Showing 33001 words to 34700 words out of 34700 words
Chapter 12 - GIRMA YA FADI Book 1 Hausa Novels by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf By arewaauthors.com.ng.pdf
shi ake yi ba mara yiwuwa ba, yaro tsaya
matsayinka…. kada zancen ‘yan duniya ya rude ka, kai zai kai nya baro. Amma wallahi zuciyar
nan mai laushi da kafiya (delicate but strong) ta ki amincewa, ita dai Imranan nan shi kadai take
so by all means. Babu abin da ya dame ta da hujjoji na, ba ta san su ba, IMRAN kawai ta sani.
Cewa take Zaynabu-Abu luv, have no boundaries…..
A kwanakin biyun da suka biyo baya, duk rabin hirar su ta Mami ce da kirkin ta. Idan na ji ba
zan iya jurewa ba, sai in tafi daki na ci kuka na ya isheni, in sa sabulu in wanke fuska. Kamar
wata zautacciya, in saka wannan in kunce da wancan. Daga karshe na alkawarta ma raina ko
Imran din nan ne autan maza na hakura da shi, don tsira da mutuncina da na iyayena. Duk wanda ka ga Hajiya Sa’a ta tashi ta rako gate da kafafunta, to tabbata ya isa, ta san shi din
wani ne, za kuma ta samu wani abu a jikinsa, duk da babu abun da Allah bai mata ba ita da
mijinta da ‘ya’yanta, ba ta da godiyar Allah ko kadan. Ko a jiya Imran ya aiko mata da sabuwar
mota (Hummer Jeep) da gaba dayan albashinsa na wata da watanni, dama ya ci alwashin ita
ne za ta fara cin gajiyar iliminsa, amma a yadda take nan-nan da Mami, sai ka rantse ba ta taba
mallakar kwandalar kanta ba.
A kwanakin da suka biyo baya ban kara yardarma zuciyata ta tuna Imran ba, na tattarasu shi da
Mamin da al’amarinsu na zuba a kwandon shara. A yau muka fara zana WAEC da practical
Biology, bamu muka fito ba sai karfe hudu na yamma. Kwakwalwata ta yi zafi, kaina ya yi zafi
rau, ga yunwa, gajiya da nannauyan barci a kaina, wanda ban samu na yi ba a daren jiya muna
ta karatu.
Don haka mun shigo gida a gajiye lis, muna tafe muna hada hanya, ban lura da bakuwar motar
da muka samu ba a harabar gidan. Muka isa falo kowacce na ‘wash-wash’, ni ko dafe nake da
goshina, idanuwana a rufe nake tafiya a cikin falon.
Ban ankara ba na ji na yi karo da mutum, kamin wani lafiyayyen kamshin turaren nan na
(Boss-Intense) ya bakunci hancina. Na yi hanzarin bude idanuna da suka yi ciki sosai saboda
yunwa da wahala, na dube shi yana murmushin nan nasa mai cike da ginshira, a hankali ya ce,
“Ya… ‘yan makaranta ba a gani ne?” Wallahi sauran kadan in fadi a tsakiyar falon sakamakon kafafuna da suka kasa daukar nauyin
jikina, saboda yadda Imran ya koma, in da dare ne ba za ki gane shi ba. Ya zama kato, ya zama
‘giant’ ya kara kyau na ban mamaki. Tsayayyun kafadun nan nashi ‘pysique’ na barazanar gabje
maza biyar a lokaci daya saboda yadda suka kara habaka har da doro na musamman, na
kasaitattun maza.
Ya kara haske ba can ba ‘chocolate’, ya kuma kara murjewa, da gani za ka san naira ce ta
zauna da gindinta. Lafiyayyen agogon ‘switch-blustery’ sai walkiya yake cikin lallausar fatar
hannun shi, yana sanye da farar shadda kal kamar takarda, dinkin mazan Maiduguri. Na yi
gaggawar ba shi hanya, ya yin da shawarar Anti Rose ta zo min cikin kaina kamar karatun
sallah. Cikin halin ko in kula na ce, “Sorry plz, ban ganka bane na gaji ne sosai. Muna barka da
zuwa”.
Da daddare muna falo muna ta hirar pepermu ta yau, ya shigo yana balle links din hannun shi
yana tambayar Mama ina abincinsa. Gaba daya muka rude mai da labarin zuwan Mami,
muryata ta fi ta kowa karadi, ina kara kuranta kyawun Mami da kurzanta kirkin ta, duk sai ya sha
kunu ya bi ya daure lallausar fuskar nan tam, alamun ba wargi. Amma bamu fasa ba, kamar ma
zuga mu yake. Hajiya na gefe tana ta murmushin jin dadi, ta ce, “To kai ka ji ‘yan kannen naka
ma sun yaba da ita”.
Ya dago fuskar nan a murtuke kamar hadari, ya kulu iyaka. Ya hade giran sama da na kasa a
take ya koma (previous IMRAN) mai gigita kannensa. Na yi mamaki da bai daka mana tsawa
ba. Ya zube min manyan idanun shi a mamakance, ya ce cikin gatse da wata murya mai kama
da ta mai ciwon makogaro, “Har da ke Zaynab, kema kin yaba da Mami?” Da sauri na gyada kai ina dariyar nan da Malam Bahaushe ke kira (yake), na ce, “Wallahi kuwa
Ya Im na yaba, a very simple lady, ba ta da girman kai”. Ya sakar min hararar da ta kada min
‘ya’yan hanji, ya ce, “Tunda haka ne ki hadata da Faruq man, kin ga shima baya da girman kan,
amma ni ta yi mun tsufa sai yarinya (sweet 16) zan dauka, yadda nake (fresh) din nan in na auri
kaman Mami ‘yar (28) ai na ci baya……”
Iftihal ta toshe baki kada dariyar da ta zo mata ta fito, Azizah da Hajiya suka daure fuska wato
sun ga samu suna neman ganin rashi. Ni ko na yi tsuru-tsuru don duk maganar nan da yake
idanunshi a kaina yake yin su, kamar da ni kadai yake magana a falon.
Ya ci gaba da cewa, “Shin ma wai ita Mamin da ta zo ne ta ce muku na ce ina sonta? ‘Yar ajin
su Faruq ce fa, daga kawai tana gani na ina zuwa wajen sa ta like min kamar kaska, amma ni
wallahi bana ra’ayin bakar mace a rayuwata, ni baki ita baka, muyi ta haifar bakaken ‘ya’ya me
aka yi kenan? Ko Annabi (S.A.W) ya ce in kai baki ne ka auri fara, in kai fari ne ka auri baka, sai ku haifi ‘ya’ya
masu kyau. To kin ga shi Faruq fari ne sol, watakila za ya iya maneji da ita su jera kafada, ko ya
ya Hajiyata?” Ta dunkule hannu ta sakar masa dakuwa, ta ce, “Ungo nan, babban banza kawai,
ka tsaya kana irin wannan maganar da kannen bayanka ko kunya baka ji, sahorami,
shashasha, kada ka auretan mana wa ya yi asara? Ka san dai ba za ta rasa mai so ba, don ba
ta yi kama da ‘yan kananan gida ba”.
Ya yi dariya ya ce, “Allah yasa Obasanjo ne Babanta ba Abdulhadi ba, barawon dukiyar
al’umma, tunda ya hau kujerar Sokoto ko kwatami bai yiwa al’ummarmu ba, sai baitil malin mu
da yake ta handamewa yana kaiwa kasar waje. Ku saurara nan da sati za ku ji shi a hannun
EFCC. Don haka sai ku samo min ‘yar sabon Gwamna, tunda ku ke da idon zaben mata ni bani
da shi.
Amma wannan bana yi, bana so a kai kasuwa, kada nima ina kwance ina shan amarci na ga
sammacin Farida….” Ta dauki filet din da ta gama cin gasasshen nama a ciki ta maka masa, ya
kauce ya fice da gudu-gudun sa yana kara gaya mata, “Ko da yake Hajiya ki yiwa Hassan din ki
kamun ta, gashi nan ya dauko tsawo kwanan nan zamu yi kafada da shi, in har da gaske
surukuta kike so da ita”.
Da haka Imran ya kashe zancen Mami a gidan amma ban da a zuciyata. Kullum Mami tana nan
like cikin raina har mafarkinta nake anyi musu aure da Imran, sai dai ko alama ba wanda na bari
ya gane halin da nake ciki.
A wannan zuwan da Imran ya yi, gaba daya ya canza mana, ya dawo YA IM din sa, mai son
kannensa da son kula su, ko da yake ma mu yanzu bama zaman gidan, kullum safe da yamma
muna makaranta.
Ni kuwa in na shige daki tun karfe shida na yamma bana kara fitowa balle mu hadu a hirar falo,
zan fiddo littafina in tisa karatu sai gobe kuma, in sha lemo in ci biskit in yi kwanciya ta zuciyata
kal babu wani Imran a ciki.
Na danganta canzawar shi da dadewa da ya yi bai ganmu ba. Ya dauki annual-leave din shi ne
na watanni uku. Allah-Allah nake mu kare jarrabawar in yi gidan ubana in huta da wahalar
rayuwa, zancen zuwa jami’a da su Azizah ke yi babu shi a wajena, sam bana ra’ayi.
A can falo Imran cike yake da mamakin rashin ganina a gidan, ya damu su Azizah da tambaye
me nake yi a daki ni kadai, sai su ce a takaice “Karatu”. Ya ce, “Ku bakwa karatun?” Su ce,
“Muna yi mana, amma bama iya irin nata. In ta yi (seat) dinmu daya muna kwafe”.
Don haushi ya rasa mai zai ce musu, ya dade yana kallon su kamin ya mike ya rufe ido ya
balbale su da fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, wai zai kai su ga hukumar
makarantar ayi musu daurin shekaru biyar na (malpractice).
Sai Azizah ta mere baki ta ce, “Wallahi Ya Im yadda ka je haka za ka dawo, don kuwa duk
(invigilators) din samarin ta ne, har wajen zaman mu suke kawo mana amsa, ita ce dai ba ta
karba, amma wallahi har principal saurayin ta ne. shima GG da ya sata wankin kashi yanzu in
zai rabu da duk abin da ya mallaka zai yarda, in har Zaynab za ta daga ido ta kalle shi…..” Allah sarki, ba ta san yadda zuciyar shi ke tafasa da kalamanta ba da ko kusa ba ta fara ba, da
wannan sabon abu da yake ji game da rayuwar Zaynab. Ya ga ba ta da alamun yin shiru balle
tunanin dasa aya, idanunsa a rufe gam, ya nuna mata kofa cikin kakkausar murya ya ce, “Ku
wuce ku bani wuri mutanen banza kawai tambadaddu, jakai, dabbobi da basu san ciwon kansu
ba….”
Ya kware ya shiga tari ba kakkautawa saboda takaicinsu da ya kasa amayarwa, suka fita suna
yi mai dariyar kwarewar da ya yi, wai masifarsa ce ta kwarar da shi. Amma Iftihal gorar ruwan
(eva) mai sanyi ta dauka a firij ta koma ta kai masa, daga nesa-nesa ta ajiye mai ta zura da
gudu. Suka zo suna kyankyasa min yadda su kai, na ce, “Kan ku kuka tonawa asiri, idan ya
gayawa Abba fa?”
Mu karasa a littafi na 2
Takori