Showing 15001 words to 18000 words out of 34700 words
Chapter 6 - GIRMA YA FADI Book 1 Hausa Novels by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf By arewaauthors.com.ng.pdf
rigarsa ya barshi a nan a duke a kan buzu. Ya fi awa daya a hakan
kamin ya mike ya shigo gidan. A lokacin Rabi na bakacen masara a fai-fai, ko kallon shi ba ta yi
ba, ya russuna a gabanta ya ce, “Barkan ku da yamma Inna”.
Ba ta fasa abin da take ba, haka ba ta dago ido ta dube shi ba sai bakacenta take cikin
kwarewa, tana huro mai dusar masara a fuska, kai ka ce da sassaken dutse yake magana. Ina
tsugunne a gefe abin yana mun ciwo a rai, na kasa daurewa sai na sa kuka.
Na yi niyyar in je in kama hannunshi in mikar da shi daga wannan durkuson da ya yi kamar na
mai neman gafara a gareta, kada gwiyoyinsa suyi ciwo, amma tsoron abin da za ta ce dani ya
hanani. Daman a daren jiya ta ce mun,
“Idan abin duniyar da Sa’idu ke kawo mana ne yasa nake neman juya mata baya, to za ta mika
ni gare shi mu tafi, kuma ko a lahira kada in ce na santa”.
Wannan tunani da na yi ne yasa nayi hanzarin shiga daki na kwanta a dandaryar kasa, nayi ta
kukan tausayin Baba Sa’idu. A ganina duk wulakancin da Inna ke masa shi yake jawowa kansa
da yake shiga sabgarta, tunda ta nuna ba ta ra’ayi meye dole zumuncin? Ko bashi da uwa a
duniya ya dace ya fita sabgar Inna Rabi, tunda ba ita ke raba wuta da aljanna ba. Haka na yi ta faman mummuke ‘yar akwatun zobunana cikin bante na (dinkakken siket mai
hade da shimi da ake dinkawa a kauye). Don na tabbata muddin Innata ta ga wannan akwatu,
to sunan ta badaddiya, koda kuwa a ce za ta sayi duniyar ne da abinda ke cikinta.
Na matsu matuka da zuwan Ya Faruk, na yi matukar damuwa da zuwansa. Abubuwan nan sun
addabe ni, na kuma tabbatar babu mai amsa mini duk duniya in ba Faruk ba. Shi kadai ne zai
tsaya ya fidda ni duhu, ya ganar dani al’amuran Innana da suka fi karfin hankalina.
Ina zaune bisa kujera ‘yar tsugunne ina cin magarya, yayin da Innana ke kiciniyar daura sanwar
dare bayan ta sauke rogon da ta dafa. A gefe Innar Faruk ke surfen gero, Inna Rakiya da
Zulkiflu wani yaro da take riko suna tuyar gyada marau-marau da take sayarwa. Daga zaure
almajiran Malam ne suka rude da karatu kamar sa tsaga gidan, cikin muryoyin su daban-daban,
da surorin su daban-daban, ba mai jin na wani. Inna ta dan juyo ta dube ni ta ce,
“Yau ba a zuwa karatun ne Kyauta-Abu?” Na ce,
“Rubutun da na yi nake jira ya bushe Inna”.
Wata yarinya da ba ta kai ni ba, ta yi sallama cikin sassanyar muryarta ta shigo, hannuwanta
duka biyu rike da ledoji, jikinta da fuskarta kamar an wanke a inji sumul-sumul da ita kamar
tarwada abin sha’awa.
Gaba daya muka amsa mata banda Inna da ta juyo ta kalle ta, ta juya ta ci gaba da abinda take.
Na mike da sauri na amshi ledojin hannunta ina yi mata sannu da zuwa, muka zauna bisa
tabarma, sai zare ido take na rashin sabo.
Inna Rakiya ta ce, “Kamar Azizan Sa’idu, ‘yar wajen Hajiya Azumi, ina abokiyar tagwaitakar
taki?” Ta ce, “Ba Aziza ba ce Iftihal ce, Aziza tana Porthearcourt”. Inna Dubu ta ce, “Ikon Allah,
kamar taku ce har ta baci, wa zai iya banbance ku banda iyayen ku?” Ta yi murmushi da dan
bakinta mai kyau. Jin an ce diyar Baba Sa’idu ne sai na yi ta kallonta, nan da nan na ji ina kaunarta. Dan mai
kaunarka, ai abin kaunar ka ne. da gani babu tambaya, ko daga yanayin fatar jikinta da irin
kayan da take sanye dasu, tana kuma yanayi da Baba Sa’idu da irin Hausarshi ta Sokkotawa.
Cikin murmushi na ce, “Dama ke ce Iftihal?” Ta gyada kai tareda cewa,
“Wa ce ce Anti-Abu?”
Na kai duba na ga Innana wadda ko juyowa bata kara yi ba. Inna Rakiya ta zuba gyada da
ruwan sha a babban kwano ta kawo mata tana nuna ni,
“Ita ce Zaynabu Abu, ‘yar’uwarki gata nan”.
Wani uban kallo da Inna ta juyo ta yarfa mata kadai ta san ta yi laifi, ta yi karambani, ta yi ba
dai-dai ba. Amma ita din sai ta yi murmushi cikin bagararwa ta kara da cewa, “Ga Innar Abu nan
tsugunna ki gaishe ta Iftihal”.
Ta kai gwiwoyinta kasa ta ce, “Inna ina wuni?” Sai da ta yi kamar ba za ta amsa ba, can dai ko
me ta tuna? Ta daga mata hannunta na dama ba tare da ta juyo ba.
Banda dai ina tsoron Inna, da na tambayi Iftihal ina Baban yake? Sai na buge da ce da ita, “Ya
Faruk yaushe ya ce zai zo ne?” Ta ce, “Ai sun tafi Bindawa shi da Ya Im, amma ina jin ya ce
daga can nan zai taho, kullum yana zancen ki, yana cewa zai kawo mu wurin ki, koyaushe
kuma sai ya yi tafiyarsa. Yau ne da na ji Baba zai zo na ce zan biyo shi tunda Aziza ba ta nan, shine ya taho dani”.
Inna Dubu ta wanke min dattin raina da cewa da ita “To ina kika baro Baban?” Ta ce, “Yana
zaure tare da Malam din nan gidan, amma ya ce komawa zai yi, nice zan kwana tare da Abu,
idan zai koma jibi zai zo mu tafi”.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Mafari kenan da wannan ya sayo min tsana mai tsanani a
wurin Hajiyar su Hassan da iyalanta, sai da na gwammace dama Abba bai ji al’amarin ba.
Tsakanin mace da mijinta sai Allah, bamu san ya a kai suka shirya ba, mun dai gansu kuma sun
hade abinsu. Amma Mama ta ce take jin Imran (dan lelen Abba) ne ya yi waya ya ba Abban
hakuri.
Na sha kimantawa raina ko ya Imran yake? Yadda abin ya bayyana a gareni shine, duk gidan
kowa na son Imran, babba da yaro kowa bakin shi baya daina ambaton (Ya Im) kamar yadda na
ji suna kiran sunan a takaice. Na san zai zamo mai kyawun sura kamar su Hassan, mai kyan
hali kamar Baba Sa’idu. Tun ban ganshi ba na san dole ganinsa ya fi jin sa. Iftihal kan ce; “A duniya ba mutum irin Yayana Abu!”.
Na tambayi kaina mai yasa shi din suke son sa, basa son kannensa su Hassan? Me yasa zai
kasance na daban din, kamar yadda suke ikirari? Abubuwa da yawa kan sa a so mutum,
muhimmi shine halayensa. A ganina ni ya dace in fadi cewa ba mutum irin Yayana Faruq amma
ba su ba. Na kan so Ya Faruq in kaunace shi, kauna irin ta su Iftihal ga Yayansu, saboda halayensa.
Faruq mutum ne mai tsarge gaskiya komi dacinta, ko da hakan na nufin ya bata maka ne,
hakan ba zai dame shi ba in har ya gaya maka ita wannan gaskiyar. Ba ya shiga abin da ba
ruwan shi, baya da karya, baya da daukar duniya da zafi.
Babban abin da yake burge ni da shi shine, addininshi da gudun sabon Allah, a ko da yaushe
yana kokarin fin karfin zuciyarshi a kan abinda take so, musamman idan ya fahimci wannan
abun ba alhairi bane a gare shi.
Idan kuwa aka juya ta bangaren halitta, to su Faruq sune ‘maza’ da za a kira su da wannan
sunan suyi gaggawar amsawa a ko ina. Ga tsayi ga zati, irin wadanda kowacce mace za ta yiwa
kanta burin mallakar su.
Tunda na taso a rayuwata bani da abin tsoro irin MAGE, na tsani mage, ina tsoron mage tun ina
mitsitsiyata. Idan na ga mage na kan firgita ne ko in kwalla kara. Idan kuwa ta hada
yankwalallen jikinta da nawa, na kan suma ne ko in fita hayyacina, in yi ta firgita a yayin barci.
Wannan dalilin ne yasa duk son kiwon mage da Malam ke yi ya hukura. Rannan muna dawowa makaranta a motar yara (school bus), dama kullum sai an fara dauko su
Hassan da suke da nisa, sannan a biyo ta makarantar mu a debo mu. Mun dauko hanyar gida
Hassan ya ce, “Wai Rufa’i baka san magen gidan su Na’im ta haifi ‘ya’ya har guda goma ba?
Suna nan baka gani ba in suna boxing abin sha’awa”. Jauhar ya ce, “To su sammana man ko guda uku ne muyi kiwon su?” Rufa’i ya ce, “Ka ga ko
Hajiya na son missa, don da tana da (Laura) da ta mutu ne ba ta sake samun wata ba”. Hassan
ya juya ya ce da direba, “Maza kamin mu shiga gida juya kaimu gidan su Na’im”. Tuni Shehu
direba ya cika aikinsa. Ban san sanda na fashe da kuka ba na ce, “Don Allah don Annabi Hassan kada ku amso ‘yar
mussan nan”. Rufa’i ya ce, “To ‘yar iko da gidan Uban wasu, idan Malam mai almajirai ne ya
sayi gidan sai ki hana mu zuba mage”. Hassan ya ce, “Bar ‘yar banza, mai bakin baki irin na
karuwai. Tunda an hana mu ce da ke BARAROJI to SADAKA-YALLAH ce??? Suka bude motar da kafa fut! Suka shige gidan mataimakin Abban su. Basu dade ba sai ga
kowanne dauke da farar babyn mage, in ban da mazari ba abinda jikina yake. Suna shigowa
suka watso su jikina. Da na kwalla wata azababbiyar kara sai da suka razana dukkansu, na
mimmike ba ko kwakkwaran motsi balle kyakkyawan numfashi. Iftihal tasa kuka ta ce, “Ai ga shi nan kun kashe ta, wallahi sai na fadi ma Abba”. Shi kansa
Shehu direba ya tsorata, ya ja motar da gudu yana cewa, “Ku dai Hassan baku da kirki wallahi”.
Yana sanya hancin motar cikin gate din dai-dai lokacin da Faruq ya yi parking karamar Honda
Prelude ta Imran, suka fito a tare, dukkaninsu sanye da kanyan NYSC, bakin Abia, zuwan su
garin kenan.
Azizah ce ta fara fitowa daga motar a rude tana kiran “Ya Im!”. Shi ko Faruq ido yake warawa ya
ga bullowar Abun shi, ya ga wane GIRMA da wane irin kyau ta kara, wane irin sauyin rayuwa ta
samu a tsayin lokacin da ya yi bai ganta ba?
Kullum, cikin sabani suke, sau tari duk sanda suka zo Sokoton daga Abia, wanda kwata-kwata
ma zuwan su uku cikin shekara daya, za su tarar su kuma anyi musu hutu suna Gwarzo, sanda
suke Gwarzon su kuma sun dawo Sokoto abin dai kamar shiri, amma ya faru ne cikin ikon Allah.
Kuma gareni sai ya zamanto rayuwa da su Iftihal ya debe min kewar Faruq din kusan kashi
saba’in cikin dari.
Azizah ke fadin “Ya Im, su Hassan sun zubawa Anti Abu mage ta sume mana a motar”. Gaba
daya Imran da Faruq suka yo motar, Imran ya riga Faruq dauko ni. Wannan shine karo na farko
da ya daura idanun shi a kan Abun-Faruq, Abun-Baba Sa’id.
Maimakon ya yi sauri, tafiya yake dauke da ita a hannun shi tamkar wanda ya taka kaya, ko ko
wanda kwai ya fashewa a ciki. Ganin irin tafiyar da yake yi ne ta marasa kuzari ya sanya Faruq
karbe Abun daga hannunshi zuwa dakin Mama. A ransa yana cewa,
“Ashe Imran duk wannan physique nashi ragon maza ne, mace wannan kamar ‘yar shilla ya
kasa daukar ta”.
Mama ce ta yayyafa min ruwa na farfado tana shafa kaina tana zagin su Hassan kaman ta ci
babu. Farfadowa na yi ina makyarkyata, hawaye na tsiyaya ta gefen idona, fadi nake ina
maimaitawa, “Mage ce fa a cikin jikina Mama”. Ta aza kaina bisa cinyarta ta ce, “Ba wata mage,
sai ni sai Ya Faruq, gashi nan ya zo”. Ni ko na dage, “Gata nan fa a hannun su Hassan har
guda uku wallahi….”
A ranar dai daga ni har Mama da su Imran babu wanda ya kwanta da wuri, don da na rufe ido
barcin ya fara fizgana zan farka a firgice ina kiran mage. Washegari Imran ya tattara magen ya
sanya a buhu ya ba Shehu direba ya ce ya mai da inda suka karbo. Ai kuwa a ranar su Hassan
sun sha tafka da belt, sunyi kuka da majina, daman Imran ba daga nan ba
(very-disciplined-brother).
Duk hakan bai ishe shi ba sai da ya sanya su duka cikin store ya kulle, ya hana masu aiki basu
abinci tun safe har yamma. Hajiya Sa’a ba ta san me ake yi ba sai yamma lis ta dawo aiki. Ta yi
murna da zuwan Imranan ta da kammaluwar bautar kasar sa, suka barke da hirar yaushe gamo
irin na Da da Uwa a babban falon ta. Ta nemi su Hassan ta aika su kawo mai lemu, ya ce, “Ai suna (store) ya kulle su”. Ta ce, “Dalili?”
Ya yi kwafa cikin takaicin su da ya ki sakin sa har zuwa lokacin, ya ce, “Sun san yarinyar nan
‘yar Malam ba ta son mage suka watsa mata maguna ta suma, har yanzu ba ta san inda kanta
yake ba”. Ga mamakin shi sai ta buga tsaki ta ce, “Shine me? Gidan Uban su ta zo, ban ga dalilin da za ta
takura su ba ta hana su yin abin da suke so. In ba ta son magen ta koma gidan Ubanta mana?
Sallamamme kawai ka san me ake a cikin gidan ne? A kan Buzuwar nan aurena da ubanka ya
kusa mutuwa, da sai dai ka dawo ka nemo ni a kauyenmu, in baka sani ba in gaya maka dalilin
cewa da ya yi in tafi kenan kwanakin baya da na gaya maka a waya don sun ce da ita
BARAROJI, ko ka bude min yara yanzu-yanzun nan ko in sabar maka wallahi”.
Ba musu Imran ya bude su Hassan domin dai shi mutum ne mai biyayya da baya saba umarnin
iyayen shi ko ya ya ne. Ya samu Faruq a dakinsu yana cin abinci, ya zauna bakin gado ya dafe
kai ya rasa abin da ke mai dadi, anjima kadan ya yi tsaki ya girgiza kai duk sai ya ba Faruq
dariya. Ya ce, “Kai Imran ya ya za ka yi when you become a father? (in ka zama uba) baka san
sha’anin yara bane?” Imran ya sake yin tsakin ya ce, “Ni ba wannan ke damuna ba,
maganganun Hajiya ne ban ji dadinsu ba, ban gane inda ta dosa ba. Ita fa babba ce, da ya
dace ta dauki kowa nata ne a gidan nan, duk da dai na san ita mai nuna son ‘ya’yanta ne,
amma saboda Allah su Hassan basu yi laifin da suka cancanci a hukunta su ba?”
Faruq ya dafa kafadunshi cikin murmushi “Common dear, don’t talk about this matter again,
plz…” Shima sai ya share zancen bai kuma yin shi da Faruq din ba, to amma sai ya rika jin
nauyin Faruq din ta yadda zai ga mahaifiyarshi a matsayin maras tunani, ga Faruq din shi bai
dauki al’amarin wani serious ba ma.
Kwana biyu na warware case din mage ya wuce, sai dai cike nake da tunanin mene ne
BARAROJI mene ne SADAKA-YALLAH?
Wannan tambaya ce da ta dade tana cina a rai, na kuma rasa wanda zan yi mawa, don haka da
na ga abin ya fi karfin tunanina, dole na yakice shi karfi da yaji.
Imran dogo ne baki kakkaura, sai dai bai kai tsayin Faruq ba, amma ya fishi kauri da fadin kirji
(physique), yana da kyakkyawar sura sosai, ya aje zagayayyen gashin baki dan siriri wanda ya
tafi ya hade da kauraran zagayayyun lebban shi masu sulbi. Yana da hakora masu haske,
jerarru kuma masu sheki. Komai nashi attractive wato mai daukar hankali ya dube su ko da bai
yi niyya ba.
Kallon yanayin fatar jikinshi kadai ya isheka kimanta irin hutu da jin dadin da yake ciki, haka
idanunshi za su nuna maka tsantsar ilimin da ke cikin su. Ba a fiya son mace mai kamun kai ta
fiya sanya idanun ta sosai a kan maza irin Imran ba, domin ba wuya za a aikata zinar ido.
Wanda kuma shi abin ya zo ne da halittar shi ba wai da gangan yake yi ba. Yana da yawan amfani da karamin gilashi (medicated) ba don lalura ba sai don kara karkon
idanu, haka nan Imran baka raba shi da cin biskit din nan na alkama (hob-nobs), yana da fada
sosai kamar barkono, amma in ka fahimce shi ya fi ruwan sha saukin sha, raini ne baya so.
Shine babban da a ‘ya’yan Farfesa, sun haife shi a kasar England zamanin da shi Farfesa yake
karatu, inda ya samu ilimin firamare da sakandire. Don haka ne in yana lallausar Turancin sa ba
za ka so ya daina ba. Sai bayan haihuwar shi da kimanin shekaru goma, sannan aka haifi
Hassan, Rufa’i ya biyo baya sannan Jauhar da dan karamin su Aliyu da Baban ya sanyawa
sunan Malam Ali, suna kiran shi Haidar.
Sai da ya fara aiki a UDUS ne ya auri Azumi, wadda take basakkwata usul, kuma diyar wani
abokin shi Farfesa a nan Sokoto wai shi Dr. Isma’ila Taura, ya ganta ne ranar ba da shaidar
(Degree) ga daliban shekararsu da matsayin da ta fito da shi ne (best overall student in MBBS)
na shekarar su baki daya. Yana daukar lasifika abin da ya bude baki ya ce a filin taron shine, “Idan Azumi ba ta da aure shi
V.C zai aure ta, wannan kawai shine kyautar da yake jin zai ba ta ya nuna kwazonta a duniya.
Ba kuma tare da ya ganta ba, tsohuwa ce ko yarinya ce?”
Gaba daya filin taron rudewa ya yi da sowa, masu ihu na yi, masu kabbara na yi da sanyawa
abun albarka. Babanta ne ya shige mai gaba ya ba shi auren ta. Ita kanta ta san ba karamar
sa’a ta yi a rayuwar ta ba.
Imran da Faruk na tare tun daga farkon karatunsu na Jami’a, wato tun dawowar Faruq Sokoto,
sun shaku sun kuma amince da juna,