Showing 36001 words to 39000 words out of 61257 words
Beenerfa shima Daddyn ki ne... Kallon Mama Asabe Ummu tayi kamin ta yi mata ido da
ta ci mana zaman me take yi... A hankali Ummu ta É—auki Fork tana fara cin Talia ,Kun san Abun
ka ga Rainon Boko , babu abu mai daÉ—i da ya wuce indomie sai Spaghetti , wannan yasa a cikin
schedule na time table din Kitchen Talia a ko wacce safe ana yin shi da yawa best food din
Beenerfa kenan . DaÉ—i Talian tayi mata ,wannan yasa ta sam mantawa da Daddy dake Wurin ,
SambaÉ—an Abincin ta take ya ,tare da kallon Mama Asabe tana fadin " Mama kin iya girki yayi
dadi sosai na Yau .
Ai kullum ma indai abinci na ne yana daÉ—i , Kedai kawai Kice a yunwa ce kike ...! Murmushi
Daddy Yayi yana jinjina kai ,a Zuciyar shi cewa yake " tana da Saurin Sakewa da mutane .
Ummu wani Position Kika Zo a school din ku...Cak ta ja ta tsaya ,sai ji kake ƙufulll...ƙuful ƙuful ta
ƙware . Don hankalin ta tashi yayi tuno da wannan shine silsilar komai har ƙiyayyar su da
Beenerfa . Shiru ta masa ta kasa magana sai kallon sa da take yi ...Ehemm ina jinki kodai na
baya ne kika zo?. Yayi maganan cike da sokana . Tuntsirewa da Dariya Ummu tayi har tana
kyakyatawa rabon da tayi irin wannan dariyar har ta manta . A'a Daddyn Beenerfa ,Ni nazo 1
position a class din mu Baki daya . Wow' mashaallh yayi kyau , yau idan na fita zan sayo maki
kyautar ta É—aya da kika yi ....BuÉ—e Baki Ummu tayi cike da yarinta tace " Serious Daddy? Eh
mana ai kin yi kokari sosai . Murmushi Ummu tayi tana cewa " Thank you Dad ngd . Murmushi
Daddy Yayi yana miƙewa tare da kallon Mama Asabe yana ce mata" Don ALLAH ki tabbatar da
Ummu tana cin abinci sosai . Cikin sauri Mama Asabe tace " Inshaallhu .
Daddy sai ka dawo , Allah ya tsare ya kiyaye hanya ,ya dawo kai lafiya yanda ka barmu lafiya.
Amin ya Rabb ya furta cike da jin dadin Addu'oi n Ummu a gare shi ....
***
Sojoji ne birjik a ƙame duka suna sauraron Maganan Babban naso wato kanar ne ake fadi da
Hausa koí ½í¸‚ yayin da Captain Omar Farouk ke tsaye a daga gaban su yana fuskantar Kanar
Jabir Baban gida ....Sauran kuma yaran sojojin Omar Farouk na daga bayan sa . Bayani ya
gama yi mawa Omar kamin ,Farouk ya juya yana kallon Sauran taron sojojin ...Cike da Muryar
sa ta matashin Soja mai ji da ƙarfin ƙuruciya ya fara da cewa ". Dajin nan da zamu shiga domin
binciken Abun dake kashe da yawa mutanen dake gyegar Wurin ,ciki kuwa har da Sojojin mu da
dama sun mutu a sanadiyar wannan bincike akan Dajin . Mu sani a yanzu mun amsa Wannan
aiki , tawagata mu zamu shiga Wannan daji ,don musan meye a ciki ,waye abokin hamayyar
Al'umma....numfawa yayi kamin yace " The only thing I remembered you is that , gamu a Zamu
tafi , amma kuma ba lallai mu dawo duka ba ,ina so kowa yasa hakan a ran sa , Sannan abun
da nake tuna maku na biyu shine " Mutuwa a wurin yaƙi wannan wajibi ne ga ko wani Soja
,sunnar yaki kenan . Fatan kowa na tare dani.! Hannun su suka saka suna ƙame masa tare da
sara masa tare da cewa" yesss Captain.!
Juyawa yayi yana kallon Fahad tare da cewa " Kowa yaje yayi shiri gobe zamu dauki hanya in
Sha Allah . Yana gama faÉ—in haka ya juya tare da Fahad Suna barin wurin . Can rumfar su ta
manyan Sojoji ya nufa yayin da Fahad ke cewa " Omar kai a tunanin ka me yasa Sojojin mu da
yawa ke mutuwa a wannan dajin? Shin....Hummmm ban sani ba Fahad ,Amma daga gobe
zamu sani , zan kokarin ganin na Ga karshen wannan Makiyin , mai kashe mutane basu ji basu
gani ba . Fito dasu Zamuyi a masu hukunci yanda kowa zai shiga taitayin su ,idan ma É—an
ta'adda ne ... Cewan Fahad Yana Kallon Farouk dake bude taswirar Nijeriya yana ci gaba da
bincike akan wannan baƙin daji . Wanda yake shirin tunkarar sa babu tsoro .
Kai waye Zai ba Gomnati Wannan mugun ,ai bazasu amshe sa a raye ba ,sai dai a mace ,kai
kasan ƙa'idar farauta na indai a jeji ne , ban taɓa ganin mugu na barshi da gomnati ba ...! Shiru
Fahad Yayi Yana jinjina kai tare da cewa " Ko mun basu ,shekaru ƙalilan zasu sake su ..yanzu
bari naje mu fara shirin mu .
***
Wuraren Karfe Biyu na rana , Mom Salma ne ta fito tare da Beener cikin shigar Alfarma
Atampha ce jikin ta mai ratsin Brown da milk , gyefen ta guda Beenerfa ce da shigar ta irin na
comrade marasa kirki ,dama ita haka take shigar ta irin na turawan England . Shiga ce tayi shi
na kanunun kaya , riga da Wando , tayi rolling da yar karamar mayafi , sai É—auki tabarau
bangajeje Ja tana saka ma fuskar ta ...Tare da dauko irin wannan manyan rigunan masu kama
dana sanyi tana daurawa a sama Turkish switter , ƙafarta kuma cikin Takalmi ne mai rufi , sai
tashin wani irin ƙamshi take yi ....bakin ta ne ke rawa cike da mmkin ganin wannan sauyi take
kallon masu decoration din dirning Area tana cewa " You people what are you doing there?? .
Tayi maganan Mom Salma na amshewa da cewa " Waye ya saka ku sauya Dirning Area daga
kujeru HuÉ—u yanzu ya koma biyar?....
GN
MMN TEDDYP
*Littafin nan na kudi ne Regular group ₦300...VIP group ₦500... Special ₦1000 via 6037312299
Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number 08081202932*
Mom Salma ne ta amshi Beenerfa da cewa " Waya saka ku wannan Aikin ne? Babban sune ya
fara mawa Mom Salma bayani akan Daddy ne yasaka ayi wannan Aikin .... Shiru Mom Salma
tayi kamin ta juya tana faÉ—in " Okay Beener mu tafi ...Zuciyar Beenerfa a dagule cike da rashin
fahimtar inda Wannan gyara na Daddy ya nufa ta bi bayan Mom Salma , a tare suka fice daga
Falon Suna nufar Harabar farfajiyar Gidan , Driver ne ya ƙari ko don ya tafi dasu inda zasu je
,amma nan take Beenerfa ta dakatar dashi tare da cewa " A'a Adamu ka bar shi ,Ni zan yi
driving da kai na ,bana buƙatar kowa . An gama Ranki yadade a dawo lafiya ...ba tare da
Beener ta tanka shi ba ,tayi shigewar ta moton , wanda dama Tuni mom Salma ta dade da
shiga ita Beenerfa take jira . A haka ta yi ma moton key tana yin horn masu gadin suka wangale
tamfatsestsen Gate ÆŠin tana ficewa daga Gidan .
Ƙarfe Uku na Yammaci Daddy ya dawo gidan , yayin da Tun da ya shigo Ummu dake Falo take
jin Ƙara kaman na jiniya , Gyaran Pillows din kujerun Falon take Yi , tare da shirya su inda ya
dace , a takaice tana taya sauran yan Aikin gyaran Falon . Ƙamshin Turaren Daddy yasata
Saurin juyowa ,yayin da Masu aikin suka zube suna kwasar gaisuwan su ...itama Ummu yanda
suka yi tayi ,tana faÉ—in Sannu da Dawowa . Murmushi Alh Abdullahi ÆŠan Shuwa yayi yana
Mawa Ummu alamun ta taho inda yake ...Miƙewa tayi daga Tsugunun da take tana takawa a
hankali tare da nufar inda Yake . Hannun ta ya kama yana jan ta da hira yanda zata saki jikin ta
sosai ,kana ya nufi Under ground room din shi da ita .
Bin falon Daddy take da kallo ,cike da mamakin tsaruwan shi , Wow shine Kalmar da ta furta a
zuciyar ta , Dama falon Daddy yafi na Waje kyau ?. Muryar Daddy taji Wanda shi ya katse mata
tunanin ta ,da kuma zancen zucin da take yi . Ummu zauna anan , Bari na shiga na fito .
Murmushi ta sakin masa tare da gyaÉ—a masa kai ,tana ja baya tare da bin dakin duka da kallo .
Wuce ta yayi yana nufar Inner room din shi .... Yayin da Ummu ta ja baya tana bin babban
Hoton Su duka Familyn da kallo , Beenerfa a jikin Daddy ,sai Farouk dake gyefen Momy tana
riƙe da hannun sa...dukan su fuskar su ɗauke yake da matsanancin Fara'a ,ko ba'a faɗa ba kai
da gani kasan Suna a cikin farin ciki a wannan lokacin .
Me yasa yanzu Momy Salma Bata dariya ne kaman yanda na ganta a hoton nan??. Abun da
Ummu tace kenan kamin ta ɗan taɓe baki na ban sani ba dai . Sai kuma ta juya tana nufar Wani
teddy da ta gani ƙaton gaske irin wanda ake ajewa just for decoration na falo . Hannu ta tasa
tana Murmushi tare da shafa Yar tsanan tana dariya .... Tana a wannan wurin sam bata ji fitowar
Daddy ba, Sai dai jin Muryar sa da tayi yana cewa" Kina Son Teddy bear ne sosai Ummu?.
Saurin É—ago da kan ta tayi tana kallon sa ,tare da wangale masa baki tana dariya tare da cewa "
Ehh Daddy. Okay Taho muje ki rakani Wani wuri . Hummmm... Bin bayan sa tayi tana ƙwance
Mayafin Doguwar rigar ta da ta É—aura a kanta , tare da yafa shi yana sauka mata sosai . A tare
suka fito zuwa babban Falon gidan , wanda yan Aikin kowa baki bude yake kallon Ummu da
Kuma Daddyn, kowa da tambayar da yake a cikin zuciyar sa . Meye alaƙar Ummu da Daddy?
Shine tambayar ta kowa . Nufar farfajiyar Gidan Suka yi yayin da cikin Sauri Excourt din Daddy
suka rufa masa baya wasu na yin gaba tare da buÉ—e masa moton Ummu yasa ta fara shiga
mazaunin baya ,kamin shima ya shige suna rufo ƙofar Securities na biyo bayan su , Driver ne
ya shigo kamin yace " Alhaji ina muka nufa yanzu ?. Joy Mall ". Kallon Sa Ummu tayi kamin
tace " Daddy me zamu yi acan ?. Zaki É—auki duk abun da kike so ne ,sai na siya miki . Shiru
Ummu tayi kamin tace " Daddy me yasa to? Beenerfa zata yi faÉ—a fa.! Ko itama zaka siya mata
ne?.
Murmushi Daddy Yayi cike da jin tausayin Yar nashi kana yace " Eh itama sai ki zaɓa mata nata
. Kallon sa tayi tana dariya cike da jin dadi kamin ta juya tana kallon gyefen hanyar da suke
wucewa ...!
***
Mom Abun da kika yi baiyi ba , Ummu itama Æ´ace fa , Aihuwar ta akayi ..bai dace kina
rinƙa....Ya isa.! Nace ya isaaa...!! Na zageta ka rama mata ,idan ka isa, ƙarikon So da ƙauna tun
da na ɓata mawa Habibty n ka Rai ,nima ka ɓata mun sai zuciyoyin ku yayi sanyi kaji Ko Nurein
? Me kuma ka tsaya yi eyye ...? Mom I'm sorry ,ba Haka nake nufi ba...Ya kake nufi eyyeee
,dama nasan yace , Amma ba kaman namu ya'yan ba , ita baka ga tsitson da ta fito ba , Tsitson
talauci , ba kaman kai ba , Wanda Idan ka so Rana ba zai taɓa jikin ka ba , hakan kuma zai
yiwu ,amma su kuwa fa ,talakawa dole Rana ta zama masu tamkar AC É—in da kai a yanzu a
cikin ta kake ... Dole suyi mana ƙwadigo mu kuma mu biya su ,haka Allah ya tsara masu nasu
rayuwar a duniya suci wahala , a kuma lahira idan basu yi aiki na mai kyau ba ,Suma suci
ƙaniyar su....Mu kuma life Destiny namu shine muji daɗi anan muji acan shima.... Kaga muna
ba talaka kudi a matsayin Zakka ,muje hajji muje umra mai yayi saura mu kuma yi ibadan nan
da aka turo mu duniya domin ta ... Don haka ka fahimta aƙwai babbancin ƙwarao tsakanin ka da
Wancen yar matsiyatan....ko hannun talaka ka taɓa zakaji kaushi ne tamkar Bayan Bushiya ....
Kallon Mom Zeena Nurein ya tsaya yana yi cike da rashin jin dadin furucin nata ...Muryar ta ya
kuma tsinkaya tana cewa " Har yaushe ka daina kyamatar talaka ,kaida Abincin yar aiki baka ci
sai dai Ni na dafa maka , baka so inda kake talaka yazo ,amma a yanzu kace kana Son Æ´ar
matsiyata Æ´ar Mai gadi a rana?. Yaushe ka sauya haka Nurein?.
Mom daga Lokacin da nayi ido Biyu da Ummu ,ki sani gaba É—aya life style É—ina ya sauya , Ki sa
a Ranki ba Wancen Nurein É—in ne a gaban ki ba ,mai kyamatar talakawa a yanzu yar talakan
nake So.! Ina Son Ummu ,ita kuma zan Aura Inshaallh . Kiyi haƙuri Mom Zan sanar da Dad
yanzu.! Ba tare da ya jira jin na bakin Mom Zeena ba ya juya cikin sassarfa yana hayewa up
stairs Inda Falon Daddyn Sa yake ....
***
Zaune ya hango Alh Ahmad ÆŠan Shuwa ,wanda ya kasance Mahaifin su duka , Wato Omar
Farouk da kuma shi Nurein Ɗin , Sai kuma ƙaramar su Wato Saratu ,wanda ta ci sunan kakan
su ,suna kirar ta da Saraaa. A yanzu haka tana Ƙasar Spain a can take Digiri ɗin ta na farko
kuma itace Autan su....Mom Zeena tana kirar Nurein da É—a É—aya tilo ne ba don komai ba ,don ta
cire Omar a cikin ya'yan ta , tuni ta bada shi Ga Mom Salma , halak har Abada . Sosai suka
shaku ita da Nurein , shine abokin hirar ta , abokin koman ta ,Son É—an nata take tamkar rayuwar
ta . In ba Ka sani ba ,ka É—auka shine kadai dan ta a duniya , in ba an faÉ—a maka akwai mace ba
,wato Saraah.
Nufar inda Alh Ahmad Shuwa yake yayi yana zaune idanun sa cikin farin tabarau medical eye
glss , Yana duba magazine É—in dake a gaban sa ..ko ba'a faÉ—a maka ba kai dagani kasan sune
yan sahun farko a boko , sosai girma ya fara kama shi ,don ya kai shekaru kusan 68 a duniya .
A kasan carpet din Nurein ya zauna yayin da Dad É—in ya É—ago Kan sa yana cewa " Aa Babban
mutumin ya dai me ya faru kuma na ganka haka babu walwala?. Hummmm.... Nisawa Nurein
yayi kamin ya É—ago idanun sa da suka kada kaman zaiyi kuka yace " Daddy Ummu nake So.!
A'aahhh Dad yayi maganan cike da mamaki kamin ya aje magazine É—in yana sa masa Dariya ,
Haba Nurein To wacece Ummun ita? Ko an kasa ka ne , Ummun tace bata yi kazo nan zakayi
kuka???. Yayi maganan cikin nuna Caring É—in sa ga É—an nasa ,cike kuma da Zolaya wato shi
mutum ne mai barƙwanci . Murmushi Nurein yayi yana ɗan jin sanyi a zuciyar sa , kamin yace "
A'a Daddy ita Bata ce bata So na ba , mom CE tace Bata Son ta ,Wai ba zan Aure ta ba .
Shiru Daddy Yayi kamin yace " Wacece Ummun waye iyayen ta ? A kuma ina suke ?. ÆŠan cizan
laɓɓan sa Nurein yayi kamin yace " A'a Daddy ita ba yar kowa bane ba , Basu da kudi ,yar
talakawa ce ,shi yasa mom tace Bata son ta ...Kuma Dad Ni Ina Son Ummu , wallahi idan ban
Aure ta ba mutuwa zanyi .....Ai ko sai dai ka mutun ,don baza ka Auro mun gayyar tsiya ba ,
Talaka ai gayyar tsiya ne....Su kaji Muryar Mom Zeena dake shigowa ...kayya ..! Zeena meke
faruwa dake ne? Haba wannan maganan bai dace ta fito daga Bakin ki ba ...
Daddyn Nurein dole na fadi haka , da fari yarinyar bata da wani abu da zanji eh zan iya suruta
da ita...Matsayin karatu secondary . Iyayen ta Talakawa both side Uwa da uba . Haba Daddy ba
zan bari wannan Abu ya faru ba...Ya alkawarin auren ku da Beenerfa?? Eyyeee?? Kuma baka
ga Yarinyar ba ,da gani a ƙwai yunwar talauci Babu abinci, Sannan ba auki shi fa kalle shi ƙaton
mutumi dakai kaga Yarinya Teenage girl kana wani maganan Aure ,kashe ta zaka yi ne idan ka
Aure ta ko mene??.
Huuuuu haba Hajiya Zeena wannan ba magana bace ba , Yana Son Yarinya dai ko , to ba zai
taba bari ya cutar da ita ba , Don haka yaje idan ya shirya Auren su da kuma zama dasu duka
,ita Ummun da kuma Beenerfa yayi mana magana a kowani lokaci , a shirye nake nayi masa
Aure dasu duka ,sai a hada dana Farouk da Mufeedarh . Allah ya kyauta ya kuma kiyaye mu ,
ya tsare Ni Ni Zeena .! Nurein..!! TA kira sunan Nurein babu alamun wasa a tare da ita . Ka je
kayi shawara ,indai kana Son Kan ka da arziki . Tana faÉ—in haka ta juya fuuuuu tare da barin
Falon . Kallon Daddy Nurein Yayi idanun sa sun yi jahhh ,hakan yasa Daddy ƙwantar Masa da
hankali tare da masa Alƙawari n Aura masa Ummu , a nan kuma take ya daga Wayar sa yana
kirar Alh Abdullahi Shuwa ,don suyi maganan Auren nasu duka . Cike da jin Dadi Nurein ya
tashi yana godiya tare da nufar bangaren sa don ya watsa ruwa yaji sanyi ,kana ya nufo gidan
Mom Salma don Yaga nur ƙalbi ɗin tasa .
Kaiwa da komowa Mom Salma keyi yayin da Beenerfa ke tsaye tana bin Asabe da wani irin
kallo , kamin Momy tace " Shi Daddy É—in ne suka fita da Ummu??. Eh Hajiya sun É—an jima da
fita . Hummmm numfasawa Mom Salma tayi