Showing 24001 words to 27000 words out of 34700 words
Chapter 9 - GIRMA YA FADI Book 1 Hausa Novels by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf By arewaauthors.com.ng.pdf
da tsintsiya, da wani amai ya taho min gabagadi sai na
kwararo shi a kafafun GG kore shar da shi kamar atini, don rabona da abinci tun na safiyar jiya.
Ji nake kamar hanjina nake amayarwa.
Ya daka tsalle ya yi gefe yana kara zagina, ya ce, “Wallahi ba amai ba ko hantarki za ki amayar
sai kin wanke toilet din nan fes, kamar tuwo na ya fadi in dauka, in ya so gobe a sallameni daga
aikin gwamnati. Wannan ba abun damuwa bane ina da makekiyar gonar gado a Gumel, sai in
koma gida in cimma sana’ar Uwa da Uba watau (noma)”. Ya kira wasu dalibai da za su wuce ya ce su dauko mai kujera, ya girkata can gefe daga nesa
ya zauna yasa hankici ya toshe hancinsa, lokaci guda kuma yana wanke kafarsa da ruwa a
gwangwani da na kwararawa amai.
Haka ba yadda na iya na zage na wanke toilets dai-dai har guda shida, na kuma kwashe
busasshen kashi na zuba a dustbin, sannan ya sani a gaba muka nufo ajinmu. Lokacin karfe
sha biyu da rabi na rana ya rage awa daya a tashi. Na dauka shi kenan GG zai kyale ni, amma
me? Ina sa kai zan shiga ajin ya juyo ya dakatar dani ya ce, “Haka za ki shiga musu aji kina
warin kashi? Koma ki shanya kanki a rana har sai warin ya gushe tukunna, kneel down”.
Na koma cikin rana na zube gwiwoyina idanuna a rufe. Tsayin awa guda da rabi sannan aka
kada kararrawar tashi. Su Azizah suka rugo da gudu suka rungume ni suna tattabani suna
tambayar abin da ya yi mini, ban ce musu komi ba illa hawaye da nake ta sharewa ina fyace
hancina da ya toshe don azaba, suka tabbatar ba za su ji kalma ko daya a bakina ba sai suka
hakura suka kyale ni.
Muka zo gindin bishiyar dalbejiya inda muke tsayawa Shehu direba ya zo ya dauke mu,
shiru-shiru bai zo ba har dalibai suka fara karewa. Su Azizah suka kulu matuka, ni kuwa ta
kaina nake da kuguna da ya rike kamar zai balle saboda durkuson da na yi na awoyi da dama.
Sai misalin karfe uku na yamma sannan muka hango hancin motar Abba (Vanquish), muka
shiga ware ido cike da mamakin yau Abba da kanshi ya zo daukar mu, to ina Shehun? Ashe
dan duniyar ne ka janye da motar da Faruq a kujerar mai zaman banza.
Suka saki baki suna kallon ikon Allah, don ni har zuwa lokacin kaina a durkushe yake, tunda na
yi musu kallo daya ban sake dagowa ba. Ya daka mana tsawar da ta firgitamu ya ce, “Da Allah
malamai za ku shigo ne ko kuwa mu juya ku kwana a makarantar, ruwan wa? ‘Yan kauye kawai
kun saki manyan bakunan ku kuna kallon mutane kamar baku taba shiga mota ba a duniya…” Faruk ya katse shi da cewa, “Haba babban Yaya ayi musu a hankali man da me za su ji? Da
yunwar dake damun su ko da shanya sun da aka yi kamar kayan wanki, ko-ko da fadan ka
kamar barkono bayan basu suka kar zomon ba….?”
Ya ja tsaki “Tsut-tsut!” Kamar ya ci kansa don bala’i. Mu dai tuni mun nabba’a a bayan mota
babu wadda tai magana, ya fizgi motar da gudun ta mai kamar na tashi sama, kan ka ce meye
wannan sai gamu a gida.
Kamin mu fita Ya Faruq ya dubi Azizah ya ce, “Ya ya ne Azzy, na ga mutuniyar tawa ba yada
take?” Azizah ta dan saki ranta ta jinjina kai ta ce, “Kai dai bari Ya Faruq, wani mugun malami
ne Allah ya hadata da shi yau ya zane ta ya sata kneel down a cikin rana wajen awa daya
wallahi”. Iftihal ta ce, “Kai ina jin ba zane ta ya yi ba, wankin kashi ya sa ta. Baki ji ba yana cewa ya za ta
shigo mana aji tana warin kashi?’ Haushin su ya ishe ni na bude motar fit na fice kamar
guguwa, Faruq yana danne dariyar sa ya ce, “Asshah! Abu bai yi dadi ba, galleliyar yarinya
kamar Abu na a ce an sata wankin kashi?” Imran ya daga murya da karfi yadda zan jiyo yana cewa, “Ai madallah, kai madallah, wannan
malami ya burgeni. Yanzu haka ba ta karatu sai SOYAYYAH! Ai ni wallahi ya yi min dai-dai, da
zan ganshi da na sa Abba yasa an kara mai girma zuwa principal din F.G.C baki daya. Me ake
da yaron da ba zai tsaya ya yi karatu ba? Kuma ku shiga taitayinku wallahi don gobe insha Allahu zan je na neme shi mu kulla abota, in
ba shi izinin duk wadda ta ki tsayawa ta yi karatu ya ba ta aikin kashi….” Ni dai ban juyo ba sai
kuka nake, sai Faruq dake ta shan dariya kamar me. Su Iftihal duk a kumbure suntum suka fito
cikin dana-sanin da basu gaya musu ba. Wannan wulakancin da Imran ya yi mani, idan da zuciyata mai hankali ce da ya isa a ce ta
saduda ta fidda shi a cikin ta da duk wani al’amari da ya shafe shi. Amma ina! Abu kullum
kamar ana kara iza shi. Tun daga lokacin ya daina kaf-kaf din da yake dani ya koma treating
dina yadda yake horas da su Azizah. Duk wani wasa da shakuwa dake tsakaninmu ya janye
shi, kullum sai fada kamar Babana.
Kai ni ko Babana bai taba yi min bala’I da sababi irin na Imran ba, da abin da ya isa da wanda
bai isa ba, haka takurar da yakewa su Azizah ya kara ninkata. Ya hana mu kallon talabijin balle
kallon fina-finan India wai mun fara lalacewa. Su Azizah da basu san hawa ba basu san sauka
ba mamakin su ya kasa boyuwa, suka kai karar shi wajen Abba kan ya takura mana ko music
ya hana mu ji a radio wai duk a nan muke debo lalata. Ya sayo kasusuwan kira’ar Jabir ya rika
sanyawa duk gidan.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Na runtse idanuna da karfi, wani sanyi ya ratsa zuciyata
tare da yin wata irin kakkarfar ajiyar zuciya, amma na kasa bude idon. Babu shakka Ya Im ya yi
min bazata, ya shammace ni ya kuma gigita ni. Na rasa da idanun da zan bude in dubi su
Azizah. Wata irin kunya da nauyin su da ban taba ji ba suka taru suka yi min mayafi, na bushe a
zaunen da nake. Su Iftihal kan su bushewar suka yi, kamar sassakakkun gumaka. Cikin mu
babu wanda ya san fitar shi, sai bude ido mu kai muka ganmu a cikin mota, direba ya ja, ko
uffan babu wadda ta yi kokarin cewa a cikinmu. Sai me? Mun fito break kenan muka ga motar Ya Im a kofar ofishin principal, aka aika in zo,
wani irin kululuuu! Da cikina ya bayar ban san sanda na tsugunne a kasa ba na dafe cikina
dake hargagi, ita kanta Iftihal a tsorace take, don dukkan mu munyi tsammanin karar Malaman
mu ya kawo da Azizah ta ce suna bamu amsa. Na shiga na tarar ashe ba a nan gizo ke sakar ba, zuwa ya yi a kan makarantar ta yi mun iyaka
da su GG da ke cewa suna so na, domin ni matar shi ce an daura mana aure tuntuni. In ka kalli
fuskar nan mai bam sha’awa ta Ya Im, ta juye gaba daya da harbadadden kishi zuwa na wani
mutum daban mai zuciya da razanarwa. Na yi hanzarin daga ido na dube shi, in tambaye shi dalilin shi na yi mun haka? Wata uwar
harara da ya jefe ni da ita ba shiri na dukar da kaina kasa na mai da bakina na dinke na kasa
cewa komai. Principal ya ba shi hakuri, ya kuma tabbatar mishi za a tsawatar don wannan
dokar makaranta ce dama. Shi kuwa GG anyi neman duniya cikin makarantar ba a ganshi ba ya
gudu, tunda ya ga motar Ya Im ya tsere don bai san yau da wacce ya zo ba.
Na cika na yi famfam na fito ina hada hanya saboda takaici, wai me Imran ke nufi dani ne? Ya
hana mun kurbar ruwa a duniya ko me? Saboda kawai ina zaman cin arziki a gidansu?
Ya sanya ni cikin wani hali na matukar kunyar su Azizah, ban fita daga wannan ba ya zo ya
lankaya min auren da Allah bai lankaya min ba. Inda na gode Allah daga Azizah har Iftihal babu
wanda ta yi mun tambaya ko daya, domin dai su yara ne nutsattsu kuma wayayyu da basu faya
mai da hankali a kan abin da bai shafe su ba. Na dawo gida ina ta fushi, da dare kowa yana falo amma ni na kasa fita, gani nake kamar su
Azizah za su fadawa kowa abin da ke tsakanina da Yayan su, na ji ni duk na zama wata bare
mara gaskiya kuma munafuka, ban san sanda hawaye ya zubo min ba, nasa bayan hannuna
ina sharewa duk da haka Imran na nan like a zuciyata, haka komi da yake yi bayan bani haushi
illa wannan abu da ya yi mun cikin su Azizah da ya hanani kurbar ruwa cikin gidan gaba daya,
duk da na san ba halayyarsu ba ce fadar abin da ba a tambaye su ba.
Shi din ne dai ya shigo Iftihal na biye da shi, ya ce, “Kin gani ko abin da na gaya miki, saboda
na ce ina sonta a gabanku ta bi ta kuntatawa kanta ta hana kanta sakat, nima ta hana mini.
Tunda na zo gidan nan Iftihal Antin nan naki ba ta barni na huta ba, sai garani take kamar
gare-gare ko kuwa juyani ya waina a tanda. Ban san me take nufi ba, ban san me take so in
mata ba da zai nuna ni Imran mai so da kaunar ta ne. na yi duk iya kokari na ta saurare ni ta
kiya, wayar da na kawo dominta ta rufe ta toshe duk wata kafa da zan bi in nuna mata manufata
ta alkhairi ce a tare da ita”.
Ya samu gefen gadon da nake zaune ya zauna, ya kai hannu ya dago habana ya ga yadda
hawaye ke ta gudu, ya ce, “Jibi ki ga Iftihal, shin dama kaunar da kuke wa Anti-Abun na karya
ne, da take shakkar ku? Saboda ni dai na san in dai so ne Zaynab na sona, ba tun yau ba, tun
sanda ta fara kirgen dangi take sona balle yanzun? Dama so nake ku yi karatu kuma an kare,
ba sai aure ba Iftihal?
Yau shekaru dai-dai har uku ina rainon Zaynab a cikin raina, ina addu’ar Allah ya bani tsawon
ran da zan ga karewar karatun ku, in fiddo burin zuciyata na son mallakar ta. Ki taya ni rokon
Zaynab ta amshi kokon bara ta ko na samu nutsuwa, ita ma ta samu damar karasa jarrabawar
ta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Amma meye amfanin wannan hali da take neman jefa
kanta?”
Na matsa can gefe na takure cike da wata sabuwar kunyar, kamar in daura hannu aka in ce
“Wayyo Allah!” Iftihal ta yi tsaki ta ce, “Kema dai don Allah Anti Abu meye haka kike yi sai ka ce
wata Illiterate (jahila), mu fa ba tun yau ba mun san Ya Im na son ki, har amanarki yake bamu in
zai tafi to meye wannan mummuken da kike mana sai ka ce baki yarda damu ba? Kina
tsammanin zamu so Ya Im ya auri wata fiye da ke ne? Kin yi kuskure. Ko ita Azizah da take
yawan yi miki zancen Mami ina tabbatar miki don kawai ta ga hawayen ki ne da kukan da kike
mana cikin dare, kin dauka barci muke?” Ta fita tana dariya.
Na juya na harari Ya Im da idanuwana da suka kada suka yi jawur, ya rausayar da kai cikin yi
min wani lallausan kallo mai nuna yes, abin da yake fadi da wanda ‘yar’uwarshi ke fadi haka
yake har zuciyarsu. Cikin kuka na ce, “Don Allah mai yasa ka yi mun haka? Ni da bakina kataba
jin na ce ina son ka? Wannan ma ai sharri ne kuma wallahi sai Allah ya saka mini…..” Dariya na
ba shi sosai.
Ya ce, “Kina bani mamaki Zaynab, abin da baki sani ba shine, duk wani motsinki a tafin
hannuna yake. Kuma tun baki da wayo nake da wayo. Maganar kina sona ko bakya sona duk a
barta, na ji ni nake son ki, kuma a yau na furta. Amincewar ki kawai nake nema ba wani abu
daban ba, ina fatan ranar da kuka kare jarrabawa ranar ne za a daura mana aure, don ba zan
koma ko ina ba Zaynab sai tare da ke a matsayin matata (by my side) Insha Allahu. Abin da ya
wuce a bar shi a matsayin wanda ya wuce a fuskanci na gaba…..”
Na dago cikin murmushin takaici na katse shi da cewa, “Kana manta da wa kake magana Ya
Im, ba da Mami bane da Zaynab ne. Ka shirya shiga uku ne da kake marmarin auren
jarababbiya kamana?”
Da sauri kuma cikin murmushi ya ce, “Na shirya Zaynab, in ma sau goma-goma ne a rana duk
za ayi miki, me ake da ‘yan mazan? Ke irin ki hudu ma idan ana ciki a rana a kuma haife za ku
haife goma-goma a rana daya, in dai Imran ne mijin”.
Ya kanne min idonshi daya cikin zolaya yana murmushin sa mai girgiza zuciyana, na kyabe baki
na ce, “Ban ga alama ba, wai Liman babu Mamu…”
Da sauri ya mike ya nufo ni yana kokarin cire riga ya ce, “Eye! Me kika ce Zaynab sake fadi ban
ji sosai ba, bari in nuna miki ko waye Imranan nan da kike rainawa… wayon ki kadan ne haka
maganganunki ko daya babu respect a cikin su. Ko da yake mantawa na yi ke din babbar mace
ce ba karama ba, tunda tun kina karama babba ce, to babu laifi yau kin samu babban namijin
da zai sa ki raina kanki….”
Na ga da gaske yake tubewar zai yi, sai ‘ya’yan hanjina suka hautsine, na koma lallashi na ce,
“Haba don Allah Ya Im, idan Mama ta zo fa? Allah ni wasa nake….” Ya ce (yana kara dosoni)
“Wannan ne kuma baki isa ba, tunda ba matse bakin ki na yi kika fadi abin da kika fada ba”.
Ya wancakalar da shirt din da ke jikinsa ya rage singileti fara sol. Na dauka da wasa yake ba
cirewar zai ba, na cira kai a hankali na hango wani irin ingarman kirji lullube da muscles baibaye
da lallausar gashi baki sidik nannade da gurayen karfi ta ko ina. Ban taba ganin babban mutun
irin Imran ba, ban taba ganin Da namiji mai halittar GIRMA irin Imran ba. Na tabbata duk abin da ya fadi babu kuskure a ciki, zai iya yin abin da ya fi hakan. Ubangiji da
ya halicce shi ya iya halitta, ya kyautata halittarsa yadda ta zamo mabambanciya da ta sauran
maza kwatankwacin sa. Kenan tsarki da GIRMA sun tabbata gare shi. Ganin ya nufo ni
gadan-gadan yana shirin cafka ta, na ce, kafa! Me na ci ban baki ba! Zuwa cikin toilet na murza
key sai karkarwa nake saboda tsabar kaduwa. Ina jiyo shi yana cewa, “Karyar banza cika bakin
wofi, da ki tsaya mana ki ga aiki da cikawa, ki ga in ana haihuwa a gobe baki haifewa Abba dan
jika a gidan nan gobe ba!” A raina na ce, “Allah ya tsare ni da haihuwar SHEGE!”
Ashe har ya fito ya shiga kunnensa, ya ce, “Na ji abin da kika ce Zaynab, ina mai tabbatar miki
in baki amince da bukatata ba wato daura auren mu bayan kammala jarrabawar ki, za kuwa ki
haifi SHEGEN! In yaso daga baya ayi mana auren mu rike abin mu ko ya kika gani?”
Zaynabu dai baki ya mutu, sai Uban mazari da jikina ke ta yi kamar wadda ta yi gamo. Ya yi
dariya shi kadai yana fita daga dakin yana cewa, “Yarinya baki san Imrana ba, watakila sai a
(foot-ball field) watau filin saka kwallo, ranar Innar taki, Abban naki da Ya Faruq din naki basu
isa su kwace ki ba. Kuma in gaya miki ke karamar jarababbiya ce, su manyan jarababbun
tsayawa suke a doka kwallon don a ga hazakar kowa, in ya so mai sa’a ya dauka, ba gudu suke
suna neman mafaka ba alamar weakness (ragonta) kenan”.
Bani na fito ba sai da na ji muryoyin su Iftihal suna cigiyata a dakin za su kwanta, na kasa ko da
shakar kwakkawaran numfashi don yanzu su Iftihal sun zame min surukai, na rasa yadda zan yi
in iya hada ido da su. Sai na jiyo Iftihal na dariya tana gulmatawa Azizah, “Allah sarki Anti Abu!
Ya Im ya takurata a gidan nan, Allah ni har tausayi take bani, dazu da muka shigo baki gani ba
tana ta kuka abin tausayi, yanzu zaman falo ya gagareta tana tsoron ko zamu gayawa Mama
ne”.
Azizah ta ce, “Ke rabu da ita, gulma ce ita ma tana son sa, baki san duk ranar da na yi zancen
Mami da kuka take kwana ba? Gaskiya in suka yi sa’ar yin aure, they’ll make a perpect couple,
domin sun dace da juna. Sai dai kin san ba karamin abu bane a ce Hajiya ta amince, yadda
take son Ya Im da auren Mami, amma daga Abba ba za su samu matsala ba”. Na ga dai in zan kwana cikin bayin nan su ba abin da ya dame su, ba kuma fita za suyi daga
dakin ba hirarsu kawai suke. Karewa ma tare zamu kwana cikin dakin, to boyon har na yaushe
zan yi? Sai na share ido na murje kunyar na fito, duk suka juyo suka dube ni kamin su kyalkyale
min da dariyar su ta ‘yan biyu mai ban haushi. Ban ce musu komai ba na bi lafiyar gado na ja
bargo har kaina. A sannan ne kowacce ta bi gadon