Showing 6001 words to 9000 words out of 34700 words

Chapter 3 - GIRMA YA FADI Book 1 Hausa Novels by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf By arewaauthors.com.ng.pdf

muke ci, in za ta tafi aiki sai ta sanyamu a gaban motar muje in an
sauke ta sai direban ya dawo damu.
Fadin murnar da Iftihal ta yi da zuwana ma ba zai fadu ba. Ranar lahadi da Mama ba ta da aiki
daukarmu ta yi ta kai mu wajen wankin kai, ta yi mun sayayya mai yawa. A ranar ne kuma Aziza
ta dawo.
Farkon ganina da Aziza ban san cewa ba Iftihal ba ce, saboda kamannin su (identical twins).
Yara bula-bula dasu kamar hura su ake sai ka ce balloon, da gani duk na girme su sosai, cikar
hutu suka fini.
Azizah ce take tambayar Hajiya Azumi wai ni wace ce? Ta ce, “Anti-Abu kenan, Yayar ce
Azizah”. Ta kyakkyabe baki kamar za ta yi kuka cike da kishi ta ce, “ita ma ‘yar ki ce?” Ta ce,
“Yata ce mana”. Ta sake cewa, “To amma ai ita fara ce mai gashi irin na Indiyawa”. Ta tuntsire
da dariya ta ce, “Ke kuma baka ce mai gashi irin na Katsinawa!”.

***

Mafari kenan da sunan (Anti Abu) ya bini a bakin su Azizah har yau inda nake. Makarantarmu
jeka-ka-dawo ce ta Gwamnatin Tarayya (Federal Govt. College). Alkawarin da Baba Sa’idu ya
yiwa Rabi bai karya ba, a hutunmu na farko ko kwanaki biyu bamu yi da hutun ba ya hada mu
da direba ya kaimu Gwarzo. Su Iftihal sun fini dokin zuwa Gwarzo, ba don komi ba sai don jin dadin zaman garin da ita Iftihal
ta yi a zuwanta na farko, take kuma bai wa ‘yar’uwarta labari, musamman gidan gonar babansu.
Inna ta ji dadin yadda ta ganni, har ta kasa boye mamakin ta. Ta ce,
“Kyauta ke ce kuwa???”
Ni kaina na san na yi kiba, haskena ya kara fitowa, nutsuwar nan da ta sanni da ita tana tare
dani ba abinda ya canza ba kamar su Azizah ba, sai ma abinda ya karu. Na ji dadi da ba ta
nuna wa su Azizah kyara a kan idona ba, illa dai dakinta ne ta kulle alamun ba za su shiga ba.
A cikin kunne na na ji sanda tasa kara tana ture warin takalmin Iftihal da ban san ya a kai ya je
kofar dakin ta ba, tana kunkuni tana cewa, “Allah kai mana tsari da ire-iren zuri’ar Sa’idu, ka
kare Abuna daga dattin zina”.
Gaskiya a zamana tsawon watanni uku kacal gidan Farfesa na yi hankali gami da wayewa fiye
da nawa na da, don haka maganar Inna ta tsaya mun a rai. A kullum gidan gonar Baba muke
wuni, can ake kai mana abinci. A lokacin su Hafsisi da Indo ma sun zo hutu daga Kabo, duk
tare muke yawon. Kauyancinsu da gidadanci na baiwa Aziza matukar dariya, don komi suka gani a jikin su ko

suka ji sun fada wanda basu sani ba sai sun tanka. Inna take tambaya ta Faruq kwana biyu bai
zo ba. Na ce, “Nima tunda na je gidan ban ganshi ba, an ce karatun ne ya yi masu zafi, shi yana
(attachement) ne a Abuja da (Federal Revanue) yayin da Imran ke yi da (Company SIWES) a
Kaduna. Da zamu dawo aka hado mana tsarabar Gwarzo rankatakaf! Azizah mai son man shanu ce da
madarar shanu sabuwar tatsa, wadda ba ta kai ga zama nono ba. Ita kuwa Iftihal ta fi son a ba
ta korai da ludaya na duma masu zane mai kyau, duk haka Inna Dubu da Rakiya suka hado
masu, daga Inna Rabi ko a sauka lafiya basu samu ba, sai Abunta ta hadawa shatara ta arziki,
don haka cikin dabara na diba cikin tawa tsarabar data hadamin na basu na ce in ji ta, ko don
wanke damuwar da Azizah ta shiga kan yadda Innar ta karbe su. Ita ko Iftihal ba ta ma kula da
ita ba don ba ta dauke ta cikakkar mai hankali ba. Karfe takwas na daren ranar a Sokoto ta yi
mana.
A zamana gidan Baba Sa’idu abinda na lura na faruwa cikin gidan shine, Mama mace ce mai
kishin jaraba, ita ko Hajiya Sa’a mulki da ganin kyashi ne cike da ranta, ba ta son Abban ya
yiwa kowa wani abu sai ita sai ‘ya’yanta wadanda dukkaninsu maza ne su hudu, in ka dauke
Imran da yake babba duk yara ne, fitinannu masu dan banzan raini. Kusan duk rabin albashin
Farfesa a karatunsu yake karewa.
Za ka yi mamaki in ka ji cewa yaro karami kaman Jauhar kudin makarantar shi naira dubu dari
da hamsin ne (per-term), amma duk da haka ba ta gani, kullum idonta na kan na Hajiya Azumi
da ‘ya’yanta guda uku, sai kuma ni da yanzu aka kara mata. Tun zuwana gidan suke damawa,
kowacce tana haba-haba da miji don neman zama mowa. Shi ko Farfesa irin mugayen ‘yan
bokon nan ne da biro da takarda ya fi komi muhimmanci a gare su.
Ba shi da lokacin ire-iren gutsiri tsoman da ke faruwa a gidan, don haka ko da Hajiya Sa’a ta
kawo mai korafin wai Azumi ta zuge ni in zauna a wurin ta, sai cewa ya yi,
“Har nawa Abun take da za a zugata? Ki kyaleta ta zauna dasu tunda da su tafi sabawa, ko
cikin maza kike so ta zauna?”
Faram-faram ta tashi, tun daga ranar Hajiya Sa’a ta kulla ta dani, ‘ya’yanta Jauhar, Hassan da
Rufa’i take gaya musu wai ni BARAROJI ce Buzayen Daji su daina zama kusa dani. Daga ranar
fa suka diba wai Maman su Iftihal ta zo da Bararoji. In abinci suke ci na zo zan gifta sai Jauhar
ya tsartar da miyau ya ce, “Tir! Me za ayi da kazame?” Tun abun baya damuna har na soma share hawaye, musamman ranar da Hassan ya kwararo
amai da na wuce shi yana cin abinci. Iftihal ce ta gayawa Mama, ta yi mamaki sosai, ta yi ta
lallashina ta ce in yi hakuri za ta fadawa Abba. Su ko su Azizah ganin kwana biyu Maman ba ta
dauki wani mataki ba, su Jauhar kuma basu fasa abinda suke ba suma suka shaka. Da daddare an hadu ana cin abinci kaman yadda yake a al’adar gidan, Rufa’i ya faki idon Abba
ya tofa mun miyau a cikin plate dina, Jauhar ko ya tsartar gefe, ya ce, “Hassan gaskiya da aka
ce Bararoji babu wanda ya kai su kazanta, ka duba ka ga yadda take mixing mayonnaise da
margerine cikin farar shinkafa”. Suka tintsire da dariya. Abban ya dube su suna ta dariya, ya ce cikin mamaki, “Ku kuma ina kuka samo Bararoji?” Duk
suka yi tsit! Ya buga tebir da karfi ya kara maimaita tambayarsa, kowannen su mara ta cika fam
da fitsari. Azizah ta yi kwafa ta ce,
“Abba Hassan, Rufa’i da Jauhar ai BARAROJI suke ce da Anti Abu, in sun ganta su tsartar da
miyau ko suyi aman abin da suka ci, in tana cin abinci su tofa miyau a ciki”.

Farfesa jikinsa har tsuma yake, muryarsa na rawa ya ce, “Ai ban ga laifinsu ba, ga inda suka
samu daurin gindi nan”. Ya nuna Hajiya Sa’a da ta sunkuyar da kai. Ya koma mazauninsa yana
kaduwa kamar mazari kamin ya yi murmushi ya ce, “Sai ki nemi wani gidan kuwa, amma ba
gidan Sa’idun Malam Ali ba!”. Ba ita kadai ba hatta Mama ta kadu da wannan hukuncin na Abba. Hajiya Sa’a saboda takaici
ba ta san sanda ta ce,
“Ban gane ba, Abu ta fimu iko da gidan nan kenan?”
Ya girgiza kai don tabbatar mata tambayar ta ita ce amsar ta.
Ta ce, “Aikin banza! Su da gidan ubansu? Ba Bararojin ba ce karya suke? Da dai ba a san
asalin balbelar bane….” Kamin ta karasa ya soma kwallo da su Hassan a cikin falon, cewa
yake, “Fice min a gida, Hajiya Sa’a, sai na neme ki”.
Idanun Hajiya Sa’a suka firfito kuru-kuru, hankalinta ya tashi saboda irin dukan da yake yiwa su
Hassan kamar ba mai rai yake bugu ba, da kyar Mama ta yi waje dasu bayan sun bugu, ko ina
a jikinsu ya amsa ya haye ya yi suntum.
Ta mike ta fice, dakinta ta shige ta kulle amma ba ta je ko ina ba. Abba ya rantse ya yi rantsuwa
da Allah, “Wanda duk ya sake ce da Abu BARAROJI a cikin gidan nan sai dai ya nemi wani
Uban ba ni ba, kun ji ko ‘ya’yan iska?”
A ranar Mama da ‘ya’yanta kamar sallah, Abba ya wulakanta Hajiya Sa’a da ‘ya’yanta, su Iftihal
kamar a rungume Abba kan su ya fasu, su a dole Abba ya fi son su da su Rufa’i. Azizah har
kwarya-kwaryar liyafa ta shirya, inda ‘yan dakin Hajiya Sa’a su kai kwanan bakin ciki da takaici.

****
[7/11, 3:57 PM] +234 706 160 2791: Ai jin haka Innana ta yi hanzarin zuwa ta kamo kofar
dakinta ta bame da mukulli, wato (Iftihal ba za ta shigar mata daki ba). Ba don yarinya ba ce
kuma ba ta kawo komi a ranta ba, da ta gane abin da Inna ta ke nufi.
Sai Inna Rakiya ta dauki kayan hannunta ta ce, “Muna maraba da Iftihal Basakkwata”. Ni da ita
muka yi dariya, yayin da na yi wata asirtacciyar ajiyar zuciya.

Da alama Iftihal yarinya ce mai saurin sabo da kuma wayewar kai, gami da karbar rayuwa a duk
inda ta tsinci kanta. Kafa ta nade tana cin gyada, tana bani labarin Aziza (twin- sister) dinta.
Ba ta daddara ba ta sake kallon gefen da Inna take, ta ce, “Innar Abu sammun rogon nan da
kike tsamewa, hadawa nake da gyadar”. Inna ko kallon ta ba ta yi ba, yayin da kirjina ya shiga
luguden uku-uku. Tsoro na Allah tsoro na kada Iftihal da ta zo yau din nan ta fahimci cewa
gabar da Innana ke yi da Babanta itama ya shafe ta. Idan rogon Innar ya amsa mata, to ita ma
Innar ta amsa. Ta sake maimaita tambayar ta na Inna ta ba ta rogon. Budar bakinta sai cewa ta
yi,
“Ai ba ubanki ne ya saya ba!”.
Na yi saurin kai hannuwa na dafe kai, cikin wasu hawaye da suka ciko idona. Inna Dubu ma
ranta ya baci da wannan halayya ta Inna ta. Ta zo tana dibar rogon cikin roba tana cewa,
“Bari ta ci kasona, ai ni mijina ne ya saya idan ita ba Ubanta ne ya saya ba!”.
Tana fadi ne cikin dariya, domin gusar da damuwar da fuskar ‘yar yarinya Iftihal ta shiga.
Watakila ba a taba yi mata irin wannan gwasalen ba a rayuwarta. Ta kawo rogon ta dangwarar
mana, tana cewa da Iftihal, “Ke ci ki rabu da ita, ba ta jin Hausa sosai, ba ta fahimci me kike

cewa ba”.
Ta ce, “Abu ma ba ta jin Hausar? To wanne yare suke ji?” Ta ce, “Abu ta fita jin Hausa, ita
faransanci take ji irin na kasarsu, ai kin sani ko?” ta ce, eh na sanshi, ana koya mana a
makaranta, Abu ina ce ce kasar ku?” Na yi dan diri-diri na rashin sani, don kuwa ni ban san da
wata kasa ba banda wannan da muke ciki. Inna Rakiya dake gefe ce ta ce da ita, “Niger!”.
Malam da Baba Sa’idu ne suka shigo, suna hirarsu irin ta wadanda suka aminta da juna. A yau
ban yi gigin yin tsallen taren Baba Sa’idu ba, kamar yadda na saba. Duk da kankantata na san
ba abinda Innata ta tsana kamar ta ganni a jikin Baba Sa’idu, don haka na yi ma kaina
alkawarin na daina, daga ranar da hakan ya janyowa Baba Sa’idu wulakancin da bai taba gani
ba.
Sai muka russuna mu duka muna gaishe su, ni ina gayar da Baba ne, Iftihal na gayar da
Malam. Murmushin jin dadi ya bayyana a fatar bakin Baba Sa’idu, yayin da Malam ke ta
tsokanar Iftihal da amaryarsa.
Ya ce, “Yanzu-yanzu zai kwashe kayan dakin Rabi ya sanya ta, don ita ta tsufa ita ko gata nan
sabuwa gar a leda”. Iftihal tana ta dariya, ta ce, “Baba Malam ka ce da Abu ta rakani in ga gari
don in ba Aziza labari”. Malam ya ce, “Maza Abu sako takalmanki ki raka amaryata gidan gonar
Babanta, ki kaita har gidan Halima da Safiya, ki gaya musu diyar Babanku ce”. Muna tafe tare da Iftihal tana ta yi min hira, wadda duk rabin maganarta Turanci ne ba duka
nake fahimta ba, amma ita ta kasa gane hakan ta hutar da bakinta, ni dama tuntuni Allah bai
dauran yawan magana ba.
Da alama yarinya ce mai surutun tsiya, fadi ba a tambaye ka ba. Takaicin al’amarin Innata a kan
Baba Sa’idu ke damuna, abin har ya wuce kansa ya shafi ‘ya’yan cikinsa? Rabona da su Iftihal
tun suna kanana da suka zo da babarsu wadda abin mamaki ita suna shiri da Rabi, sabanin
uwargidan da suke narka matsananciyar kiyayya. Shin har yanzu lokaci bai yi ba da ya kamata in san duk musababbin wannan? Tambayar da
Iftihal ta jefo min ta sake jefa ni a cikin rudani,
“Abu Innarki na da tabin hankali ne?”
Nayi gaggawar juyowa na dube ta tamkar ta soka min mashi a kahon zuci, amma na kasa ba ta
amsa, don ban san me zan ce mata ba. Gaskiya ne al’amuran Innata sun fi kama da na masu
tabi hankali, kuma a yadda kowa yake biyar da ita a gidan, ba a dauke ta cikakkar mai hankali
ba. Kishiyoyinta basa kishi da ita, basa takaicin duk gwasalen da take musu. Mijinta bai dauki
yanayin rayuwarta da muhimmanci ba, balle har ya damu da hakan, binta kawai ake da yadda
take so, don a zauna lafiya.
To amma ni ba zan taba yarda da cewa da ake wai Innata na da tabin hankali ba, musamman in
aka yi la’akari da irin kalaman da ke fita a bakinta na hankali da sanin yakamata ne. Illa in ce
yanayin rayuwa ne ya mai da ta hakan, ya sanya ta daina kaunar kowanne dan adam sai mu da
muka zame mata dole. Na kan tambayi kaina don me kiyayyar ta ya fi yawa a kan Baba Sa’idu? Me ya yi mata? Me
yasa ta tsane shi fiye da kowa a duniya? Me yasa kome zai mata don ya faranta mata baya
burgeta? Tunda nake ban taba ganin mutum mai kirki, karamci da mutuncin Baba Sa’idu ba,
kamar yadda ban taba ganin mutum mai arzikinsa ba!.

Na daga kai na yi duba ga Gidan Gonarsa makeken gaske, dabbobin dake ciki dukkaninsu
farare ne sol. Girman gidan gonar kadai ya isa a gina gidaje biyar manya-manya, ba tare da
kowanne ya gogi dan’uwansa ba.
Ita kanta Iftihal sakin baki ta yi galala! Tana kallon Agwagin ruwa farare kal sama da dari na
yawo a cikin tafki, fararen Tantabaru rainon Ingila na tashi daga wannan daki zuwa wancan.
Fararen Babba-Da-Jaka dika-dika goye da ‘ya’yansu cikin jikkunansu, fararen Dawaki kosassu
na ta haniniya tare da harba kafafunsu cikin koshin lafiya, fararen kaji (buloras) wadanda ba za
su kidayu ba, haka kwaikwayen da suka sassaka mutum goma ba za su iya kwashe su a yini
daya ba.
Idan ka nutsa cikin gidan gonar sosai fararen ragunan Sudan ne buka-buka masu manyan
kahonni suma cikin fili guda. Wannan ba zai burgeka ba sai ka ga fararen Balbelun dake
shawagi cikin wayar da aka zagaye su. Ga kuma Tinkiyoyi da ‘ya’yansu suma farare sol-sol kai
ka ce kullum sai an yi musu wanka, sun fi guda dari cikin fili guda. A can wani katon fili ‘zebra’ ne (jakin dawa) guda uku manya-manya masu zanen fari da baki.
Babban swimming-pool cike yake da fararen kifi (salmon) manya da kanana, kai ka ce a
(Dambatta-Dam_ kake. Iftihal bakinta ya kasa rufo da mamakin wai na ce wannan duk na
Babanta ne. Ta daga kai ta yi duba ga Dawisu korra sharr dake ta shawagin su bisa doguwar katangar ginin
kai ka ce katangar gidan Zoo ce saboda tsayi. Sun zubo dogon bindinsu kasa, wasunsu kuwa
sun bude shi cikin nuna baiwar kyau da Allah yai musu dai bai yiwa wata dabba ko wani tsuntsu
a duniya ba. Ma’aikatan wajen sun tsinko mata kayan marmari nunannu, sun wanke sun zubo mata a cikin
kwando a matsayinta na bakuwarmu da ba ta taba zuwa ba, kuma diya ga Baba Sa’idu. Amma
ta kasa sha, extremely puzzled! Sai tambaya ta take wai Baba shekaru nawa ya kwashe yana
assasa gidan gonar nan? Wannan ai ya fi karfin a kira shi gidan gona sai gidan Zoo! Na ce, “Kin taba ganin gidan Zoo da babu zaki babu damisa? An ce Baba tun yana sakandire
ya fara assasa gidan gonar da ‘yan tsirarun dabbobin da Malam ya bashi, amma bata fara
habaka ba sai dawowar shi karatu daga Turai”.
Ta ce a sanyaye, “Amma Baba mai yasa bai taba gaya mana yana da wannan gidan gonar ba?”
Na girgiza kai na ce, “Ba zan sani ba, mai yiwuwa yawan abubuwan da ke kansa su suka
mantar da shi ga yin hakan. Don shima sai ya zo garin nan sau uku bai zo nan din ba, duk
albashin ma’aikatan ta hannun Malam yake basu”. Akwai shuke-shuke na kayan marmari musamman guava, Roman, fasa-dabur, inibi, tuffa, lemun
zaki, ayaba, cashew da abarba. Muka debi iyakar iyawarmu a leda, daga nan muka tafi gidan
Yaya Halima. A nan muka yi sallar magariba muka ci abinci.
Na yi zaton Iftihal ba za ta ci ba, musamman da yake tuwon dawa ne miyar kuka, amma ita ce
mai cewa a karo har tana side hannu.
Yaya Halima ta ba ta dakakken yajin daddawa mai dadi da ta ce tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login