Showing 1 words to 3000 words out of 34700 words

Chapter 1 - GIRMA YA FADI Book 1 Hausa Novels by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf By arewaauthors.com.ng.pdf

[7/11, 3:57 PM] +234 706 160 2791: GIRMA YA FADI 1 KAUYEN GWARZO, 1988
Sunan da na taso da shi tun ina karama shine Zaynab Aliyu Gwarzo. Asalin mahaifina mutumin
garin GWARZO ne da ke cikin jihar Kano da ake kira Malam Ali Mai Almajirai. Malam Ali,
sananne ne a ciki da wajen kauyen Gwarzo da ya shahara wajen ba da maganin cututtukan da
suka shafi aljanu daga Alkur’ani mai tsarki. Bayan magani da yake bayarwa yana karantar da dubban almajirai, kuma fitaccen manomi ne,
makiyayi. Ya mallaki manya-manyan gonaki guda biyar, tirken dabbobi zuwa tsintsayen gida irin
su kajin gidan gona, agwagi, talo-talo, jimina, gada, zabbi, akuyoyi da sauransu.
Haka nan Malam Ali mutum ne mai cikar mutunci da tsananin kyauta, duk wanda ya kwana ya
tashi a garin Gwarzo ya san da hakan. A garin Gwarzo baki dayanta Malam Ali fitacce ne da
ake matukar girmamawa gami da ganin kima da mutuncinsa. Daga inda duk ka ce kana neman
gidan Malam Ali, za a ce da kai “Mai Almajirai?” Daga ko’ina a cikin garin Gwarzo za a rakoka
har dakalin gidan Malam Ali Mai Almajirai.
Matan Malam Ali na aure uku ne, amma cikinsu babu wadda Allah ya baiwa haihuwa sai
uwargida Inna Dubu da ta haifi Umar-Faruk shi kadai ya tsaya. Sai da ta yi haihuwa tara duk
mutuwa suke tun suna jarirai wato (wabi).
Daga Inna Dubu sai Inna Rakiya, sannan Innata, Rabi. Rabi matar Malam ta karshe Buzuwa ce
fara sol, ita ce mahaifiyata kuma a hannunta na taso.
Asalin auren Innata da Malam ya samo asali ne daga kawo ta neman magani, kasancewar
Malam mutum mai ta’ammali da mutane daban-daban daga ko’ina cikin kasar Hausa da
kewayen ta, manyan ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa da ‘yan boko da manyan ma’aikatan gwamnati
kan zo neman taimako wajen sa a kan harkokin su, kuma suna ganin nasibi na hakika cikin
taimakon sa, daga garuruwa daban-daban ana kawo marasa lafiya wadanda ya ware musu
sashe guda a gidansa.
Ya kan bada lakani na kasuwa, cututtukan da suka dami bil’adama, musamman wanda ya shafi
aljanu zuwa cututtukan yau da kullum. Hakan ne yasa kullum za ka ga kofar gidanmu cike da
motocin zamani wannan ya shiga wancan ya fita.
To hakan ce ta hada shi da Alhaji Sani Buzu, shahararren dan kasuwar fata kuma dan siyasa
daga garin Yamai ta kasar Niger. Ya zo Kano ne musmaman domin nemawa ‘yarshi maganin
tabin aljanu da ta samu, tare da kanwarta Nuratu.
A cikin Kano ne ya samu labarin Malam Ali ta hanyar wani abokinsa dan kasuwar Niger zuwa
Kano, wanda shima ya sha zuwa amsar taimako hannun Malam Ali. Alhaji Sani bai san kowa a
Kano ba, karewa ma ko zuwa bai taba yi ba sai a kan lalurar Rabi. Akwai kauna sosai tsakanin
shi da ‘ya’yanshi biyu Rabi da Nuratu, wadanda mahaifiyarsu ta mutu ta bar mishi, tun rasuwar
ta bai kara aure ba.
Ya kawo su Rabi Kano da zummar neman magani ne kawai. Malam Ali, ba wai warkar da
mahaukata yake ba, illa in lalurar kankanuwa ce ta kuma shafi aljanu bata gagararshi, ya kan
raba mutum da su cikin ‘yan satittika daga ayoyin Alkur’ani mai tsarki.
Ya kawo Rabi da kanwarta Nuratu gidan Malam Ali tsayin sati biyu ana yi mata magani, anyi
sa’a lalurar tata karama ce, cikin lokaci kankani Malam Ali ya raba ta da su.
Don farin ciki Alhaji Sani ya ce ya fadi komai yake so in dai bai fi karfin sa ba shi ko ya yi mishi.
Budar bakin Malam Ali sai cewa ya yi, ai ko baka bani komai ba ka bani auren Rabi Mana? Ya
fiye mini duk abin da za ka bani, bana karbar ladar aiki sai sadaka a inda ake da bukatar ta.

Jikin Alhaji Sani ya yi sanyi, don bai taba kawo ma ranshi bukatar da Malam Ali zai nema kenan
ba, da ko kusa bai fara wannan subutar bakin ba.
Hankalinsa ya tashi matuka, yaran da basu ma taba zuwa Kano ba, ko kalmar “zo” da Hausa
basu sani ba, gashi daya ba ta iya rayuwa sai da ‘yar’uwarta, akwai kauna da shakuwa ta
hakika tsakanin Rabi da Nuratu.
A can Yamai suna tare ne da mahaifiyarshi, yana sa ran yin aure cikin wannan shekarar kamin
ayi zaben da yake nema a Jihar su (Damagaram).
Ya yaba da rayuwar Malam Ali da iyalinshi, ko kadan bai raina musu ba, suna cikin suttura da
cima mai kyau da rufin asiri, amma ita Rabin yake ji ko za ta amince, da yadda zai tafi da Nuratu
babu Rabi.
Abin mamaki da aka tuntubi Rabin farat daya sai ta amince, wannan ba karamin abin mamaki
bane, domin a haife Malam Ali ya haifi ukun Rabi.
Ita ko Nuratu ta ce kafarta kafar Yayarta wato ba za ta bi Baban ba. Shima Malam Ali ya yi
alkawarin rike Nuratu tamkar Faruk har auren ta.
Alhaji Sani bai tafi ba sai da ya yankawa Malam Ali sadakin Rabi ya biya. Allahu Akbar! Ashe
karshen rayuwar sa kenan, sallamar shi kenan ta har abada da ‘ya’yansa Rabi da Nuratu.
A kan hanyar shi ta komawa gida Niger, cike da zullumin bayanin da zai yiwa mahaifiyarshi da
‘yan’uwansa a kan auren da ya yiwa Rabi babu saninsu babu yardarsu, cikin jinsin da ko a
tunani basu taba yin na tsintar kansu a ciki ba, a kasar da basu ko sani ba, jirginsu ya fadi a
wani tsauni kafin a kai Niamey, babu maganar mai rai a ciki.
Ni dai na taso bani da labarin NURATU. Gidanmu cike yake da ‘ya’yan riko, domin kowacce
cikin matan Malam tana rikon ‘ya’yan ‘yan’uwa, don haka gidan Malam Ali da albarkarsa ba za
ka ce ba a haihuwa ba.
Na tashi tashin gata kuma tashin sangarta, kasancewata auta, wadda ba ta zo ba sai bayan
haihuwar Faruk da a kalla shekara goma sha biyu, bayan ni kuma ba a samu wata ba. Don
haka suke kira na “Kyauta” wato Kyautar Allah. Inna ta Rabi kadai ke ce dani “Abu” shi ko
Malam “Zaynabu-Abu” ne baya ragewa. Bayan Inna Dubu Innar Faruk Inna Rakiya ba ta haihu da Malam ba, ‘ya’yan kanwarta ne take
riko. Rayuwarsu cikin mutuntaka da sanin ciwo kai ce, domin kowacce cikin su ta mallaki
hankalin kanta, babu rashin jituwa ko kadan a tsakaninsu. Dukkan su sun hada ‘ya’yan ‘yan’uwa
da almajiran Malam sun rungume a matsayin ‘ya’yansu, sai dai a kan ce wane dan dakin wance
ne, wance ‘yar dakin wance ce.
Akwai Yaya Halima da Inna Dubu ta rike shekarun baya ne aka yi auren ta, Lami da Laure da
Inna Rakiya ta rike suma duk Malam ya aurar dasu sun haihu a gidan mazajensu.
Ina da shekaru goma Ya Faruk ya kammala sakandire, inda duk za shi ka ganshi rike da
hannuna, ko me ya ci a waje sai ya rago mini, idan makaranta ya je ya dawo sai ya kawo min
tsarabar rake, gurji, gyada da makani. Ina son Yayana Faruk, domin halayen sa dake burge
kowa. Da fari dai Faruk shiru-shiru ne, miskili na kin karawa, da wuya ka ga yana hira in ba dani ba ko
Rabi, haka da wuya ka ga ya daga ido ya dubi mai shigowa sai dai ya amsa masa sallama ba
tare da ya dago ba.
Akwai aminci da mutunta juna na hakika tsakanin Ya Faruk da Rabi, ta yadda duk wata

damuwar Faruk Rabi ta sani, komi nashi da ita yake shawara, haka duk wata ajiyar shi mai
muhimmanci a dakinmu take, kai ba za ka ce kishiyar Mamansa ce ba.
Halin dattaku irin na Ya Faruk daban yake da na kowa cikin gidan, yaro ne a zahiri, amma
halinshi na manya ne, tun ina yarinya a ban san komi ba, na san Faruk kyakkyawa ne, dana
kan karkace kai in bata lokaci ina ta kallon sa, shi din bai sani ba.
Idan ya juyo muka hada ido sai ya ce, “Kyauta yaya ne kike kallo na?”
Mai hazaka da mai da kai, kuma mai nasara a kan duk abin da yasa gaba. Faruk tun yana
shekaru goma ya haddace Alkur’ani, haka har girmansa da shigar sa babbar makaranta bai
daina zama yana daukar karatun buzu ba wajen Malam.
Faruk ne mai taje min dogon gashina tun ina shekaru uku, ya kallabe shi kalba biyu, hagu da
dama, shi yake zabar min kayan da zan sanya, ya kuma goya ni a bayan keken sa ya kai ni
makaranta, in an tashi ya je ya dauko ni dai-dai da rana daya bai taba gazawa ba.
In Innata na mun wanka, sai ya girka kujera ya zauna yana azalzalarta ta daina cudawa da
karfi, fatar Abu bata da kwari, ba kya gani ja ce ne? Inna sai ta tsage jini ya fito? Rannan ya ce,
“Inna Rabi daga yau kada ki sake yiwa Abu wanka ni zan dinga yi mata, don na lura wallahi da
gayya kike cudawa da karfi, ba kya tausayin fatar Abuna”.
Rabi ta yi dariya ta kira Malam ta ce ya raba wannan rigima ta Faruk. Malam ya ce, “Faruku
namiji baya yiwa mace wanka ka yi hakuri. Daga yau babu mai kuma yiwa Zainabu-Abu wanka
da soso”.

Tun tasowata na san Innana Rabi na fama da wani bakin ciki na shekara da shekaru, wanda in
har ya ciwo ta, takan shiga daki ta yi ta kuka. A irin wadannan lokutan, Faruk kadai ke iya
tausarta da kwantar mata da hankali. Na kan gansu suna ta kus-kus, na ita damuwar da ke
damun Inna Rabi, wadda yawan shekaru da yanayin rayuwa bai taimaka ba ko kankani wajen
gusar mata da wannan damuwar ba.
Ta kan ce da ni,
“Kyauta rayuwa abin tsoro ce, haka zuciyar mutum sau tari makiyarshi ce. Ta kan umarce
shi ga abin da ta san ba dai-dai bane kuma Allah ya yi hani da shi. Ki guje ma sharrin zuciya,
kuma ki tsarkake zuciyar ki, daga sabon Allah komai kankantarsa.
Ki nisanci ZINA, ki kiyaye al’aurarki, mutum da kike gani abin tsoro ne, musamman
wanda kika taimakawa, dama kuma Annabi (S.A.W) ya ce, “Ka ji tsoron sharrin wanda ka
kyautatamawa”.

A wadannan shekarun, bana damuwa da irin wadannan kalaman nata, kamar yadda bana
fahimtar komai a cikinsu, domin hankalin bai isheni ba. Abinda na sani ko kuma na fahimta
kawai shine, Inna Rabi rayuwarta daban ce da ta sauran matan Malam, komi baya faranta
mata. Haka mafificiyar kaunar da Malam ke gwada mata, bata burgeta. Tana da wani mummunan kullaci a kan mutane da al’amarinsu, haka gaba dayan rayuwarta
cikin kunci take. Sau daya na taba ganin ta tayi dariya a tun tasowa ta, wato ranar da Faruk ya
ce ba ta tausayin fatata. Kokarin Malam da Faruk a kullum shine farin cikin Rabi da farin cikina,
amma hakan baya hanata zubar da hawaye a yawancin lokuta. Duk wata kulawa ta uwa da uba kusan in ce na same ta ne daga Ya Faruk, yana sona, yana
kulawa dani tamkar ‘yar da ya tsugunna ya haifa. Haka nan komi nawa mai muhimmanci ne a

awurin Faruk, shirme ne ko akasi.
Ire-iren mutanen birni da ‘yan boko da kan zo wurin Malam, ba zan iya iyakance alhairan da
nake samu daga garesu ba, kullum cikin sabbin kaya, kayan wasa, sabbin dinkuna, kayan zaki
da kayan kwalam nake saboda farin jinin da Allah ya yi min. Wasu kuwa kan ce kyawuna ne
yake sayo min farin jinin, kowa ya ganni sai ya tanka, ya kuma tambayi Malam game dani, don
ko a farcen kafa bamu yi kama ba (komi nawa irin na mahaifiyata ne) tamkar ta yi kaki ta tofar.
Amsar da Malam ke bayarwa a kullum shine, nayo Innata ne, wadda take Ba’abziniyar Niger.
Ni kaina na san ni da Inna ta daban ne a cikin gidan, haka muke wal! Sai ka ce tocilan don
haske a cikin jama’ar gidan, ko kuma ka ce wata ne a cikin taurari.
Sai dai abin da yake matukar burge ni da rayuwar gidanmu shine, ba za ka taba ganin an nuna
wariyar launin fata ba, da ni da su Indo da Hafsisi da su Dubu ke riko, duka su Inna Dubu sun
dauke mu daya ne babu banbanci. Sai dai Malam da Ya Faruk a kullum, a komi kuma a ko’ina,
su kan nuna nice ‘yar gaban goshinsu. Halin Innata da irin rayuwar ta kam ya riga ya zame min jiki, har baya damuna, ba ni kadai ba
haka duk kishiyoyin ta babu mai nuna damuwa da yanayin rayuwar ta, don in da sabo sun saba.
Sai ta wuni ba ta yi magana ba sai bin kowa da ido, haka kullum daren Allah cikin yi min
nasihohi da tsoratarwa a kan ZINA take. Ni a lokacin ma ban san mene ne zinar ba, ban gama tantance ma’anar kalmar zinar ba. Abin
da na fahimta kawai shine; zina wani abu ne da Innata ke matukar kyamata, kuma wani abu da
Allah ya yi kakkausan hani da shi.
Na alkawarta ma raina zan guje shi, kamar yadda take gargadina a kullum, zan nisanceshi,
kamar yadda Allah ya yi hani da shi. Akwai sanda ta ce min,
“Kyauta da ki yi zina, gara mun mutuwarki da rayuwarki”.

Da hankali ya fara zuwa min sai na samu kaina a mai tambayar kaina, shin mene ne shi
wannan zina, da Inna ke damuna da zancensa? Me ke damun Innana ne? Meye dalilinta na yi
min hasiha kadai a kan zina? Shin zina shine kadai abin da Allah baya so?
Tambayoyi ne da ke min yawo a kwanya, tun ina mitsitsiyata, suke neman tarwatsa min
kwakwalwa tare da wargaza min tunani.
Don haka ban san sanda na samu Ya Faruk a dakinsa ba dake a zaure, a wani maraice,
hannuwana dafe da kaina dake neman tsagewa gida biyu saboda ciwon barin kai guda
(migraine) da nake yawan fama da shi, sakamakon tarin tambayoyi da damuwoyin da na
kimsawa raina, suke addabar kwakwalwata, suka kuma fi karfin shekaruna. Na damu kwarai da
wannan al’amari da Innana ke damuna da shi.
Na zauna a masangalin kujera kwaya daya tak dake dakin, na yi tagumi da hannuwa bibbiyu na
rasa abin da ke min dadi. Ya Faruk ya aje jaridar da yake karantawa ya juyo ya zuba min ido
sosai cikin nazari,
“Kyauta meke damun ki? Na lura a ‘yan kwanakin nan ba kya cikin walwala, kina ta ramewa
kamar kudin guzuri, akwai damuwa kwarai cikin kwayar idanunki, ki gaya min mana. Idan baki
gaya min damuwar ki ba wa za ki gayamawa?”
Na saki sassanyan numfashi na ce,
“Ya Faruk idan na tambaye ka za ka gaya min gaskiya tsakanin ka da Allah?”
Cikin mamaki ya ce, “Abu, na taba gaya miki abin da daga baya kika bincika kika taras ba haka

bane?”
Na girgiza kai da karfi, “Baka taba ba Ya Faruk, don haka na san yau din ma gaskiyar ce dai za
ka gaya mini. Wani al’amari ne da ya shige mini duhu yake sa ni cikin tunani da neman sani”.
Na yi shiru cikin duban yanayinsa da ya zubo kyawawan idanunsa masu sheki yana kallo na.
Na sarda kai cikin kunya da matsanancin jin nauyin abin da zan fada, domin duk da ban san
ma’anarsa ba, na san ba abu ne mai kyau ba, ba kuma abu ne da ake son a dinga fada ba. Bai
nuna kosawa ba har sai da na bara don kaina, na ce, “Shin mene ne ZINA da a kullum Inna Rabi ke gargadi na a kanta?”
Na tabbata bai zaci tambayar da zan yi mai ba kenan, mamaki karara ya bayyana a fuskarsa.
Ya ce,
“Ita Innar ce take miki fada a kan hakan? Ba ta san ke yarinya ce ba? Gaya min gaskiya dai ina
kika san wannan kalmar?” Na ce, “Wallahi Allah Inna ce take fada”. Na sake dukar da kai na
warware masa wa’azin Rabi gareni a kowanne dare.
Na kare da cewa, “Na rasa gane me take nufi, na rasa gane illar shi wannan abu. A da abun
baya damuna, amma yanzu ya dame ni. Ba ta bari na in yi barci kullum “Abu, kada ki yi zina”.
Shin ZINA shine kadai alkaba’in da Allah ya yi hani da shi?”
Ya Faruk ya sunkuyar da kai yana kallon yatsar kafarsa, cikin dabara ya dauke siraran hawayen
da suka cika mishi ido. Ya dade bai dago ba, cikin nannauyan tunani. Ya dago bayan wasu
mintuna, ni kuwa na tsattsare shi da ido, ya yi murmushi irin mai kwantar da hankali, kamin ya
soma yi min magana cikin tattausar murya. “Zina ba shine kadai aikin haramun da Allah baya so ba, sai dai yana cikin su. Kin ga babban
haramun shine “shirka”, amma Inna Rabi na miki gargadi a kan zina ne kasancewar ki ‘ya mace,
babu wuya an yaudare ku a wannan fannin, kasancewar zuciyar ku (delicate) wato rarrauna ce.
Ta san ba za ki yi shirka ba, kasancewar ki rainon musulmi, kin kuma tashi cikin musulunci.
Amma za ki iya yin zina, wadda take zigar shaidan ce da rudin zuciya, mai kuma jefa ‘ya’yan da
aka haifa ta hanyarta cikin wata irin wahalalliyar rayuwa da bakin ciki tabbatacce.
Abin da ake nufi da zina shine, yin rayuwa irin ta ma’aurata alhalin babu aure tsakanin ki da shi
wannan namijin. Zina babu wuya an aikatata, amma jin dadin dake cikinta na dan lokaci ne,
bakin cikin dake cikinta da abin da take haifarwa har abada ba zai gushe ba.
Kamar misali idan wani ya aure ki bayan kin aikata ita zinar a waje, har abada ba zai taba ganin
kima da mutuncinki ba. Hatta Bature da ya kawo mana ita, ya kuma yi sanadiyyar yaduwar ta
cikin al’ummar mu, a cikin philosophy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login