Showing 39001 words to 42000 words out of 55369 words

Chapter 14 - MAZAN JIYA Littafi Na Farko Rubuta Labari Abdul'aziz Madakin Gini.txt

wanda ke saman dutse, ta tuno da rayuwarta a gidan tun tana yarinya karama kafin rasuwar matar boka Sulbaini, abinda salimat ba zata taba mantawa ba shine kullum sai sunyi wasan yar boyo ita da matar boka Sulbaini, wani lokacin ma har wasan doki suke yi, ta hau gadon bayan Sulbaini tana sukuwa. A daidai wannan lokacin ne hawaye ya zubo wa salimat taji ace inama zata iya dawo da abinda ya wuce amman ina ai babu dama.
A lokacin da su Hantaru suka iso mararrabar hanya ne, inda ta rabu gida uku; daya zata kaisu izuwa cikin gari, daya izuwa dajin kufainu, dayar kuma izuwa inda suka baro. Sai Shuraim ya nuna wa Hantaru hanyar da zata sadashi izuwa dajin kufairu.
Yace ya kai Gwarzon Sadaukai wannan hanyar ita zaka bi kaje inda gimbiya Larziyya ta ke, maza kaje ku hadu, sannan ka tabbatar ka dawo gida da wuri kafin dare yayi sosai.
Koda jin haka sai Hantaru yayi murmushi sannan ya dubu salimat ya ce zan tafi izuwa ga Gimbiya idan har kinyi izini a gareni ya ummina.
Salimat ta mayar masa da martanin murmushi sannan ta ce jeka abinka ya kai dana, ina goyon baya dari bisa dari.
Koda jin haka sai Hantaru ya zaburi dokinsa cikin farin ciki ya sukwaneshi izuwa cikin dajin kufairu. Yar gajeriyar tafiya hnataru yayi ya iso inda dutsen yake, tun daga nesa Hantaru ya hango gimbiya Larziyya a bisa dutsen a zaune tana sanye da wasu kurayen tufafi, masu tsananin kyau da ban sha'awa ta lullube kanta gaba daya da mayafin kayan.
Koda Larziyya ta hango Hantaru ya durfafo inda take, sai ta mike tsaye, mikewarta keda wuya sai iska ta dauke mayafin data rufe kanta da shi ta yi kasa da shi, a wannan lokacin ne hantaru yayi arba da fuskar Gimbiya Larziyya, tsarki ya tabbata ga ubangijin daya daidaita gabban jikin gimbiya Larziyya, a iya sanin Hantaru ko a bakin ma'abota labarin duniya, bai taba jin wanda ya wassafa mace mai kyau na Gimbiya Larziyya ba, saboda tsananin kyawun fuskarta dana kirar jiki. Idan mutum yayi arba da ita sai yayi tsammanin cewa ba mutum bace aljana ce. Hantaru dai bai san sa'ad da ya ja linzamin dokinsa ya tsaya cak ba, daga kasan dutsen suka kura wa juna idanu suna sun murmushi. Nan take yaji kibiyar so ta sokeshi a kahon zuci kuma yaji cewa a haukansa ko mutuwa bata isa hanashi mallakar gimbiya Larziyya ba.
Cikin natsuwa da tafiyyar kasaita Larziyya ta sakko daga saman dutsen kufairu, tazo daf da Hantaru ta tsaya sannan ta ce lale marhabun da Sadauki uban sadaukai, tauraron zamani mai haska duniya. Ya kai Hantaru ka yi sani cewa yauce ranar da tafi kowacce rana farin ciki a rayuwata, domin a yau nayi arba da masoyin zuciyata wanda na dade ina begensa tun gabanin naga fuskarsa, ina godiya daka amsa gayyata ta bisa muhimmiyar wannan rana ta saduwarmu.
Shin daka ganni a yanzu kaji kana sona, kamar yadda na dade da kamuwa da kaunarka?
Lokacin da Hantaru yaji wannan tambaya sai yaji dariya ta kubuce masa, itama sai ta kama dariyar kamar su duka biyun sun zautu.
Lokaci guda suka daina dariyar kuma suka kura wa juna idanu, Hantaru yq ce yake wannan mafifiyar ma'abociyar kyawun, kiyi sani cewa babu wani mahaluki walau a mutane ko a aljanu da zai ganki bai kamu da tsananin kaunarki ba. Tabbas a yanzu ina ji a jikin cewa zan iya salwantar da rayuwata domin farin cikinki ko domin na mallakeki.
Koda jin wannan batu sai Gimbiya Larziyya ta cika da tsananin farin ciki, nn take rungume hantaru suka kankame juna har izuwa wani lokaci mai dan tsayi, daga can sai ta janye jikinta daga nasa suka fuskanci juna ta ce ya kai masoyina kayi sani cewa yau saura kwana goma sha tara ayi gasar neman aurena, kaine kadai mutumin da zai iya share mani hawayena, ya hana Sadauki Rabbasu samun nasara a wannan gasa, idan har kaunar da kake mani ta gaskiya ce ina so ka daukar mani alkawarika guda uku a yanzu, alkawari na farko shine; duk wuya duk rintsi ba zaka janye takarar neman aure na ba, alƙawari na biyu duk alfarmar da na nema a wajenka zaka yi mani ita, alkawarina na uku kuwa shine a duk halin da muka tsinci kanmu ba zamu guji juna ba, idan har ka amince da wadannan alkawaruka to nima na yi maka alkawari cewa zan sallamar da rayuwata domin ka, kuma har abada babu wani da namiji da zai sanni ya mace face kai, haka kuma duk irin bala'in da zaka shiga zan bika mu shiga tare koda kuwa zan hallaka.
Sa'ad da Gimbiya Larziyya ta zo nan a bayaninta sai Hantaru ya ji zuciyarsa ta buga da karfin gaske, abinda ya fara fado masa a rai ne shine batun alkawarin daya daukar wa mahaifiyarsa, Hantaru ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa anya kuwa alkawarin dana daukar wa ummina ba zai zamo kishiyar wanda Gimbiya Larziyya ta ke so na daukar mata a halin yanzu ba kuwa? Nan fa ya rasa irin hukuncin da ya kamata ya yanke.
Lokacin da Larziyya taga Hantaru yayi shiru bai bata amsa ba, kuma ya sunkuyar da kansa kasa yana tunani, sai ta dafa kafadarsa ta ce kai nake sauraro ya masoyina, wane hukunci ka yanke game da alkawarin da muka daukar wa junanmu.
Hantaru ya dago kai cikin murmushi yace yake abar kaunata kiyi sani cewa kinzo mani da babban alƙawari, wanda yafi gaban na yanke hukunci yanzu take, saboda haka ina neman alfarmar ki bani lokaci nayi tunani.
Koda jin haka sai Larziyya tayi murmushi sannan ta ce na baka lokaci, daga nan har izuwa ranar da za'a fara gasar neman aurena, amman sai kayi alkawarin cewa ba zaka yi shawara da kowa ba, sai da zuciyarka kadai.
Hantaru ya maida mata da martanin murmushi sannan ya ce nayi alkawarin ba xan yi shawara da kowa ba face da xuciyata, cikin tsananin farin ciki Larziyya ta sake rungume Hantaru a karo na biyu sannan ta sumbaci goshinsa. Kawai sai ta tafa hannayenta biyu take wani bawan sarki ya fito daga cikin duhuwa janye da keken doki.
Larziyya ta dubi Hantaru cikin wani irin murmushi mai dagula tunanin da namiji ta ce daga yau ba zamu sake saduwa ba sai ranar gasa, lallai a ranar ne zaka bani amsoshin tambayoyina, da wannan kalami nake maka sallama ya madubin zuciyata, sai lokaci yayi.
Koda gama fadin haka sai Gimbiya Larziyya ta juya ta nufi inda keken dokinta yake tana mai waigen Hantaru, shi kuwa sai ya biya da kallo kawai ya kasa cewa komai har ta shiga cikin keken dokin ta zauna.

Ina yi maku barka da wannan lokaci da fatan kuna cikin koshin lafiya 🙏🙏🙏

Ga masu son Complete Audio na Mazan Jiya Wanda Muhammad Umar Kaigama Ya karanta Ko Kuma Complete Document zasu iya mani magana ta whatsapp 08138873799


Bawan ya kafa linzaman dawakan dake jan keken dokin suka nufi hanyar cikin gari. Tun Hantaru na hango keken dokin har ya bace wa ganinsa, sai da Hantaru ya dade a tsaye yana mai nazari da tunani sannan shima jaye ya hau dokinsa ya nufi cikin gari.
Da isar Hantaru gida sai ya iske tuni Salimat ta shirya masa abinci a ajiye a dakinsa. Bayan Hantaru ya zauna ne ya huta kuma ya ci abinci sai ya fada cikin kogin tunani, ya kasa yi wa kansa zabi bisa amsar da ya kamata ya baiwa Gimbiya Larziyya a ranar da za a yi gasa. Yana cikin wannan hali ne Salimat ta shigo cikin dakin ta riskeshi a cikin halin tunani.
Cikin matukar damuwa Salimat ta zauna daf da shi sannan ta ce ya kai dana na sani cewa ka kamu da kaunar Gimbiya Larziyya domin babu wani da namiji da zai yi arba da ita ba tare d ya fada tarkon begenta ba. Ya kai dana ka fada mani dukkanin abinda kuka tattauna kai da ita, ni kuma zan baka shawara wacce zata fissheka a rayuwa.
Koda jin haka sai Hantaru ya ji zuciyarsa ta buga da karfi ainun, kuma ta gargadeshi akan kada ya fada wa Salimat gaskiyar maganar da yayi da Gimbiya Larziyya.
Hantaru ya dubi Salimat cikin murmushi yace yake ummina kiyi sani cewa babu abinda muka tattauna face kalmomin kauna gami da alkawarin zamu so juna da gaskiya.
Koda jin haka sai murna ta kama Salimat ta sa masa albarka sannan ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin.
Kash! Hakika rashin sani yafi dare duhu, inda Hantaru yasan abinda zai biyo baya bisa boyewa Salimat gaskiyar al'amari da bai boye mata ba. Tabbas zuciya bata da kashi, kuma itace abar dake jefa mutum ga halaka dare daya.
Daga wannan rana Shuraim da Hantaru suka rinka motsa jiki, yana nuna masa yadda ake yin wannan gasa ta tseren gudun kamo barewa a daji, a kullum sai su wuni suna gudu a daji, kuma suna gudun ne a bisa dawakai suna yakar juna domin daya ya jefo daya daga bisa dokinsa. A wannan lokacin ne Hantaru ya tabbar da cewa lallai Shuraim ya cika Sadauki domin yayi mamaki matuka da yaga irin juriyarsa gami da jarumtakarsa wajen shanye duka da kuma zafin namansa na kare sara da suka yayin da suke gudu a kan dokin, duk da cewa girma ya fara kamashi.
Duk irin kokarin da Hantaru ke yi a wannan motsa jiki da suke yi, kullum.sai yaga Shuraim baya yaba masa, domin a kullum ce masa yake ya kai jikana ka kara kwazo domin har yanzu baka yi rabin kwazon da Sadauki Rabbasu zai iya yi ba yayin gasar, nasan yanayin gasar nan kuma nasan sirrinta ciki da bai, sannan nasan iyakar jarumtakar Rabbasu, bugu da kari duk shekara idan za a yi wannan gasa sai Rabbasu ya fito filin gasar ya zuba idanu yana nazarinta.
Tabbas ya fika sanin sirrinta shiyasa nake da yakinin sai ya fika kokari dan har baka kara jajircewa ba, gobe zan gayyato samarin zuri'armu mu fita daji tare domin mu gwada wannan gasa tare da kai, a sannan ne zanga iyakar kokarin da zaka iya yi.
Kashegari kuwa da sassafe samarin zuriar makera suka taru a gidan Shuraim sannan suka dunguma suk tafi daji domin jarraba gasar tseren barewa tare da Sadauki Hantaru. Ai kuwa ana fra wannan gasar sai Hantaru ya raina kansa, domin kuwa kafin ya farga tuni anyi masa fintinkau. Sabida samarin sun kware ainun wajen sarrafa doki, kuma kowannensu ya dade yana hora dokinsa saboda zuwan wannan rana.
Sai da Hantaru ya zamo shine a can baya na karshe, koda ganin haka sai hankalin Hantaru ya dugunzuma, zuciyarsa ta harzuka ya tuno da gwagwarmayar da yayi a baya, ya kuma tuna cewa shifa sadaukine na kwarai, lallai idan bai dage ba ya ci wannan gasa ba, to kamar ya rasa Gimbiya Larziyya ne, kuma ya kasa karbo kambun gasa daga zuri'ar mafarauta wanda shine burin mahaifiyarsa Salimat. Hantaru yace da kansa a cikin zuciyarsa, me zanyi na saka wa da Salimat a rayuwa bisa shayar dani da tayi a matsayin dan cikinta? Kuma ta rikeni amana ba tare da tasan cewa ba dan cikinta bane ni. Abinda zanyi shine ya wanke bakin cikin zuri'arsu gabadaya wanda ya addabi zuciyarsu tsawon shekara da shekaru.
Koda hantaru ya gama ayyana haka a cikin zuciyarsa sai ya kara zaburar dokinsa yayi masa kaimi ya kutsa cikin jaruman gasar nan yana bangaje wasunsu, bisa mamaki sa sai yaga yana matsawa gaba-gaba, sannu a hankali sai da riski wadanda ke kan gaba wasu zakwakuran samari jaruman gaske su uku, wadanda ya kasa wucesu, Hantaru ya dage iya karfinsa yana kai masu sara da suka da mangari, suma suna mayar masa da martani, amman saboda nacinsu sai ya kasa zubar da su a kasa, sai da suka yi doguwar tafiya a haka har suka fara hango barewar da aka saki tana ta tsula gudu ana so su cimmata.
A karshe dai da hantaru da wadannan zakwakuran samarin jarumai uku ragas akayi, wato duk sun banke junansu sun fado kasa daga kan dawakansu, dayansu bai samu nasarar kamo barewar ba.
Al'amarin daya dugunzuma hankalin Hantaru kenan, ransa ya baci kuma gwiywarsa tayi sanyi akan wannan gasa. Amman sai Shuraim ya karfafeshi akan cewar ya kara kwazo nan gaba akwai alamar cewa zai zamo zakara.
Haka dai aka cigaba da wannan gasa ta baiwa kai horo dan tanadin ranar babbar gasa ta ainahi, ya zamana cewa a kullum sau biyu ake yin gasar safe da yamma, sai da ya rage saura kwana daya jal ranar gasar ta ainahi ta zo, a wannan rana ne Jarumi Hantaru ya samu nasarar banke wadannan zaratan jaruman guda uku ya zubar da su kasa, sannan ya cimma barewar da keso a kamo ya cafketa.
Nan fa jama'ar zuri'ar makera suka cika da tsananin farin ciki, domin sun san cewa yanzu kam sun samu Gwarzon da zai karbo masu kambun gasa daga hannun zuri'ar mafarauta.
A wannan rana kwana akayi suna walima, kadede-kadede gami da raye-raye, babu wanda yafi Shuraim da Salimat farin ciki a wannan rana, domin kuwa basu san iyakar dukiyar da suka raba wa jama'a ba.
Wannan shine abinda ya faru a bangaren makera na birnin Darul Habur.

*******************

Acan bngaren zuri'ar mafarauta kuwa lokacin da sarkin mafarauta Zaharu Ibn Dauwar ya isa gida tare da dansa Rabbasu a sume, tare da dukkanin jama'arsu, sai suka taru a cikn fadar Zaharu aka shimfide Rabbasu a bisa wata doguwar kujera, nan take Zaharu ya karanta wasu dalasiman tsafi ya tofa masa, nan take rabbasu yayi atishawa ya farfado, a dimauce ya mike tsaye zumbur yana mai kokarin kai duka, domin shi a zatonsa har yanzu yana fafatawa ne da Hantaru. Bisa ga mamaki sai yaga mahaufinsa tre da jama'arsu a tsaitsaye suna kallonsa kawai. A sannan ne ya dubi inda yake ya gane gida yake ba kasuwa ba.
Cikin tsananin fusata Rabbasu ya dubi mahaifinsa ya ce ya abbana ina abokin fadana yake ne? Yaya akayi nazo nan gida?
Koda jin wannan tambaya sai Zaharu ya bushe da dariya sannan lokacin guda ya murtuke fuska kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa, nan take kuma kwallar takaici ta zubo masa ya ce ya kai dana kayi sani cewa ba wani bane ya zo ya raba fadanku da wannan bakon saurayin ba face babban abokin adawata boka Sulbaini, wannan bakon jarumi ya kasance babban barazana ga zuri'armu gabadaya, domin yazo ne domin ya rabamu da kanbun gasar gudun tseren barewa, kuma shi gimbiya Larziyya ke son ta aura.
Koda jin wannan batu sai Rabbasu ya kwarara uban ihu, wanda ya firgita kowa dake wajen, fuskarsa ta kama kakkarwa kamar zata zazzago ta fado kasa, cikin tsananin fushi ya dubi Zaharu ya ce ya kai abbana ka sani cewa yau shekaru sittin kenan ina tanadin neman auren Gimbiya Larziyya, ka sani cewa ina matukar kaunar Larziyya irin kaunar da in har na rasata to lashakka sai na rasa rayuwata, yaya kake tsammanin cewa zan bari wani yazo ya mallaketa.
Zaharu ya dafa kafadar Rabbasu ya ce ka kwantar da hankalinka ya kai dana, kaima ka sani cewa babu yadda za a yi ina raye a doron kasa hakan ta faru, ina tabbatar maka da cewa yanzu lokaci yayi da zan baka gabadaya sirrinkan tsafina sabanin da dana baka rabi kawai, ka sani cewa abinda yasa ban baka sirrikan tsafina ba, shine kana da tsananin fushi da bakar zuciya, idan ka mallaki sirrin tsafina duka cewa zaka yi zaka yaki boka Sulbaini, duk ranar daka yaki boka Sulbaini kuwa a ranar wannan birni namu sai ya baje kowa ya hallaka. A halin yanzu bani da wani zabi face na baka sirrikan tsafinnawa tunda ni bani da ikon shiga wannan gasa, domin kare martabar zuri'armu da kuma mallakar gimbiya Larziyya.
Abu na biyu dole ne mu baka sabon horo akan wannan gasa, domin ka samu karfi ninkin na da da kake da shi, dan kada abokin gabarka ya samu nasara akan ka, ka sani cewa da mutum dubu uku ake wannan gasa ta tsere, to amma daga yanzu kullum zaka rinka jarraba wannan gasa da mutane dubu shida, lallai indai ka samu nasara akan mutum dubu shida to ba makawa sai ka samu nasara akan abokin gabarka, wato wannan bakon jarumin daya zo.
Koda jin haka sai Rabbasu ya cika da farin ciki. Daga wannan rana aka soma baiwa Rabbasu horo da mutum dubu shida, kuma kullum sau uku ake yin gasar, safe, yamma da dare.
Tun a ranar farko Rabbasu ya rinka banke zaratan dakaru, duk inda ya ratsa ta cikinsu sai dai kaga maza na zubewa kasa, wani lokacin ma har dawakan nasu yake bankewa kasa, saboda tsananin karfin Rabbasu sai da ya lashe gasar nan.
Daga ranar farko da aka fara wannan gasar zuwa ranar karshe kullum Rabbasu ne yake lashe gasar, kuma ko dau daya ba a taba kaishi kasa ba.
Tabbas Rabbasu ya cika sadaukin Sadaukai domin yafi hantaru karfin damtse, a ranar karshe ana gobe za a yi gasar ainihi ta neman auren Gimbiya Larziyya boka Zaharu ya sanya dukkanin sirrikan ttsafinsa a jikin Rabbasu. Nan take Rabbasu yaji wani gagarumin karfi ya shige shi, tamkar zai iya nada gammo a ka a dora masa duniyar gabadayanta. Nan take ya cika da farin ciki, ya ji a zuciyarshi cewa dole ne ko ta halin kakama yaci wannan gasa da za'a yi.
Acan cikin gidan Shuraim kuwa har dare ya raba amman boka Sulbaini bai zo ba kamar yadda yayi alkawari, al'amari daya dugunzuma hankalin Shuraim, Samilat da mahaifiyar Samilat kenan, domin sun san cewa muddin Hantaru bai samu taimako daga boka Sulbaini ba, babu yadda za a yi ya ci wannan gasa akan Rabbasu, saboda sanin cewa dole ne Zaharu mahaifin rabbasu yayi masa gagarumin shiri irin wanda bai taba yi masa ba. Haka dai aka kwanta cikin ta tarrabi da jimami.
Al'amarin Sadauki Hantaru kuwa ko kadan baiji wata damuwa ta shigeshi ba, saboda koda yaushe yana da yakinin cewa indai yana cikin hayyacinsa babu wani tsautsayi da zai taba lafiyarsa. Hantaru na kwanciya sai bacci ya dauke shi, tamkar babu wani gagarumin abu dake gabansa a gobe, daf da ketowar alfijir ne Hantaru ya farka daga bacci, kawai sai yaga boka Sulbaini a zaune daf da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login