Showing 1 words to 3000 words out of 61257 words
*️THE VIRGIN MAID️*
&
The Womanizing Boss
#Romantic
#Caring Kiss
#Forever love
#Comedian and
#Best love couple Story.
Page
1
*A HAUSA NOVEL FROM YOUR BEST WRITER MAMAN TEDDY*
***
(A.B.U teaching Hospital) .
Cike da Azama Nurse Hamdiyya ta fito daga Ɗakin labour ɗin tana nufar Office ɗin ta ,fuskar ta
fal cike da annuri bata ko ganin gaban ta saboda tsaban farin ciki . Tsayawa nayi ina ƙare mawa
farfajiyar Wannan babban asibitin kallo , wanda duk da kasancewar Dare ne ,Amma haske ta ko
ina kaman Safiya ko hantsi saboda Solar dake haske ko ina na wannan Asibiti . Muryar Nurse
Hamdiyya naji daga baya na , wanda jin hakan ya sani Saurin juyawa ina mai ƙare mata kallo ,
wayar hannun ta ta kara a kunnen ta cike da matsanancin Farin ciki ta ke faɗin "
Congratulations Alhaji Abdullah , Madam ta sauka cikin ƙoshin lafiya an samu ɗiya mace ". Eh
yanzu haka tana ɗakin hutawa ita da babyn ta . To sai kun iso". Katse kirar tayi tana nufar Ɗakin
da Mai haihuwar take ,wanda ko ba'a faɗa maka ba da'alama matar wani babba ne a ƙasar nan
tamu ko daga yanayin yanda aka keɓence ta a ɗaki ita ɗaya ba hayaniya , Sauke Ajiyar zuciya
Nurse Hamdiyya Tayi ganin Hajiya Salma Har ta samu barci , Alhmdllh Allah ya cika maku burin
ku , tsawon shekaru Ashirin da Auren ku baku taɓa samun ƙaruwa ba sai a wannan shekara ,
hannun ta Nurse takai zuwa inda Jaririyar ke ƙwance , gaban ta ne ya buga dammm jin Jaririyar
bata numfashi , sakin Wayar hannun ta tayi nan take ta ratsatstsake a saman tiles .
Ba tare da ta tsaya bi takan Wayar nata ba tasa hannun ta tana girgiza Jaririyar , Hawaye ne ya
fara bin kuncin ta , Innalilahi wa'inna ilaihir rajiun shine Kalmar da take maimatawa . Maida
Jaririyar tayi ta aje tana ɗurƙusawa tare da ɗaukar Wayar ta da yayi part part a ƙasa . Ganin
babu yanda za'a yi tayi kira dashi yasa Ta saurin Fitowa tana nufo ƙasan Down Stairs .
Eh ta sauka lafiya yanzu mun samu ɗiya mace". Taji Muryar Wani daga wurin yana faɗa . Cikin
sauri ta ƙarisa ga mutumin jikin ta na Rawa haka idanun ta na xubda ƙwallah ta kalle shi tana
cewa " Yallaɓai don Allah ka taimaka mun da Wayar ka nayi kirar Ujila yanzu ya kamani . A
fusace ya juyo yana bin Nurse Hamdiyya da wani irin kallo , Itama kallo Ɗaya tayi masa ta gane
irin masifaffun matsiyatan talakawan nan ne ,marasa mutunci su burin su su tijara mai arziƙi
wanda Allah ya rufa masa.
Cike da Tsawa na talauci da ya ishe sa yace " Ke bari na gama sanar da ƙauye cewa mata na
ta haihu ko , idan zasu taho ko buhun Masara aka kawo mun ai na rage zafin talauci a wannan
marran.
Kallon Sa Nurse Hamdiyya Tayi cike da Muryar shiga tashin hankali tace " Ka taimaka mun
Yallaɓai , Matar Alh Abdullah Shuwa ne ta haihu yanzu , kuma suna tare fiye da shakaru Ashirin
da Aure basu taɓa haihuwa ba sai a wannan karon , bayan na sanar masu ne cewa ta haihu na
koma duba Jaririyar na tadda bata motsi Yallaɓai ,ina cikin tashin hankali kome ya faru Ni zasu
zarga kuma na sanar masu cewar Komai suna lafiya Madam Hajiya Salma da kuma babyn ta
,yanzu haka sun ce suna hanya ka taimaka mun yallaɓai na sanar dasu kamin su ƙariso .
Jikin Malam Kadarko ne yayi sanyi , a hankali ya miƙa mata Wayar tasa kirar Nokia rakani toilet
, ko murfi bayan ta babu ,gashi Kirawo su ki sanar dasu . Yayi maganan yana bata Wayar
hannun nasa ,wanda cikin sauri ta amsa tana fara latsa nombibin Wannan Attajirin mahaukacin
mai arziƙi Wato Alh Abdullahi Shuwa . Ji tayi Malam Kadarko ya buge hannun ta yana cewa "
Ina zuwa dakata . Gimtse kirar tayi tana kallon sa . Cikin wani irin yanayi tamkar na salihan
mutane yace " Wannan wanda kike maganan sa , Mai gida na ne Alh Abdullahi Shuwa ,
shekara ta Goma sha biyar kenan ina aiki a ƙarƙashin sa ,duk Bama Flower ruwa nake yi ,
Amma ya gama mun komai a rayuwa . Mutumi ne Adali , ina cikin gidan Ƙannin sa ya ba matar
sa Ƙyautar ɗan sa na fari cikin sa ,halak har Abada . Wanda yanzu da faruwan Hakan Shekaru
sha biyu kenan ,ba kowa Ni yaro bane face Wato Umar Farouk.
Babu ta hanyar da zan saka masu da ya wuce nima na sadaukar da tawa farin cikin , Wannan
Jaririyar dana Haifa a ɗauka a basu .
Cikin sauri ta kalle shi tare da cewa " Ban gane ba yallaɓai . Jirani ina zuwa . Yana
maganan ya juya tare da nufar ɗakin da matar sa take , Barci ya same ta take Yi ,wannan ya
bashi damar ɗaukar jaririyar yana yo Waje da ita . Nurse Hamdiyya ya tarar da ita a inda ya
barta . Taho muje a musanya mata da Ƴata ,Ni na ɗauki matacciyar mu saka mata rayayyar.
Yallaɓai babu matsala kuwa??. Mai rai fa zamu basu , mu tafi babu komai . Cikin sauri Suka
shiga Ɗakin Da Madam Salma take har a wannan lokacin bata farko daga barcin nata ba . A
hankali Nurse Hamdiyya Tasa hannun ta tana ɗago da Matacciyar Jaririyar ,shi kuma Malam
Kadarko yana saka Tasa Rayayyar Jaririyar . Cikin Azama suka fito a tare ,suna saukowa ne
daga Down Stairs ne ruwan sama ya kece ana sakin wani irin tsawa nan take Jaririyar Hannun
Nurse Hamdiyya ta fara tsala ihu ...
Laa alhmdllh Yallaɓai Jaririyar tasu ba mutuwa tayi ba tana kuka jiba yallaɓai.! Cewan Nurse
Hamdiyya tana murmushi na farin ciki , Shiru Kadarko yayi yana ƙin mata magana . Wannan
yasa Ta cewa " Yallaɓai muje a mai da masu da ƴar su ,sai ka ɗauki taka Jaririyar .
Wani irin kallo yayi mata , Yana sa hannu tare da amsan Jaririyar daga hannun ta . Ke Malaman
Asibiti dakata kiji , Wancen ƴata ƙaddararar ta shine ta rayu cikin masu arziƙi taji daɗin Rayuwa
, ita kuma wannan Ɗiyar tasu nata ƙaddarar shine ta rayu damu cikin talauci da ƙuncin Rayuwa
,wannan shine ƙaddarar su duka babu yanda muka iya .
Fiddo da ido Nurse Hamdiyya Tayi cike da tsorata da maganganun sa tana kai hannu tare da
Son Ƙwatar Jaririyar daga gare shi tana cewa " A'a Yallaɓai ,wannan Abun da kake shirin yi
zunubi ne babba , badai dai bane ba , Allah ba zai bar mu ba , ka kawo Jaririyar su a maida ta
ka ɗauki naka . Ganin yanda Nurse Ke hayaniya tana shirin tona masa asiri yasa shi kai hannun
sa yana mata angaza irin na mutanen ƙauyen nan wanda suka saba saɓa garma da fatanya .
Tura ɗaya yayi mata tayi baya tare da faɗawa daga benen tun daga na biyu har zuwa ƙasa nan
take tayi ƙwance babu alamun rai a tare da ita . Cikin sauri ya saɗaɗa ya gudu tare da shigewa
Ɗakin da matar sa take yana mai da mata da ɗiyar Madam Salma da yayi exchanging .
Hayaniya ne yasa shi fitowa nan yaga motoci guda biyu ana ɗaukar Nurse Hamdiyya tare da
ficewa da ita daga Asibitin cikin Azama , ko ina za'a kaita Allah masani . Wata Nurse ne tazo
wucewa nan ya tsaida ta yana cewa " Lafiya Nurse ,me ya faru ?. Cike da jimami take shaida
masa Da ƙila Nurse Hamdiyya ta mutu ne . Juyawa yayi yana murmushi tare da cewa " Kin huta
Malaman Asibiti .
After a Six 6 years
*(Bayan Shekaru Shida 6)*
Wata yarinya ce ta shigo gidan tana raɓe raɓe tun daga kwangon gidan nasu . Ummu na.!
Ummu na..!! Cewan Umman ta da fitowar ta kenan daga madafi dama tuni ita take nema , tun
safe har la'asar. Ƙyale shegiya karfa kar ta shigo , mai ƙyaun Aljanu , Anya wannan yarinyar ba
ƴar Ruwa bace ba .
Malam Kadarko dake zaune a tabarma yana cin ɗumamen tuwo yake faɗin Haka . bin sa da
Kallo Umma tayi cike da Ɓacin Rai akan maganganun sa da kullum yake jifar ƴar ta dashi tun
tana jaririya har yi zuwa wannan lokaci. Bata bi ta kan sa ba ne ta nufi soro tana kama hannun
Ummul khairy dake raɓe raɓe ,don tasan kashe din baban nata akan ta , don yace tayi kuskuren
yin abun kirki a makarantar da take sai ya kakkarya ta .
Muryar Malam Kadarko Umma taji yana cewa " Jita fa ,Ni muni ke muni tayaya zamu haifa
wannan yarinyar in ba wurin dibar ruwa a rijiya da cikin ta an musanya mana ba , Nifa yarinyar
nan ba mutum bace ,shiyasa tun tana jaririya nace maki mu kaita rafi a saka ta , acan ta haɗu
da yan uwan ta Aljanun ruwa .
Jin kalaman sa yasa Ummu Yin narai narai da ido tana kallon Umman nata cike da zazzaƙar
Muryar ta na yara da kuma shegen Wayo kaman ba ƴar shekaru Shida ba tace " Umma na ba
zaki kaini Ruwa ba ko?. Ƙwallah ne ya ciko idon Umma , hannu tasa tana riƙo ta tare da cewa "
Taho Gare Ni Shalelen Umma , Ina takardar jarabawar taki ? ,Karima tun ɗazu ta shigo tace an
sallame ku an baku hutu ,ina kika tsaya baki dawo ba ?.
Umma tsoron Abba nake ji yace idan naci jarabawa sai ya karyamu Hannu . Amsan takardar
Jarabawar umma tayi tana dubawa . Murmushi ta saki tare da juyawa ga malam Kadarko da
bakin ciki ya ishe sa . Yeeeee Malam Shalelen Umma na Biyu tazo a duk yawon ɗaliban ajin su
,kasan dai yanda makarantar gwamnati ke da yawan dalibai . Kai mashaallh Shalele na Yau
ɗaya daga cikin kazan kiwo na zan yanka miki muci daɗi . Dariya Ummu tasa tana wangale baki
don ita ɗin yarinya ce mai matsanancin Fara'a .
Miƙewa Kadarko yayi yana nufowa inda suke , Amsan takardar yayi tare da cewa " Me yaci
sauran Ɗayan da baki Kada shi ba ,kin zo na ɗaya ? Ke dakikiya ce?? Kamin Ummu tayi
magana ne taji ya dauke ta da wani irin gigitaccen mari tassssss . Nan take shaidar yatsun sa
ya kwanta a saman jajayen suɓu² n kumcinta . Saurin faɗawa jikin Umman ta tayi wanda itama
ta riƙota tana rungume ta ƙammm . Haba Malam Duk wannan kokarin da tayi kace tayi
dakikanci??.
Bai tsaya bi takan Umma ba a tsiyace yake faɗin daga yau wannan karfan ta bar makaranta har
abada . Yana faɗin haka ya juya fuuuuu yana ficewa .
Cike da Ɓacin Rai umma har tana zubo da ƙwallah tace Wallahi baxan lamun ta ba , zuwa
makaranta ko kaman Shalele tayi . Ai baka mata komai na makarantar .
Cikin Muryar yarinta da wauta Ummu ta kalli Umma sai ta sakar mata fara'a tana cewa " Umma
daina kuka , tun da Abba yace na daina zuwa bazan ƙara zuwa ba . Kallon ta Umma tayi tana
shirin magana ne , Ummu ta mike tana cewa " Umma ina bokiti na ɗebo maki ruwan Sallar
magriba . Nufar madafi tayi tana ɗaukar bokiti tare da ficewa daga gidan ,daga ita sai kayan
makarantar gomnati , hijabin ta mai dashi kallabi tayi tana daurawa aka .
Abun mamakin shine tsiwar Ummu , sai da ta gama tsokanan fadarta da yara , da surutu
sannan ta dauko ruwan bokitin tana yo hanya .
A gyefen ƙaramin titin ne taji wani irin sauti na ƙarar diskon waƙe , wanda abun da bata taɓa ji
ba a titin nasu yasa ta juyawa tana kallon gyefen hanya . A jikin moton ta kyakyawan matashin ,
Tsayawa tayi tana bin sa da kallo kamar yar ƙauye , sarƙar wuyar sa take kallo , matashi ne da
ba zai wuce 20 yrs ba . Kuma ya iya mota ? Dama yara suna tuƙi? Abun da take cewa kenan a
zuciyar ta ,wanda bata yi tsammani ba taji Muryar sa kaman bana cikakken bahaushe ba yana
cewa " Ƴar boko taho ki samun ruwan ki nasa a mota na . A hankali Ummu ta matsa tana kallon
sa , kamin tace " Meye Sunan ka.?
Umar Farouk".
Murmushi tayi tana ware masa fararen haƙoran ta , gyefe da gyefen kuncin ta na lobawa , kana
tace " Sadauki kenan . Nidai duk mai sunan Umar Sadauki nake ce masa . Murmushi yayi yana
mmkin surutu irin na yariya ƙarama haka . Mene sunan ki Ummu khairy. Ta yi masa maganan
kai tsaye . Kamin yayi magana ne yaji tana cewa"
Zan baka Ruwan nan ,amma kai kuma kasan wahalar da nasamu har na ɗebo shi? . Yanzu idan
na baka kai me zaka bani?. Shiru yayi yana juyawa gyefe da gyefe hannun sa yasa yana ciro
mata sarƙar wuyar sa , kamin yace ga wannan ƙanwata zan baimawa da ,amma yanzu na baki
kyauta . Murmushi tayi tana cewa " Yauwa ngd Sadauki na.!
Ummuuuuu..!!! Taji kirar Malam Kadarko daga can nesa dasu . Wayyo Abba na ne tayi
maganan jikin ta na rawa ,bokitin ta sa hannu tana ɗauka cike da tangal² ta tsallaka titin tana
nufan can lungun da ta hango Mal Kadarko yana sababi .
Tana isa ya kamata ya fara ƙwaleta da mari , tun yanzu yanzu kina ƙarama kin fara bin Maza
,ina ga kin ƙara shekaru goma kan naki yar iskar yarinya . Mene yace maki ?? Cike da kuka
take cewa " Abba ba komai . Ingizata yayi yana cewa " Wuce gida dan Uban ki ,don idan ina
ganin ki ji nake kaman na badda ke daga doron duniya na huta..... Da gudu tayi cikin soron
gidan nasu....
*Bayan shekaru 10*
Tsaye yake a gaban mirror yana bin kansa da comb , Duk da Rigar Wanka ne jikin sa , Amma
bai rufe Tattu ɗin dake bayansa zuwa shafin wuyar sa fitowa ba . Kyakykyawa ne ko ba'a faɗa
maka ba ajin ƙarshe , Gyefen Fuskar sa kewaye yake da siririn saje , A hankali yaji takon
Mahaifiyar nasa , wanda miskilanci Bai saka sa juyowa ba , har ta ƙarako zuwa inda yake .
Hannun ta tasa tana rungume Yaron nata da ashekaru zai kai 30 a duniya . Welcome back to
Nigeria my Son . Lumshe idanun sa yayi yana juyowa tare da ɗan murmusawa wanda ko ba'a
faɗa ba kasan mai wannan murmushin ba sababben ta bane ba. I really tired Mom". Ayya Sorry
ka huta yanzu ,bari nasa wata maiid ta zo tayi maka massage nasan Gajiya ce ,zaka warware .
Ohk ". Yace yana cigaba da yin comb din , Mom ɗin tana fita daga side din nashi .
Yana nan tsaye ne yaji Motsin Shigowar wata ma'aikaciya tana neman iso . Ƙa'idar shi baya
magana da ko wacce ma'aikaciya , don shi ba gwanin magana bane , wannan yasata tsayawa
na minti biyu ,kamin ta kutso kai tana shigowa . A wannan lokacin ya sauya shigar sa ,zuwa
Boxer iya gwiwa yana zaune a sofa cushine , Idanun sa na akan Laptop . Cikin sauri
ma'aikaciyar ta ƙariko zuwa inda yake tare da zubewa gwiwowin ta ƙasa gaban sa . Niko
mamaki ne ya kamani ganin ƙaton namji jikin sa a murɗe irin na cikakkun tsayayyun sexxy ,
Arrogannt kuma ingarman namiji , ko riga babu jikin shi , gashin luff ya rufe saman ƙirjin shi
...hannun ta tamiƙa yana ɗaura mata ƙafafun sa tana fara matsa mishi a hankali yana lumshe
dulu dulun idanun sa na yaudarar ƴammata . Wayar sa ne ya hau ruri ,wanda jin hakan yasa
maid din kai hannu tana miƙa masa wayar , a handsfree ya aje wayar gyefe yana sauraren jin
Maganan ɗaya daga cikin Dadiron nasa . Ina Special Romantic House yanzu . Kaman ba zai
bata amsa ba ,sai kuma cike da izza da miskilanci yace " Nace kije ne , Ba na buƙatar kowa a
yau , ina buƙatar hutu . Jin wannan maganan tasa yasa Daga Ɗaya ɓangaren saurin cewa " Pls
Babe I will do massage for you, you here?. Miƙewa yayi yana janye ƙafarsa daga hannun
ma'aikaciyar kamin yace " Ohk I'm coming now".
***
Zufa ne ke tsiyayo mata ta ko ina , yayin da Kitchen ɗin nasu ya cika makil da Masu sayayya
hayaƙin ya gama cika idanun Ummu , Babu abun da take yi sai hura hanci tana masifa , tare da
jefa Ɗan Waken da hannun ta . kai Don ALLAH ku fita mana daga Waje , za'a sallami kowa
aaa.! Gani tayi kaman ana daɗa danno yaran Kitchen ɗin , wannan yasa ta cewa " Wallahi zan
dallama yaro mari KU fita mana.! Ni dai Allah ka sauya mun sana'a wannan