Showing 45001 words to 48000 words out of 61257 words

Chapter 16 - THE VIRGIN MAID Hausa Novels by Maman Teddy.pdf

19 Oct 2025

2316

fashewa da kuka i love You Momy .... Ta yi maganan tare da kai bakin ta tana
Kissing Ɗin pic din Momy . A Hankali ta sauke hoton daga laɓɓan ta tana ajewa a gyefe . Yah
Farouk ta furta yayin da idanun ta ke akan Fuskar Farouk wanda yake ɗauke da faraa kaman
bashi ne mai hade girar nan na sama da ƙasa ba . Ka nuna mun So irin na yaya da kanwa , Ka
goya Ni a bayan ka babu adadi ,ka sakani dariya a lokacin dane cikin kunci ...I really Love you
ya Farouk ... Kissing Ɗin Hoton shi tayi tare da ajewa kana ta dauki Hoton ta tana kallo , a
hankali ta furta " Beenerfa taho ki koma wurin naki iyayen na asali. Juyawa Tayi tana saka hoton
ta a cikin trolly bag din tare da ɗaukar mayafin ta tana saka kafa tare da kallon dakin nata .
Daga hannun ta tayi cikin kuka tana cewa " Mom ,dad Farouk byeeeeeeeeeeee.!

Juyawa tayi tana share Hawayen ta tare da barin Falon kasa tana ficewa daga farfajiyar gidan .
Kai tsaye moto park ta nufa inda ta shiga buss da zai kaita garin Gombe , don tun a ranan da
taji maganan Daddy na ita ba yar su bace ta yi bincike akan nata iyayen ta kuma san inda suke
Rayuwa . A moton haya duk ta jigata ƙwarai don bata saba wannan wahalar ba ,ammma kuma
babu yanda zata yi kamin su sauka ta gama ficewa hayyacin ta . A haka har Allah ya sauke su
a garin Gombe .
**

Shigowa gidan sukayi Familyn duka har da Nurein mom Zeena , ko wannan su fuskar sa ɗauke
da fara'a don jikin Ummu Alhmdllh. Farouk ne ya kalli Momy tare da cewa " bari na kirawo
Beenerfa yanzu . Okay idan tana barci ne kar ka taso ta . Okay momy Yayi maganan tare da
hayewa saman Stairs ɗin falon . Kama hannun Ummu Mom Zeena tayi tana zaunar da ita tare
da taba saman goshin ta tana cewa " Babu abun dake Mali ciwo ko??. Gyaɗa mata kai Ummu
tayi don ita dai duk bata da walwala a tare da ita . Kin tabbata? Cewan Mom Salma tana kallon
Fuskar Ummu wacce tayi kasa da idanun ta . Muryar Omar suka ji yana cewa " Momy na duba
ban ga Beenerfa ba . Saurin ɗagowa sukayi mom na dafe kirji kamin tace " Ka duba ko ina
mana.! Momy na duba babu Beener a cikin gidan nan ." Wani iri Dauke wuta Duka suka yi
kamin Momy ta kalli Daddy tana faɗin sunan sa kai tsaye ,wanda tun da Su Omar suke basu
taɓa ji ba , Abdullah Kaine ka gani ko?. Tayi maganan hawaye na fara sauka mata . Dafe kai
Farouk yayi yayin da Nurein yace " Mom yanzu ina zata je kenan .? Tsayawa sukayi cirko cirko
yayin da Ummu gaban ta ke matsanancin faduwa .

**
A gaban gidan mai adaidaita ya dauke Beenerfa yayin da ta fara sauko da trolly bag din ta ,
sallamar Mai adaidaita Tayi tana tsayawa ƙurrr tana kallon gidan , wanda ƙofan arziƙi babu , this
is my own destination . Kalmar da tayi kenan tare da furta" Alhmdllh . Jan trolly din take Yi
,Kamin Ta fara nufo kofar gidan ne taga Auwalu ya fito yana buƙar Sigari ...Tsayawa yara da
manyan layin sukayi suna kallon Beenerfa tare da tambayar wacece ita?. Auwalu ne yasha
gaban ta yana cewa " Ke Nan ba inda kika zo bane ba , ko baki ga gidan ba irin naku bane ba
?.

A'a Yallaɓai nan nazo , Umma na ciki?. Wata Umman kuma wurin wa zaki zo a gidan nan ,kalle
ki da kalli fatar ki , Banbancin ki da yan Nigeria.... Umma ne ta fito daga gidan nata da mayafi
da'alama wani wurin zata tafi ...Kallon Auwalu tayi tana cewa " Yanzu Naira Talatin din magin
miyar shine ka ɗauka ka siye Sigari ? To Umma a haƙura da girkin yau ,Ni idan ban sha sigari
ba ban jin dadin Rayuwa . Ummmaaa.!

Beener ta kira sunan Umma tana tsayawa tare da bin ta da kallo . Cakk Umma ta tsaya tana yin
mawa Beener ƙurrr da ido . Girgiza kai Umma tayi tana saka gyefen mayafin ta tana sharce
hawayen daya zubo mata . Nasan dama wannan ranan dole wata rana zai zo . Domun duk
abun dake faruwa zuwan Alh Abdullahi Shuwa naji duk abun da ya wakana da Malam Kadarko .
Shigo daga ciki . Bin bayan umma Beenerfa tayi jikin ta a sanyaye babu wannan kuzarin nata .
Wacece Wannan kuma Umma? A ina kuka samo mana jinin turawa?. Auwalu yayi maganan

yana cigaba da buƙar sigarin sa .

Sam umma bata basa Amsa ba , Trolly din Beenerfa ta Amsa suna shigewa daga ciki , a cikin
zauren ne Beenerfa ta riƙe Umma gammm don gani take tamkar Soron zauren zai faɗo mata
aka . A haka suka shiga tsakar gidan dai dai Malam Kadarko na fitowa daga dakin sa da buta a
hannun sa . Wacece Wannan ?. Kallon sa Umma tayi tana kauda kai cike da jin Zafin abubuwan
da ya aikata shekaru sha bakwai baya . Abun da ka shuka ne yau ka girbo , baka gane ba ? Ai
yar kace Beenerfa da ka musanya a asibiti ,yau Ummu ta koma gidan su itama kuma da kafarta
ta dawo nasu gidan. Tari ne ya kwace mawa malam Kadarko kuful³ . Haushi ne ya kama Umma
wannan yasa ta kama hannun Beenerfa tana cewa " Shigo daga ciki . A bakin gadon Umma
Beenerfa ta zauna tana yin shiru ,kamin ta ji Muryar Umma cikin kuka tana cewa " Ina Son
Umma na ,ina Son Shalele na a yau ta bar Ni...! Malam ka cuceni kuma ka cuci kan ka. Saurin
miƙewa Beenerfa tayi tana tsugunawa gaban Umma tare da rungume ta tana cewa " Umma kiyi
Haƙuri komai bai Baba yayi maki ki yafe masa . Ke Kadarko baya da hali ,kalli Abun da yayi
maki Wanda nasan har Abada ba kowani yaro zai yafe mawa iyayen sa da sukayi masa
wannan yankar ƙaunar ba . Girgiza kai Beenerfa tayi sai hawaye sharrrrrr³ , Umma Ni na yafe
mawa Baba kema ki yafe masa , koba komai shine wanda ya haife Ni ....! Shiru Umma tayi tana
nazarin kalaman Beenerfa kamin ta miƙe tana ficewa daga Ɗakin tare da nufar Ɗakin Malam
Kadarko wanda ya shige tun ganin Beenerfa da yayi .

***
Ɓangaren Momy da Daddy sun ɗauka Beenerfa tana gidan kaka ne ,wannan yasa Su nufar
gidan ,da duk inda suke tunanin zata je amma babu ita , a ƙwana na ɗaya ne Ummu itama ta
gudu ,wanda anan ne suka mai da hankalin su wurin nufo Gombe .
Da misalin hantsi wuraren ƙarfe Biyu na yammaci ne Auwalu na Zaune a a dakalin Mudi mai
rake yaga fitowar Ummu daga napep . Cikin Sauri ya ƙarisa inda take ,tana kallon sa ta fashe
da kuka Ya Auwalu ina Umma na?. Sakin Baki Auwalu yayi kamin yace "Ashe ke shashasha ce
Allah yakaiki gaba kin huta da kangin Talauci shine kika sake dawowa cikin fitinan wannan
talaucin gidan ?. To an gane ke ba yar su bace ba ,dama Baba ne yayi komai don haka yanzu
shawara Ummu ki koma wurin iyayen ki masu kuɗi ,idan kin samu nasan ki da zuciyar rahama
don ALLAH kar ki manta dani... Juyawa Ummu tayi tana yin gaba tare da nufar cikin gidan , kan
ta tsaye ta kutsa tana kirar Sunan " Umma na.! Umma na .!!

A farfajiyar gidan ta hango su , Umma na tankaɗar Gari , Beenerfa na Wanke wanke...Miƙewa
Umma tayi da Sauri , Yayin da Ummu ta nufe ta tana rungume ta jikin ta . Aje Soson Beenerfa
tayi tare da nufowa inda Ummu take , A hankali tasa hannun ta tana ɓanɓare Ummu daga jikin
Umma kamin tace " Nan ba gidan ku bane ,Gidan mu ne ,ki fita bana Son ƙara ganin ki a cikin
gidan nan . Beener Pls Beenerfa ki Yi haƙuri , ni Umma na nake so.! Nima ita nake so. Just
Outttt...! Tayi maganan tana fizgar Ummu tare da hankaɗata nan take tayi ƙasa tana faɗi.

Can yafi dacewa dake Ummu ki tafi . Umma tayi maganan tana xubda hawaye , Saurin miƙewa
Ummu tayi tana cewa "a'a Umma na ke nake So. Sallamar Momy Salma ne yasa su duka
juyawa suna kallon ta . Tsayawa tayi tana bin Beenerfa da kallo wanda itama tana ganin Momyn

naya zuciyar ta ya karaya . Bin gidan da Take ciki Beenerfa a yau tayi ,kawai sai Momy ta fashe
da kuka , Ware mata hannu tayi wanda da sauri Beenerfa ta faɗa jikin ta tana rungume ta....!


*Littafin THE VIRGIN MAID na kudi ne ... Regular group ₦300... VIP group₦500... Special
₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number
08081202932....Ina Kira ga masu ba wasu kudin littafaina suna faɗin wai Ni maman teddy na
wakiltasu ,su ɗin Wai wakilai na ne , To Wallahi Ni Maman teddy ban san su ba , Kawai
Scammers ne yan damfara su amsan miki kuɗin ki ,daga bisani suyi blocking naki , da yawa a
rana fiye da mutane 4 biyar suna zuwa mun akan wannan matsalar sun tura mawa wasu
kudaden su since masu wakilai na ne To ƘARYA ne , bana Wakilta kowa a harkar Sayar da
littafaina ,Ni nake rubutawa don haka nice mai sayarwa , ga number na da kullum zaku same Ni
08081202932 ko kuma wannan numbern 09061466409 bayan Wannan nombobin ban san
kowa ba , Scammers ne . Ga kuma gerangiyar littafan nawa nan a ƙasa , saboda na ƙara Wayar
mawa mutane kai akan wa'annan masu damfarar yasani na saki wannan PAGE din Bonus.*
*WALIJAAM, YAR WAYE , SIYASATA ,DIJAMA YAR FULANI, GIDAN ƘWARATA , KWARTON
MANYA , THE SEXXYY BOSS ,MY LADY BOSS ,ZUMA DA MAƊACI , KAWALIYA ,HABIBI
DA'IMAN, BINTOTO, BAFULLATANAN RUGA , SIYASATA , GIDAN KWARATA , ƘWARTAR
SAMA , SADAKA YALLA , TAƁARAH , ƳAR AIKI NA GASUNAN LITTAFAINA DA YAWA A
SOCIAL MEDIA ,DUKA NIKE SAYAR DA KAYA NA , BA WANDA NA TAƁA WAKILTAWA GA
KUMA NUMBER NA 08081202932 BAYAN HAKA KO WAYA AMSA KUDIN KU TO DAMFARA
NE ,NI BAN SAN SHI BA BAN KUMA SAN TABA, DON ALLAH ZAKU NA IYA SHARING
WANNAN SAƘON DOMUN WANDA AKE DAMFARA SU FARGA SU GANI SU KUMA
SANI...MUN GODE...!*https://www.youtube.com/@mamanteddy4123 Subscribe our new
YouTube channel pls @ MAMAN TEDDY HAUSA NOVELS AUDIO

DOMUN SAMUN LITTAFAN MMN TEDDY NA SAURARE DA ZARAR MUN ƊAURA MAZA KU
YI MANA SUBSCRIBE KAR KU MANTA DA DANNA MANA LIKE MUN GODE....
https://www.youtube.com/@mamanteddy4123

T
Rungume Juna suka yi Beenerfa da Momy ko wannen su na ƙwallah na ƙwaranya daga idanun
sa, cikin Sauri Ummu ta nufi Umma tana faɗawa jikin ta ,tare da Fashewa da Kuka , dai dai su
Yah Farouk Daddy ya Nurein na shigowa gidan . Ko wannan su ja yayi tsaya zuciyar su a
karaye kuma cike da Tausayin junan su . Malam Kadarko ne ya tsaya jiki a sanyaye domin
shima fitowar sa kenan daga Ɗakin sa . Kallon sa Hajiya Zeenatu tayi kamin cike da ɓacin Rai
ta hau cewa " Yanzu me kayi kenan? Abun da ka shuka yau gashi ka girbe kayan ka , Anya
Wa'annan Yaran da kayi masu yankar ƙauna zasu yafe maka kuwa?. Wallahi ka nemi gafarar su
,sannan kuma ka nemi tuba zuwa ga nahalicci ... Kallon Mom Zeena Ummu tayi idanun ta na
tsaka da zubo da hawaye ta motsa bakin ta daƙyar wurin cewa " A'a Momy duk Abun da Baba
na yayi ,ba kansa bane , Allah ya hukunta dama hakan zata faru , Kuma da sharrin shaiɗan kuyi
haƙuri Ku yafe mawa Baba ". Kallon ta Umma tayi tana girgiza kai Ƙurum ,zuciyar ta tafi mata
zafi fiye da raɗaɗin hawayen dake sauka mata . Tabbas zan yi rashi kuma zan yi kyewar Ummu

, Yarinya mai Hankali tawakalli haƙuri juriya , Amma yana iya hakanan zan baku ɗiyar ku , Daga
Kuma ƙarshe Don ALLAH Hajiya Salma , Alh Abdullah Ina Mai Baku haƙuri bisa ga Abun da
Malam ya aikata maku akan jinin ku . Umma ta ƙare maganan wasu irin Zafafan Ƙwallah na
zubo mata . Malam Kadarko ne ya amshe maganan nata cike da matsanancin nadama da dana
sani ,ga kuma kunyar Abun da ya aikata .


Kuyi haƙuri bani da baki ko wata kalmar da ta wuce mun wannan ,duk da na san da wuya ku iya
yafe mun . Baba Nice Ƴar ka kayi mawa Hakan , kuma tsakanin Uba da Ɗa babu kalmar yafiya
,Ni yar kace kome kayi mun dai dai ne Baba . Ummu tayi maganan tana Matsawa Kusa da
Malam Kadarko da idanun sa suka kaɗa sukayi jajir , Ƙwallah ne ya ciko idanun sa jin furucin
Ummu akan sa . Tabbas sai a sannan ya fara jin Abun da Umma take ji na Rabuwa da Ummun
,tabbas zasu yi kyewa ƙwarai kuma sun yi rashi . Gaban sa ta tsaya tana sa hannun ta tare da
goge masa ƙwallahn idanun sa kana cikin maida komai ba komai tace " Baba Meye na kuka ,ka
bari don ALLAH , Idan Beenerfa kake tunani Daddy Umma na ko Momy duka Ni nasan sun yafe
maka .


Gyarar Muryar Da Daddy Yayi ne yasa su ,su duka mai da hankulan su akan sa . Kamin ya ce "
Ƙwarai Kuwa Ummu ,an zama Ɗaya komai ya faru na rashin jin daɗi mun yafe , Allah ya yafe
mana baki Ɗaya . Amin Ya rabil Alamin , cewan Su duka kamin Momy da Umma su shige Ɗakin
Umma , duka har da Hajiya Zeenatu , Farouk Nurein ,Auwalu daddyn Nurein ,Daddy Baba
Kadarko a tsakar gidan suka zauna ana shimfida masu tabarma , anan suka zauna kowa nan
su na ba ɗan uwan sa haƙurin Abubuwan da ya faru . Kusan ƙarfe Biyar na yammaci Daddy
ƴace su fito domin su ɗauki Hanyar komawa Abuja . Gaba Ɗaya Ummu babu walwala duka a
tare da ita ,duk da tana san ran dawowar Beenerfa cikin gidan , don sosai taga ta saki jikin ta
tun da Momy Tazo tana jikin ta har izuwa yanzu da suka fito domin tafiya . Hannun Beenerfa
Momy ta kama dana Ummu ,wanda cikin Sauri Beenerfa ta kalli Momy tana girgiza mata kai No
Mom ba Zan bi KU ba , Ina so na zauna da Umma anan nima . Wani irin bugawa Ƙirjin Momy
yayi wanda ya sata saurin kallon Beenerfa kamin tace mata Wani Abu ne Farouk yace " Ke
Beener taho mu wuce , me zakiyi anan Ɗin ?. Taho .! Ɗago da rinannun idanun ta tayi tana
kallon sa ,kamin da sauri ta nufe sa tana faɗa wa jikin sa rungume ta yayi tsam jikin sa , wannan
wacce irin musiba ce? Tambayar da yake mawa kan sa kenan ? Kamin yaji Muryar ta tana cewa
" Yah Farouk bye. Tana Juyawa da sauri tana shirin wuce Momy , cike da zafin nama Momy
Tasa hannu tana riƙo ta . Pls Beener Kar ki son zama damu ,don a yanzu Kinji mu ba iyayen ki
bane , Beener Ni Momyn Kice ba zan taɓa sauyawa daga hakan ba har abada . Wani irin huci
Beenerfa ta sauke Na Wanda yayi kuka yayi har ya gode Ma Allah ,kana ta kalli Mom Salma
tana cewa " I love You Momy , And I love my family , Ina Son zama da Umma na ,ba don komai
ba sai don itama na saba da ita kaman yanda na saba daku , Kuma zan ji Dadi nima naga
nasan Wasu dangi na ko ba duka ba , Mom Ku tafi ,ina fa anan , a duk lokacin da nake son
Ganin ku zan zo.! Kar kisa Wannan a Ranki har abada bazan taɓa iya sauya ki a uwa ba ,
Saboda ba zan iya ba ....ta ƙare maganan tare da Fashewa da wani irin kuka mai gunji , Cike da
tashin hankali Mom Salma ta sa hannun tana hugging ɗin Beener zuwa jikin ta ,kuka suke sosai

, yayin da kowa na wurin sai da ya xubda ƙwallah na tausayawa . Kusan mintuna biyu suna
ƙanƙame da juna kamin Beenerfa ta ɓanɓare kan ta ,da sauri tana faɗin " Momy Bye bye , ta
ƙare maganan tana barin wurin da gudu . Ummu dake tsaye ne idanun ta har basa gani saboda
kuka da kumburar da suka yi , Ba tare da ta ankare da zuwan sa ba , Sai hannun ta da taji ya
riƙe yana furta " Mu tafi .!


Saurin ware idanun ta tayi a saman fuskar Nurein ,kamin ta juya tana kallon Farouk wanda suna
haɗa ido yayi mata wani irin kallo ko na meye bata fahimta ba . A hankali ta fara bin bayan
Nurein yayin da Momy Salma cikin matsanancin damuwa ta fito gidan , Hajiya Zeenatu ita ta
tsaya sallama da Umma ,itama duk taurin zuciya irin nata ta gagara ɓoye Hawayen ta . A
wannan yammaci suka ɗauki Hanyar dawowa Abuja ,ko wannan su Ka kalli Fuskar sa babu
walwala sam."

"Bayan Wasu watanni".

Parking moton sa yayi a Inda aka tanada na aje motocin gidan , Kana ya fito cikin zatin sa
,idanun sa na a cikin ɓakar tabarau . Ga wani Saje da ya kuma ajewa fiye dana da baya . Wani
ƙyau ya ƙara na musamman . Cike da earphone ɗin Kunnen sa yaji Muryar Momy tana cewa "
Welcome back my Son , Ina Under

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login