Showing 21001 words to 24000 words out of 34700 words
Chapter 8 - GIRMA YA FADI Book 1 Hausa Novels by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf By arewaauthors.com.ng.pdf
normal, na sunkuyar da kai kasa cike da burin ina ma a ce…. kasar za ta tsage da na shige na
huta da kunyar Ya Im, amma shi bai damu ba. Sharewa ya yi ya bagarar ta hanyar yin zaman direshan a gabana bisa carpet, yayin da ni nake
zaune a gefen gado na zubo fararen kafafuna kasa, na tokare gefe da gefena da hannaye na
biyu. Imran ya sunkuyo ya leka fuskata muka hada ido, ya sakar mun lallausar murmushinsa
cikin son ganin na saki jiki na daina jin kunyar tasa. Na sanya tafukana na rufe fuska ina
murmushi.
Ya ce, “ZAY-NA-B”. Yadda ya kirayi sunan sai da tsigar jikina gaba daya ya kara tashi, ban iya
na amsa ba. Ya ce, “Maza sauke hannuwanki daga fuskarki, kada ki sa in taba su”. Da sauri na
sauke amma har yanzu ban bari mun hada kwayar ido ba. Ya ce, “Na ce ki gaya mun ciwon da
ke damun ki, a kalla idan ban baki maganin sa ba zan baki shawara a matsayina na babba
wanda ya fi ki shekaru. Idan kin barshi a ranki kin ki fadi, mai yiwuwa ne ya ci gaba da cutar
dake ba tare da kowa ya sani ba, wanda a karshe hakan zai iya zamowa illa ga lafiyarki”.
Ya yi shiru yana mai kokarin son mu hada ido amma na ki. Na yi tunanin dukkanin maganganun
shi a kan hanya suke, ba wadda babu gaskiya a ciki. Don in ban mance ba Baba Sa’idu ma ya
sha gargadi na a kan barin sanya abu a rai illa ne ga lafiya da kwakwalwa.
To amma ni kaina wallahi ba na ce ga hakikanin abin da ke damuna ba, abin ya fi karfin
bayyanuwa, ya fi karfin kwatance, ya fi karfin duk kokarin harshe na ya fassara shi.
Unxpressable feeling kadai zan iya kiran al’amarina. Wanda in ban da ni da zuciyata da kuma
Ubangijin da ya assasa mani shi a ruhi da gangar jiki, babu wanda ya san iyakar sa. Abin da na
sani kawai shine, “I need Imran! I need Imran!! I need Imran a tare dani”.
To amma idan na fadi mishi ai kamar na zubar da mutuncin kaina ne, na zubar da tarbiyyar
gidanmu, duk da ban san wannan abun mene ne ba? Na san ba abun kirki bane, haka ba abin
alheri bane kamar yadda ya fada mani. Don haka na kasa magana, tunda na fara tunanina bai
katse ni ba. Ya yi nacin ya yi juyin duniyar nan amma na ki magana har ya gaji ya zuba mun ido da alamun
ranshi ya baci, duk kuma sai na ji babu dadi. Wasu hawaye suka zubo min na sanya bayan
hannuna ina sharewa. Ya mike zai fita ba tare da ya ce dani komi ba, har ya kai bakin kofa ba
tare da ya juyo ba, ban san sanda na samu kaina ina mai cewa cikin rishin kuka “Ka yi hakuri Ya
Im, mara ta ce take ciwo!”.
Ya juyo a hankalce ya dawo, hannayenshi duka biyu cikin aljihunshi, ya dube ni sosai, na nutsar
da kaina kas, kamar in ce, “Wayyo Allah!” Ya fi mintuna biyar yana kallo na kamin ya ce, “Al’ada
kike yi ne ko zaki yi Zaynab?’
Da wata muhimmiyar kunya da haushin kaina mai tsanani suka taso suka kara lullube ni ban
san sanda na fashe da kuka ba, yau tozarcin duniya na gama jin shi a rayuwata, da wanne ido
zan daga in kuma duban Ya Im? Na wulakanta kaina na tozarta kaina na yi abin kunya.
Imran ya ce dani kamar cikin tsawa, “Ba tambayar ki nake ba za ki sakar min sauti sai kin tara
mana mutane a ka?” Na hadiye kukan gaba daya ji kake “mukut”, sai hadiyar rai nake tare da
fyace majina da bakin dankwalina. Ya sake maimaita tambayar sa, wannan karon babu alamun
wasa cikin maganarshi. Jikina na karkarwa na ce da shi, “A’a, ban ma jima da gamawa ba”. Ya yi ajiyar zuciya ya sassauta murya ya ce, “To meye abin kuka? Daga na tambaye ki don in
san maganin da ya dace in amso miki sai ki bare baki ki fasa min kuka a zaci ma wani mugun
abu nake miki, yanzu idan su Azizah suka zo suka ga irin wannan kukan da kike kamar na fitar
rai suka tambaye ki me za ki ce musu? Maza share hawayen nan ki mai da mood din ki, mu yi
karatun tun ban sa kafar wando daya dake ba”.
Na koma cikin nutsuwata, na share fuskata tas na dauko littafin na budo mishi aikin. Ya zauna
gefena yana dubawa, ya ce, “An excellent handwriting! Zaynab haka kika iya rubutu?” Sai
yanzu ne na yi murmushi, domin dai ni mutum ce mai son yin abin yabo a yaba mani, yana kara
(encouraging) dina. Cikin dan lokaci Ya Im ya fahimtar dani abin da na kasa har ma da abin da ban sani ba, da
dabarun cimma nasara a darasin ‘Physics’ da muke cin kwakwa a kan shi ni da su Azizah. Ji na
yi in zamu kwana muna karatun ba zan gaji ba, don kuwa Imran ba dai hikimar koyarwa ba.
Imran S. Bindawa cool ne, reserve! Ga wani lafiyayyen kamshi da ban taba jiba dake fita
bakinsa (Albaan mouth-fresh) in yana magana. Sai nake tambayar kaina dama akwai wadanda
Allah ya halitta da kamshin baki ne? Ko da yake in ban manta ba ai Iftihal ta ce Yayanta daban
yake a cikin al’umma. A haka su Azizah suka shigo kwanciya suka tadda mu, karfe goma sha daya da rabi na dare,
don su tuni har sun yi barci a falon taso su aka yi. Suka saki baki galala! Suna kallon mu don
basu zaci har lokacin yana nan ba. To shi kuma sai ya bi duk ya daure fuska, ya buga musu
tsawa ya ce duk su dauko nasu littafin. A take kowacce ta shiga taitayinta barci ya nemi inda ya fito. Karatu ya dawo sabo, ya hadamu
gaba daya yana koya mana, bai kyale mu ba sai da ya tabbatar mun gane, ya bamu aiki muka
gwada mai a kan idonshi ya gani, sannan ya fita ya ja mana kofa, ko kallon mu bai kara yi ba.
Azizah tana ta korafin ita dai da Abba bai ce Imran ya koya min karatu ba, gashi nan yanzu ya
jawo mana masifa sai ya mai damu wasu alhuda-huda, su kam sun shiga uku kenan. Iftihal
dake ta fi kowa son Ya Im cikin gidan ta ce, “Ai ba zama zai yi ba, baki ji Abba ya samo masu
aiki ba? Yanzu haka next week in ya tafi duk da fadan shi ke da kanki za ki yi kewar shi”. Sai na ji duk hankalina ya tashi, Imran zai tafi aiki, ina? Ni kuma ina zan sanya rayuwata?
Kasancewana tare da shi a yau na wani lokaci mai tsawo, ya kawo sauki 50% cikin ciwon
zuciya da gangar jikina, ya wanke wani babban kaso na ciwon shi dake damuna, ya kuma kara
gina wani makeken al’amarin da ya wuce na jin shi a gangar jiki kadai, maimakon haka, sai ya
shigo har cikin bargo da kasusuwana.
Ni kaina na san yau idan na ce idanuwana sun ga barci, to wannan karya ne. cikin kowanne
juyina IMRAN ne, cikin kowanne kiftawar ido IMRAN ne, cikin kowanne zama da tashi IMRAN
ne, cikin kowanne kwanciya da mikewar kafa IMRAN ne, cikin kowanne mafarki da ido biyuna
shi din ne dai kadai ya mamaye, ya babbake yayi babakere a ko ina, bai barni da ko sako daya
da zan sanya tunanin kaina ba.
Da safe na sanya (uniform) dina cikin sauri ne saboda makarar da na yi, su Azizah tuni sun
gama suna diniing suna karyawa, wannan ya samo asali ne da rashin isasshen barcin da na
samu daren jiya, bayan sallar asubahi kuma wani nannauyan wahalallen barci ya yi awon gaba
dani mai cike da mafarkai na ni da Y Im cikin wata irin rayuwa mai dadi, da kyar Mama ta tashe
ni.
Na ja cambas na daura na juya a hankali ina kallon kaina a mudubi. Ban yi mamakin ‘yar
zabgewar da na yi ba cikin ‘yan kwanakin nan da duniyar Imran ta sanya ni gaba. Banda su
Azizah shiriritattu ne ya dace su fahimto sauyuka da dama a tare dani, to ita kanta Mamar su
haka take, ko cikin dare ba ta rabo da call na emergency case, don haka ba ta samun nutsuwar
da har za ta fuskanci kananun abubuwa kamar wannan.
Na ci gaba da kallon kaina cikin mudubin, ba wata kwalliya na yi ba ban da mai da farar powder
da na shafa, amma ni kaina ina alfahari da ‘yar zagayayyar kayatattar fuskata, wadda in ba son
kai irin na dan adam ba, zan iya cewa alhamdulillahi, babu abin da Allah subhana bai kawatata
da shi ba. Fararen idanu, giran ido kakkaura, dogon hanci da tsararren baki mai daukar hankali. Idan
kuma aka yi maganar zubin halitta abin sai shukrah ga Maqagina, domin ko yaro dan shekaru
biyar ba zai iya yi min kallo daya bai maimaita ba.
Farina kuwa ba fari ne sol ba, ja ce ni kalar uslin Abzinawa na Damagaram. Ko a farce ba za ka
ce na hada jini da Bahaushe ba, domin komi nawa har yatsun kafata irin na Inna na Rabi ne.
Na dauki jakata (school bag) na rataya a kafadar hagu, nasa kai zan fita, Imran na sawo kai zai
shigo sai muka yi karo garam, da goshinmu, kasancewar nima ba baya ba ce wurin tsawo zamu
yi kafada da Imran, illa ya nuna min kaurin jiki.
Na yi saurin ja da baya ina ta faman ba shi hakuri don ni har ga Allah ban ji tahowar shi ba,
kasancewar shi mutum mai nutsatstsen taku, duk na gigice saboda yadda ya yi min jiya na dan
fara shakkun sa, da alama dariya na ba shi. Ya ce, “Ni ne mai ba da hakuri Zaynab, kin kwana
lafiya?” Kalaman shi sun matukar bani haushi, wannan rainin hankali ne, kuma kamar son jin halin da
mutum ke ciki ne, wanda shi din ba zai maganta mini ba, ba sai ya kyale ni in ji da ciwona ni
kadai ba?
“Don haka maganar na kwana lafiya ko ban kwana lafiya ba, ba damuwar ka bane….”
Magana nake a zuci, ban san cewa har ta fito fili ya ji ba. Ya yi murmushi kamar bai ji ni ba, ya
sake matsowa gareni ya russuna ya dauko min jakata da ta fadi a dalilin karon mu ya miko
mani, ya sake cewa,
“Kin kwana lafiya Zaynab?”
Wannan mugun mutum ne, bani da zabi ban da na daga mishi kai domin ya gama kashe mun
jiki da fitinanniyar muryarshi. Ya ce, “Amma ni kin ga ban kwana lafiya ba, Zaynab saboda ke!”
Ya ci gaba da mugun murmushin, yana magana ne kasa-kasa yanda in har akwai wani cikin
dakin bayan ni dake kusa da shi, duk kasa kunnen shi ba zai ji abin da yake fadi ba. Na kyabe
baki na ce, “Allah yai maka magani”. Dariya ya yi ya ce, “Ya yi mana magani baki dayanmu za ki
ce Zaynab. Ba gara ni ba, amma ke maganin naki ai mai GIRMA ne, wanda ni kadai ke iya
maganta miki, kuma ba zan yin ba, saboda ni mai hankali ne sabanin ke da kuruciya ke
dawainiya dake”.
Ya sake jifana da mugun murmushin, sannan ya miko min ledar da ke hannunshi, tuni na yi
suman tsaye. Wani takaici ya zo ya tokareni a kahon zuci kamar in yi aman zuciya don bakin
cikin maganganun da ya yaba mani. Bai kuma bani damar in yi magana ba ya juya yana cewa,
“Ki yi maza ki tafi makaranta kin zauna nan kina shirme, tun baki tafasa ba kenan wannan in
kika kara shekaru uku a gida ban san me za ki zama ba, gara Abba ya tattaraku da zarar kun
kare makarantar nan ya ba wani mai tsautsayin sadakar ku. Balle ke Zaynab irin jarababbun
matan nan ne wallahi (nympho), duk wanda ya aure ki ya shiga uku”. Ya juya zai fita yana mun
dariyar keta, na ga idan na bari ya fice ban yi wani abu ba na fadi ba nauyi. Idanuna suka ciko
da kwalla, bayan kadawa da suka yi suka yi jawur na ce, “IMRAN!”
Tunda yake yaran gidan baki dayansu babu wanda ya taba gigin kiran shi da Ya Imran ma balle
IMRANAN gabagadi. Iyakacin kowa YA EM, don haka ya hanzarta juyowa cike da mamaki ya
dube ni, da na wulwula ledar da ya bani na maka masa, niyyata ta fasa mun wannan bakin dake
tozartani, ta illata wannan halittar da ke jan zuciyata ga abin da yake goranta mun a kanshi. Amma sai ya yi saurin dukawa ledar ta wuce ta saman kanshi, kayan shafar da ke ciki kowanne
ya yi nasa wuri. Na yi murmushi na ce, “Baka da abin da za ka bani Imran, kamar yadda baka
da maganin da zai yi maganin ciwo na, don ‘yan mazan naka da kake tinkaho, bai yi isar da zai
isar da jarababbiya kamana ba. Amma ka san ina da surar da in maza dari nake so a rana zan
samu, kuma daga yau zan fara, Allah za ka yi nadamar wadannan kalaman da ka gaya min”.
Na wuce shi nan dafe da lebban shi yana girgiza kai kamar kadangare yana mamaki na
gasken-gaske amma ya kasa magana. Kan mu zo makaranta kiris ya rage in yi kuka a gaban
su Azizah, amma na yi kokari na daure na cije ina ta kukan zuci. Hirarrakinsu ko daya ban
tsoma baki ba, haka fuskana babu annuri. A cikin aji ana ta aiki, amma ni ban rubuta komai ba, ashe wai har aikin aji (class work) malamin
ya bayar suka yi suka gama ni ban sani ba, na yi nisa a tunanin rashin mutuncin da Imran ya yi
mani.
Malamin yana bin kowa yana sa mishi hannu har ya zo kaina, ya ce, “Ke ina aikin naki?” Na yi
firgigit na dube shi, a sannan ne Azizah da Iftihal dake bencin bayana suka shiga zungurina da
nasu litattafan, na mika hannu ta karkashin bencin na karbo na fito masa da shi kamar daga
jakata na fiddo. Kuskuren da na yi shine, duka biyun na hada masa wato na Azizah da na Iftihal na kuma ba shi
ba tare da na duba ba. Ya karba yana dubawa duka biyun, ya daga murya ya ce da ‘yan ajin,
“Wace ce Azizah Sa’idu?” Gaba daya aka nuna Azzy da ta yi tsuru-tsuru. Ya sake cewa, “Iftihal
Sa’idu Bindawa?” Wata kabila Ngozi ta nuna Ifty. Ya nuna ni ya ce, “Wannan kuma fa ya sunan ta?” Aka ce da shi, “Zaynab Aliyu”. Ya ce, “To ku
taso dukkan ku mu isa wurin principal, yau idan uban ku gwamna ne ya daure ni har sai igiya tai
rara. Dabbobin banza ni za ku mai da shashasha! Na zo duniyar na kuma je makaranta tun kan
ayi cikin uwarku balle ayi tunanin haife ta, shine za ku mai dani sakarai?” Su Azizah suka tsugunna a kasa suna ta ba shi hakuri har da hawayensu, don ba abin da suka
tsana a rayuwarsu irin a kai su wurin shugabar makarantar a ce sun yi laifi, don ta san Baba
Sa’idu farin sani a take za ta gaya masa.
Ni ko ko gezau, don zuciyata ta riga ta kekashe da bakin cikin Imran da ya yiwa zuciyata katutu,
don haka don an duke ni gani nake dukan ba zai shiga jikina ba ko da kuwa da bulalar karfe ne.
Ya ga ni ban ba da hakuri ba, karewa ma wani gefen daban nake kallo kai ka ce ba dani ake
case din ba, kuma dama shine (discipline master) din makarantar baki daya, kowa ya san
Malam GG watu Garba Gumel a wurin mugunta babu na biyun shi duk fadin makarantar.
Ya ce, “Su Azizah su koma su zauna, ni kuma in taso in biyo shi”. Ban yi musu ba na karkade
rigata na bishi a baya, Iftihal ta biyo ni tana ta ba shi hakuri ya daka mata tsawa ya ce ta koma
mazauninta, ya kuma sanya monitar ajin Suhaila ta yi mai gadinsu, idan suka fito ta kira shi a
waya ta gaya masa.
Tafi-tafi ina bin shi kamar jela, ina gayawa kaina na cancanci a hora ni, wauta ce tun farko ta
hanani gane Imran ai ba tsarana bane da zan kallafa zuciyata a kansa, don haka kome GG da
Imran suka yi min dai-dain su ne.
Wani kazamin (student toilet) ya sani in wanke kana tafiya kana karo da busasshen kashi, zarni
kuwa ba a magana. Hankalina ya tashi, na soma hawaye amma GG in ban da narka min zagi
ba abin da yake.
Cewa yake, “So nake in ga matsayin ubanki a garin nan, in tabbatar da cikar ki ‘yar masu kudi.
Allah yasa ‘Yar Aduwa ne ya haife ki, da kike wannan bunkasar. Kin ganni nan duk kyawun
mace da farar fatarta ba ta burgeni, ko da kuwa ta hurul-eeni ce. Ko dai ta yi karatu ko in bautar
da ita, bautar da uwarta da ubanta basu taba yi mata ba. Ke ni ko a aljannah bana fatan Allah
ya hadani da mace, ba don komi ba sai don cewa ita ba komi bace face fitina a doron kasa,
balle irin ku masu narka-narkan…….sai ku lalata mutum in ba ana wulakanta ku ba….”
Na daga idona a hanzarce da hawayena suka kafe karaf, na dubi GG din nan na ‘yan dakikai
don ji nake kamar Imran ne yake gaya mun hakan. Ashe dalilin Ya Im kenan na wulakanta ni,
kada in lalata shi? Dalilin shi kenan na gaya mun abin da zai bata mun rai in ji har abada bana
son mu hada hanya? Sai na ji GG ya yi gaskiya, na shiga kada kai ina mai gasgata kowacce
kalma dake fita bakinsa.
Na duka na soma ture busassun kashi