Showing 33001 words to 36000 words out of 61257 words

Chapter 12 - THE VIRGIN MAID Hausa Novels by Maman Teddy.pdf

19 Oct 2025

2332

tana ɗaga Ƙwanon Jaloap rice ɗin . Amma sanin kan ki ne ina da ci sosai .
Sa Dariya Ummu tayi tana cewa "Ƙwarai kuwa Mama Asabe na sani ,kefa har cikin Dare tashi
kike yi kina cin Abinci ... Dariya Asabe tayi tana cewa ":Shakiyiya maza ki ci , sai ki ƙwanta kiyi
barci , Don har yanzu ana can ana kai ruwa Rana da Wancen fitinanniyar Beenerfa ɗin ....Tana
ta rigima su Hjy Salma na aikin rarrashi ,don haka ki ƙwanta yau kar ki fito sam ,sai zuwa gobe
,nasan komai ya mutasa . Gyaɗa kai Ummu tayi tana yin shiru kaman ba itace mai wannan
barkwancin ba?.

***

A washe gari , wuraren ƙarfe biyu na rana , gidan sai kaye² ake yi ,kowa ka ganshi yana a bakin
aikin sa , Ko ba'a faɗa maka ba ,kai kasan an yi babban baƙuwa . Ɓangaren Ummu dake can
Part ɗin su tana zaune a dakin su , Asabe ta shigo ranta a dagule , kallon tausayi tabi Ummu
dashi kamin tace " Ummu taho muje ki tayani Aiki a part din Hajiya Salma ,munyi Baki yau ...
Murmusawa Ummu tayi a sanyaye ta bi bayan Asabe zuwa Falon . Wani irin babban Dirning
room suka shiga tare da Asabe ,inda ta hango Hajiya Salma , Mom Zeena gyefen ta Beenerfa ,
sai Farouk da idanun sa ke akan Wayar hannun sa , Gyefen Mom Salma kuma Nurein ne da
gaba ɗaya hankalin sa ke akan hanyar da Su Ummu ke shigo ita da Asabe....!

Alamun miƙewa Zaiyi Mom Salma tayi saurin cewa " Ina kuma zaka je , Zauna mana.!
Murmushi yayi idanun sa na akan Ummu dake ƙariko cikin sanyin Murya tace " Barka da Rana
." Brk Ummu yau baki taho da Safe ba , barci ne kika yi??. Mom Salma tayi maganan cike da
sokana...bayan ita babu wanda ya tanka , sai Nurein dake murmushi yana kallon Ummu ...
Sunkuyar da kan ta tayi ƙasa don bata Son haɗa ido da su duka , Asabe ne tace " Umma fara
srving ɗin kowa .... A hankali Ummu ta matsa tana kai hannun ta tare da Fara Buɗe plstic Bowl
ɗin tana fara aje Plate a gaban Binafa don tafi jin tsoron fitinan ta .... Fatan Irish ne da kifi ta fara
zuba mata , tana aje mata ruwa da lemu a gyefen ta....Haushi ne ya kama Beenerfa ,wanda
kamin Ummu tayi Aune gani tayi Beenerfa ta ɗauki Plate ɗin faten Irish din tana yaɓo mata a
jikin ta duka har Plate din ....Cikin Sauri Ummu tayi baya tare da yin narai narai da ido ƙwallah
na ciko idanun ta ,cike da sanyin Muryar ta tace " Beenerfa What's This? Me nayi miki???. Uban
ki kikayi mata.! Cewan Mom Zeena tana yarfe hannu na bala'i .
Miƙewa Nurein yayi yana nufo inda Ummu ke tsaye....!M²T
MAMAN TEDDY COLLECTION
Dealers in All kind of Supplements natural herbal with Zero chemical Reactions such As: Breast
Elargement ,Hips elargement , slimming capsules ,body Whitening capsule and more...;
Contact us via this number 08081202932 M²T come 1 come All️
*Littafin nan na kudi ne , Regular group ₦300... VIP group₦500... Special₦1000 via
6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number 08081202932
ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biya Ni ba Don ALLAH*

M
Hannu Nurein yasa yana riƙo Hannun Ummu tare da dafa ta yana shirin yin magana ne Mom
Zeena ta daka masa tsawa cikin Muryar tijara ta ke faɗin " Nurein Meye kake yi haka? Okay
dama maganan da maganan da yazo mun a kan ka gaskiya ce kenan?. Mom... Don Allah ki
fahimce Ni , Niiii...Ya isa babu abun da zaka faɗa mun ,sai dai umarni ɗaya da zan baka shine
kayi gaggawar cire yarinyar nan a zuciyar ka , Don ba zan lamunta wannan shashancin ba...
Idanun Ummu ne suka karkaɗa , cikin sauri ta janye hannun ta daga na Nurein da ya riƙe mata ,
cikin Sanyin Muryar ta ta kalle su duka kamin a sanyaye tace " Kuyi haƙuri ... Eyyeee..! Lallai
wannan yarinya ta samu wuri ,ji idon ta ƙyar³ a cikin idanun mu ,babu alaman shakka ko tsoron
mu ,wai muyi haƙuri ....Waye Uban ki meye sana'ar shi ? Kuma sannan Ke a wani matakin ilimi

kike da har kike ƙoƙarin haɗa kafaɗa da Ɗana wanda yake da Masters degree ....Nawa Uban ki
ya tara??. Pls Mom Stop.!!! Nurein Yayi maganan cike da jin Zafin Maganganun Mom Zeenatu
akan Ummun , Wanda Beenerfa da daɗi ya gama cikata , tsayawa tayi tana bin Ummu da wani
irin kallo na sama da ƙasa zuciyar ta fari ƙal". Cike da rashin Karsashi Mom Salma ta kalli
Hajiya Zeena tana cewa " Abi a hankali Hajiya Zeena komai zai....A'a Hajiya Salma magana ce
ta gaskiya , Sam ba zan amince yaro na ya Auri Yar matsiyatan talaka ba...Ai Auren ƙwarya tabi
ƙwarya muke yi ...ina mu ina talaka...!

Kamin wani ya kuma magana ne Omar Farouk ya miƙe tare da aje spoon din yana cewa " Mom
Da misalin 11am zamu wuce jaji daga can zamu tafi inda za'a muje domin binciken ....
Hummmm sauke numfashi Mom Salma tayi kamin tace " Okay Allah ya kuma tsarewa Son A
dawo lafiya ..."
Cike da takon sa na ingarman Soja Ya fara takawa tare da barin dirning room din .....!



ManageN




*Littafin nan na kudi ne Regular group ₦300...VIP group ₦500... Special ₦1000 via 6037312299
Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number 08081202932*


Jikin Ummu ta ko ina Rawa yake yi , Maganan sa taji kaman na mai raɗa ,wanda duk girman
wurin babu wanda zai iya jiyo Abun da Taji kunnuwan ta Farouk na faɗa mata sai ita kaɗai , Ina
Son Ɗayan Amma ba Wannan ba.! Wuce ta yayi yana barin dirning Room ɗin ,babu wani
Damuwa a tare dashi ... Mom Salma ne ta kalli Ummu tana kawar da kan ta ,babu alamun nuni
ga tausayawa ko kan cin mutuncin da sukayi mata tace " Asabe tasa ta ku tafi ,idan ina bukatar
wani Abu zan saka a kirawo ki ... Cikin Sauri Asabe ta kama hannun Ummu suna barin falon .
Kamin Shima Nurein A fusace ya mike yana barin falon ,ransa a matuƙar dagule akan Abun da
Mom Zeena tayi mawa Ummun ita da Beener .

***


Wani irin kuka Ummu keyi mai ban tausayi da taɓa zuciya , gaba ɗaya a ƙwana ɗaya zuwa biyu
ta gana ficewa daga natsuwar ta ,komai a daburce take yin sa ....cikin dasasheshiyar Murya na
wanda yayi kuka kuka kaman ran sa zai fita take cewa " Me nayi masu suke Son Kullum sugan
Ni cikin rashin walwala? A wata ɗaya baya izaya ɗaya na sani tun farkon Rayuwa ta ,amma
kuma a yanzu ya linku zuwa linkin linki izaya na mutane da ban daban , ba zan iya Ba ya

Allah....Zubewa take shirin yi ,don duhuwa ta fara gani kan ta na mata wani irin bugu ,yayin da
idanun ta ke rufewa..... Innalilahi wa'inna ilaihir rajiun Ummu..! Ummu...Shine kalmar Da Mama
Asabe tayi tana riƙota jikin ta ba tare da ta bari tayi ƙasan ba... Ɗaukar ta tayi cakkk don Mama
Asabe irin matan nan ne gija-gija Wanda Sam duk girman jikin su basa jin nauyin shi, Aƙwai
Zafin nama Kaman ba mata ba ,basu da Salɓi ko kaɗan .

A saman Katifan Ɗakin ta ƙwantar da Ummu tare da Saurin ɗaukar Mafici tana mata firfita ,tare
da shafa fuskar ta tana kirar sunan Ummu ...kusan mintuna biyar ta ɗauka bata san Inda kan ta
yake ba ,sai dai tana iya juyo Muryar Mama Asabe .... Ummul khairy buɗe idanun ki kinji." Ta
ƙare maganan tare da ɗan shafa mata ruwa a fuskar ta ,cikin sauri Ummu tajah wani irin ajiyar
zuciya ,tare da yin zumbur tana miƙewa daga Zaune ... Pls Beenerfa live me alone pls ,me nayi
maki??. Ƙwallah ne ya zubo mawa Mama Asabe cike da jin Bala'in tausayin Ummu ta yi saurin
dafa kafaɗan ta tare da cewa " Ummu babu ita anan ,nice Maman ki ,mama Asabe juyo ki kalle
Ni ..." A hankali Ummu ta juyo tana ƙara Ware idanun ta akan Fuskar Mama Asabe ,kamin ta
saki Kuka a maraice tace " Mama Pls What did I do for them? Me nayi masu ? Me nayi masu Ni
Ummu??. Hannu Mama Asabe tasa tana shafa kan Ummu tare da cewa " Kiyi haƙuri Ummu
Kinji , Duk ɗan aiki yana fuskantar dama Wannan matsalolin , Walau ya samu soyayya ko kuma
ƙiyayyar Yaran gida...Yanzu faɗa mun mene kike ji a tare da ke? Ina yake maki ciwo.?


Hannu Ummu tasa tana ɗago na Mama Asabe tare da ɗaura shi saman ƙirjin ta , Mama nan
yake mun zafi , ina tunanin yunwa nake ji ,zanci Abinci ... cike da jin tsoron Saitin bugun zuciyar
ta da Ummu ta nuna mata Mama Asabe tace " sha ruwa sai kici abinci , ki goge lissafin kowa a
zuciyar ki ,koda kuwa ɓata miki rai akayi Kinji Ummu na?. Gyaɗa kai Ummu tayi tana jan jikin ta
daga na Mama Asabe tare da komawa tana ƙwantawa a saman Katifan har kuma Wannan
lokacin Zuciyar ta bai daina mata zafin da take ji kaman ana watsa mata ruwan zafi ba...

***


A wannan Rana ne Farouk ya koma barack ɗin su...Abun da yaba Mom Salma Mamaki shine
,kamin ya tafi da yake sanar mata cewa " A dawo da Ummu cikin Part ɗin ta ...empty Room ɗin
nan dake passing din na Beenerfa a gyara mata ta koma nan da zama ,kamin ya dawo .
Wannan sosai ya jefa Mom Salma cikin tunanin furucin nasa . Wanda wuraren yammaci tasa
Mama Asabe ta dawo da Ummu nan Part din nasu , Sam Mom Bata bari Beenerfa ta sani ba ,
har sai da tazo ƙwanciya , Anan ne tana Rarrashin ta ta faɗa mata . Duk da shakkar Farouk da
take yi ,amma sai da tayi masifan ta iya Son ranta da koke koken ta , a cewan ta ita kawai ta
tsani Ummu ne . Haka mom tayi ta rarrashin ta har ta samu tayi barci kana ta mike tana kashe
mata hasken Bedroom tare da fitowa . Wuce Bedroom Din Ummu da aka bata tayi , tare da
shirin nufar Down Stairs na falon ,don Ɗakunan nasu yana Upstairs ne su . Har ta fara Sauka
Stairs ɗin sai kuma ta juyo tare da nufar Dakin da Ummu ke ciki .... Tsayawa tayi a jikin ƙofan
tana kai hannun ta tare da murɗa Handle door ɗin sai kuma ta saki a hankali tana juyawa tare
da nufar Window inda zata iya hango Ummu daga ciki .... A zaune ta hango ta a tsakiyar Gadon

tasa Hannun ta biyu ta rafka uban tagumi ,da ganin ta ko ba'a faɗa maka ba , kasan tana
kyewar abubuwa da dama ...ciki kuwa har da rashin kulawar Uwa ... Tsayawa Mom Salma tayi
kusan Na mintuna Biyar tana a tsaye , ji take kaman taje itama ta rarrashe ta ,ta sata tayi barci
sannan ta fito , amma kuma sam zuciyar ta ta kasa yin hakan... Ɗiyata nake ji...Saboda nafi Son
Beener ,nafi Son Farin cikin ƴata gaskiya ...' juyawa Tayi tana sakin cotton din Window Glass
din tare da barin wurin ....


Itako Ummu a haka ta zauna har kusan 11 na dare , tana tunanin Abubuwa da yawa ,ciki har da
Umman ta , Nayi kyewar ki Umma na , Yaushe xan gan ki ? Yaushe zan dawo gida ,mu cigaba
da rayuwar mu...Kuka ta fara yi har da jan Su Ajiyar zuciya ita dai kawai burin ta Taga Umma . A
haka tana a zaunen ba tare da ta ƙwanta ba ,barci ya fara fizgar ta ....Wanda a hankali taja jikin
ta ,tana ƙwantawa .

Ɓangaren Umma itama haka yake ,tun da Ummu ta bar gidan barci yayi mata ƙaura a idanun ta
,kullum bata iya barci sai dai nafila da salloli tana kai kukan ta zuwa ga mahalicci , don ita har a
yau bata san meye gaskiyar al'amarin ba .!


***

Da safe ne bayan Mama Asabe sun kammala aikin hada karin kumallo , Beener Mom da Daddy
duka suna zaune a dirning Area , mama Asabe cike da Girmamawa kan ta a ƙasa take cewa "
Hajiya Bara na taso Ummu , Don yarinya ce bata tashi da wuri ,kullum sai na tashe ta , Don
ALLAH Kuyi haƙuri da baku gan ta a bakin aikin ta ba." Shiru Duka suka yi mata ,har beener
dake jifan ta da wani irin mugun kallo , don a yanxu har da ita Asaben take jin haushi .
Jin shirun nasu yasa Mama Asabe saurin raɓawa tana wucewa tare da nufar Bedroom din
Ummu ta take acan tun da ta farka motsi ta kasa yi....Sai tunani barkatai take yi a kan zaman
nata da kuma rayuwar ta na cikin wannan gida .


Murɗo Handle door din da akayi yasata saurin ɗago kan ta tana kallon mai shigowa . Mama
Asabe kin tashi?. Allah ya tashe mu Ummu.' me yasa baki watsa ruwa ba ,gaki kuma ga Toilet .
Kallon Mama Asabe Ummu tayi idanun ta duk sun kumbura saboda tsaban kuka , a hankali ta
furta " Na shiga ciki ,ban san ya ake amfani da koman privacyn bane . Ayya muje na koya miki.

A tare suka shiga Toilet din ,yayin da Mama Asabe ta koya mata abubuwa da dama na amfanin
wurin , wanka tayi tana dauro Alwala ,duk da Mama Asabe sai faɗa take yi mata akan Ta
makara bata yi sallah ba har rana ya fito . Shiru Ummu tayi bata tankata ba har sai da ta gama
sallahn ta kimtsa sannan ta kalli Mama Asabe da suke shirin fitowa zuwa falo tana cewa " To
laifin waye Mama Asabe da Banyi sallah ba , kene Mana Tun da ke kika kawoni nan Ɓangaren .
Yanxu dai kina so Kice laifina ne ? Shrkaranki nawa ne?? Kin isa hukunci a shari'ar Musulunci

... A haka suka isa Dirning table ɗin inda Su Daddy Ke zaune a yau su uku ne ,babu Farouk
babu Nurein . Momy ina ƙwana .! Daddy Ina ƙwana". Cike da Harka wanda Mama Asabe sakin
baki tayi don bata taɓa ganin Daddy cikin wannan yanayin ba ya amsa Ummu da cewa "
Morning dear daughter ,Kin tashi lafiya?. Barcin yau yayi yawa, Jiya bakiyi barcin da wuri bane
ba?. Gyaɗa kai Ummu tayi tana murmushin nan nata , don ita kun san ta ma'abociya fara'a ce ,
nan da nan ta watsake tana fara cewa " Eh Daddy , Gashi yanzu na tashi ,dana shiga Privacy
na kasa amfani da komai ban iya ba , Sai da Yanzu Mama Asabe ta koya mun , ban yi Sallah da
wuri ba , ai Daddy laifin Mama Asabe ne ba laifi na ba , Allah ba zai rubuta mun zunubi ba , tun
da itane bata zo da wuri ba .... Dariya Daddy da Mom Salma suka saka , mama Asabe dai shiru
tayi itama tana murmushin jin wannan wauta irin na Ummu .... Kamin suyi magana ne Ummu ta
juya tana kallon Beenerfa dake ta tuƙuƙi tana cewa ' Beenerfa kin.... Keeee! Shut up.! Kar ki
kuskura kimun magana ,im I your Mate?.


Shuru Ummu tayi tare da Girgiza kan ta tana cewa " Sorry . Hannun ta takai tana shirin fara
gyara zaman abucucuwan Wurin , Sai taji Muryar Daddy na cewa " Ummu zauna kema a yanxu
Farouk ya yan taki yace ba yar aiki bace ba , baki ga Har daki ya baki ba...zauna muyi break
tare ....Shiru Momy Salma tayi sam maganan tasa bai mata daɗi ba , kallon Beenerfa tayi
wanda itama Daddy take kallo . Ban fahimta ba Daddy wacece ba ƴar Aikin ba? Wannan dai
yarinyar?? To ta koma gidan uban ta mana...!


No Beenerfa Ba ƙawar ki bace ,kinga idan kun koma school sai kuna zuwa tare da ita...! Wace
wai? Ni zan je da wannan yar talakar School Dad? Allah ya mun tsari , ta tashi ta bar wurin nan
,ko kuma Ni na tashi ....Tsayawa Daddy Yayi yana mamakin ƙiyayyar dake tsakanin Beener da
kuma Ummu . Kamin yayi magana ne tuni ta mike tare da barin wurin ...ganin haka yasa Mom
Salma Itama miƙewa tana bin Daddy da Ummu da wani iri kallo , Wanda yasa Ummu saurin
sada kan ta ƙasa , jikin ta duk yayi sanyi . Barin wurin Momy Salma tayi tana bin bayan
Beenerfa ....!



*AISHA MMN TEDDY*O




*Littafin nan na kudi ne Regular group ₦300...VIP group ₦500... Special ₦1000 via 6037312299
Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number 08081202932*


Bin bayan Mom Salma Ummu tayi da kallo ,kamin ta ɗaga ƙafarta tana shirin barin wuri ne taji
Muryar Daddy Yana cewa " Ummul khair dawo ki zauna , Ni ai nace muyi break tare ...kuma

daga Yau Can Bedroom ɗin da kika ƙwana nan ne ɗakin ki , lokacin da kowa ke a dirning Area
kema ki tabbatar kin taho ayi dake kina jina ? . Yayi maganan yana ware idanun shi a kan
Ummu wanda ta tsaya tsumi ,wannan fara'ar nata Duk ya ɓace daga fuskar ta a lokaci guda .
Gyaɗa masa kai tayi a hankali ,kamin Daddy yace " Good zauna anan ki saki jikin ki kinji , Ai
Daddyn

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login