Showing 18001 words to 21000 words out of 61257 words

Chapter 7 - THE VIRGIN MAID Hausa Novels by Maman Teddy.pdf

19 Oct 2025

2352

miki Kinji , aiki kawai
zai baki a gidan su , Yana da Mahaifiya mai kirki kuma Sannan yana Ƙanwa wanda nasan zata
ɗauke ki tamkar yar uwa . Share hawayen ki ki bar kuka . Hannu ta sa tana goge Hawayen
fuskar ta . A haka suka ƙarisa Inda moton Omar ke tsaye . Bari nazo .!


Fahad Yayi maganan yana shiga moton da Omar ke ciki .


Ita ba zata shigo bane ba?. Omar yayi masa maganan cikin dakiyar murya . Ni nace ta tsaya .
Farouk kasan menene? Pls duk wani Plan da muka shirya na mugun ta akan wannan Jaririyar
yarinyar mu aje a gyefe , don Allah kayi haƙuri kayafe mata yarinta ne . Taban tausayi . Wani
kallo Omar ya watsa masa ,bai basa amsa ba sai dai gani yayi ya fice daga moton yana daka

mawa Ummu tsawa tare da cewa " Malama Zaki shigo ne ko sai na zo na karairaya ki ,na karya
banza .!


Jin Muryar sa kaman saukar Aradu yasa Ummu saurin yi kaman zata kifa ,jikin ta ne ya ɗau
rawa kar³ , kamin tayi wani motsi Fahad ya fito ,Inda take ya zo yana amsan Aƙwatin hannun
ta tare da buɗe mata mazaunin baya yana cewa " Sorry kar ki tsorata shiga mu tafi . Ba tare da
tace komai ta shiga moton yana rufowa , tare da nufar bayan Boot yana saka aƙwatin nata .
Muryar Omar yaji yana cewa " Ɗan Wahala , Ko son ta kake ne ,sai na baka kuyi kwana biyu .


Kallon sa Fahad yayi tare da cewa " Ƙagan ka da wani magana ,me zan cinta a jikin ta yar
yarinyar nan , ai sai ta kara girma . To na sani Da Allah shiga mu tafi . Allah ya sanyaya zafin
zuciyar nan taka Omar , Abun da Fahad yace kenan yana nufar moton tare da shigewa ,nan
take Omar ya fara driving tare da ficewa daga Asibitin yana nufar Gidan Madam Dr Salma......
****
Tsayawa Daddy Yayi cakkk Yana bin gidan Malam Kadarko da kallo . Wani irin tafasa zuciyar sa
keyi zufa na sakko masa har ƙirji ....nan take ya fito daga moton yana dakatar da Sauran
makararraban sa masu take masa baya . Nufar inda mudi yake mai saida Rake yayi yana
sallama tare da zama babu nuna girman kai ko banbancin girman mai kuɗi da talaka . Sannu da
Zuwa Alhaji wani Abu kake bukata ?. Sauke ajiyar zuciya Daddy Yayi kana a siyasance ya fara
Tambayar Mudi yaran malam Kadarko ,wanda nan take ya fara Rattabo masa . Yana cikin
maganan ne Mom ta fara kirar Wayar sa , wanda nan ya dakatar Da Mudi yana ɗaukar Wayar
Mom tare da sanar mata inda yake . Jin haka yasa Mom cewa kar ya kashe wayar tana Son jin
abun da Mudi zai faɗi . Haka Dad ya Sauke wayar ba tare da ya datse kirar ba yace ina jinka
malam. akwai Auwalu , Akwai Nasiru , Da Ishaq sai kuma autan su mace Wato Ummu . Yarinyar
kirki ,amma izayar da yake mawa yarinyar nan Alhaji wallahi bani kaɗai ba ,har mutanen layin
nan tunani ake akan cewa ,sai kace ba yar cikin sa ba. Akwai ranan da Da Wutan itace yayi
mata lalas yana dukan ta dashi haka abun ka ga farar mace jikin ta duk ya salɓe ko ina ta wuce
sai an ga dukan nan. Yanzu haka Umman yarinyar matan shi kadarkon tayi yaji sakamakon
ɗaukar ƴar Ummu da yayi yabada ita wai acewan shi aikatau ..... Innalilahi wa'inna ilaihir rajiun
shine kalmar da Daddy Ke furtawa kamin yace taimake Ni kayi mun sallama da shi malam
Kadarkon....!




*VIP da mutanen SPC don Allah haƙuri zuwa ranan sati zamu fara maku update Sau biyu a
rana ..na gode.**️THE VIRGIN MAID️*


....Mmn teddy

*C*

*Kiyi haƙuri don Allah Kar ki karanta mun wannan labarin indai baki biyani haƙƙi na ba , Haka
don Allah kar wanda suka biyani su fitar mun na roƙeku ...ga masu buƙatar labarin Womanizing
Boss and the Virgin maid regular group ₦300... VIP group₦500... Special₦1000 via
6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number 08081202932*
***


Cikin Sauri Mudi yake faɗin An gama Alhaji , yayi maganan tare da nufar Soron gidan yayin da
shi kuma Daddy Ke bin sa a baya. A bakin kofar gidan suka tsaya Malam Mudi na shirin ƙwaɗa
Sallama ne suka ji motsin tafiyar daga Bayan su . Umma ne da Wasu Tsofaffi mata biyu ,da
Alama sun dawo da ita ne ,sai kuma bayan su Malam Kadarko . Cikin Girmamawa Daddy ya
matsa yana basu hanya ,don shi sam bai gane ko ɗayan su ba . Sannu Alhaji yau kaine a gidan
namu da ƙafarka? Umma tayi maganan tana gyara zaman mayafin kan ta tare da jah tana
tsayawa a gaban Daddy Jikin ta na Rawa na girmamawa . Allahu Akbar ashe kece matar
Malam Kadarko yi mun sallama dashi . Saurin juyawa Umma tayi inda Malam Kadarko yake
gaba ɗaya ya gama jiƙewa da zufa na zullumi da tsoro . A'a Malam Ga Alhaji ...ehh.ahhh sannu
Alhaji mu shiga daga ciki ....cewan Malam Kadarko yana maganan tare da in Ina . A'a nan ma
ya isa Malam Kadarko bana shigo gidan mata ba da wannan yammacin . Kamin Malam
Kadarko yace wani Abu ne Umma ta amshe Daddy da cewa " Alhaji ka manta kai ka saya mana
wannan gidan da muke ciki? A lokacin da tsohon cikin ɗana na fari , masu haya suka kore mu
akan bamu biya su kuɗin su na shekara ba ,kaine ka bada kudi aka saya mana wannan gidan
,wanda baka taɓa shigar ta ba . Alharan ka ba zamu taɓa mantawa dashi ba ,shigo Alhaji don
Allah . Jin haka yasa Daddy sakin murmushin su ta manya , kamin yace Wani Abu ne malam
Kadarko yayi gaba yana shiga gidan tare da cewa " Bismillah Alhaji .

Ganin haka yasa Su inna Atine tambayar Umma waye Wannan mutumin? Nan ta basu
takaitaccen Labari Akan Alh Ɗan Shuwa . Kamin suyi sallama da ita a soro suna kuma bata
haƙuri akan lamarin Baba Kadarko .


Tabarma Malam Kadarko ya zauna haka Daddy a tsakar gidan , Umma ne ta shigo cikin sauri ta
nufi ɗakin ta tare da Fitowa da sabuwar Ƙwanan sha da ruwa me sanyi a ciki. A gaban Daddy ta
aje tana kuma tsugunawa tare da gaishe sa har ƙasa.kana ta miƙe daga bisani tana nufar Ɗakin
ta .
Ganin tafiyar Umma yasa Daddy Cigaba da cewa " Malam Kadarko abun da mukayi mun
zalunci kan mu , Ƙasa duka yaran nan cikin rayuwar garari , Bazan mu taɓa tona wannan sirrin
ba , saboda Bamu san halin da Beenerfa zata shiga ba , mun bar maka Ƴar tamu halak malak

duniya da lahira , muma muna So kabar mana Beenerfa har Abada.! Wani irin sanyi zuciyar
Malam Kadarko yayi akasin da baya da ya fara tunanin nufar gidan kurkuku . Wani irin matso
hawaye ya fara yi na ƙarya wai ala dole yayi nadama ,kana ya fara magana da cewa" Ku yafe
mun Alhaji nayi kuskure komai ya faru sharrin sheɗan ne , ban....Aaaa Haba Malam Kadarko ai
wannan ya wuce har a cikin zuciyoyin mu . Sai dai ina Son Naga Ɗiyar tawa ta wurin ka , kamin
na wuce ... Jin wannan furucin nasa yasa malam Kadarko saurin kallon Daddy kuma cike da
kame² yake cewa " Ai Omar Farouk yaron ka ya zo yau ƙwana huɗu kenan ya ɗauke ta a
matsayin ƴar Aikin gidan sa.


Kaman yaya ban gane ba.! Cewan Alhaji Ɗan Shuwa cike da Rashin fahimtar inda zancen
Baba ya nufa . Nan take ya feɗe masa biri har wutsiya tun daga samun makarantar scholarship
ɗin da Ummu tayi har marin Omar da tayi ,da kuma yanda yazo nan yace ya basa ita ,shi kuma
ya miƙa masa . Jin wannan maganganun nasa yasa Daddy ɗauke Wuta . A hankali ya miƙe
yana cewa " Tana babu damuwa nasan zai dawo maku da ita ,amma don ALLAH kar mu manta
mu rufe wannan sirrin a iya nan . Ina sha Allah Alhaji . Bin bayan Daddy malam Kadarko yayi
har moton sa ,kamin yayi masa Alherin da ya saba yana kirar Mudi shima yayi masa nasa ,
secutin da yake tare dasu ne sukayi saurin buɗe masa moton yana shiga . Nan take motocin
nan kusan goma sha suka fara barin layin a tare , Yayin da Malam Kadarko ke a tsaye har sai
da yaga wucewan su ,sannan ya sa hannu yana sauke ajiyar zuciya tare da furta " Ƙadsarar ki
kenan Ummu zama a gidana , ita kuma ya ta nata ƙaddarar kenan ta rayu cikin jin daɗi ."


A farfajiyar gidan Alh Ɗan Shuwa Farouk ya aje moton sa kamin ya buɗe ne ya juya yana kallon
Fahad tare da cewa " Fahad Ina da buƙatar Mace yau na ƙwana da ita a gidana ,sam bana
tsammanin zan iya ƙwanan gidan nan yau . Murmushi Fahad Yayi yana sakin Dariya tare da
cewa " Kace kana buƙatar cin durin Ƴammatan naka . To wanne ciki na sanar masu , Hajiyoyin
ko Yara yammata. Tsitt Ummu tayi tana wurga ido ta ko ina jikin ta har a wannan lokacin ɓari
yake yi. Don ALLAH Yaya na ku maidani gida .


Dafe kai Fahad Yayi don ya manta sam da Ummu a moton , Cike da jin kunya tamkar a gaban
ƙanwar sa ya faɗi wannan magana yace " Ayya Sorry my Khairat , Fito mu shiga ciki . Saurin
saka hannun ta tayi tana buɗe murfin moton yayin da suma suke fitowa a daga ɓangaren su .
Tsayawa Ummu tayi tana bin wannan gida da kallo tare da faɗawa Duniyar tunanin wannan
wani irin makeken gida ne , parking lot yafi Guda sha biyu ta ko ina motoci ne kake gani na
zamani sai mala'ikatan gidan ,ciki har da sojoji .... Ɗaga kan ta tayi tana kallon benen gidan ,
kamin daga Sama taga Wani Rubutu tare da zanen love ❤️ an rubuta they're Forever lovers,
Yah Farouk and Anty Rufaida . Sai kuma taga an kuma rubuta Beener & Nurein anyi alamun
love . Tsayawa tayi tana tunanin inda tasan mai irin wannan rubutun wanda tana tsaka da
wannan tunanin ne Taji Muryar Fahad Yana cewa " Ummu Khairat taho mu shiga daga ciki .

Wani irin kallo Farouk ya watsa masa yana masa kallon cewa "Wannan sanaben duk na meye
?. Ganin haka yasa Fahad sakin murmushin babu komai tare da kauda komai da cewa " Farouk
Ashe Nurein Ya dawo daga Span ?. Gyaɗa Masa kai yayi alamun eh kamin ya wuce ciki...Yah
Fahad waye shi Nurein Ɗin ?. Ummu tayi maganan a ɗaɗare dasu duka . Murmushi Fahad Yayi
yana cewa " Ƙannin Farouk ne . Jin haka yasa ta kama bakin ta tana bin bayan su duka .
****
Ɓangaren Daddy Kuwa yana shiga moton sa ya kara wayar a kunnen sa , shashsheƙar kukan
Madam Salma Ke tashi daga ciki , wanda dama yasan tabbas za'a yi hakan tun da duk taji
komai . Kamin yayi mata magana ne yaji tana cewa " Yanzu Ita yarinyar tana hannun Farouk?.
Ƙwarai kuwa yanda Malam Kadarko ya faɗi. Leƙawa tayi ta window tana sa hannun ta tare da
hango farfajiyar parking lot din , okay Ina zuwa ina ganin kaman ga Omar ɗin nan ya shigo
yanzu . Datse kirar tayi tana saurin miƙewa tare da nufar hanyar saukowa daga Up stairs ɗin da
take .

Wal³ Ummu ta gani aljannar duniya irin arzikin da ko a mafarki bata taɓa ganin irin sa ba .
Youuuu??? Taji Muryar Beenerfa tana ce mata tare da miƙewa daga kan Royal ɗin da take .
Juyawa tayi tana kallon Farouk da yake shirin wuce su ya nufi stair Inda Yaga Mom na saukowa
. A wani irin zafafe Beenerfa ta nufo Ummu ,wanda ganin haka yasa Ummu saurin yin bayan
Fahad , Amma Ina fizgota Beener Tayi tana wanke fuskar ta da mari tassssss . Tare da fincike
mayafin kan ta da tayi rolling .Nan take Abun ka ga gashi irin na Shuwa ya barbazo har fuskar
ta ,kama gashin nata tayi tana dukan ta tare da jan gashin tana fizgar gashin kaman zata cire
mata kan duka . Ihu Ummu keyi tana faɗin Don Allah Beenerfa ki ƙyale niiiii....Bazan rabu dake
ba dan uban ki ,yar matsiyan talakawa , marar hankali muguwa.... kasa takawa Momy tayi haka
shima Omar da bayajin zai iya ƙwatar Ummu a hannun Beenerfa saboda abun da tayi masa
yake kullun ta . Fahad ne ke kokarin riƙe Beenerfa amma sai shirme take masa da hauka dukan
Ummu kawai take ya tare da kwalleta da mari....Kee Wacce irin muguwar yarinya ce ? Taji wani
irin Murya na in a Arrogannt voice ya daka mata tsawa tare da fincikar Beenerfa yana wurgi da
ita ɓarayi guda , Dukan da Ummu tasha yasa ta fizagar Beenerfa da akayi tayi baya zata faɗi
,cike da zafi da kuma zafin Nama Nurein ya riƙo ta....!


Ware lulun idanun ta tayi tana zuba su akan Fuskar Nurein ,sai Hawaye sharrr³ . Hannun sa
yasa yana gyara gashin kan ta da ya rufe mata fuska daƙyar take iya ganin su . Wani irin Ƙarar
ihun Beenerfa yasa Nurein juyowa a fusace yana cewa" Ki mun shiru ko nazo na tattaki anan ."
Gummm cike da tsoron sa Beenerfa tayi shiru kamin ta juya tana kallon Mom Salma tana ƙara
rushewa da kuka .

Omar ne ya katse Nurein da faɗin " Tarkata ka bar gidan nan ,ka koma gidan ku , Ina yawan ja
maka kunne akan Beenerfa , ina ruwan ka ,in ma kasheta tayi ai yar aikin gida ce ,ko tana da
abun da zata iya yi ne ,ita ko iyayen ta ?.


Huuuuhhhh Sauke Numfashi Nurein yayi tare da furxar da iska , haushi ne ya Kamasa kurar da

Farouk yayi masa daga gidan su . Cike da kunar rai yace " Ohk Yah Farouk zan tafi gidan mu
,dama nasan ai nan ba gidan mu bane na tafi . Yana faɗin haka ya juya a fusace yana barin
falon . Mom Salma ne tayi saurin kirar sunan Nurein Amma ina bai ma san tana yi ba don yayi
nisa da nufar parking lot .

What's This , All this for What?? Meye Haka Omar? Abun da Nurein ya fadi ai gaskiya
ne....malam kaima jeka Abun ka . Omar ya katse Fahad da yake shirin shiga daga tsini. Beener
kuwa nufar Mom Salma tayi , yayin da Mom ta rungume ta tana shafa bayan ta alamun rarrashi
. Kama ta tayi tana hayewa da ita Up stairs tare da cigaba da rarrashin ta . A hankali Ummu ta
tsuguna a nan wurin ƙwallah duk ya gama ɓata mata fuska . Malam jeka Abun ka .okay Sorry
My boss . Fahad Yayi maganan cike da zolaya yana juyawa tare da barin falon. This is just the
beginning ...yanzu za'a fara ,wannan ba kuka kikeyi ba sai kinyi na jini ...! Omar yayi maganan
yana takowa tare da tsayawa a kan Ummu da idanun ta ke akan Mom Salma da ta tasa yar ta
sukayi na ciki , a zuciyar Ummu cewa take wannan wacce irin uwa ce , da bata Son kowani ɗa
sai nata??? . Tana tsaka da wannan tunanin ne tayi mawa bayan su ƙurrrr da ido , mom Salma
Itama ta juyo tana kallon ta da yanda take a tsugune gwiwowin ta ƙasa tana cigaba da sharce
hawaye..!*️THE VIRGIN MAID️*


....Mmn teddy


*D*

*Kiyi haƙuri don Allah Kar ki karanta mun wannan labarin indai baki biyani haƙƙi na ba , Haka
don Allah kar wanda suka biyani su fitar mun na roƙeku ...ga masu buƙatar labarin Womanizing
Boss and the Virgin maid regular group ₦300... VIP group₦500... Special₦1000 via
6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number 08081202932*
***
Juyar da kan ta Hajiya Salma tayi suna shigewa tare da barin Falon . Juyawa Omar Farouk yayi
tare da faɗin " Wannan ne mafarin yanzu aka fara .! Bai tsaya kallon Ummu ba ya juya yana
saka ƙafan sa tare da ficewa daga Falon . Komawa Ummu tayi tana gyara zaman ta ,tana yin
zaman dirshan tare da sakin marayar kuka wanda babu mai rarrashin ta sai don kan ta ,tayi har
ta gode Allah . Komawa Tayi tana tattare ƙafafuwan ta wuri guda ,ji take gaban ta na faɗi cike
da matsanancin Fargaba ta fara wai gawa gyefe da gyefen ta ganin babu wanda ya kulata a
ma'aikatan falon kowa na aikin sa tare da wuce ta babu mai damuwa da damuwan ta , Ganin
yanayin raguwar Ma'aikatan ya bata tabbacin magriba tayi , lokacin sallah ma ta wuce . Saurin
miƙewa Ummu tayi tana kallon Wata matashiya da ta sauko daga benen tsakiyar falon tana
nufo inda Ummu ke a tsaye . Kece sabuwar Mai aikin sashen Abincin da Sir Farouk ya kawo ?.

Ƙwallah ne ya gangaro saman kuncin ta ,cikin sauri ta gyaɗa kan ta tare da cewa " Eh nice.!
Okay Muje na nuna miki Ɓarayin Ƙwanan mu masu girke². Ba tare da ta kuma cewa komai ba
tabi bayan wannan mata , tafiya taga suna yi mai nesa sosai da sashen Da suka baro , Wannan
yasa Ummu cikin Muryar kuka tace " Baiwar ALLAH ki taimaka mun ki kaini Wurin Shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login