Showing 18001 words to 21000 words out of 34700 words

Chapter 7 - GIRMA YA FADI Book 1 Hausa Novels by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf By arewaauthors.com.ng.pdf

domin halayensu duk kusan daya ne, daman an ce wai
sai hali ya zo daya ake abuta, wannan haka yake. Halayensu duk kusan daya ne, nutsuwar
Imran daban take da ta sauran ‘ya’yan Farfesa, mutum ne da ya san ciwon kansa kwarai, yana
adawa sosai da aqidun Malam Bature, yanayin rayuwar shi na Sokkotawan usli ne ziryan,
hakan yanayin sutturarshi shadda ne, caftan ko babban riga a kullum, kai ka ce wani magidanci
ne, da wuya ka ganshi da wani kaya ba shadda da hula ba, ra’ayinshi kenan.
Bayan kammala karatun su sun samu an yi posting din su gari daya yin bautar kasa, wato jahar
Abia, duk da ba fanni daya suka yi karatu ba, shi Imran ‘civil engineer’ ne.
Sanda na kai aji hudu a sakandire duk wasu alamomin girma na ‘ya mace sun soma bayyana a
jikina, da yake ban fara karatun sakandire da wuri ba, ni kaina na san na sauya wane shekarun

baya. Abin nufi, halittar jiki da tsarin rayuwa. Zan iya kimanta shekaruna goma sha biyar a
lokacin, mun yi sabo sosai da Imran duk da cewa ba zaman gidan suke ba suna fafutukar
neman aiki.
Ba zan manta da yadda sunan “Abu” ya bace min a shekarar ba, ta dalilin Imran. Ya dauko mu
ne daga makaranta yana tuki ina gaban mota, ya ce, “Shin wai ke ya sunan ki ne?” Na dube shi
galala! Baki a bude ciki da mamakin wai duk kiran nan da ake Abu-Abu bai san sunana ba?
Wannan ai rainin hankali ne, don haka na juyar da kai ban amsa ba. Daga bayanmu Iftihal ta ce, “Kai Ya Im, da gaske baka san sunan ta ba?” Ya ce, “Gaskiya ban
sani ba, na ji dai kuna cewa wani abu wai “ABU”, ni ko na san kyakkyawar yarinyar kamar
wannan kallo daya za ayi mata a san ba sunanta Abu ba”.
Gaba daya suka tintsire da dariya, ni ko na yi murmushi kawai. Ya kafa mun ido kamin ya mai
da hankalin shi a titi cikin son karantar karbar da na yiwa zancensa. Na kalli can wani gefen
daban, cikin raina ina cewa, gaskiyan Iftihal ne, gaskiya ne ba mutun irin Yayan ta! Komi nashi
mai ban sha’awa ne, hatta furucinsa. Azizah ta ce, “A school ma ba a ce da ita Abu sai Zainab”.
Ya ce, “That is good, ZAYNAB, daga yau cikin ku kada wanda ya sake ce da ZAYNAB (ABU)”.
Wannan shine mafarin al’amarin. (Takori).

****

Na kwanta a daren nan ina maimaita kalmar “ZAYANB” da Imran ya ambata, na fadi ya fi cikin
carbi, amma ban ji na fadi dai-dai ba irin yadda shi ya furta. Na yi tunanin abubuwan da suka
faru a ranar tare da Imran na kasa mantawa. Idanuwanshi suka sanya zuciyata cikin wani
sabon al’amari da ban taba tsintar kaina ciki ba. Na yi kokarin in yakice Imran a zuciyata na
kasa, inda duk na juya shi ke zuwa cikin idanuna.
Na ji wasu sassa na jikina suna wani irin kaduwa da ban san na mene ne ba. Marana ya kulle
tamau kamar zan yi fitsari, don haka na rarrafa zuwa (toilet) na yi ta kakalen fitsarin amma bai
zubo ba. Na dawo daki na kwanta a dandaryar carpet, na ware fanka da A.C amma ban daina
zufa ba. Wannan al’amari ya tsoratani, domin wani al’amari ne sabo a gareni da ban taba tsintar kaina a
ciki ba, ban kuma san ko mene ne ba. Hawaye ya zubo min ina kallon su Azizah dake ta
barcinsu cikin kwanciyar hankali, na rasa abin da ke min dadi, na rasa mene ne shi wannan
abun, haka na rasa me zan yi ya gusar min da wannan sabon abu da nake ji cikin jikina har
kuma cikin kwakwalwata. Wannan shine mafarin shigar rayuwata cikin gararin da har yau take
ciki, cikin halin bakin ciki da dakacen ina ma ba a haifeni ba.
Da ban hadu da Imran ba, watakila da rayuwata ta ci gaba da garawa a yadda take. Wato ba
bakin ciki ba kuma farin ciki, sai godiyar Allah. Haduwata da Imran shine silar warwarewar
al’amuran rayuwata da na Innana da suka shige min duhu, suke damun zuciyata tun ina
kankanuwa. Har ila yau, Imran din ne sanadiyyar rushewar farin cikin rayuwata. Wata zuciyar ta ce dani, wannan al’amari da ke neman samuna ba alheri bane a tare dani, don
haka in nemi tsarin Allah. Wannan ita ce tarbiyyar da iyayena suka dora ni a kai, wato duk wani
abu da ya fi karfin iyawa ta, ya fi karfin sani na, ya fi karfin kariyata to in nemi tsari da kariyar
Allah, domin shine mai iko a kan komi. Sai na mike ina layi na yi bayan gida, na dauro cikakkar alwala na yi (brush) na fito na suturce

jikina na fara sallah, a cikin sujjada ta ina rokon Allah cikin yi masa kirari da ya yaye min
wannan matsala da ya daura min a kan Imran, ya kawo sanadin da Imran din zai bar gidan
gaba daya in huta.
Washegari na tashi da azumin tadauwa’i a bakina, kasancewar ranar Alhamis ce dama na kan
yi azumi litinin da alhamis. Wallahi sai na ji ni sawai, kaman an yaye mani. Na yi ta yiwa Imran
boyo cikin gidan har aka sha ruwa, gani nake kamar idan ya kalli kwayar idona zai karanto abin
da ke damuna game da shi, wanda ya hana mani barci daren jiya. Wannan ya faru ne tun ina da
shekaru sha biyar a duniya.
A daren Imran da Faruq na zaga gari cikin motar Imran din, Faruq ya ce,
“Yau tun safe ban ga Abu na ba, na shiga sassan Mama ya fi sau biyar ban ganta ba, ina cikin
damuwa wallahi”.
Imran ya yi murmushin da shi kadai ya san dalili yin abin shi, amma bai ce komai ba.
Ya yi parking a wani katafaren shopping complex suka shiga tare, shi Faruq ya dauka biskit din
nashi zai saya da baya rabo da saye. Don haka shi ya yi wani barin can daban yana
saye-sayen shi. Kafin ya zagayo inda Imran yake, ya ganshi ya cika kwando taf da kayan shafa
na mata (designers) yana jujjuya kwalbar turaren cool-water watau (Davidoff) a hannun shi,
turare ne mai sanyin kamshi na ‘ya macen da ta san sirrin da ke cikin turare.
Sai daga baya ne ya dauki kayan shaving din shi da biskit din nashi na (Hob-Nobs) ya yi gaba
ya bar Faruq da baki bude. Mamakin Faruq yaushe Imran ya yi budurwa bai sani ba? Ina ya je
shi kadai ba tare da shi ba har suka hadun?
Imran S. Bindawa, tamkar ya san me Faruq din ke sakawa a ranshi, sai ya yi murmushi ya
kanne mai idon shi daya cikin tsokana, ya ciza lebbanshi masu sulbi, ya matso dai-dai
kunnenshi ya ce,
“Don’t be nervous mana (kada ka ji tsoro) ba kowa na sayawa ba face kanwata, ZAYNAB”.
Ya yi gaba ya barshi nan yana mai son convincing zuciyarshi ta yarda da abin da take ji, amma
zuciyar ta ki yarda, karyatawa take da cewa, ba ZAINAB ya ce ba ZUBAIDA. Da Imran din bai yi
gaba ya barshi ba, da ya ji irin hautsinawar da ‘ya’yan hanjin shi ke yi, da kukan da akuyar
cikinsa ke yi. Ya kuma ga kallon firgicin da ya bishi da shi da gumin da ke ta yankowa daga
kowanne sako a jikinshi.
Ya shiga gyada kai tamkar kadangare yana girgizawa, yana gayawa kanshi cikin lallashi cewa,
ba da wani nufi Imran ya fadi kalaman shi ba, ba da wani nufi Imran zai yiwa Zainab kyauta ba,
abin da yake kokarin fahimta ba shine ba. Zumunci ne kawai da alkhairi irin nasa, domin shi
mutum ne mai alheri ga kowa ma ba Zaynab kadai ba.
Abinci ake ci bisa makeken dining din gidan, to amma me? Imran idanun shi kyar bisa
kyakkyawar fuskar Zainab, tana kai lomar ta a nutse ba irin su Aziza ba hannu baka hannu
kwarya. Idan tana tauna kumatunta duka biyu da tsakiyar habarta lotsawa suke ciki sosai. Komi
nata a yangace amma naturally ba wai tana sane take yi ba, yana tafiya ne da halittar Ubangiji. Sanye take da doguwar riga fara sol, ta matse dogon gashin kanta daga tsakiya da farin ribon
ya sakko ya kwanta lamban bisa dogon wuyan ta kamar na barewa. Zainab a mike take sosai
ga kuma alamun ‘mace’ dake neman bayyanuwa a jikin ta daga yanzu zuwa kowanne lokaci. Ya
kasa cin abincin sai ko juya cokali cikin farfesu? A bangarena, nima ba cin abincin nake yi ba, bugun da zuciyata ke yi a duk lokacin da na ga Ya

Im, na yau har ya fi na kullum. Kaduwar da sassan jikina ke yi yanzu, wane na daren jiya. To a
haka aka kare cin abincin ba tare da na ci wani abin kirki ba, haka tunda na dukar da kaina kasa
ban dago ba. Idan akwai abin da nake son gani, nake kuma gujewa ganin nasa, to Imran ne. ba
don komi ba sai don abin da hakan yake haddasa min a cikin gangar jiki da tsokar zuciyana
baki daya.
Karfe tara na dare ana falo har Abba ana kallon network news amma ni ina uwar dakinmu
dukunkune cikin bargo, ga littafin assignment dina a gabana na kasa hassala komi sai fama da
abin da ya dameni. Zan so in samu wani ya fassara mun ma’anar wannan abu dake damuna.
Abin bakin cikin shine, ni bani da kawa, su Azizah duka yara ne na girme su, ni kaina ban san
mene ne ba balle su da na kere sosai a shekaru. Kaduwar da jikina ke yi shi ya haifar mun da
zazzabi da sarawar kai, haka abin da na dauka ciwon mara ke karuwa mini. Ga (assignment)
din da na tabbatar in ban yi shi na bayar a gobe ba na rasa C.A dina na darasin physics, amma
bai dameni ba kamar wannan ciwon Imran da Allah ya dora mini. Hawaye masu zafi suka soma
biyo kuncina, na kara kudundunewa tamkar curin alkaki, haka al’amarin yana kara habaka a
tare dani.
Imran sanye da farar shirt (DKNY) da shudin wandon (Jeans) ya shigo falon, ya zauna ana
kallon da shi ba don kallon ne ya kawo shi ba. Ya mike tsaye cikin damuwa ya zura hannunshi
cikin aljihun bayan wandon shi kamar mai laluben wani abu, yana kallon su Azizah suna ta
shewar su, ya hanga ya duba iyakar ganin shi bai ga mai rikirkita shi ba a ‘yan kwanakin nan. Cikin mamakin rashin ganin ta da yake cikin jama’ar gidan a dan tsukin ya ce, “Azzy ina Zaynab
ne?” Iftihal ce ta amsa masa da cewa, “Tana can daki an ba ta assignment ta kasa shine take yi
tana kuka”. Ya ce, “To ku baku taimaka mata in kun iya?” Iftihal da Azizah suka dubi juna suka
kama baki, can kuma suka hadu suka tintsire masa da dariyar su ta ‘yan biyu mai ban haushi.
Ya shaka, ya kulu, kadan ya rage ya yi kwallo dasu.
“Mama ki ji Yaya Im don Allah, mune ma masu koya ma Zaynab karatu?”
Mama ta ce, “Zainab ce malamar su Azizah ai, in ta iya su koya a wurin ta, in ba ta iya ba duk
haka suke lalacewa”.
Hajiya Sa’a ta kyabe baki, saboda neman fitina babu wanda ya sako ta cikin zancen su, amma
sai cewa ta yi, “Ai tsiyar ‘ya’ya mata kenan duka tumaki ne, duk ba kwakwalwa sai ta
shashanci”.
Mama ta wani irin juyo ta dube ta, ta bude baki za ta yi magana Abba ya daga mata hannu
ganin yadda yaran suke kallon su, ta yi shiru tana ciccika tana batsewa, kiris take jira ta yi kuka.
Wannan dabi’ar Hajiya Sa’a ne, babu yadda za ayi a zauna da ita a tashi ba ta san abin da za ta
ce wanda zai bakantawa Azumi ba, ko da kuwa ta cikin ruwan sanyi ne. Ita kuma Azumin ba
hakuri, ba ta barin ko ta kwana da an tabo ta za ta hau suyi sama suyi ta yi kamar sa cinye juna.
Shi kuma Abban ya zuba ma takarda ido yana rubutu kai ka ce dabbobi ne ya aje ko dagowa
baya yi balle ya san suna yi. Ya kan ce cikin zuciyarshi mace daya ce ta ishe shi duba a duniya,
mace daya ce ta isa ya daga ido ya dube ta ya ji sanyi a zuciyarsa kuma ta yi mai nisan da har
abada ba zai kamo ta ba. Ta tafi da duk wata soyyarshi a kan diya mace. Don haka duk wata mace kallon ta kawai yake a
dage, a kaskance, a hagunce, ma’ana ba ta da abin da za ta burge shi da shi har ya bata
muhimmin lokacinsa a kanta. Sai zaman aure domin neman lada gami da kariyar kai daga
dattin zina, da rainon ‘ya’ya wanda wannan daman dole ne.

Ya dago ya dubi Imran idanunshi sun kada sunyi jazur da tunanin wani al’amari mai GIRMA da
ya taba zuciyarshi, ya ce da karfi, “Dan Abba! Jeka koyawa Zaynab assignment”.
(Kuskuren da iyaye ke yi kenan, musamman iyaye ‘yan boko da attajirai, kan dauki kebantuwar
‘ya’yansu mace da namiji baligai ba a bakin komi ba duk a cikin wayewar ne, wanda ko Annabi
(S.A.W) ya fadi mana kebancewar mace da namiji, na ukun su shaidan ne, musamman ga ita
Zaynab, da Abban ya yi tunani bai dace ya yi hakan ba, tunda shi da bakinsa ke yi mata nasihar
mu’amala ko ya ya da namijin da ba muharraminta ba).
Tamkar ya yi mai susa a inda ke yi mai kaikayi, da sassarfa ya nufo dakinmu. Har zuwa lokacin
kwance nake kudundune cikin bargo ga littafin a gaban filon da na ta da kai da shi, idanuwana
cike da hawaye amma basu kai ga zubowa ba.
Daga bakin kofa ya dakata ya tokare a jikin kofar da hannunshi na dama kafafunshi na daga
waje ya ce,
“Zaynab mene ne haka? Cewa aka yi in baki iya assignment din ba korar ki za ayi daga
makarantar?’
Shiru na yi masa tamkar da littafin yake magana, don ban san me zan ce masa ba. Shirun shine
mafi alfanu. Ganin haka ya karasa shigowa dakin gaba daya, ya ce, “ki tashi na ce, ki tashi ki
zauna Allah tun ban kwaye bargon ba”. Nan ma ba amsa, sai ido da na bishi dasu, luuu!
Wadanda suka kankance suka yi jawur, tamkar an gumbuda musu barkono. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Ya yi tsai da ransa cikin son karantar me ke damun
Zaynab? Ko me Zaynabu ke ciki? Ba tare da tunani ba kuma ya janye bargon ya wancakalar.
Subhanallahi! Ba shiri ya mai da mun abuna saboda kananun (minis) da ke jikina.
Ya juya mun baya da sauri cikin rawar murya yana fadin, “Ki tashi ki sa kaya in koya miki
assignment din. Ki tashi tun baki yi sanadin da na idasa kai hannu gareki ba, wannan hawayen
da kike zubarwa Zaynab ba zan iya jurarsu ba. Zaynab ya kike so in yi da raina? Kin hana mun
ganin kyakkyawar fuskarki, kin haramta min jin lafuzan ki masu taushi, kin hana mun barci
yanzu ma a ido biyun kina so ki mai dani wani zararre, haba Zaynab! Ke wace irin yarinya ce
mara tausayi da halin ko in kula……..”
Baki na saki galala! Ina jin abin da ko a mafarki ban taba yin na zan ji hakan daga Imran ba, ko
a tunani, ban yi na wai Imran zai taba fadin hakan gareni ba even in my imaginations! To ko
shima irin ciwon nawa ke damunsa? Bai san halin da nake ciki duk a kansa bane? Bai san duk
wannan kukan ba na assignment bane na rashin abin da zuciya da gangar jiki ke so ne, wato
shi YA IM, da nake ganin har abada ba zan samu ba.
Still bai juyowa ba ya saki wata irin ajiyar zuciya ya ce, “To ni yanzu Abba ya ce in zo in koya
miki karatu, me kike so in je in ce masa? Baki da lafiya ko-ko bakya jin magana?”
Da sauri na lalubi jallabiyana na zurma, na daura mayafin ta cikin wani irin dauri maras fasali,
cikin dasasshiyar murya na ce, “Ka yi hakuri Ya Im, bani da lafiya ne”.
Da sauri ya juyo ba tare da ya yi tunanin nasa sutturar ko ban sanya ba, ya tako da sauri ya
zauna a gaban gadona. Ya kai hannu goshina, “me ya same ki?”
Wani irin shock ya same ni ya kuma taso da lalurar da ke kwance lumus cikin jikina. Jikina ya
soma kyarma tun daga kai har yatsar kafata mazari nake. Ai Imran ba yaro bane, na san ya
fahimci halin da nake ciki, sai ya yi azamar janye hannunshi a goshina ya ja da baya.
Ya yi murmushi ya ce, “Zaynabu gaya mun irin ciwon da ke damun ki in ji ko zan iya maganin
shi. Nima bani da lafiya amma nawa bai yi tsanani kamar naki ba. Kuma ni ina kokari a kullum in

fi karfin zuciyata, in hana mata abin da na san ba alkhairi bane a tare da ita, in ce mata a’a,
wannan ba dai-dai bane, bana biye mata domin sharrin dake cikin ta Allah ya yi yawa da shi.
Sai ta kai ka garin DANA SANI ta baro, ita ba abin da ya dame ta. In yi hakuri in dauki kaddara,
in roki Allah ya kawo mun sauki cikin al’amarina. Ni Imran da kike gani a duk sanda na ji zuciya
na neman rinjaya na cewa nake, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’ouun!”
Wallahi sai na ji matsananciyar kunyar shi ta saukar mun, na kuma shiga maimaita
“Innalillahi…..” a fili da zuciyata. Wata nutsuwa ta musamman ta same ni, komi nawa ya koma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login