Showing 48001 words to 51000 words out of 61257 words

Chapter 17 - THE VIRGIN MAID Hausa Novels by Maman Teddy.pdf

19 Oct 2025

2333

ground . Murmushi Farouk yayi kamin yace " Okay mam .
Cike da takonsa na matashin Soja yake takawa cikin sassarfa yana nufar Part din Momy Salma
.
Cike da matsanancin Farin ciki ya fara wuce falon gidan yayin da ma'aikatan ke gaishe sa
amma da yake baya ta kansu ,mutum biyu ya kosa ya gani Ummu da Momy , don sun fi watanni
Hudu basu haɗu ba , Ta dawo gidan da kwana biyu yayi tafiyar su ta sojoji sai a yau ya dawo .
Yana shirin bin lifta zuwa under ground na ga mom har ta fito da Sauri tana hugging din Farouk
cike da matsanancin Farin cikin ganin sa . I'm happy to see you Son . Ya hanya ? Tayi maganan
tana ɗagowa daga jikin sa cike da matsanancin Farin ciki . Murmushi yayi yana faɗin " All is
Well Mam , Ina Ummu take?.


Fuskar Momy ne ya sauya a lokaci guda ,idanun ta na ciko da ƙwallah , a sanyaye tace " Tana
Bedroom ɗin ta . Okay Yayi maganan yana raba jikin sa dana Momy tare da Son nufar Bedroom
din Ummun . Hannun sa Momy ta riƙe a hankali ta fara faɗa masa halin da suke ciki da Ummu a
gidan , Sam kullum ka ganta cikin damuwa take ,taƙi sakewa dasu , Idan kaga Walwalar ta to da
Nurein ne idan ya zo , ko break fast Bata Sanyi dasu , idan ko ta zauna a ɗaki ita kadai bata da
aikin da ya wuce na kuka . Idan na tambayeta meke damun ta sai tace babu komai . Momy Kiyi
haƙuri Kinji ? Zata dawo yanda kike so Inshaallh . Farouk don Allah kayi mun kokarin hakan ,
ina damuwa sosai idan na ganta a hakan . Gyaɗa kan sa yayi alamun to ,kamin ya juya yana
saurin hayewa Stairs ɗin da zai kasa Bedroom din Ummu .

**

Zaune ya hangota kafafun ta na naɗe saman kujerar da take kai , hannun ta rungume da teddyn
ta , Idanun ta a lumshe suke amma hawaye ke zuba mata , Sosai ta sauya tayi kyau ta ƙara
murjewa fatan ta har sheƙi yake , tsayawa yayi yana kallon ta don bata san da shigowan sa ba
,alamu tayi nisa a tunanin da ta saba . Ummu.! Taji Muryar wanda bata yi expecting ba ya Kira
sunan ta , cikin Sauri ta ware idanun ta tana kallon inda yake a tsaye . Murmushi ya sakin mata
,wanda tun da suke bai taɓa mata irin shi ba . Yah Farouk ka dawo?. Hummmm bai bata amsa
ba sai zama da yayi kusa da ita ,yana sa hannun sa tare da zagayowa ta gyefen kafaɗan ta .
Meke damunki?. Yayi mata maganan yana mata ƙurrr da ido . Saurin Girgiza masa kai tayi
alamun a'a babu komai . Amma sai ya kauda kan sa kaman bai ga me tayi ba ,cewa nayi meke
damunki ,buɗe baki kimun magana . Cikin Ɗan rawar murya ta ce " Babu komai . Kin tabbata?.
Yayi mata maganan yana kallon ta ido cikin ido . Shiru tayi masa kamin ta kuma cewa " Eh .
Murmushi yayi yana ɗan yin shiru tare da nazarin ta , hannun sa taji yasa yana ɗago Fuskar ta
,kamin tayi Aune ita dai taji ya haɗa bakin shi da nata ne yana tsotsan laɓɓan ta , wani irin abu
taji yana mata yawo a ƙwanya wanda bata taɓa ji ba ...Ƙoƙarin janye kan ta take amma ina
riƙon tamau yayi mata motsi ƙwaƙƙwara ta kasa . Ji tayi yana lalubar Harshen ta tare da cafkar
sa yana cigaba da sha mata yana tsotsa mata tare da mannata jikin shi , nan take ta koma wata
ƴar Babe da ita , gaba ɗaya ya rufe ta . Numfashin ta ne ya fara ɗaukewa na tsoro ,wanda sai a
sannan ya zare harshen sa yana sauke numfashi tare da kauda kan sa tamkar bai mata komai
ba . Gyefen sa ma yake kallo inda kayan tarkacen make up din ta Suke . Tsayawa tayi jikin ta ko
ina rawa yake yi wanda kamin ta gama dawowa hayyacin ta ne taji ya kuma cewa" Meke
Damun ki kike kuka kaɗai anan ?. Yah Farouk babu komai . Okay Yayi maganan tare da juyowa
yana passing din Fuskar ta ,hannun sa taga yasa yana ɗago fuskar ta tare da shirin haɗa bakin
shi da nata ,wato yayi mata irin yanda yayi mata yanzu . Ya...yah Farouk Please ,ka bari don
ALLAH ...shii meke damun ki to?. Yayi maganan yana ɗaura yatsar sa a labɓan ta alamun tayi
masa shiru sai kuma ya kuma maimaita mata tambayar? . Cikin Muryar shagwaɓa kuka na
shirin ƙwace mata tace " Gida nake So naje. Ina kyewar Umma na , Beenerfa duka .

Jikin sa ne yayi sanyi ,a hankali ya sa hannun sa yana tallabo fuskar ta kamin yace " Okay zan
kai ki gida ,amma sai da sharaɗi guda ,kome ne nasaki yanzu babu musu kin amince? Idan kin
amince next week Zan Kai ki Gombe ,kuma ki daina noƙe mawa Momy tamkar ba Mahaifiyar ki
ba ,ina so ki sake da ita tamkar yanda kika saba da Umma Kinji . Gyaɗa masa kai Ummu tayi
cikin sauri ,kamin taga Ya miƙe yana cewa " Yau goyaki zanyi ,sau nawa kike Son mu zagaya
Bedroom din Nan naki ?. Ware idanun ta tayi cike da mmki kamin tace " A'a . Kallon ta yayi
yana jin babu daɗi ,don so yake yaga yasata nishaɗi da walwala kaman yanda Mom ke So.
Wayar ta ne ya fara ringing ,Wanda cikin sauri idanun ta suka fito ganin sunan Nurein , hankalin
ta ne ya fara tashi , kasan daga Wayar tayi sai kallon Farouk da take yi ,wanda shima ita yake
kallo . Saurin aje Wayar tayi tana kashe ta baki daya . Har a lokacin Farouk bai ce mata komai
ba yana kuma anan tsayen da yake , wannan yasa ta miƙewa a hankali idanun ta na cikowa da
ƙwallah , takawa tayi tana zagayawa ta bayan sa kaman yanda yace mata , hannun ta tasa tana
rungume sa tare da ƙwantar da kan ta a gadon bayan sa . Wani irin zuuu zamm zamm yaji
,wanda yasa shi Saurin lumshe idon sa yan jan ajiyar zuciya . Ƙwantawa tayi a bayan basa
yayin da a hankali ya ɗan rage tsawon sa tana hayewa ya goya ta cak... Shashsheƙar kukan ta
yaji amma bai dakata ba , nufar ƙofar fita yayi yana ficewa da ita zuwa love garden nasu na

gidan ,inda suka saba hutawa . Tsayawa tayi tana kallon wurin don bata taɓa sanin dashi a
gidan ba".




*Littafin THE VIRGIN MAID na kudi ne Regular₦300 VIP group ₦500 SPC₦1000 via
6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan Numbobi
08081202932*
Alhmdllh alah khulli haaleen.!https://www.youtube.com/@mamanteddy4123 Subscribe our new
YouTube channel pls @ MAMAN TEDDY HAUSA NOVELS AUDIO

DOMUN SAMUN LITTAFAN MMN TEDDY NA SAURARE DA ZARAR MUN ƊAURA MAZA KU
YI MANA SUBSCRIBE KAR KU MANTA DA DANNA MANA LIKE MUN GODE....
https://www.youtube.com/@mamanteddy4123

U

Bin wurin Ummu take da kallo cike da jin dadin ganin ta a wannan Wurin , Yah Farouk sauke Ni
. Kin bar kukan ? Gyaɗa masa kai tayi cikin zazzaƙar Muryar ta tace " Eh ai dama Ni Umma
nake Son Gani shiyasa nake Kuka . Hummmm numfasawa yayi tare da sunkuyawa ƙasa kaɗan
yana cewa " Okay Sauka to. A hankali ta sauka tana murmushi tare da juyawa tana kallon gyefe
da gyefen Wurin baki ɗaya . Tsayawa yayi cike da jin dadin ganin ta a wannan yanayin ya koma
yana zama a wani rest chair dake wurin a can gyefe . Wow ,Nan Wurin yanda kasan ba A
Nigeria ba ... Saurin kallon gyefen ta tayi ,nan taga babu Farouk , cikin Sauri ta juya tana shirin
sa ihu don wurin babu kowa sai Muryar shi taji daga bayan ta yana cewa " Yadai Madam kuka ,
Bakya gajiya da yin kuka ko da yake Ni nasan shagwaɓa ne yayi maki yawa . Kallon sa tayi
tana ɗan cuno masa baki kamin ta yafito sa da hannu alamun yazo . Miƙewa yayi yana
Matsawa zuwa inda take tsaye . Ɗaga kan ta tayi tana kallon Fuskar sa , wanda ta tsaya iya
kafaɗan sa . Kai na namun zafi ,ba zan iya dunga ɗaga kaina Sama ba Yah Farouk ka sun kuyo
ƙasa mana . Kallon ƙasa ƙasa yayi mata mai nuni da fassarori da dama kamin yasa hannun sa
cikin aljihun sa yana sunkuyo da kan sa ƙasa tare da ɗan rage tsawon sa . Buɗe baki tayi zata
masa magana sai taga yana nufo da bakin sa zuwa lips ɗin ta . Da sauri ta kauda kai tare da kai
bakin ta sai tin kunnen sa tana raɗa masa Wurin yayi mun ƙyau ya Farouk.
Gani tayi ya tsaya yana kallon ta bai ce mata komai ba sai zuba mata idanun sa da yayi baya ko
ƙiftawa , hannun shi taga yasa yana ɗago da fuskar ta ,a hankali yasa Bakin sa yana tsotsan
laɓɓan ta cikin salon sa zafi zafi ...Ƙoƙarin janye jikin ta take , Hawaye na ciko idanun ta , ganin
tana shirin saka masa gardama yasa shi , kama mai gaba ɗaya , abun da bata taɓa jin yayi
mata ba , hannun sa yasa yana kama Breast din ta wanda yasa ta ɗauke wuta jin yanda yake
ligwigwitar su , A hankali ya zare bakin sa daga nata kamin yace " zaɓa ɗaya Wanne kike So?
Nan ko nan ? Ya yi maganan yana Kissing ɗin saman lips din ta , sai kuma ya nuna mata
nonuwan ta da hannun shi ,wato ta zaba wanne ciki take so yayi mata . Don ALLAH kayi haƙuri
,Ni baka ce mun haka zaka mun ba shi yasa na biyo ka , Wayyo....Shiiiii Kara kame bakin ta

yayi yana cewa " Okay bara nayi maki duka . Jin hannun sa tayi yana cukurkuɗar nonon ta
,wanda tuni hawaye ya fara wanke fuskar ta ,don har ga ALLAH taɓa mata nonon da yake zafi
suke mata . Gashi ya riƙe ta tsam motsi ta kasa yi , tsotsan bakin ta kuwa ji take tamkar yana
mata waiwayi...kusan mintuna Huɗu yana ligwigwita duk inda yaso kana ya ɗago a wahalce
dagani kasan yana tsananin buƙatar ta mace tare dashi ...idanun sa sun sauya , cikin wani irin
murya yace " Me kika ce? Ummu zaki bini muje Gida na yanzu? Please?? Yayi maganan bai
ma san yayi ba . Fiddo da idanu tayi jikin ta na ɓari na tsoro tace" don kar kamun komai ,bazan
je ba Wallahi . Ta ƙare maganan tana shirin guduwa , hannu ɗaya yasa yana riƙe ta . Kana ya
kalle ta yana sakin murmushi kaman bai mata komai ba." Kallon ta yayi yana kara
Murmushin nan nasa kana yace " Kema a gidan ki aƙwai irin nan Wurin ,kina So kigani? Just
trust your Life , Ba Abun da....Ni ba zani ba , wallahi ba zaku haɗu kai da Ya Fahad KU kashe Ni
ba ,irin yanda kukayi mawa Wancen yarinyar ta ranan nan. Kuma Ni Na faɗa mawa Momy Yah
Nurein nake So ba Kai ba.
Wani irin abu yaji yazo masa wuya mai ɗacin gaske ,wanda nan take ya sake ta yana mata
Wani irin kallo mai cike da tsananin ɓacin Rai da kishi . Okay kin san Waye Nurein a wuri na?
Ƙanina ne Uwa ɗaya Uba ɗaya , ba kuma zai Aure ki ba na faɗa miki , Wannan maganan da
kika faɗa mun duka sai kinyi dana sanin faɗar su , Abubuwa biyu kenan nake bin ki bashi ,
Marin da kika mun ,da kuma Wannan maganan .

Ƙirjin ta ne ya buga sam ta manta da marin da tayi masa , Muryar sa taji yana cewa " Saura
idan kin shiga ciki ki faɗa masa Momy cewa nayi kissing din ki ko na taɓa maki nono , zaki
faɗa?. Yayi maganan yana tambayar ta fuska babu rahama gira a haɗe .

Ja baya tayi tana gyaɗa masa kai cikin kuka tace " Wallahi sai na faɗa mawa Momy ,ta daina
bari kana zowa inda nake , zan faɗa mata abun da kayi mun. Wani irin murmushi yayi kamin ya
ɗaga hannun sa yana cewa " Da ƙyau , that's what I want to hear , ki faɗa mata daganan ba
zaki ƙara sati guda ba a gidan nan zaki dawo gida na wato gidan mijin ki da zama . Wallahi ba
zan faɗan ba...Ta ƙare maganan tana rushewa da kuka irin na tashi ga ukun nan. Kallon ta yayi
yana cewa " Gyara Rigar ki mu wuce ciki , ko na gyara miki ne?. Hannun ta tasa tana saurin
gyara bra din jikin ta da yayi sama dashi don ya yi abun da ransa ke so . Ji tayi ya kama hannun
ta yana Wucewa da ita zuwa falon Momy . Fitowan Momy Salma daga kitchen kenan dai dai
suna shigowa ,wanda cikin matsanancin Fara'a da jin dadin ganin su a tare a haka tace "
Farouk kai Ummu Rest Room ta huta kamin na gama....Kamin Momy ta ƙarike Ummu ta fasa
ihu har da buga ƙafa tana cewa " Wallahi ba zani dashi ba , kin san meyake mun ne? Ni bazani
ba. Tana maganan ta haye sama da gudu tana barin falon cikin kuka.

Shiru Farouk yayi ,kan sa a ƙasa tun da yake bai taɓa jin kunyar wani Abu ba sai a yau ɗin nan
,ganin Momy a gaban sa . Gyarar murya Momy tayi kana tace " Je ka rarrashe ta Farouk
uhmm?. Okay Yayi maganan yana bin bayan Ummu . Kallon sa Momy tayi kamin tace " Farouk
matar sa ,ya kamata Daddy mu tsaida ranan tarewa a satin nan ayi a gama komai . Ta ƙare
maganan tana gyara zaman ear phone din dake kunnen ta ,don tun shigowan su magana suke
da Daddy ta Waya . Kar ki damu bari na dawo ,zan zaunar da Farouk ɗin muyi magana naji ."

Okay Shine kalmar da Momy tayi tana takawa tare da nufar Dirning Area .

Kama kan ta tayi da gwiwa tana kuka , wanda koda taji an murɗo Handle door din Bata ɗago ba
, ƙamshin turaren sa da ta shaƙa ne yasa ta fahimtar Farouk ne ya shigo , cikin sauri ta miƙe
tana rarraba lulun idanun ta...Humm zaki yi shirun ko sai na yi miki abinda bakin naki zayyi shiru
don dole ?. Tsitt tayi tana daina kukan nata . Wani kallo yayi mata yana sakin murmushi mai
fassarori kana yace " ina Tausaya miki Yarinya , Bakya baki da Kunya ba? Zan yi maganin ki .
Yana gama faɗa mata haka ya juya tare da ficewa daga Bedroom ɗin nata .

**

A hankali suke shiga layin Ummu sai Nurein da ya kawota tun daga Abuja zuwa Gombe . Ba
tare da ta tsaya ko Momy ta sani ba , duk da shi a yanda tace masa Momy tasan da tafiyar nata
, bai san ba haka bane ba ,don Company n sa ta biyo sa akan ya kawota Gombe. Yauwa
Yauwa yah Nurein mun zo . murmushi yayi yana cewa " To shiga sai ki faɗa masu tare muke
yanda zasu shirya kar Na shiga gidan babu excuse . Dari ya Ummu tayi kamin tace " Okay Sir .
Waye Sir ɗin anan? . Juyowa tayi tana dariya tare da cewa" Haka da naji ma'aikatan ka nace
maka . Kema sau ki cemun ?. Ok I'm sorry , na Manta ne My Champ. Dariya yayi itama tana
dariyar ta fice daga moton tare da nufar gidan Malam Kadarko . Wani irin tasss³ take ji tun daga
zaure ƙarar mari baba Wasa ba , yayin da Muryar umma ke kai kawo tana kirar sunan Auwalu ?
Kana da hankali kuwa ? Me tayi maka? Auwalu zan buga maka Wannan itacen. Saurin kutsa
kai Ummu tayi tare da shiga gidan . Auwalu ne taga ya kama Beenerfa yana duka da mari ,
yayin da Umma itama ke bugun shi da itace. Wannan yasa shi sakin Beenerfa dake ihu tamkar
ranta zai fita .

Da gudu Ummu ta nufe Beener tana Rungume ta tare da Fashewa da kuka , Hannu Beenerfa
tasa itama tana Rungume Ummu tare da cewa" Ummu dai na kuka , Ai ya tafi ,yanzu kika zo?.
Hawaye ne yake bin kuncin Ummu , Hannun ta takama tana cewa " Don ALLAH Beenerfa ki
dawo gida Kinji? Idan ba haka ba Kullum Auwalu dukan ki zai tayi . Kema haka yake miki?
Beener ta tambaye ta tana shafa gyefen kuncin ta da ya kumbura ga Shatin mari ta ko ina .
Cike da damuwa Umma ta amshe su da cewa " ai Ummu tasha dukan shi babu adadi ,mugu
marar hali . Eyya Umma kiyi Haƙuri addu'a zaki na masa ba wannan maganan ba. Beener ce
tayi wannan maganan kamin ta kalli Ummu tana sakin murmushi na farin cikin ganin ta .. keda
Waye kuka zo?. Cikin kuka Ummu tace " Yah Nurein ."

Yana ina ne bai shigo ba to?. Bari na saka hijab Muje a Shigo dashi . Juyawa Beenerfa tayi tana
ɗaukar hijabi a wayar shanya kamin ta saka tana cewa " Muje to .


Tun daga nesa Nurein ya tsaya yana mmkin yau Beenerfa ce da hijab ? Abun da bai taɓa gani
ba . Saurin ƙarikawa yayi gaban su yana ware mata hannu alamun tayi hugg ɗin shi ,amma sai
ta tsaya tana ɗago idanun ta tare da masa murmushi . Shafin Mari ya Gani kwance a Fuskar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login