Showing 30001 words to 33000 words out of 34700 words
Chapter 11 - GIRMA YA FADI Book 1 Hausa Novels by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf By arewaauthors.com.ng.pdf
tsane shi? To da WA?????
(Wa’iyazubillahi). Wama taufeeqee illa billahil aliyul azeem…. Kada Allah yasa tunanin nawa na
banza ya zama gaskiya, kada Allah yasa tunanin nawa na wofi tabbatacce ne. ya Allah ka fitar
mun da wannan mugun tunanin a zuciyata…. Allah ka dube ni, kasa tunanina ba gaskiya bane
rudin shaidan ne.
Ba abin da ke dadadawa Innana kamar ganin yadda nake girma da wani irin murjewa, kai ka ce
irin Larabawan nan ne na Lebonon. Duk na fi ‘ya’yan Farfesa daukar ido da kwarjini, haka duk
kalar kayan da nasa kyau suke min su kuma amshe ni kasancewata jajur, masu tsada ne ko
akasi, kai ka ce don ni aka kirkire su. Ni Zaynabu-Abu shiru-shiru ce, bani da kwaramniya, kuma
bana sonta. Da wuya ka ga ina magana in ba a kan abu mai muhimmanci a gareni ba. Sun baro Gwarzo bayan motarsu cike da tsarabobin da suka saba komawa dasu, wato kamar
su man shanu, garewanin man gyada, kindirmo, madarar shanu, kwan kaji da na zabbi da
sauransu. Wannan karon har kajin gidan gona ishirin Malam ya ba su Hassan, amma an fige an
gyara ya kuma ba Haydar takwaransa dan maraki, Abba ya ce a bar shi a nan a kiwata masa. Ni da su Azizah bamu so rabuwa ba, don dai ina son samun lokaci da Innana ne su kuma sun
kallafa ran su a son zuwa Porthearcourt, akwai tambayoyi da dama da nake son in yiwa inna,
musamman a kan irin gore-goren da su Hassan ke mani a shekarun baya, wanda wancan
lokacin karancin shekaru da rashin wadatar hankali bai barni na kuma waiwayarsu ba, sai
yanzu da hankali ya zo mini nake ganin hakan tamkar wani barazana ne ga mutuncina a nan
gaba.
Mun kwanta ne da daddare, sauro ya gallabe mu, duk kuwa da maganin sauron da muka kunna
da (Rambo) da na fesa, amma ni ko jin cizon suron bana yi balle in sosa, abubuwa ne da yawa
ke damuna a zuci. Wurin karfe daya na dare na ja tsuka “Tsut!” don tuno shekarun baya. Ashe
Inna Rabi barcinta ba wani nisa ya yi ba, ta ce, “Ke in wani abu ne ya dame ki, ba kya gaya
mun? Haka kawai ki bi ki isheni da tsaki cikin dare”.
Maimakon in amsa mata sai tsakin ne (by mistake) ya sake subutowa daga bakina, na ce, “Kai
abin ne ma Inna na kasa ganewa wallahi”.
Ta ce, “Can gidan Baba Sa’idun naki, fi sauran-Babanni ne kike da matsala ko-ko satittikan da
za ki yi mana ne kike ganin kyashin su, kin baro A/C sauro na cizon ki? Abin da na guda kenan
ai tun farko Kyauta na hana tafiyar ki hannun su Azumi, amma Malam bai saurare ni ba, saboda
dukkanku baku dauke ni a cikakkar mai hankali ba sai SA’IDU. Sa’idu ya fini GIRMA a idanun
ku, komi Sa’idu ya ce shine dai-dai, amma Rabi ai MAHAUKACIYA ce…..”
Wasu hawaye suka balle min, na ce cikin rishin kuka, “Ki daina gaya min haka Inna,
wallahi-wallahi a kowanne hali, a kowanne matsayi babu inda ya fiye mun dakin nan naki
kwanciyar hankali. Babu inda nake ji na sake, freely, cikin walwala da kwanciyar hankali tamkar
nan. Bani da wanda ya fiki, bani da wanda nake so fiye dake. Baba Sa’idu bai taba daukar ki
matsayin maras hankali ba, ke ce dai kike zaton haka.
Ya sha cewa inda mai hankali a duniya to ke ce, in da wanda zan dage wurin bin maganarsa to
ke ce, in da wanda ta san ciwon kanta a duniya to ke ce. Abin da ke damuna kwata-kwata bai
shafi abin da ke kike tunani ba. So nake in tambaye ki ashe mu ba Fulanin Gwarzo bane?
Kuma meye BARAROJI? Mene ne SADAKA-YALLAH?????” Inna Rabi ta mike zaune a nutse ta yi murmushi. Ta mika hannu ta latsa makunun wutar lantarki
dakin ya gauraye da haske, iare-iren wadannan gorarrakin ita ma ta sha su wurin kishiyoyinta a
zamanin kuruciyar ta, ta kuma tabbata watan-watarana za a yiwa Abun ta. To amma ba ta zaci
tun yanzu ba, ta dauka sai a gidan aure ko lokacin aure. Ba ta san daga inda ya fara fitowa ba,
don haka ta ce, “Shin wa ke ce da ke hakan a gidan Sa’idu?”
Na ce, “Maganar fa ba ta yau ba, tun farkon zamana dasu ne. kuma tun lokacin Baba ya saba
musu basu sake ba. Ita Hajiyar ma yanzu ba ta shiga harkata kowa zaman kansa yake a gidan,
babu mai shiga shirgin wani. Ita Hajiya Sa’a ta gayawa su Hassan suka samin kahon zuka a
wancan lokacin, wai suna kyankyami na saboda mu BUZAYE ne, kazame. Su tofar da miyau,
suyi amai wai BARAROJI babu wanda ya kaimu kazanta. Sai nake jin tsoron ko wani ciwo ne
hakan abin kyama”.
Inna Rabi ta hasala ta ce, “Ita Sa’ar har tana da bakin gaya mun haka? Tana da bakin ce dake
SADAKA-YALLAH ba ta fadin babban? Koma meye ta ce a yanzu ai duniya ce, ita din kuma
makaranta ce babu abin da ba za ka gani a cikin ta ba. Wanda bai zo ba ma tana nan tana jiran,
kuma tarihi MAIMAITA KANSA yake, sannan kowa ya kwana lafiya shi ya so. Idan a yau na ga dama wallahi ba za ta kara jin dadi a rayuwarta ba, daga ita har Sa’idun da
take takama da shi, domin GIRMANSU YANA HANNUNA, yau ne ko gobe in na ga dama sai in
FADAR DA SHI, in ga karshen kudi da boko, wadanda basu da amfani idan babu mutunci a
idon duniya. To amma ba zan yi hakan ba saboda wasu manyan dalilai, akwai ranar da dubunta za ta cika.
Tara su nake daga ita har Sa’idun ina jiran ranar da wani a cikinsu zai wulakantaki, ina jiran
ranar da zai nuna fifiko tsakaninki da ‘ya’yansa….” Sai kuma ta razana da ta fuskanci ko da wa
take magana, Zaynabu ce ba Au ba, da cikakkar budurwa mai hankali take magana ba
Kyauta-Abun d ata sani a baya ba ce,.
Ta yi hanzarin gyara zancenta da cewar, “Zaynab mu ba Bararoji bane. Sune ‘yan kasarmu
dake daji, mu ‘yan kasar Niger ne ‘yan uslin wani gari DAMAGARAM, amma iyayenmu da
‘yan’uwanmu duk a babban birnin Yamai (Niamey) suke zaune, har yanzu suna can.
Mahaifinmu fitaccen dan kasuwar fata ne da ya yi fice a Niger, kuma mashahurin dan siyasa ne
da ya rike mukamai da dama a gwamnatin Damagaram, wanda gab da rasuwarshi yake dan
takara mafi rinjayen magoya baya da suka tsaya neman kujerar gwamnatin Damaragam. Duk
dangina suna Niamey, ba fakiri ko daya, bamu taba yin talauci a rayuwarmu ba, bamu san shi
ba ni da iyaye da dangi na gaba daya. Kaddarar aure da rabon haihuwar ki ya kawo mu
Najeriya mu da mahaifinmu da kanwata NURATU da ta bata a hanuna.
Batan Nuratu ne ya hanani komawa gida, ya hanani neman dangina har yau don ban san me
zan ce musu a kanta ba, kuma rashinta ne ya tsomani a halin da har yau kike ganina a ciki ake
min kallon MAHAUKACIYA ko TABABBIYA.
Su kuma danginmu basu san inda muke ba, don mahaifinmu rasuwa ya yi a sanadiyyar hadarin
jirgi a kan hanyarshi ta komawa gida, ya gaya masu cewar ya aurar dani ba da saninsu ba. Ki
taya ni addu’a Allah ya bayyana min Nuratu, ni kuma na yi miki alkawarin a ranar da na ganta a
ranar ne zan sadaki da danginki na wurin uwa. Sai kin raina zamanki da su Sa’ar da ke ce dake
SADAKA-YALLAH, sai dai ki basu SADAKAR ki wuce.
Idan kika shiga Niamey ko Damagaram kika ce kina neman wani da ya shafi iyalin MAINASARA
KANGIWA, ko yaro kankani ya san wannan sunan.
Ki yi hakuri ki kyale ta, akwai dalilin da yasa ba ta son ki, ba kuma za ta so kin ba har abada, illa
ta boye hakan a ranta don amfanin kanta, amma ai……” Ta sunkuyar da kanta. Ta dade tana
kallon kyawawan yatsun hannunta, can ta dago ta ce, “Ke Zaynab kada ki damu kanki a banza,
da dangin Uba ai ake tutiya ba na Uwa ba, ko ta isa ta ce da Malam SADAKA-YALLAH? Ni ta
fada ta more, akwai ranar da GIRMA ZAI FADI!”
Na yi shiru ko kwakkwaran motsi bana yi, sauraron Innana nake da dukkan hankalina. Ta ga
akwai alamun rashin fahimtar wasu abubuwa cikin kalamanta a tattare dani, sai ta ce, “Ke yi
kwanciyar ki don Allah kada ki kara sa wannan shirmen a ranki, na ce dake da dangin Uba ake
tutiya ba na Uwa ba.
Kuma ni nan da kike gani, zaman jiran Nuratu nake, amma ba zaman soyayyar Malam Ali ba,
ko zaman jiran Sa’idu ya dauko ya bani. Domin har yau Sa’idu bai yi arzikin da zai bani in
mance takaicin da ya tusa mini ba, da rayuwarmu da ta gurbata a dalilin son zuciya irin nasa…”
Da maganganun Inna na kwana ina taunawa ina cizawa, ina hurawa a cikin raina. Abubuwa da
yawa na kasa fahimtarsu, I’m confused! Da maganganunta masu daure kai da caza hankali, illa
na samu kaina a daukan ‘Diary’ dina na rubuta kalmar “MAINASARA KANGIWA” da wasu cikin
kalamun ta da ban fahimta ba. Nake fatan duk ranar da Allah ya dawo da Ya Faruq zan sanya
shi ya fidda ni duhun da ke cikin su.
Hutuna na wannan karon a Gwarzo na ji dadin shi fiye da na ko yaushe, don muna tare da
mutanena su Hafsisi. Ita Indo an sa mata rana da wani malamin su a can Kabon, ita ko sarkin
rigima Hafsisi ta ki kula kowa wai ita Faruq take jira, shi kadai take so duk fadin duniyar nan,
idan ba shi ba sai dai ta mutu ba ta yi aure ba. Na yi dariya har da fidda hawaye, na jinjina kai, na jinjina mata, don ni dai tunda nake da Ya
Faruq dai-dai da rana daya ban taba jin ya ambaci wata ‘ya mace a duniya da sunan so ba,
balle wata Hafsisi. Sanda muke aji hudu ne ma Azizah ta taba rubuta mishi leta wai tana son
shi, in ta kare karatu ya gayawa Abba yana son auren ta. Tun lokacin ya kirata kamar abin arziki, ya kwakkwada mata mari ya ce kuma ba shi ba, ko wani
daban ta sake cewa tana so sai ya gayawa Abba, in yaso a cire ta makarantar ayi mata auren
da Shehu direba dai amma ba da shi ba. Tun daga lokacin ko da wasa Azizah ba ta kara shiga
shirgin sa ba, shima kuma sai ya rage wasan da yake dasu duka. Na ce, “Hafsisi in za ki ji shawarata, ki samu wani mai sonki tsakani da Allah ki yi auren ki ya
fiye miki alheri, don shi wannan Ya Faruq da kike gani ko zancen aure baya yi, kuma nan da
shekaru biyu ma albarka ya dawo. Azizah ma bai karbeta ba balle ke?” Hafsisi ta kulu, ta kawon
duka ta ce, “Me Azizar ta fini ban da Turancin banza, nima yanzu meye ban sani ba a Turacin?”
Na ci gaba da dariyar da ta kara kular da ita, cikin zolaya na ce, “Turancin ma ba fa fiki ba”.
(maganar da na zo ina dana sani da ban yi ta ba).
Budar bakin Hafsisi sai cewa ta yi, “Ba wani nan, ai dama ba tun yau na san kin fi son su Azizah
dani ba, saboda su masu kudi ne kuna samu a jikinsu kuna ci ke da Malam da Ya Faruq din
naki. Duk kun ki mahaifarku kun je kun tare masu a gida saboda tsabar kwadayi. In dai don dan
abin da ake ikirarin Malam ya yiwa Alhaji Sa’idu ne da yana karami, ai yanzu ya biya shi har da
riba, tunda har Makkah ya kai shi sau ba iyaka. Kada dai kuke mantawa a kullum an ce, inda
kwadayi…..” Ta murguda baki ta yi tafiyarta ta barni da baki bude.
Maganganun Hafsisi sun haifar min da ciwon kai, na dade ina maimaita kalamanta a zuci. Babu
shakk duk abin da ta fadi gaskiya ne, kuma kalamanta duk shigen na Innana ne. Sai na ji wasu
dumammun hawayen tausayin kaina masu zafi sun digo a kan yatsun kafata. Mafari kenan da
Hafsisi ta daina yi min magana, ta dauki gaba dani, ta shiga nuna kyashin ta dani muraran. Tun daga lokacin na ji Sokoto ta fice min a rai, na rika gudun cikar kwanakin hutuna. Na
alkawartawa raina ko da na koma gidan Baba Sa’idu da na kare makaranta ko kwana daya ba
zan kara ba zan dawo gida.
Don haka a komawata wannan karon su Azizah sun ga sauyi da yawa, gaba daya na yi sanyi,
na mai da kaina bare a cikinsu. Na daina amfani da kudin da Baba yake bamu sai dai in ajiye
kawai. Shima don ina jin nauyinsa ne amma da na ce ya daina bani.
Na rage cin abincin gidan, idan na ci da karfe biyu bana kuma ci sai dare, na daina karin
kumallo, don a ganina duk hakan yana cikin kwadayin abin hannun su. Daga baya ma in an
tashi daga makaranta sai na dinga shiga restaurant din makaranta in saya in ci, in mun dawo ba
zan ci na gidan ba. (Na manta cewa shi kansa kudin da nake sayin ai daga aljihun Baban yake
fitowa). Su Azizah dai na kallon ikon Allah sun rasa ta cewa, sai Iftihal ce rannan ta ce,
“Anti-Abu dai ta zama waliyyah”.
Ranar wata alhamis mun dawo daga makaranta, a harabar gidan muka tadda Hajiya ta yowa
wata kyakkyawar budurwa rakiya, ga wasu ‘yammata uku suna takewa budurwar baya sun rike
mata jaka, za ta yi shekaru ashirin da shida. Baka ce amma a goge take, ko ina a jikin nan nata
sumul-sumul, ga sullubebiyar mota ta (end of discussion) baka sidik sai daukar ido take. Tsayawa fasalta sittirun da ke jikinta ma bata lokaci ne, sai jifa mu take da wani irin
murmushinta kamar madara, da hakoranta kamar kankara. Ta yafito mu da hannu muka je ta
kama hannunmu mu duka tana tambayar mu ya ya shirye-shiryen (WAEC).
Mamaki ne ya kama mu na yadda akai ta sanmu har ta san jarabawa zamu yi. Hajiya ta shiga yi
mata bayanin mu, wai wadannan Azizah ne da Iftihal (twin sisters) din Imran. Wannan kuma
Abu ce kanwar Faruq. Ta ce, “Lah! Ke ce Abun Faruq Aliyu?’ Ta makale ni sosai a jikinta ta sake
cewa, “Ina jin labarinki sosai a bakinshi, amma ban zaci haka kike da kyau ba kamar Baturiya.
Dan’uwanki ya damu da ke sosai Zaynab, da wuya a zauna da shi bai yi zancen ki ba, ina taya
ki murnar kasancewa ‘yar’uwa ga mutum irin Faruq Gwarzo”.
Na lumshe ido wani dadi ya kashe ni. Kowa ya budi baki alheri yake fada a kan Ya Faruq, ban
taba jin wanda ya aibata shi ba, dai-dai da rana daya. Haka duk wanda ya san shi in ya ganni
zai ce ya sanni, Faruq yana yawan ambato na. wannan ne yasa har abada ban da mutum mai
kimar Ya Faruq. Ta mikawa ta bayanta hannu ta miko mata jakarta, ta sanya hannu a ciki ta damtso kudi da ba
ta san adadinsu ba, (American-Dollars) ta fito dasu tsurar su ta raba su gida uku, ta mika mana.
Azizah uwar son kudi ta riga kowa amsa, har da mu aka rakata bakin motar ta, ta ja ta fita cikin
wani irin ubansun tuki. Azizah ta buga tsalle ta yi cikin gida tana cewa, “Yanzu zan shirya in tafi
canji, in Allah ya yarda sai na zama MAMI ABDULHADI”.
Na samu kaina a maimaita sunan Mami Abdulhadi fiye da cikin carbi, na so in ji sunan a baya
amma na rasa daga inda na ji shi. A dakinmu na ce da Iftihal “Wai ita wannan Mami wace ce?”
Ta ce, “Baki san Adda Mami ba? Diyar Gwamnan Sokoto Abdulhadi Talata Mafara, budurwar Ya
Im?” Wallahi ban san sanda na saki kudin da ke hannuna ba suka tarwatse a kasa, a take na ji na
tsane su bana son ganin su kamar yadda na tsani wadda ta bani. Na ji haushin kaina da har na
tsaya na kula Mami, wani kululu ya zo ya tokare min a makogaro ko miyau na kasa hadiya.
Su Azizah sun dauka wai mamakin ita ‘yar waye ne ya kamani, don son kara burge ni da
tabbatar min da Mami wace ce, Azizah ta zura da gudu dakin Mama ta zo da mujallar
‘OVASION’ da bama gajiya da kallo ta auren Aishah Babangida tana nuna min Mami cikin
‘yammatan Aishah, dama kuma na so in tuno inda na ga fuskar Allah ne ya mantar dani. Irin rudewar da Azizah ta yi a kan Mami sai na ji ina tausayin kaina, da burin da na daura a kan
Ya Im. Yanzu idan ta san ni din ina son dan’uwanta ko ya ya za ta karbi al’amarin? Ni
Zaynabu-Abu ‘yar Malam Ali, jikar Mamman Gwarzo, da bamu da komi sai tumaki, sai tsintsaye.
Na fara fidda rai da Imran a karo na farko a rayuwata. Na san Imran ya fi karfina nesa ba kusa
ba, wai wan ce ‘kwarya ta bi kwarya…..’ Anya maganganun Anti Rose za su taba zama gaskiya
kamar yadda take ikirari?
Kwana na yi a ranar nan cike da kishin Mami, ko rintsa ido na kasa, gami da wani azababben
son Imran dake kara daidaita zuciyata. Sai dai wannan karon kam kauna ce ta hakika, da har
nake jin ko ya ya ne, ko ya nake ba zan iya barwa Mami shi ba.
Amma a dole washegari na shiga tirsasa zuciyar da ta fidda Imran da duk wani al’amarin shi a
cikin ta. Ina nuna mata beke da illar dake cikin hakan, ina nuna mata Imran ba alkhairi bane a
tare da ita, ina nusarsheta da cewa a kul, Zaynabu! Igiyar rakumi… ta yi nesa da kasa, tsira da
mutunci…. ya fi tsira da kudi, abu mai yiwuwa