuma nayi maka tuni bisa abinda na fada maka a baya idan baka manta ba, a ranar da kuka je gidana nayi maka gargadi akan kada ka kuskura Gimbiya Larziyya ta umarceka da yin abinda zai lalata alakar ka da jikita wata Salimat, bayan ka samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara, idan ka kuskura ka aikata hakan tabbas zaka yi biyu babu a rayuwa, domin zaka rasa masoyanka kuma ka rasa daukakarka, har ya zamana cewa ka gwammace mutuwa da rayuwa, saboda haka ka kiyaye kuma kayi matukar nazari a duk lokacin da Gimbiya Larziyya ta zo maka da bukatarta.
Lokacin da Hantaru ya ji wannan batu sai yayi murmushi yace kada ka damu ya shugabana, lallai zaka samenk mai kiyayewa bisa wannan shawara daka bani.
Gama fadin haka keda wuya sai ga wani manzo yazo daga gidan sarki. Da zuwansa sai ya fadi gaban Shuraim ya ce ya shugabana sarki ne ya aikoni yace na sanar da kai cewa ana juran Hantaru a fada domin a sallamesu shida abokin tafiyarsa Rabbasu.
Koda jin wannan batu sai Hantaru ayi wa mutanen gidan sallama karshe, ya kama doki ya hau ya tafi izuwa fada yana waugen su Salimat yana zubar da hawaye, suna zub da hawayen suma, masu daga masa hannu nayi haka dai har ya mace masu da gani.
Lokacin da Hantaru ya isa fadar Sarki sai ya iske tuni Rabbasu na zaune a gefe daya cikin gagarumar shigar yaki yana muzurai tamkar zai ci babu, da zuwa sai Hantaru ya wuce gaban Sarki ya zube kasa ya kwashi gaisuwa, sannan ya koma gefe daya ya zauna shima, inda suka fuskanci juna shida Rabbasu.
Koda suka hada ido sai Rabbasu ya daka wa Hantaru harara, wacce inda karamin jarumi yayi wa ita zai iya tsurewa ya kama gudawa, shi kuwa Hantaru sai yayi murmushi kawai ya kawar da kansa ga barin kallon Rabbasu.
Ashe duk abinda ya faru sarki ya lura dan haka shima sai yayi murmushi ba tare da yace komai ba. Nan take sarki ya tura aka kira Gimbiya Larziyya ta zo ta zauna daf da sarki, a wannan lokaci fada ta cika taf da jama'a babu masaka tsinke face inda sarki da jam'arsa ke zaune.
A wannan rana dai Gimbiya Larziyya ta ci ado na gaban kwatance irin wanda ba a taba ganinta da shi ba, kuma ta bar fuskarta a bude sabanin rufeta da take yiko gaishe. Wohoho! Lokacin da Gimbiya ta fito ta nufu inda karagar sarki ta ke tana yin tafiyar kasaita, sai ganadaya jama'ar dake fadar suka zuba mata idanu, kuma take suka dimauce saboda ganin tsananin kyawunta, da yawan jama'a basu san sa'adda yawu ya ka dalala da cikin bakinsu ba tamkar basu taba ganin gimbiya ba.
Hatta Hantaru da Rabbasu ai da suka firgice suka bita da kallo, ko kifta ido basa yi, domin basu san cewa kyawunta ya wuce yadda duk suke zammani ba sai yau. Kai shi kanshi mahaifin nata binta yayi da kallo ya kama wasi-wasi a zuciyarsa yana mai cewa anya kuwa wannan Larziyyata ce, yaya aka yi naga kyawunta ya zarce na kullum a yau?
Abinda sarki bai sani ba shine tsananin kwalliyar data yi ne gami da tsaba adon da ta yi, suka kara mata kyau na ban al'ajabi, domin idan kyau ya hadu da kyau sai idanuwa su kasa banbance wanda yafi wani.
Bayan Gimbiya Larziyya ta zauna kan wata kujera ta alfarma wacce ke kusa da karagar sarki, sai sarki yasa hannu a cikin aljihunsa ya dauko wani dan karamin madubi na tsafi ya ajiyeshi a tskiyar fadar, sannan yayi gyaran murya ya ce ya ku jama'ar birnin Darul Habur, kuyi sani cewa ayau ne masoyan yata Gimbiya Larziyya wato masu neman aurenta, zasu yi gagarumar tafiya dan tabbar da gasa ta karshe a tsakaninsu, domin fitar da zakaran da zai zama mijin Gimbiya, kowa ya sani wannan gasa b komai bace face tafiya zuwa dajin hayatul Maut dan shiga kogon Mazabatul Darshal a dauko takobin Saiful Lujara. Duk wanda ya dauko wannan takobi ya zo da ita tsakanin Hantaru da Rabbasu shine mijin ya ta.
Koda sarki yazo nan a zancensa sai fada ta rude da shewa, sai da sarki ya daga hannu aka yi tsit sannan ya dubi Hantaru da Rabbasu ya ce kunga wancan madubin tsafin dana ajiye a tsakiyar fada? Shine alkalin wannan gasa da xaku tafi, duk abinda zai faru a cikin wannan tafiya zamu gani a cikin wancan madubin saboda akwai dokoki da zamu shimfida maku a yayin wannan tafiya. Duk wanda ya karya doka daya daga cikin dokokin koda ya dauko takobin Saiful Lujara to ba zai auri Gimbiya ba, doka ta farko ita ce;
Babu yaki a tsakaninku, wato ba a yarda dayanku ya cutar da dan uwansa ba.
Doka ta biyu ba a yarda dayanku ya taimaki abokin tafiyarsa ba, abinda ake so shine kowa karfin damtsensa dana sihirinsa ya cece shi.
Doka ta uku wacce ita ce ta karshe wanda duk ya samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara, to kada ya tsaya ko ina face anan fadarmu. Da fatan zaku kiyaye wannan dokoki domin tabbatar da burinku, da wannan furuci nake maku bankwana da fatan samun nasara ga dukkan mai sa'a a cikinku.
Koda gama wannan jawabi sai sarkk yasa aka kosassun dawakai kuma ingarmu guda biyu baki da fari, kowanne da guzuri akansa, ya dubi Hantaru da Rabbasu yace kowanne ya zabi wanda yake so.
Cikin hanzari Rabbasu ya tashi tsaye yaje ya kama bakin dokin ya haye, shi kuwa Hantaru sai ya kama farin dokin ya haye.
Nan take suka jera suna tafiya tamkar abokai suka nufi hanyar fita gari, jama'a na biye da su duu... Kamar kiyasai. Sai da aka raka su Hantaru har izuwa iyakar gari sannan aka tsaitsaya ana kallonsu suka kutsa kai cikin daji. Tun ana kallonsu har sai da suka kule suka bace bat! Hantaru da Rabbasu suka cigaba da tafiyya a jere suna ketawa ta cikin kwazazzabai da duwatsu, sai da suka yi tafiyyar sa'a shida cur dayansu bai ce d dan uwansa kala ba, sannan suka iso bakin wata korama.
Anan ne fa dawakansu suka yi turjiya suka kama shan ruwa, saboda daman sun debo rana kuma sun gaji, su kansu su hantarun sun gaji kuma suna jin yunwa da kishin ruwa, amman saboda dakakkiyar zuciya irin ta mazan kwarai sai suka basar saboda kada suka cewa dayansu ya gaza.
Lokacin da dawakan nasu suka tsaya a bakin gabar koramar suka kama shan ruwa, sai Hantaru da Rabbasu suka dubi juna, bisa ga mamaki sai suka yi wa juna murmushi. Rabbasu yayi gyaran murya ya ce ya kai abokin gaba ina ganin cewa ya kamata mu yada zango anan, domin mu huta kuma dawakanmu ma su huta, dan na lura cewa akwai gajiya a tare da mu.
Hantaru yace kwarai kuwa ka zo da shawara mai kyau.
Nan take duk su biyun sauka kayan su dake bisa dawakansu kowa ya kafa tantinsa, kuma suka bude jakar guzirinsu suka ci kuma suka sha. Bayan sun gama kimtsa cikin nasu ne sai kuma hira ta barke a tsakaninsu, inda Rabbasu ya dubi Hantaru yace ya kai bakon garinmu, kayi sani cewa ina da wata tambaya a gareka, wacce zan so ka bani amsarta bilhakki.
Koda jin wannan batu sai Hantaru yayi murmushi sannan ya ce fadi duk irin tambayar dake bakinka ni kuma nayi alƙawarin zan baka amsa iyakar gaskiyata.
Rabbasu yayi gyaran murya sannan ya ce ina son ka fada mani alakar dake tsakaninka da Salimat yar sarkin makera Shuraim, shin ita ce ta haifeka ko ba ita bace?
Yayin da Hantaru yaji wannan tambaya sai ya cika da mamaki kuma yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai ya ce alakata da Salimat itace ta shayar d ni, amman ba ita ce ta haifeni ba.
Koda jin Wannan batu sai idanun Rabbasu suka zazzaro, kawai sai ya takarkare ya kwarara uban ihu cikin tsananin bakin ciki, ihun nasa ne ya firgita kananun dabbobin dake cikin dajin da tsuntsaye suka kama tashi da guje-guje wasu suna sauya ramuka, nan take kwallar takaici ta cika idanun Rabbasu ya dubi Hantaru yace hakika nayi babban kuskure da banyi cikakken bincike akanka ba, tun a farkon zuwanka garin nan, inda nasan cewa kai ba jinin zuri'ar makera bane da bazanyi wannan gasa d kai ba, da tuni na kashe kaina na da huta da takaici.
Cikin tsakanin mamaki Hantaru ya dubi Rabbasu yace kai kuwa sabida me yasa ka fadi haka?
Rabbasu yace saboda bincike ya tabbatar da cewa babu wani dan zuri'ar makera da ya isa ya samu nasara