Showing 18001 words to 21000 words out of 39022 words

Chapter 7 - Gawa Taki Rami Book Complete Writing By Ayuba Muhammad Danzaki.pdf

a wurin ba tare da ta
motsa ba, kuma babu wanda ya fito daga cikinta.
Qatuwar qofar gidan ta buxe bayan wani
siririn maigadi ya gwada mata qwanji yana nishi
yana komai, wata mota kalar makuba ta fito daga
ciki, jibgegiya ce wadda hamshaqan masu kuxi ke
kece raini da ita. Gilasan motar a rufe.
Motar ta tsaya a qofar gidan tsawon mintuna
ba tare da an yi magana ba, maigadin ya yi saurin
rufe makekiyar qofar gidan sannan ya garzayo da
sauri ya tsaya saitin tagar direban motar ya kasa
kunnuwa.
A hankali aka zuge gilasan tagar, wani mutum
kakkaura fari ya leqo ya yi magana da maigadin
na wasu mintuna sannan ya kuma zuge gilasan
tagar ya hau titi abinsa ba tare da ya kalli baquwar
motar da ke tsaye a qofar gidan ba. maigadin ya
juya da sauri ya koma bakin aikinsa.
Motar ta miqe titi samval yayin da baquwar
motar ta rufa mata baya, duk inda motar ta cire
taya sai motar da ke bin ta ta mayar.
Sun daxe suna tafiya a dogon titin kafin su
samu wuri su yi fakin nesa da juna kaxan.
Alhaji Lado da ke gaba ya buxe ya fito
sannan ya qaraso inda motar da ke bin sa ta tsaya.

Gawa ta qi rami
90 A.M. Xanzaki

Na cikin motar ya buxe gilasan tagar suka kalli
juna.
“Hajiya Halima kin ga yadda shirin yake ko?
Bana son a fahimci akwai wata alaqa tsakaninmu
har aikin ya kammala, ina son a yi abin cikin sirri,
kin san idanuwan jami’an tsaro suna kan mu.”
Hajiya Halima ta gyaxa kai, “Alhaji ka san
yadda nake, matuqar za ka ba ni kuxi to kaina ma
zan iya ba ka, ballantana qaramin aiki irin
wannan, ka kwantar da hankalinka, ina mai
tabbatar maka mai laifin ya kusa shiga hannu,” ta
faxa cike da qarfin gwiwa.
Ya gyaxa kai, “Da kyau, ai da ma mai kamar
zuwa kan aika, na yaba da hikimarki, yanzu me ya
rage?”
Ta kalle shi sosai, “Yanzu na samu labarin
inda take, hatta ‘ya ‘yanta ina da cikakken labari a
kansu, dukan su suna karatu ne a jami’ar Bayero.”
Ya gyaxa kai alamar gamsuwa sannan ya
kalli titi kafin ya dawo da hankalinsa kanta, “Well
done, good job, a samar da cikakken adireshinsu
da yanayin zirga-zirgarsu a tsawon mako guda,
daga nan aikinki ya qare.”
Ta gyaxa kai sannan ta fara qoqarin zuge
gilasan motar.
Ya juya ya fara tafiya, “Sai kin ji alert.”

Gawa ta qi rami
91 A.M. Xanzaki

Ta bi shi da kallo yayin da take zuge gilasan
tagar.
Alhaji Lado ya koma wurin motarsa ya ciro
wayarsa ya danna wata lamba ya kira ya saka a
kunne. Yayin da Hajiya Halima ta zo ta wuce ta
kusa da shi ta kuma hawa titi.
Ya bi motar da kallo yana murmushi, “Duniya
zumvutun kaza.”
***
Misalin qarfe takwas na dare a gefen wata
kasuwar zamani ta Jujin Labbo Zahira na zaune
cikin mota ta rufe gilasan tagar motar tana duba
wata mujalla yayin da haske ya wadaci cikin
motar sai aka qwanqwasa gilasan tagar motar a
hankali.
Zahira ta zuge gilasan tagar wanda hakan ya
ba ta damar ganin na waje, ta xan vata rai kaxan
yayin da take kallon Alawiyya sanye da baqin
tabarau tana murmushi, akwai hular sanyi da ta
rufe kanta da su gaba xaya da kuma wata kot mai
tsawo har qasa kalar ruwan qasa don maganin
sanyi da ke sanye a jikinta.
“Zagayo mana mu zauna, gaskiya kin ci mini
lokaci sosai.”

Gawa ta qi rami
92 A.M. Xanzaki

Alawiyya ta zagayo ta buxe motar ta samu
wuri ta zauna sannan Zahira ta rufe gilasan tagar
ruf saboda sanyi ta ajiye mujallar a gefe sannan ta
kalli Alawiyya.
“Lafiya kika daxe haka? Ko da yake manta da
wannan mu tattauna abin da ya kawo mu, bana
son tara ta yi mini a nan domin a kowanne lokaci
Alhaji zai iya dawowa yau.”
Alawiyya ta saka hannu a aljihun kot xinta ta
xauko wata takarda doguwa ta fara warware ta.
Zahira ba ta ce da ita komai ba har ta gama
warwarewa gaba xaya.
“Takardar mece ce wannan kuma?” ta
tambaya daga bisani tana qarewa takardar kallo
irin kallon qudan da ya faxa mata a abinci.
“Bayani ne daki-daki,” in ji Alawiyya sannan
ta fara karanta mata.
Har ta kammala bakin Zahira a buxe yake
tana cike da mamaki.
“Da gaske duk abin da kika faxa haka yake?”
ta tambaya.

Gawa ta qi rami
93 A.M. Xanzaki

“Ga zahiri! Amma lallai za a yi kirvin
sakwarar gwari, wannan kwamacala da me ta yi
kama? Shi Alhajin da kansa?”
Alawiyya ta nannaxe takardar ta xorawa
Zahira a bisa cinyarta.
“Na kammala contract xina saura kuxin aiki.”
Har yanzu Zahira tunani take yi, fuskarta duk
ta sauya sannan ba ta ji duk abin da Alawiyya take
faxa ba.
Alawiyya ta tava ta, “Ina son tafiya gida
domin ba ke kaxai kike da mafaxi ba ni ma idan
dare ya yi mini za a yi mini faxa.”
Zahira ta yi ajiyar zuciya, “Bari mu je in kai
ki gida,” ta kunna motar ta fara qoqarin barin
wurin.
Ba su daxe da hawa kwalta ba wata mota
baqa mai rufaffun gilasai ta fito daga kan wata
kwana ta rufa musu baya.
“Ki bi a hankali kada Alhaji ya san komai
game da al’amarin nan domin idan ya san kin sani
na tabbata akwai babbar matsala,” in ji Alawiyya
bayan sun miqe titin da zai sada su da hanyar
zuwa gida.

Gawa ta qi rami
94 A.M. Xanzaki

Zahira ta numfasa, “Kada wannan ta dame ki
domin zan bi duk matakan da suka kamata wajen
warware matsalar.”
“Mene ne shirin ki na gaba?” Alawiyya ta
tambaya.
“Ni ma ban sani ba,” Zahira ta ba ta amsa.
“Kada fa lissafi ya kuvuce miki, don ni daga
yau na fita daga maganar nan.”
“Lissafi ba zai qwace mini ba Alawiyya, idan
kuwa lissafi zai qwace mini to ki tabbata zai
qwacewa lafiyayyar na’ura mai qwaqwalwa.”
Alawiyya ta san Zahira masaniyar na’ura mai
qwaqwalwa ce haka nan kuma digirin ta biyu a
wannan vangaren kuma ta tabbata tana taskace
komai daki-daki a na’urar tata, don haka sai ta yi
shiru tana kallon gaba.
Sai da ta sauqe Alawiyya a qofar gida sannan
suka yi sallama.
“Za ki ji saqo cikin daren nan in Shaa Allahu.
Ki wayi gari da farin ciki.”
Ta juya akalar motar ta miqe ta ci gaba da
tafiya.
***

Gawa ta qi rami
95 A.M. Xanzaki

Sani direba ya danna hancin motar Alhaji
zuwa cikin gidan bayan maigadi ya buxe masa
qofa. Alhaji Haruna Tinqwal ya yi masa alamar ya
dakata sannan ya zuge gilasan motar ya leqo.
Maigadi ya fahimci ana son magana da shi ne don
haka a gaggauce ya qarasa rufe qofar ya zo kusa
da Alhaji ya rusuna.
“Barka da dawowa Alhaji.”
“Yauwa barka ka dai, mun same ku lafiya?”
Alhaji ya amsa masa, “tana ciki kuwa ko ta fita?”
“Ta fita tun da yamma amma ta kusa
dawowa”
Alhaji Haruna ya gyaxa kai sannan ya umarci
Sani direba da ya ajiye motar a rumfar adana
motoci.
Alhaji ya fito daga motar yana save malum-
malum tare da kallon Sani direba.
“Tafiya a jirgi na fara qosawa da ita, ba don
matsalar rashin tsaro a qasar nan da ya yi yawa ba
da tare za mu dinga zuwa Abuja a mota.”
Sani direba ya yi murmushi yayin da yake
kulle motar bayan ya fito, “Alhaji ni kuwa ina
sha’awar hawa jirgi.”

Gawa ta qi rami
96 A.M. Xanzaki

Alhaji ya yi murmushi, “Sani ke nan, ai hawa
jirgi sai ka gaji da shi muddin za ka ci gaba da
riqe mini amana.”
Sani ya xauko jakar Alhaji ya biyo shi da ita
zuwa falo in da ya ajiye masa ita a kan kujera ya
juya ya fita.
Alhaji ya cire babbar rigarsa da ‘yar cikin ya
zauna daga shi sai singileti yana mamakin yadda
Zahira ta san da dawowar sa amma ta sa qafa ta
fita daga gidan ya shiga banxaki ya watsa ruwa ya
fito ya zauna.
A lokacin ne kuma xaya daga cikin
wayoyinsa ta yi qara ya sa hannu ya xauka ya
amsa.
“Jagwado yaya aka yi ne? Dawowata ke nan
daga Abuja ka bari da safe sai mu yi magana a
gajiye nake.”
Jagwado ya amsa daga xaya vangaren,
“Alhaji matarka muka gani tare da yarinyar da ka
sa mu sa wa ido, abin ya ba mu mamaki.”
Nan take Alhaji ya ji ya wartsake, “Ka
tabbata?” ya nemi tabbaci.

Gawa ta qi rami
97 A.M. Xanzaki

“Yanzun nan ta sauqe ta a mota fa, har gida ta
kai ta gaskiya muna zargin duk yadda aka yi
akwai abin da suke shiryawa.”
Alhaji ya xan yi shiru yana tunani kafin daga
bisani ya yi magana, “Ka manta da wannan amma
duk yadda za a yi ina so gobe qarfe tara na dare ku
xauke yarinyar ku kai mini ita guest house xina na
titin North west sai na ji dalilin da ya sa take
bibiyar al’amurana. Gobe da safe zan zo na same
ka.”
“To Alhaji, an gama.”
Daga nan aka kashe wayar.
Alhaji bai san Zahira ta dawo ba sai da ya
ajiye wayar sannan ya ji sallamar ta a kansa. Ya
xaga kai ya kalle ta yana fatan Allah Ya sa ba ta ji
wayar da yake yi yanzu ba.”
Ta yi masa murmushi, “A yi haquri na yi laifi
Alhaji.”
Ya gyaxa kai, “Babu matsala,” ta samu wuri
ta zauna kusa da shi tana murmushi, “Allah Ya sa
dai ka ci abinci, domin tun xazu na kammala
maka shi kafin na fita.”
Ya dube ta shi ma da murmushi, “Idan kina so
in ci ai sai in ci.”

Gawa ta qi rami
98 A.M. Xanzaki

Ta miqe da sauri ta nufi xakin girki wanda ke
kusurwar gabas ta falon. Jimawa kaxan sai falon
ya qume da qamshin abincin lale-marhabin ga
Alhaji.
Suka zauna bisa teburin cin abinci ta zuba
masa a filet ta tsiyaya masa tattacen sovarodo xan
kamfani, domin Alhaji ba shi da abin shan da ya
wuce sovo, musamman ya buxe kamfanin yin sa.
Zahira ta zuba suka fara ci suna hira.
Alhaji ya ce; “Matsalar auren ‘yan boko sai
su dinga fita babu iznin miji su kuma dawo a
lokacin da suke so.”
“Ni kuma babbar matsalar auren mai kuxi
rashin zama a gida yau yana London gobe yana
Dubai jibi yana Jamus,” Zahira ta rama
“Ka yi magana a ce maka seminar ce ko wani
muhimmin taro,” Alhaji ya mayar mata.
“Shi kuma mai kuxi ba shi da buri illa ya
killace mace a gida don kawai a ce yana da iyali.”
Alhaji ya yi murmushi, “Ga binciken
qwaqwaf akan rayuwar mazajensu sai sun san
komai na sirrin dukiyarsu.”

Gawa ta qi rami
99 A.M. Xanzaki

Zahira ta dakata da tauna yayin da Alhaji
yake kallon fuskarta da wutsiyar ido don ya
nazarci yadda ta karvi saqon a can qololuwar
zuciyarta.
Zahira ta yi dariya, ‘Wato Alhaji duk da tarin
shekarun ka wannan bai hana ka zauna ka yi ta
barkwanci da iyalinka ba, abin sha’awar da
waxansu matasan mazajen ke kasa ba wa
iyalansu.”
Sun ci gaba da hira tare da yin maganganu a
baibai har zuwa lokacin da ya kammala cin abinci
ya kuma nemi shiga xaki don ya huta. Zahira
kuma ta nufi xakin ta.
Sai da ta kulle qofar ta tabbatar babu mai jin
ta sannan ta kira Alawiyya a waya.
“Kina gida ne? Akwai wata matsala fa.”
“Ta mece ce kuma? Network ne babu ko
kuwa?”
“A’a yanzu zan saka miki kuxinki amma
kamar Alhaji ya fahimci wani abu fa, domin hirar
da muka kammala da shi yanzu yayin da muke cin
abinci na fahimci abubuwa da yawa.”
“Kamar me fa?”

Gawa ta qi rami
100 A.M. Xanzaki

“Ya gane ana bincike a kan al’amuran sa,
amma abin da nake so da ke gobe qarfe tara na
dare kada ki je ko ina idan so samu ne ma kada ki
bari wani ya san inda kike ko da wasa, zan kira ki
in gaya miki abin da yake faruwa.”
“Wai me yake faruwa ne?” Alawiyya ta
tambaya cike da damuwa.
“Ke dai ki yi abin da na ce, domin xazu ina
shigowa gidan nan na ji Alhaji yana waya bai san
duk na saurari maganganun da yake yi da wani
ba.”

Gawa ta qi rami
101 A.M. Xanzaki

_________BABI NA 5_________
hirye-shiryen biki sun kankama tamkar
wutar daji, watanni kaxan da kammala
karatun su Bilkisu aka saka rana aka ci
gaba da tsare-tsare kamar yadda al’ada
take.
Hajiya Abu ta gayyato wakilanta daga qauye
waxanda suka karvi kuxin gaisuwar uwa da uba
haka kuma ta sanar da mutanenta na kusa da ita
musamman irin su Hajiya Hindu cewa su matso
kusa fa ranar da ake jira yau ga ta ta zo.
Hajiya Hindu ta sauqa a Najeriya da yamma
haka kuma sai da ta fara biyawa gidan
uwarxakinta kafin ta je gida inda ta gaisa da
babanta ta dawo gidan Hajiya Abu suka ci gaba da
shirye-shirye.
A vangaren iyayen Nasiru kuwa kada ka so
ka ga yadda ake ta zumuxi da zuwan wannan rana,
duk wasu ‘yan uwa da abokan arziqi an sanar da
su an kuma gayyace su wannan gagarumin
shagalin biki na xa xaya tilo da ake ji da shi.
Nasiru da amaryarsa Bilkisu da sauran
qawaye da abokan da ke kewaye da su suka tsayar
da ranar wata Lahadi a matsayin ranar da za a yi
S

Gawa ta qi rami
102 A.M. Xanzaki

gagarumin fati don murnar saka rana wadda
dududu bai fi kwanaki goma sha huxu ba.
Bayan kammala kama makeken wurin taro da
ake ji da shi a faxin jihar Kano haka kuma an ba
da kwangilar yin abinci da kawo haxaxxun
abubuwan sha daga wuraren da wuyansu ya yi
kauri a vangaren abincin taro, ban da anko da
sauran abubuwa da qirqirarru ne a wannan fati.
A ranar Lahadi tun da qarfe huxu na yamma
wurin ya fara xinkewa da taron samari da
‘yanmata suka fara cika wurin cikin shiga ta fita
kunya da qure adaka, ba ka jin komai sai qarar
gangunan zamani da bushe-bushe da waqe-waqe,
ana ta faman hidima. Akwai mawaqan zamani
shahararru da aka gayyata kuma har waxansu daga
cikinsu sun yi riga-malam-masallaci sun fara
cashewa gabanin lokacin farawa.
Misalin qarfe biyar saura kwata amarya da
qawayenta, ango da abokansa suka samu isowa,
nan fa aka ci gaba da sha’anin biki. Ba a jima ba
sai ga Hajiya Abu da Hajiya Nadiya sun iso a
motoci daban-daban a lokaci guda tamkar haxin
baki, kowaccensu ta sha kwalliya ta gani a faxa a
tare da su akwai Hajiya Hindu da mutanenta na
Saudiyya da ke zaune a Najeriya. Aka sama musu

Gawa ta qi rami
103 A.M. Xanzaki

muhalli suka zauna, kusan kowanne dangi daga
vangaren amarya da ango sun hallara a wannan
wuri.
Bayan mai gabatarwa ya gabatar da kowa sai
aka buxe da addu’a daga nan sai aka shiga shagali
ka’in da na’in.
Hajiya Abu ta kira mai gabatarwa inda ta yi
masa wata magana a kunne tare da ba shi wata
takarda mai qunshe da wasu bayanai, ya dawo rike
da amsa-kuwwa ya xaga murya.
“Hajiya oganniyar voye wadda ta fito fili
yanzu ta buqaci saka wata kacici-kacici ta
musamman kuma ta yi alqawarin bayar da kyauta
ta musamman har ta naira dubu xari biyu ga duk
wanda ya bayar da amsa daidai. “
Nan take wuri ya yi tsit aka saurara.
MC ya gyara tsayuwa ya ce; “Wani mutum ne
yana gadin dare a gidan wani attajiri ana biyan sa
albashi. Da shi da Maigidan nasa suna matuqar jin
daxin aikin nasa, rannan sai Maigidansa ya ce
masa zai yi tafiya jibi da Asuba.
Ranar da ogan nasa zai yi tafiya Maigadi ya
zauna zaman jiran fitowarsa domin Asuba ta yi.
Jimawa kaxan kuwa sai ga Maigidan nasa ya fito.

Gawa ta qi rami
104 A.M. Xanzaki

Maigadi ya tare shi da zumuxinsa suka gaisa.
Maigadi ya ce; “Ranka ya daxe jiya da daddare na
yi mafarki tafiyar nan da za ka yi babu alkhairi a
cikinta, ina ma za ka fasa.”
Maigidan nasa ya yi jim yana tunani sai kawai
ya kalli Maigadin nasa ya ce; “Bello.”
Maigadi ya amsa, “Na’am Alhaji.”
“Nawa nake biyan ka albashi?”
Maigadi ya ce; “Ranka ya daxe dubu talatin
ne ban da abinci da na sha da kyautuka na
musamman da ake ba ni.”
Alhaji ya ce; “To yanzu albashinka ya koma
dubu ashirin da biyar.”
MC ya yi shiru kafin ya ce; “abin tambaya a
nan shi ne, wai me ya sa Alhaji ya rage wa
Maigadi albashi?”

Wurin ya yi yi tsit da fari sai kuma aka fara
hayaniya har sai da aka nutsu.
“Wanda ya sani kawai hannu zai xaga ya ba
da amsa daidai ya zo ya karvi dubu xari biyunsa
cash ba transfer ba,” ya nuna Hajiya Abu.

Gawa ta qi rami
105 A.M. Xanzaki

Hajiya Abu ta buxa jakarta ta zaro bandir xin
kuxi ‘yan dubu-dubu sababbi ta xagawa mazowa
taron.
Wuri ya sake ruxewa nan da nan sai ga
hannaye a sama.
MC ya ba wa wata budurwa mai suna Fatima
amsa-kuwwa ta karva ta miqe muryarta na rawa ta
ce; “Sunana Fatima Abdullahi, saboda ya ce masa
ya yi mafarki.”
Ta miqa wa MC abin magana.
MC ya karva ya fara qoqarin miqawa wani
matashi da ya sha babbar riga har da hula dara,
“Ba ki faxi amsa daidai ba.”
Matashin ya yi saurin karvar abin magana ya
gyara murya ya kai ta bakinsa, “Sunana Alhaji
Safiyanu Qusa, saboda ya karyawa Maigidansa
gwiwar yin tafiya tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login