Showing 12001 words to 15000 words out of 34700 words
Chapter 5 - GIRMA YA FADI Book 1 Hausa Novels by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf By arewaauthors.com.ng.pdf
jiki shine, duk wannan
hidimar da Baba Sa’idu ke min, ko kadan baya burge Rabi, haka ko sau daya koda wasa bata
taba sanya hannu ta taba kayan da suka fito daga hannun Baba Sa’idu ba.
Kwankwalatin lemu ne da ni guda talatin, a karkashin gadon Rabi me fameka, kullum sai in ciri
daya in jefa a kofi, ranar da suka kare kenan ita ce ranar zuwan Baba Sa’idu. In ina wannan
kirgen, Rabi kallona take kawai, sai dai ba ta magana, na san tsabar takaicina ke hana ta
magana. A raina sai in ce, “Inna ai ke rayuwarki sai ke, tunda Malam da Ya Faruk ma basa
burgeki, shi Baba Sa’idu wane ne da zai maki gwaninta?”
Ni dai haka nan nake son Baba Sa’idu saboda kirkinsa, saukin kai da haibarsa, ba shi da
girman kai ko kadan, haka yadda yake sonmu ni da Ya Faruk yake kuma janmu a jiki, ko ‘ya’yan
cikinsa basa samun hakan.
Tun karatun sakandire ya so ya dauki Ya Faruk ya koma gidansa ya yi karatu a can Sokoto, Ya
Faruk ya ki don a lokacin babu wani babban da namiji a gidan kusa da Malam sai shi, sai ko
yanzu da manyan almajiran Malam su Lawal da Harisu suka tasa.
Baba Sa’idu Malam ya dankawa alhakin nemawa Faruk gurbi a Jami’ar Ahmadu Bello, inda
Faruk ya jima yana burin shiga, sai dai shi Farfesa so yake Faruk ya je UDUS don ya zauna
kusa da shi, don haka ba tare da shawara da Faruk ba, a can Danfodiyon ya nema masa gurbi
mai kyau, inda za ya karanci (computer-science). Dole Faruk ya koma gidan Farfesa
kwata-kwata, sai bayan watanni uku-uku yake zuwa mana hutu.
Na yi kewar Ya Faruk ba kadan ba, na yi kewar kulawa da kaunar sa, na yi kewar komai nashi,
domin shi Yaya ne mai karamci da nuna kauna, mai muhimmanta zumunci da kyautata shi, mai
gudun duk wani abu da zai zubar da mutuncina da na mahaifinmu. To amma ni kaina ina son ya
yi karatun, kasancewar sa babban burin rayuwarshi. Ya kan ce yana so ya zamo mutun irin Baba Sa’idu, yana sha’awar duk wasu halayen shi banda
abu daya, yana son ya zama mai hidima da iyayenmu da al’umma kwatankwacin Baba Sa’idu.
Kwaikwayon halayen Alhaji Sa’idu dole ne ga duk wani mutum da ya san ciwon kansa, mutum
ne wanda ilimi, daukaka, da duniyar da Allah ya ba shi basu sa ya manta alkhairin da wasu
tsirarun mutane su kai mishi ba, he’s really a model!
Kullum cikin hidima yake da Malam da almajiransa, da lafiyar shi, aljihunsa da karfinsa a
gwamnati, amma ko kadan wannan baya burge Inna Rabi.
Kai ni sai da na fara wayo ma na lura inda wanda Innana ta tsana da gani a duniya, take kuma
kyamatar abin hannunshi, to Baba Sa’idu ne.
Daga sanda ta ji rurin motarshi a kofar gida, kasancewar karar motar shi daban take da ta duk
sauran motoci masu zuwa wurin Malam, domin ba ta da kwaramniya sai dai ka ji wani irin
suuuuu! Kawai, to za ta shige dakinta ta bame da sakata, har ni ba ta kara nema na sai ya tafi,
don ta san inda duk yake cikin garin to ina nanike da shi yana ta haba-haba dani.
Yau da dare har mun kwanta na tuna ban saka kwankwalatin zuwan Baba Sa’idu a kofi ba.
Sadaf-sadaf na sauko daga gadon, kada motsina ya tada ita. To amma duhun dare bai sa na ga
kwankwalatin ba, don haka na kunna aci bal-bal na zarosu daga kasan gado.
Abin takaici abin bakin ciki, sai na taras baki daya an hade min su wuri guda baki dayansu,
bayan sun kusa karewa. Na tabbatar Inna ce da ta zo shara dazu ta sharo su daga kasan
gadon ta hade su waje guda. Kenan wannan watan ban san takamaiman ranar zuwan BABA
SA’IDU ba. Sai nasa kuka, ina yi ina karawa har da shessheka. Gunjin kukana ya ta da Inna Rabi, ta zuro fararen kafafunta kasa daga gadon ta ce,
“Kyautar Allah me ya faru?’
Cikin kuka na ce
“Bayan kece kika hade mun kwankwalatan ZUWAN BABA SA’IDU???”.
Ta yi shiru na lokaci mai tsawo, na dauka zagina za ta yi ko ta rufeni da duka, ko me ta tuna?
Sai ta yi ajiyar zuciya a sanyaye ta ce, “Ki yi hakuri Kyauta, ban sani ba na hade miki, amma
gobe ba zan kuma ba”.
Muka koma barci, amma har garin Allah ya waye idanuna basu rintsa ba, zuciyata ba ta bar
tukuki ba, haka ban bar yin nannauyar ajiyar zuciya ba, yadda na ga rana haka na ga dare, na
kuma tabbata ita ma Innar ba ta yi baccin ba sai juyi a kan gado.
Kwanaki biyar da yin hakan, ina durkushe a bakin ramin da na haka don wanke allona a ciki,
misalin karfe biyar na yamma, allo na nake wankewa don shiga sabuwar sura. A gefe toka ce a
cikin dan kokon ludayin duma da zan shafe allon da ita kamin in sake yarfa wani sabon rubutun.
Ina diban ruwa daga cikin kwarya ina wanke allon a hankali tamkar mai wanke jariri, na
tallabeshi da hannuna na hagu cike da tunanin Ya Faruk dake Sokoto, kowacce wainar yake
toyawa?
Na yi murmushi ni kadai a raina ina kwatanta Ya Faruk a cikin babbar makaranta, na tabbata
nan ba da jimawa ba zai bada mamaki.
Domin ko da nike yarinya kankanuwa ‘yar kimanin shekaru goma sha biyu, na san samun maza
irin Yayana, ba abu ne mai sauki ba.
Faruk ko a cikin tsararrakin shi daban ne a komai, haka yake da aji na musamman, sannan
jarumi ne ko ta yawan kunyaryakin da yake nomewa Malam, wanda aiki ne da almajirai goma
majiya karfi ke yi. Shi ba wani mugun kyakkyawa bane amma namiji ne ta kowanne fanni, kuma
baiwarwakin da Allah yai mishi suna da yawa, har ba zan iya lissafasu ba. Kasancewar shi da
namiji guda daya amma Malam bai taba takaicin rashin ‘ya’ya ba. Ya kan ce,
“Faruk daya ne tamkar da goma!
Da haihuwar yuyuyu, gara daya kwakkwara, ta kowanne fanni yana alfahari da Umar-Faruk….!!
Ban ji karar (horn) din mota ba ko kadan, nayi nisa a cikin tunanina, illa takun Baba Sa’idu na
GIRMA da nutsuwa, da ya bakunci kunnuwana. Yana kwarara mana sallama da wankakkiyar
muryarsa tamkar wani balaraben Madina, saboda yadda muryar shi ke fita tar-tar.
Ita kanta Inna Rabi na san ba ta zaci zuwansa a wannan lokacin ba, kasancewar ranar Juma’a
ce ba Asabar din karshen wata da ya saba zuwa ba, wannan tabbas ne, da tun kan ya shigo ta
shige dakinta ta rufe.
Da na wulwula allon na yar sai a kan gadon bayan Inna Rabi dake gefe tana barar gyadar miya,
ji kake tim! Ba kuma tare da na san aika-aikar da na aikata ba na yi tsalle na rikeshi ina “Oyoyo
Babana!”
Mikewa daya Inna Rabi ta yi sai ji na yi tana fizgata tana cewa, “Gafara ki bawa mutane wuri”.
Shi kuma cikin ladabi ya russuna rike dani tamau yana “Allah ya baku hakuri Inna, Inna Allah ya
huci zuciyarku”.
Ta ce, “Sakar min ‘yata na ce Sa’idu, na yi ma kama da wadanda kudi ke rudinsu, a yaudare
su? Da zuciyar ba ta huce ba da na kawo yau ne?”
Kanshi a duke, cikin tsananin girmamawa da kaskantar da kai, ya ce,
“Bani da kudin da za na yaudareku dasu Inna!!!
Har gobe ni almajirinku ne dake neman albarkarku, dake neman abin da za ya sanya a bakin
salatinshi daga tukunyarku.
Hakurin nan nake dada badawa, wanda har abada ba zan daina ba, ko da yawun bakina zai
kare.
Dukkanmu ‘yan Adam ne da bama sama da aikata KUSKURE, ‘yan adam ne da shaidan ya yi
alkawarin janmu ga ba dai-dai ba, kamar yadda ya ja Ubanmu Annabi Adamu Alaihis Salamu.
Amma da ya roki Ubangijinsa, sai ya yafe mishi bai barshi ya rafkana ba.
To Ubangiji ma kenan yana afuwa a garemu balle ku mutane?”
Ta fiddo fararen idanunta ta zube su a kanshi za ta fara lailayo ire-iren ashariyar da ta ke narka
mishi kenan Malam ya shigo gidan rike da tazbaha yana ja, ya ce,
“Subhanallahi! Rabi’atu meye haka? Me zan gani haka? Saketa mana, karyata za ku yi?”
Ni kam sai kuka nake ganin Baba Sa’idu yana kuka, abinda ban taba gani ba. Ta sake ni bayan
ta ja wani mikakken tsaki da wasu dunkulallun hawaye da suka biyo kumatunta, ta shige
dakinta. Bammm! Ta danno kofa, muna ji bayan sakata da ta sanya har kuba tasa ta kara kulle
dakin. Allah kadai ya san halin da take ciki a yau. Haka ya ci gaba da durkuson bai dago ba. Malam ya samu wuri ya zauna yace,
“Sa’idu lokaci ya yi da kai da Rabi za ku fuskanci gaskiya, ku daina aiki da karya, lokaci ya yi
da za ku fuskanci abin da ya dace, wannan rayuwar ina za ta kaimu? Meye amfaninta?”
Ya dago ya dubeni yana murmushi. “Yanzu cikata in aike ta tukunna”. Baba Sa’idu ya cikani, ba
tare da ya dago ya dubi Malam ba. Ya ce, “Maza Zaynabu-Abu a samowa Sa’idu ruwa a randar
Inna Dubu”.
Na ruga da gudu dakin Inna Dubu amma kamin in shiga sai da na rabe na share hawayen
idanuna. Na ce, “Inna kawo sabon kwanon shan ki a bawa Baba Sa’idu ruwan randarki”.
Ta ce, “Abulle ‘yar gidan Sa’idu, ko dai kema can Sokoton za ki bisu ne wajen Yayanki?” Na yi
murmushi domin ta yi mun susa a inda ke min kaikayi, na ce,
“Ai kema kin san Inna ba za ta bari ba.
Tun yaushe Baba Sa’idu ke cewa in bishi muje Sokoto a sani a makarantar su Iftihal, in na
fadawa Inna tasa ludayi ta bubbuge min baki”.
Ko kamin na iso sun gama maganar Innana sun koma ta karatun Faruk da amfanin gonar Baba
Sa’idu dake nan Gwarzo. Isowana duk suka maido hankulansu gareni suna min murmushin su
mai cike da kauna. Tsakanin Malam da Baba Sa’idu na kasa tantance wanda ya fi kaunata,
dukkaninsu abu daya nake gani cikin kwayar idanunsu tun ina jaririya. Na russuna na mika mishi ruwan randar Inna Dubu, garai-garai da shi, ga sanyi kamar na firinji,
duk gidan shi muke sha, abin kamar karama, ruwan randar Innar Ya Faruk ya fi na randar kowa
sanyi, gardi da ratsa zuciya. Don haka ne kowa ya zo cewa yake a debo mishi ruwan randar
Inna babba, ban da Ya Faruk mai son na Inna Rabi. Ya kan ce shi ta fi mishi ta kowa sanyi, duk da a zahiri ba hakan bane, illa kasancewar shi wani
mutum mai son faranta mata a koyaushe, da kokarinsa na gusar mata da bakin cikin dake
damun zuciyarta, amma duka a banza, wai kirari a gidan kurame.
Baba Sa’idu ya ce,
“To Zaynabu ni za ni koma, yau ban kawo miki komai ba saboda nima tafiyar ban shirya mata
ba. Na je taron ‘convocation ’ ne a nan cikin Jami’ar Bayero, na ga don me zan koma ban biyo
ba tunda gani a cikin Kano?” Na ce,
“Babu komai Baba Sa’idu, Allah ya kaika lafiya”.
Ya ji dadin addu’ar da na yi mishi. Ya kamo hannuna ya ce, “To meye sakonki ga yayanki da su
Aziza?” Na washe dukkan hakorana ina fara’a, don jin dadin ya tuna min da Ya Faruk wanda
dama ke makale cikin raina.
Na ruga da gudu dakin Inna Dubu inda na boye kullin (awara da yaji) da Innar ta soya dazu,
kasancewar shi mai son ta. Haka kawai yake sayo waken suya (soya-bean) ya kawowa Inna
Rabi ya ce tayi mishi Awara, ya yi ta ci yana dangwala yaji yana santi. Wani zubin ya kan ce,
“Amma dai ana hadawa da kwai ko Inna?” Sai ta yi murmushi ta ce, “Eh, ana hadawa amma
kwan wake”.
Na dawo da gudu na kawo mishi, na ce, “Ka kai mishi wannan”. Bai damu da maikon da ya
mamaye ledar ba ya karba ya sanya a aljihun farar sassalkar shaddar dake jikinshi da a kalla ta
ba naira dubu talatin baya. Ya ce, “To ina na su Aziza?”
Na sunkuyar da kai ina murmushi na ce, “Ai basu sanni ba, kuma su ‘yan gayu ne basa cin
awara”. Daga shi har Malam dariya na basu. Ya ce, “Wa ya gaya miki haka? Kada in kara jin
haka, dake dasu duka daya kuke, sai ma ke da kika fisu. Ke da kike da haddar Izfi talatin a cikin
kanki, su ko ko izfi biyu basu haddace ba, wawaye ne kurum! In zan dawo zan kawo miki su
suyi sati tare da ke, ki dinga koya musu irin karatun nan naki mai dadin sauraro, mai kira’ar ‘yan
Aljannah (warshu), kin ji Zaynabu?” Na ce, “Na ji Baba Sa’idu. Allah ya kaika lafiya”.
A ranar sai a dakin Inna Dubu na kwana, don Inna na har washegari ba ta bude kofar ba. Kayan
abincin da Baba Sa’idu ya zo mana dasu su doya da dankali, da safe Inna Dubu ta kasa ta
kaiwa kowacce kasonta kofar dakinta.
Inna na bude kofa ta ci karo da tsarabar Baba Sa’idu, ni kuma ina gefe ina rubutuna a allo da
ban samu jiya na yi ba saboda zuwan Baba Sa’idu. Sai gani na yi ta samu fanteka tana jida
tana fita dasu tana kaiwa almajirai. Tana dawowa ta hango katon din taliya da na kayan shayi a
gefe, suma ta kinkima ta je soro ta rabar. Daga matan gidan har ni babu wanda ya yi mamaki,
kamar yadda babu wanda ya daga ido ya dube ta, don in da sabo mun saba ganin abin da ya fi
haka.
Akwai sanda ta zuba turamen Holland da ya kawo musu da sallah cikin masai, ta gidan
gabadaya, ranar ne ta ga bacin ran Malam irin wanda ba ta taba gani ba, Inna Dubu ce ta
gayamasa, yace,
“Wannan almubazzaranci ne, kuma masu almubazzaranci iyalan shedan ne. In bazata daura
ba to ta bayar, amma ba za ayi wannan almubazzaranci a gidansa ba”.
A dan tsukin na dage da addu’ar Allah yasa in ci makarantar sakandiren da nake so wato
GGSS Kabo, ba don komi ba sai don su Hafsisi ‘yar dakin Inna Dudu da Indo dake can aji biyu
‘yar dakin Inna Rakiya, mun shaku dasu sosai, musamman Hafsisi da take kusan tsarata,
shekaru biyu kawai ta bani. A satin Ya Faruk ya zo, amma ba jimawa zai yi ba don basu yi hutu ba. Na rasa inda zan sa
raina in tsaida murnar, haka shima. Yayo min saye-saye masu yawa har da sabuwar jakar
makaranta da wata na’ura mai koyar da harshen Turanci. Na ce,
“Ya Faruk ina ka sami kudi haka, kai da kake karatu?”
Ya ce, “Karatun ma ai don ku nake yin shi Kyauta, haka komi nawa naku ne. Kada ki damu da
wannan alawus din dalibai ne da ire-iren kudin da Farfesa yake bamu ni da Imran wanda ni
bana bukatarsu, saboda ci da shana da makwancina duk a gidansa yake.
Iyalin Farfesa mutane ne masu karamci da suka san hakkin dan adam, suna kyautata mani
sosai, haka shima Abban komi bai banbanta ni da Imran”.
Na tambaye shi ko wane ne haka? Ya ce, “Shine babban dan Farfesa tare suke karatun. Ya ce,
“Imran mutum ne mai kirki da dadin mu’amala, yana da saukin kai kamar Farfesa, I would like
you to meet him even once (zan so kwarai watarana ki hadu da shi ko da sau daya ne). In kika
zauna da shi wuni daya, za ki so ci gaba da zama da shi muddin rayuwarki”.
Yawan labarin Imran da Ya Faruk ke bani, na irin rayuwar shi da yadda yake tafiyar da ita, sai
na samu kaina da son ganin sa. Bayan wata guda jarrabawarmu ta fito, inda na ci makarantar
‘yammata ta gwamnati dake garin Gashuwa ba inda na so in samu ba. Muka yi ta kuka ni da
Hafsisi, sai Malam ya ce, “Me ya yi zafi? Bari Sa’idu ya zo gobe in da abin da zai iya a kai, a
maida ke Kabon”.
Baba Sa’idu bai zo ba sai a sati na sama, saboda ya yi tafiya zuwa Brunei. Muna bakin motarshi
ya miko min wata ‘yar akwati kankanuwa mai tsananin kyau, ya ce,
“Ga tsarabarki Zaynabu”.
Na karba cikin mamaki ina juyata a hannuna, cikin raina ina raina ‘yar tsarabar a zuciyata, tunda
kuwa akwatu ya saba ciko min da kaya a duk sanda yai tafiya irin wannan. Da kyar na bude
akwatin cikin gidadanci. Wani haske ne ya dallare min ido, musamman da yake a cikin rana ne.
Duk da karancin shekaruna a lokacin jikina ya yi sanyi, na san ko yaya ne wadannan zobba
guda biyu ba karamin abu bane. Kuma a matsayina na ‘yar Malaminsa kawai, ban kai matsayin
da zai mallaka min wannan abu mai daraja ba. Ya lura da rashin kuzarina, ya kamo hannuna
muka shigo soron gidan, almajiran Malam na ta gaishe shi yana yi musu kyautar shi da baya
gajiya.
Sai da suka dauke kafa ya ce dani cikin murya kasa-kasa “Ko me Inna za ta yi dake, kada ki
bari ta yi kyauta da zobban nan naki. Ba gwal bane, ya fi zinare daraja, kusan rabin abin da na
mallaka ne. Ki kula dasu sosai, a nan gaba za su yi miki amfani”.
Sun dade suna magana da Malam, inda ya yi mishi zancen makarantata. Kai tsaye ya ce, “Ai
tuni ya yanke shawarar tafiya dani Sokoto, ya sanyani makaranta tare da su Aziza in ba haka
ba, ba zamu taba shakuwa ba”. Malam ya shiga girgiza kai yana cewa,
“Ba zai yiwu ba, Sa’idu, na ce ba zai yiwu ba. To a barshi a hakan!”.
Ya tashi ya karkade babbar