Showing 27001 words to 30000 words out of 34700 words
Chapter 10 - GIRMA YA FADI Book 1 Hausa Novels by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf By arewaauthors.com.ng.pdf
ta suka kwanta suma.
Dakin nau gadaje ne na ‘silver’ kanana guda uku, nawa ne a farko sai na Iftihal sannan na
Azizah. Can anjima Iftihal da ta fi makotaka dani ta kwaye bargon da ta rufe kanta iya wuyanta
ta ce cikin rada yadda Azizah ba za ta ji ta ba, “Anti Abu don Allah in ce wani abu?’ Na dauka
tsokanata za ta yi sai na sha mur na ce, “Ki rike abunki bana son ji”. Ta yi shiru, can ta ce, “Am
serious, don Allah ya ya so yake? Ina nufin ya ya za ki iya kwatanta son Ya Im a zuciyarki?”
(Tana murmushi mara amo).
Na lumshe ido na a hankali ina jin wata sabuwar kauna na ratsa zuciyata. Ni kaina na san son
da nake ma Imran ba za ya kwatantu ba, ba shi da iyaka, kwakwalwata ba ta yi kaifin da za ta
fahimce shi ba, harshena ba zai iya bayyna shi ba, domin ya fi yawan silin gashin kaina.
Ta tabbatar ba za ta ji kalma ko daya daga baki na ba, (shiru ma amsa ce, amma ga mai
hankali), sai ta hakura ta juya ta kwanta.
Washegari ya kama asabar din karshen wata, kuma rana ce da muke sanitary watau kakkabe
komi na dakin mu, mu fidda kaya masu datti mu cire yana, mu kintsa sif din mu. Wannan wani
aiki ne da muka sanya kanmu bama son masu aiki suyi mana saboda baya gamsar damu.
Imran yayi sallama a dakin ya shigo, turaren da ya fesa na (Gucci-Rush) ya bakunci hancinmu.
Na lumshe ido zuciyana na girgiza domin ba karamin kyau ya yi ba, cikin bakar shadda ghalila.
Mu kuwa ko wanka ba muyi ba.
Ni sanye nake da doguwar rigar barci fara sol mai gajeran hannu, sai dai na daura zanen
atamfa a kai, kaina babu kallabi, don haka murdaden gashin kaina ke dunkule cikin tufka guda a
gadon bayana, rike da abin sharo yana ina sharowa. Su Azizah duk suka russuna suna gayas
da shi, ya amsa yana cewa, “Zance na zo Azizah, ina fatan ban yi sammako ba?” Kunya ta kama su duka, suka dukar da kai
suna dariya kasa-kasa, ta ce, “Gaskiya ka yi sammako, Anti Abu ko wanka ba ta yi ba”.
Ya ce (idanun shi a kaina), “Kin san meye ne Azizah? In da kin san kyan da ta yi min a haka, da
na ce ta daina wanka. Wannan Zaynabun dake tsaye gabana, ta fi mun duk matan duniya. Idan
na daga ido na dubi wata mace, komi wankanta da kwalliyar ta sai in ganta kodaddiya a kan
Zaynab dina. Wanka da kwalliya ba su ke sawa a so mace ba, wannan daga Allah ne. Don haka in kina
tunanin hakan ki daina. Ina tabbatar miki in Zaynab za ta shekara ba ta yi wanka ba, ba zan
daina sonta ba, ba zan daina ganin ta a matsayin wadda ta fi kowacce mace a idanuna ba….”
Dariya suka yi suna kokarin ficewa saboda su dai basu saba jin irin wadannan maganganun ba,
balle kuma daga bakin da suke matukar girmamawa.
Ya ce, “Ku yi zaman ku ayi hirar da ku, watakila in ci arzikinku ta amshi kokon bara na, in kun
tafi ko kallo na ba za ta yi ba. Ku taimaka ku tambaya min Zaynab, shin kalamanta masu tsada
na sayarwa ne? Ko-ko kwalliyar da na yo mata ne bai burge ta ba in koma in sako?”
Suka sa dariya gaba dayansu, nima kaina ban san sanda na murmusa ba, still ban juyo ba na ci
gaba da abin da nake, kamar in ce da shi shin ba yanzu ka gama cewa ba kwalliya ke sawa a
so mutum ba?
Ya karaso ya amshi abin sharar a hannuna yana cewa, “Kawo nan in karasa miki ko kya zauna
mu yi zance?” Ya dubeni cikin idanun shi cike da abubuwa da dama, na yi hanzarin zama a
gefen gado saboda kafafuna dake neman kayas dani. Iftihal ta ce, “Hala baka taba zuwa zance
wurin Mami ba?” Ya ce, “Eh, yes, ban taba ba, ita ne take zuwa”. Ta girgiza kai ta ce, “Ko da na
ji”.
Ya dube ta bayan ya aje sandar ya ce, “Me kike nufi?” Ta ce, “Na ga baka iya bane, duk da ban
taba yi ba na san ba haka samari ke gayawa ‘yammatan wai sun zo zance gatse-gatse ba, abin
babu ko dadin ji”. Ta zura da gudu Azizah ta rufa mata baya ita ma ta ce, “Gaskiya idan baka
koyo zance ba, ba za a karbe ka ba”. Ya zauna a gefena na yi saurin rufe fuska da tafukana ina dariyar su, ya ce, “Da gaske ne ban
iya ba Zaynab?”
Na girgiza kai ba tare da na bude fuskar ba. Ya ce, “Wallahi ko ki bude fuskar nan ko in sumbaci
hannun ki”. Da sauri na bude. Ya ce, “Ashe dai yanzu an san ni wane ne, da kar ki bude mana”.
Na tsuke fuska gami da baki gaba daya, ya yi dariya ya ce, “Yi hakuri don Allah saki bakin kada
fushin ki ya lahanta ni, ya jawo min asara ya dai-daita zuciyata”.
Na yi wani irin murmushi a raina na ce, “Ni kuma fa? Da ka sanya tawa zuciyar cikin wata irin
wahalalliyar rayuwa da wani al’amari mai wahalar bayyanawa”. Ya ce, “Zaynab don Allah?” Tare
da rausayar da kai gefe tamkar marayan da ya rasa uwa. Na ga in ban yi da gaske ba mutumin
nan zai yi galaba a kaina, sai na juyar da kai gefe ba tare da na ce komi ba.
Ya sake kankan da murya ya ce, “Zaynab don Allah!” Wallahi na ji wannan kira har cikin
kwakwalta ta, kaina ya sara,z uciyata ta yi wani irin bugu da karfi. Na kai hannu na dafe kai da
kirji duka a lokaci daya. Roko nake kawai Allah ya kawo sanadin da Imran zai tashi ya rabu
dani, in ji da abun da ya dame ni. Ya sake kaskantar da murya tare da sakkowa bisa gwiyowin sa, ya daura kai bisa gefen gadon
ya sake cewa, “Don Allah Zaynab…” Duk dauriyar da nake yi abin ya ci tura, wai yau Imran
dake wahalar da rayuwata ne yau ke roko na da gwiwoyinsa a kasa. Tsinkayen Anti Rose ya
tabbata kenan. Ba zan iya jure ganin shi cikin wannan halin ba, ban san sanda na ce, “Me kake
so Imran?”
Ya dago da hanzari ya dube ni da idanunshi da suka kada suka yi jawur, ya ce, “Zaynab muyi
aure shine kawai abin da nake so. Na san kema shi din kadai kike so, duk wannan turjiyar
wahal da kanki kawai kike yi, ba kuma solution ne ga problem dinki ba, wanda ni na san shi ba
tun yau ba. Illa in ce ke jaruma ce na kuma yaba da jarumtakar ki. Duk wasu experiment da na
yi a kanki baki fadi ko daya ba. Wallahi Zaynab ba tun yau nake son ki ba, tun ranar da na fara
ganin ki, na dauko ki a sume baki san inda kanki yake ba, tun baki mallaki komi ba.
Na ci gaba da rainon son har kawo sanda kika fara zama mutum, na kuma yi nufin bayyana shi
gare ki. A lokacin ne na fahimci kema kin kamu da sona, amma ba irin son da ni nake miki ba,
naki ragagge ne wanda sha’awa ce ginshikin sa.
Sai na yi tunanin idan na ci gaba da nuna miki son da ni nake miki, wanda ya sha bamban da
naki ba mamaki wata rana ki rinjaye ni na afka irin nakin, muyi abin da ba dai-dai ba. Kuma a
shekarunki na wancan lokacin hakan babban hatsari ne ga rayuwar ki. Na yi tunanin abubuwa
da dama a kanki a wancan lokacin, musamman inda kika samo wannan al’amari, duk da
tarbiyyar da kika taso a kanta, wadda iyaye da dama ke son ‘ya’yansu suyi koyi da ke.
Babu irin zargin da ban yi ba a kanki a lokacin, musamman sani da na yi bakwa
kallace-kallacen banza, ba kwa karatun banza. (Excuse me pls) a lokacin sai na ji na kasa
yarda da ke, don sai na ga idan kin so ni nta wannan siga, kowa ma za ki so shi da hakan,
musamman wanda ya fini. Babu kuma namijin da za ki nunawa hakan ya iya kawas da kai a
kanki, ba yabon kai ba sai dai-daiku masu tsananin tsoron Allah, domin ba karamar baiwa Allah
ya yi miki ba. Daga baya ne na fahimci abin a halittarki ne nature”.
Na yi tunanin idan har da gaske nake ina kaunar ki, to abin da zan yi in nuna hakan shine in yi
ignoring dinki, ba don na daina son ki ba, sai don in yi kokarin daura ki a kan sahihiyar soyayya,
ba wadda za ta zamo nakasu ga rayuwarki da mutuncinki a idanuna ba.
Ha horas dake ta hanyoyi da dama domin ki azabtu ki koyi kaunata, kuma alhamdulillahi na yi
nasarar hakan. Duk wasu experiment (gwaji) da na daura ki a kai kin haye su, na san a yanzu
kina sona, kina kaunata kwatankwacin yadda nake kaunar ki.
Don haka Zaynab don Allah ki yi hakuri ki fasa duk wani ramuwar gayya da kike son yi a kaina.
Ban yi da wata manufa ba illa don amfanin kanmu gaba daya. Ban yi don in wulakanta ki ko in
tozartaki ba, illa don in samawa kaina kyakkyawan matsuguni a zuciyarki. Ki yi hakuri ki daina
wahalar damu haka, we need each other Zaynab plz stop this childishness. Na gaji Zaynab, na
yi hakuri na yi juriya kema kin yi, to ki hutar da zuciyoyinmu su samu abin da suke so, tun baki
sa na rushe ginin da na dade ina yi ba”.
Hawaye ne na ji sun fito min sur-sur, na yi azamar dauke su kada ya gani, amma ya ganin. Ya
dawo gabana a kasa ya zauna dirshan, ya kama hannuna na dama ya rike cikin nashi, ya ce
cikin karyayyar murya, “Kuka Zaynab, why? Idan akwai abin da ya bata miki rai cikin kalamai na
ki dubi Allah ki yafe mani, ban yi da niyyar in bata miki ba, na fada maki gaskiyar abin da ke
zuciyana ne domin wanke zargina da kike da wulakanta ki.
Ban sani ba ko kina daya daga cikin mutanen da ke son a fada musu karya don a faranta musu.
Na fada miki iyakar gaskiyata ne domin ki fahimce ni, ki tsayar da zuciyarki wuri daya….”
A nan ma ban ce komi ba sai hawayen dake ta bilbilo mini. Ya yi duk iya kokarinsa don jin wata
kalma daga bakina na ki cewa komai, sai hawayen dai da nake ta fitarwa ina sharewa kamar an
sunce famfo. Daga karshe sai haka ya fita ya kyale ni yana cewa, “Na baki kwanaki biyu ki yi
shawara da zuciyarki Zaynab, ba zan takura miki ba. Na kuma yi alkawarin yin biyayya ga duk
hukuncin da kika zartas garemu”.
Kuka nake ba don komi ba sai don farin ciki da bakin ciki duka a lokaci daya. Kuka nake na farin
cikin zuciyata yau ta tabbatar da abin da take shakku a kan shi, yau ta same shi. Kuka nake
domin bakin cikin ba zan iya auren Imran ba, domin tsira da mutunci da martabana da na
iyayena. Kwanaki biyu duk hanyar da na san zan ga Ya Im ina kauce mata. Shima bai matsa da lallai sai
mun kebe din ba. Za su yi ta hirarsu shi da su Ifty da Mama ba tare da na tofa ko uffan ba.
Ranar lahadi ne da daddare ya ce in je in kawo mishi wayana, ba musu na dauko har layin da
na cire na kawo mishi. Ya dubi Mama ba zato na ji ya ce, “Mama na kawo miki karan Zaynab”. Cikin son fahimtar mene ne tsakanin Imran da Zaynab din suke share junansu ta ce da shi, “Me
Zaynab din ta yi maka dan Abba? A sanina yau shekaru dai-dai har shida babu wanda ya taba
budar baki a gidan nan ya ce ga laifin Zaynab, ko ya ce ta bata mishi sai kai yau. Amma ban
sani ba ko Zaynab din dana sani, mai kirki mai addini, mai girmama na gaba da ita da tsantseni
cikin al’amuranta ta canza hali ne. tunda ni ba zama nake yi ba”.
Ya yi murmushi ya ce, “Ba ta canza ba, tana nan a Zaynab dinta da kika sani. Cikin kyawawa
halayenta sai ma abin da ya karu. Waya ce na basu kowa yana amfani da shi amma ita ta rufe
nata, ko kunnawa ba ta yi ta raina kenan?”
Ta girgiza kai da sauri ta ce, “A’a, Zaynab ba ta rainuwa, ko kiyashi ka ba ta a matsayin kyauta
za ta ce nagode, Allah ya kara budi. Watakila dai akwai dalilinta na rufewar amma ba wannan
ba”. Ta juyo ta dube ni tana murmushi, na sarda kaina kasa nima ina murmushi cike da jin dadin
yabon da take yi mun. Ta ce, “Ina sauraron dalilin ki na rufe wayar da Imran ya baki Zaynab, don in yi hukuncin adalci
a tsakaninku”. Na ce a hankali, “Mama firgita ni take, karar ta na damuna, musamman in ina
barci”. Suka kyalkyale da dariya ban da Imran, kallona kawai yake cike da matsanancin so da
kauna. A hankali ya ce, “Ai ana canza tune din, ko kuma ki sanya shi a silent ba za ya ke firgita
ki ba, ko kuma ki sanya kiran sallah for your own convience”.
Ranar litinin Allah-Allah nake mu fito paper in nemi Anti Rose, kuma da yake paper din Islamic
Studies ne bana jin wuyar sa, nice farkon fitowa. Gudu-gudu sauri-sauri na bita hanyar fita
ganin tana kokarin juya motar ta domin tafiya gida. Na daga murya tun karfina daga nesa ganin
cewa duk saurina ba zan iya cimmata ba, na ce, “Anti Rose”. Ta dakata kamar tana nazarin ta inda kiran sunan ya fito, kana ta yi hanzarin juyowa ta dube ni.
Lokaci guda ta kashe motar ta fito. Sai murmushi nake ita ma murmushin take min tun daga
nesa. Tana karasowa inda nake kuwa ta ce (tana mai nuna ni da dan yatsanta) “Akwai
daddadan labarin Imran a bakin Zaynab dina”.
Ta kama hannuna har staff-room, babu kowa duk suna dakin jarabawa, muka zauna a kujerun
dake fuskantar juna ta ce, “Hurray Zaynab, bani in sha”.
Na yi murmushi na zayyane mata dukkan abubuwan da suka yi ta faruwa tun dawowar Ya Im,
ban rage kalma daya ba. Ta ce, “Thank God! Na kuma gode miki da baki yi saurin amsawa ba.
Hakan ma wani abu ne da zai kara miki matsayi a zuciyarsa. Ki ci gaba da kin amsa bukatar shi
har sai kin koma gaban iyayen ki. Idan ya biki ya cika mai kaunar ki Zaynab, sai ki nuna mai
matsayin ki na cewa ke talaka ce, kasa da shi. Kina gudun wulakanci. Idan ya ce ya ji ya gani
yana son ki haka, Zaynab ki yarda da Imran ku yi auren ku, ina muku fatan alkhairi”.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Mun baro Katsina ranar Lahadi, kai tsaye muka zarto
Kanon Dabo, yaro ko da me ka zo an fika, mai Dala da Gwauron Dutse, tushen Maguzawa ta
Dabo tumbin giwa. Kwanan mu biyu a gidan Baba Sa’idu na Kano dake Sultan Raod sannan
muka tattaro muka yo Gwarzo. In ba don idon Abba ba, da Hajiya Sa’a da iyalanta ba za su Gwarzo ba iyakacinta Kano, domin
ita a gareta takura ne zaman kauye ai sai dole. Amma shi Abban baya ganin haka. Kar ku yi
mamakin jin cewa Hajiya Sa’a ‘yar Gwarzo ce ‘yar kanwar Inna Dubu da aka rike a gidan Malam
Ali, domin iyayen Dubu talakawa ne futuk amma duk sun rasu. Don haka Dubu ta daukota ta
rike. Shi kuma Abban a rayuwarshi ba shi da kamar Malam Ali, a shirye yake kuma da ya bata
da kowa in dai a kanshi ne, daga ‘ya’yan shi har matan shi ya sha gaya masu wannan. Don
haka wannan lokacin take taka-tsan-tsan.
Ita dama ‘yar dakin Innar Faruq ne, don haka can suka sauka da ‘ya’yanta. Ni da su Mam, ‘yan
biyu da Gambo muna dakin Innana dake ta faman makale ni kamar ta maishe ni ciki. Yau abin
da sauki tunda kuwa ban ga ta hana su Iftihal shiga dakinta ba, ko don ganin idon uwarsu ne,
oho! Ko kuma ‘yan mutuncin ne a kanta? Na danganta hakan da dokin zuwana da take, domin
na yi dadewar da ban taba yi ba har watanni shaida ban zo ba.
Rabi da Mama sun barke da hirar yaushe gamo wadda duk rabinta labarin rayuwata ne da ke
burge kowa, yake kuma baiwa kowa sha’awa a can Sokoto. Ta ce, “Zaynabu-Abu uwar addini
ce, ban taba ganin yarinya Abida (mai ibada) irin Zaynabun ki ba”. Inna ta kara janyo ni ta
rungume tana murmushi dadi ya cika ta. Don ba abin da take so a rayuwarta irin ta ji ana yabon
Abun ta, Kyautar ta, Kyautar Allah (kamar yadda take cewa).
Sai na samu kaina da kara godiya ga Allah da ya kare ni daga aikata ZINA, kamar yadda
zuciyata da gangar jiki ke so, har suka so su ja ni. Wannan ya samo asali daga addu’ar da
Malam yai min a sanda aka haifeni a al’aurata, domin kariya daga aikata zina. Aya ta ( ) cikin
Suratul-Maryam. (Don haka iyaye a dage da kula da ita wannan addu’ar a yayin da aka haifi
yaro, to insha Allah ba dai ya aikata zina a rayuwarshi ba).
Na tabbata da na karya zuciyar Inna Rabi, fiye da wanda ta samu kanta a gaba dayan tsayin
rayuwar ta, wanda ni ba zan ce ga shi ba. Da duk wannan kaunar da take mun, ta koma
kiyayya, watakila irin kiyayyarta ga BABA SA’IDU. Sai na samu kaina a mai tambayar kaina,
wannan na nufin BABA SA’IDU ya aikata ZINA ne shi yasa ta