Showing 39001 words to 42000 words out of 61257 words

Chapter 14 - THE VIRGIN MAID Hausa Novels by Maman Teddy.pdf

19 Oct 2025

2306

, tana a tsaye a falon ne taji Shigowan Nurein yana
isowa tare da faɗin Momy Barka da gida . Danne damuwar ta tayi kamin tace " Nurein Ya hanya
, maza zauna Asabe kawo masa ....No no Momy Ina Ummu Wurin ta nazo.! Saurin juyawa Mom
Tayi tana kallon Beenerfa itama wacce Momy take kallo , tana jin wani irin tsananin tsanar
Ummu a zuciyar ta...! Sun fita da Daddy tun... Kamin mom tayi maganan ne suka jiyo
dararrakun Ummu tana magana da Daddy tare da cewa "Gobe Daddy Zamu ƙara zuwa ko?.
Ehh mana gobe ki shirya....Cakkk Duka suka tsaya su duka shidan Mama Asabe ,mom Salma
Beener , Daddy Nurein Ummu duka suna kallon kallo . Hannun Ummu riƙe da wani teddy Mai
ƙyaun gaske So romantic , Nurein ne cike da rawar jiki irin na wanda yaga abun da yake So ya
nufo inda Ummu take , Hannun sa yasa yana amsan Teddyn tare da faɗin " Wow so Romantic
Yayi kyau . Murmushi Ummu tayi a hankali ,kamin tace Wani Abu ne taga ya kama hannun ta
yana cewa " Come lemme show you
something.......https://www.youtube.com/@mamanteddy4123 Subscribe our new YouTube
channel pls @ MAMAN TEDDY HAUSA NOVELS AUDIO

DOMUN SAMUN LITTAFAN MMN TEDDY NA SAURARE DA ZARAR MUN ƊAURA MAZA KU
YI MANA SUBSCRIBE KAR KU MANTA DA DANNA MANA LIKE MUN GODE....
https://www.youtube.com/@mamanteddy4123

Q


"Bayan Fitar Nurein ne Ummu ta kalli Daddy ,Kamin tayi magana ne Beenerfa cike da complain
ta fara cewa " Daddy meyasa Ka ɗauki Wannan yarinyar ku ka fita tare? Me yasa kake Son ta
eyee Dad?. Tayi maganan cike da Son jin Amsa daga Bakin Alh Ɗan Shuwa ....ammm Beenerfa
ai itama kinga Yarinya ce kamar ki teddy na sayo mata....Kamin ya ƙare maganan ne ta juya
fuuuu tana barin Wurin cike da jin haushin Abun da Daddy Yayi mawa Ummu . Wannan Abun
sam baiyi ba , Bai kuma dace ba . Haba Daddy Banbanci kake kokarin nunawa akan Beenerfa?
Wannan ba dai dai bane ba sam..."

"Mom Salma tayi maganan tana takowa zuwa inda Daddy yake tsaye".

Banbanci Salma kike cewa ? Ai kece wacce kike nuna banbanci da halin ko in kula akan ƴar ki
ta cikin ki...Kar ki manta Ummu Ƴar ki ce ,kuma jinin ki , Wallahi ko na faɗa maki ko ban faɗa ba
ke kin san bakya nuna Soyayya dai dai da ƙalilan Akan Ummu , kin mance da Uƙubar da ta fito
? Kin manta Wahalar da ƴar mu tasha a hannun mahaifin Beenerfa ? Waye ya jawo duka
wannan ? Shine shidai Malam Kadarko ,munyi masa Rana yayi mana Dare , Dare baƙinƙirin.
Hummm Nisawa yayi yana juya baya kaman zai bar wurin sai kuma ya ja ya tsaya yana cewa "
Ni ba zan ƙyamata jini na ba , don kawai na faranta mawa Ƴar Wanda ya raba ya ta ,gudan jinin
mu daga jikin mu , Zan nuna mawa Ummu Soyayyar Ɗa da Uba ,ke kuma kije ki nuna mata
ƙiyayya ba zan hanaki ba ,amma Hjy Salma ki sani ba a taɓa sauya mawa Tuwo suna ,yana
nan a inda yake ... Yana gama faɗa mata haka ya juya tare da saka ƙafarsa yana nufar hanyar

da zai sada shi da Apartment din shi...Daddy."


"Mom Salma ta Kira sunan Daddy Wanda Jin hakan yasa shi dakatawa ba tare da ya juyo ba ya
tsaya yana sauraren ta ..." Ba'a taɓa Sauya mawa Tuwo suna kace? , Humm to Ni zan sauya ,
Ba zan riƙe Ummu ba , idan mukayi haka bamu cika iyaye ba , Beenerfa wani irin tashin hankali
zata shiga ? Kar ka manta bata saba da Wannan Rayuwar talauci ba sam , Amma ita Ummu ta
saba mu barta don ALLAH acan , mu bar ta a hannun iyayen Beenerfa kaman yanda ta taso a
hannun su ...mu kuma mu cigaba da riƙon namu Ƴar . Ka duba mun na saba da Beenerfa
,kuma sannan itama Ummu zata fi jin dadin zama da Iyayen ta su Malam Kadarko .


"A matukar fusace Daddy ya juyo Kamin ya fara cewa" Ina Son Ƴata ,kuma tun da ta shigo
gidan Uban ta ,ba zata fita ba , Saboda ina Son itama tayi rayuwar jin dadi kaman na saura . Ke
ki riƙe Beenerfa Ni kuma zana kula dasu na riƙe su duka . Daddy hakan ba zai yiwu ba. Momy
tayi maganan idanun ta na fara tsiyayar da Hawaye . Zai yiwu ,daga lokacin da kika cigaba da yi
mawa Ummu riƙon sakaina daga lokacin Ni kuma zan sanar mata da komai ,domun yana ba
zata kamu da wani ciwo na daban ba . Juyawa Yayi yana ba Momy wuri , yayin da ta ja baya
tana zubewa a 3ster ɗin falon , Idanun ta Duk sun duddulo waje sunyi ja waye na cigaba da
zuba mata....ta rasa samun mawa kan ta mafita sam . Mama Asabe dake Bayan su duk abun
da ya faru a gaban idanun ta ,itama saurin jan jiki tayi ba tare da ta bari Momy Salma ta ganta
ba ta fice daga Ɓangaren ,hankalin ta kaf a matuƙar dagule...Waye yayi wannan Aiki ?
Tambayar da take mawa kan ta kenan kamin a zuciyar ta tayi ta hailala tana kirar sunayen Allah
tsarkaka .

Tun daga Wannan Rana , Momy Salma ta daina Walwala , Haka Ta rarrashi Beenerfa har ta
sakko a yanzu suna yin break fast tare da Ummu ,sai dai Abu kaɗan Beenerfa zata fara zagin
Ummu tana cin mata mutunci . A haka Ummu take rayuwa a cikin gidan , babu wurin wanda
take samun sassauci sai mutane biyu , Nurein da Daddy . Don ɓangaren Daddyn Nurein tuni ya
sami Daddy sunyi maganan Auren Ummu da Nurein ,amma anan Daddyn ya dakatar da
maganan akan cewa " A bari su kammala Secondary . A haka rayuwa ke tafiya yake gungurawa
. Yau hutun su Ummu ya ƙare , wanda Daddy sam yace ba zasu koma yin kwanan makaranta
ba , Kullum Driver zai rinka kai su ,idan an tashi ya dauko su ..Sam hakan baiyi mawa Beenerfa
daɗi ba , Don sosai tayi kywar abokanan Iskancin nata . Amma ya ta iya ,dole ta amince da
maganan Daddy . Safiyar Litinin . Sanye suke cikin uniform iri guda ,school shoe , school bag
komai nasu iri daya har lunching basket . Hugging Din Beener Momy Salma tayi tare da mata
sai ta dawo . Wuce su Ummu tayi cike da jin dadin yau zata koma makaranta wani masifar na
Beenerfa yayi mata Sauki . Sam bata damuwa da Yanda Momy ke nuna Soyayyar ta ga
Beenerfa a cewan Ummu ai dama Ɗiyar tace .

Gidan baya ta shiga yayin da Beenerfa ta zauna a gidan gaba gyefen Driver a cewan ta ba zata
zauna gata ga Ummu ba." A hankali Ummu ta lumshe idanun ta tana rufe su tare da buɗewa ,
Fuskar Omar Farouk ta tuno , yayin da mafarkin nan nata da kullum take yi akan sa ya dawo

mata ƙwaƙwalwa. Ummu kiyi ma Farouk Addu'a Kinji?. Jikin ta ne yayi wani irin sanyi , hankalin
ta yana neman ya tashi , me yasa Yace mun haka ?. Yana ko a cikin koshin lafiya??. Ummu
sauko an iso." Muryar Drivern taji wannan yasa Ummu saurin sakkowa tana cewa " To mun
gode . Ba tare da ta tsaya jirar Beenerfa ba ta nufi cikin makarantar nasu kan ta tsaye....Oyoyo
kissss me , kissss meeeee uhmmm . Anam ce ta nufo Ummu tana Kissing din kumatun ta
tana faɗin Wannan maganan . Murmushi Ummu tayi suna Rungume juna tare da nufar class ɗin
su fuskokin su duka cike da matsanancin Farin cikin haɗuwar su .

***

"Zaune Suke a falon Momy Salma , Beenerfa na a can tana playing game Yayin da Nurein yake
gyefe kunnen sa cikin head phone , Alamu magana yake yi .... Okay ya Farouk . Cewan Nurein
yana miƙa mawa Beenerfa Wayar sa tare da cewa " Yah Farouk ne . Cike da shagwaɓa har da
hawayen ta ,take fadin " Yah Farouk i miss You , When are you back?. Ba tare da naji mai yake
cewa ba ,naga ta saki ranta tana murmushi tare da miƙa mawa Nurein Wayar , A kuma dai dai
Nan Ummu na saukowa cikin shirin zuwa islamiyan da Dad ya saka su. Ohhh Yah Farouk ga
Ummu itama ku gaisa . Wani irin bugawa ƙirjin ta yayi dammm...wanda jiki a sanyaye tasa
hannu tana amsan Wayan Tare da ƙara shi a kunnen ta . Shiru babu wanda yace masa komai
daga ita har shi Farouk ɗin , kusan mintuna uku , shidai Nurein bai san me suke yi ba ,don da
ya bata juyawa yayi yana cigaba da aikin gaban sa... Beenerfa ce ke kallon komai dake faruwa ,
Wannan yasa Farouk cike da jin haushin wato shine zai mata magana cewa " Ke dallah bashi
wayar sa , yar ƙauye kawai mtswww". Yayi maganan yana jan dogon tsaki tare da kashe wayar
nasa . Tsayawa Ummu tayi tana yin shiru kusan mintuna biyar . Kamin Beenerfa ta wani sheƙe
da dariya tana cigaba da danna Laptop din ta . Baki masa magana ba ne ?. Taji Muryar Nurein
wanda yasa Ummu saurin cewa " A'a Yah Nurein . Okay kin shirin Islamiyan ne?. Eh . To muje
na kai ki .


"Nima yah Nurein ka jira Ni ,ka kaini . Ni Driver n ki ne?. Yayi maganan yana haɗe girar sama
da ƙasa . To ai itama din kai ba drivern ta bane ba". Cewan Beenerfa tana turo bakin ta gaba .
Okay naji wuce kiyi sauri ki shirya ,idan kuma baki fito da wuri ba ,Zamuyi tafiyar mu . Ya ƙare
maganan yana kallon Fuskar Beenerfa . Juyawa tayi cikin Sauri tana nufar Bedroom ɗin ta don
ta shirya .

Mai do da hankalin sa yayi akan Ummu kamin cikin tausasiyar Murya yace " Babe me , ina
iPhone din Dana siya mikii? Me yasa Bakya using dashi ,ban taɓa kirar ki na same ki ba
,Kullum switch off . Kin taɓa kunna ta ma kuwa?. Shiru Ummu tayi kaman ba zata masa
magana ba ,sai kuma ta kalle sa tana cewa " A'a Ban amfani da ita ne. Amshe ta yayi da cewa "
Bakya So ne ? , Sai a sauya wani . At list Ina so na rinƙa jin Muryar ki kamin nayi barci a kullum
. Idan kuma so kike duk dare na rinƙa zuwa na ganki sannan na koma nayi bacci to". Saurin
kallon sa tayi tana girgiza kan ta alamun a'a don sarai tasan zai aikata hakan fiye ma . To zaki
kunna wayan taki?. Murmushi tayi tana cewa " Eh , Amma kar ka fito da da da saboda Ni . Ba
gani nan ka ganni ba.

Ina miss ɗin ki ko wani dakika ,kin sani babe me ". I miss you always . Ina Son ki Bana gajiya da
kallon ki , Burina kawai muyi Aure na cigaba da Son ki , Mu ƙwana mu tashi duka tare ... Saurin
saka hannun ta tayi tana rufe fuskar ta cike da jin kunya , wanda yasa shi dariya yana sa
hannun sa tare da buɗe mata fuskar ta , Seriously Ummu ina Son ki.! Na san kuma kema zaki
Soni. Kamin tayi masa magana ne taji yasa bakin sa saman goshin ta yana ɗan sunkuyowa
kasa tare da rage tsawon sa yana Kissing din ta . kallon sa tayi tare da narke masa fuska cike
da shagwaɓa . Yah Nurein babu kyau haka . Sorry I'm eager Naga na Aure ki Ummu , Na kosa
na ganki tare dani a gida na . Ware idanun ta tayi da Sauri kamin cike da kunya tayi waje da
sauri tana dariya . Beener ce ta fito tana kallon Nurein itama cikin hijabi wanda yau shine rana
ta farko da na taɓa ganin ta da hijabi . Yah Nurein mu tafi .

**
Tun bayar Kiran nan da Farouk yayi Ya daka mawa Ummu tsawa , Ko ya kira barin wurin take a
siyasance , Ba tare da kowa ya fahimta ba . Yau ranan Saturday babu school don haka tun da
suka yi break fast Bata ƙara fita zuwa falo ba ,tana cikin Bedroom din ta tana sauraren littafin
Audio a YouTube channel din MAMAN TEDDY HAUSA NOVELS AUDIO da Wata ƙawar ta ta
bata labarin littafin Ƴar Waye? Littafin MMN TEDDY ,Wanda Inshaallh shi zamu fara ɗaura
maku a wannan YouTube channel namu ,kar ku manta da yi mana Subscribe and like mun
gode..." Wayar ta ce ta fara ruri wanda hannun ta tasa tana picking call ɗin duk da taga baƙuwar
number Amma mutum ɗaya ta kawo a zuciyar ta wato shine " Nurein . Cike da Sanyin murya
yaji zazzaƙar Muryar ta tana faɗin " Miss You Yah Nurein ".


Wani irin Damm ƙirjin sa ya buga masa kamin daga bisani yace " Okay Kai mawa Momy Wayar
muyi magana . Hasbunallah ta furta da karfi tare da sakin wayar a ƙasa ,jin Muryar Omar
Farouk . When ? Tayaya ya Samu number na? Na shiga Uku .! Kasa ɗaukar Wayar tayi don
anan wurin ta bar shi a ƙasa . Komawa tayi tana hayewa gadon ta , tare da jan bedsheet tana
rufe kan ta , a wannan rana littafin da bata karanta shi ba kenan , duk da an inda take so a zo
,amma hakan nan ta haƙura bata karanta shi ba .

**

One class". Shine Kalmar da Ummu tayi a daidai lokacin da daliban suka kacame da surutu ,
gank ɗin su Beenerfa ne suka kece da dariya yayin da dayan su ke cewa " Me aikin Dafa Abinci
fa tana magana , tace ayi shiru . Tsitt ki kaji Sauran Ɗaliban sunyi , Yayin da Anam da Nana
miƙewa suna kallon Zee tare da cewa " wannan wani irin iskanci ne Zeee kike yi? . Ai gaskiya
ce ba mai aikatau bane ita?. Murmushi Beenerfa tayi kamin tace ' ato idan karya akayi mata ai
ta Muusa . Wasu irin zafafan Hawaye ne suka fara bin kuncin Ummu , a hankali ta fara goge
Hawayen nata , kamin Anam ta Yi tsalle tana cafkar Wuyar Beenerfa ji kake tass³ har sau uku
tana wanke fuskar Beenerfa da mari ,yayin da Nana ita kuma ta kama Zee Suna fara kokawa .
Meke Faruwa ne anan Class ɗin ?? Anam.! Suka ji Muryar Auntyn su wanda yasa su duka

dakatawa . Omar Farouk ne tare da Malaman yazo tafiya da Ummu da Beenerfa . Tsayawa yayi
yana kallon su su duka , yayin Da Ummu tayi saurin saka hannun ta tana goge hawayen idanun
ta . Good morning Uncle ". Ɗaliban suka yi maganan tare da miƙewa suna gaisar da Farouk ,
wanda kallo ɗaya yayi mawa Ummu ya kauda kai yana kallon Beenerfa da Fuskar ta duk yayi
shatin mari . Antyn nasu ce tace Beenerfa da Ummu su taho ana Son ganin su a PC Office .
Jakukunan su suka ɗauka , wanda suna fitowa Suka nufi moton Da Farouk ya shiga , Beenerfa
ne ta fara shiga kamin Ummu ta shige gidan baya kaman kullum ,ita kuma ta zauna gyefen
Farouk . Ya Farouk Walcome Back". Murmushi Yayi yana kallon Beenerfa tare da cewa ' wa ya
buge ki?.


Ƙwallah ne ya ciko idanun ta ,kamin tace ' Kawai saboda nace " Wannan yarinyar tana aikatau a
gidan mu Shine Ƙawar ta Anam ta mare Ni . Shiru yayi yana cigaba da driving tare da ficewa
farfajiyar makarantar . "me yasa kika ce haka?."

Yayi maganan yana kallon Beenerfa , kamin cike da rashin nadama tace " Saboda Yah Farouk
tana Soyayya da Yah Nurein , kuma bana Son ganin hakan . Nurein..!

Ya maimaita maganan kamin suga ya ja burki y tsaya . A hankali ya bude murfin moton sa yana
ficewa tare da shiga gidan bayan inda Ummu ke zaune . Kallon ta yayi fuska babu alamun wasa
kamin yace " Faɗa mun yana da kyau matar Aure tana rinƙa kula wasu mazan har su rinka
soyayya ???.

Ɗago da idanun ta da suka ƙara girma na tsaban kuka tayi kamin ta girgiza masa kai alamun
a'a . Keee yi mun magana da bakinki Are You deep??? Yayi maganan a tsawa ce . Cikin sauri
Hawaye na cigaba da wanke Fuskar ta tace " A'a . To me yasa ke kike yi??.

Ya Farouk Saboda ita ba matar Aure bace ba. Beener ta amshi maganan tana kallon sa . Kamin
ta cigaba da cewa " Kawai kayi mata warning ta kiyaye Familyn mu ,mu ba sa'oin talakawa
bane ba eheee.! Waya faɗa miki ita ba matar Aure bace ba? Tana Da Aure.! Saurin kallon Sa
Ummu tayi kamin cikin kuka tace " Wallahi Ni bana da Aure. Yi mun shiru ko yanzu na murje
wannan ɗan mitsilun bakin naki da har yasan yace " I miss You...Yau yanzu zan koma dake
garin ku ,ki tambayi Mahaifin ki , Shin kina da Aure na akan ki ko babu , Daga nan sai na dawo
dake nan .!

Buɗe baki Ummu tayi cike da tsoro da tashin hankali ,kamin cikin wani irin hautsinanniyar Murya
tace " A'a Wallahi bana Son ka ,bana Son ka , Abba bai mun aure da kai ba ,dauko Ni kayi ...
Ke Ni mijin ki ne , tun kan kizo gidan Momy na sai da na tabbatar na mallakar kin zama tawa ,ta
har Abada ,kula wasu mazan zunubi kike ai kawa babba ki sani daga yau....Luuuuuu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login