Showing 27001 words to 30000 words out of 39022 words
Chapter 10 - Gawa Taki Rami Book Complete Writing By Ayuba Muhammad Danzaki.pdf
ma ita qadangaruwa ce da ta bi bangon
xakin har zuwa sama inda take hango wata qofa
da hasken rana ya keto ta cikinta ya sauqa a fusace
Gawa ta qi rami
138 A.M. Xanzaki
a kan fuskarta. Ina ma a ce ita tsuntsuwa ce da sai
ta lave a bakin qofar fita ta xane qofa da yatsun
qafarta, idan wani ya buxe qofa sai ta tashi fir! Ta
nufi inda take so.
Da ta ga waxannan tunane-tunanen ba za su
kai mata ba sai ta dawo hayyacinta ta nutsu ta sake
nazarin xakin tsaf! Amma ba ta ga wata qofar fita
ba sai qananan qofofin da ta gama nazari a kansu
yanzu in ka xauke qofar da Alhaji Haruna ya fita
yanzu. Ta miqe da sauri ta nufi qofar ta tsaya ta
kasa kunnuwa tana saurare, a qoqarinta na tura
kunnuwanta jikin qofar ne sai ta ji kanta ya
dunguri qofar, ta yi sauri ta ja baya cikin tsoro
Ahaf! Ai da ma ta bar wani jin tsoro domin qofar
a buxe take hangangam!
Alawiyya ta tattare doguwar rigar barcinta da
ke jikinta ta nannaxo ta daga qasa zuwa
cinyoyinta ta kama geffa biyu na rigar ta qulle
sannan ta fara sanxa tamkar hawainiya ta nufi
qofar fita sosai. Da ta fito ba ta yi qoqarin mayar
da qofar ta rufe ba saboda tsabar garaje, sai kuma
ta diririce ta fara makyarkyata tana tunanin hanyar
da ta kamata ta bi. Ta sake kasa kunne tana
saurare, tabbas safiya ce haka kuma ta tabbata ko
da ta fita akwai qarancin mutane a babban titi.
Gawa ta qi rami
139 A.M. Xanzaki
Wai ma tukuna nan wanne gida ne? A ina ma
take? Jin kamar motsi ta bayan xakin ya sa ta
hanzarta ta nufi wata mavoya inda ta hangi wani
tsohon tankin roba da ake tara ruwa ta lave
jikinsa inda take tsammanin babu wanda zai gan ta
ko da daga wacce kusurwa ya fito.
Sauti ta jiyo kamar ana magana daga sashen
xakin da ta baro, ta kalli dogon tankin roban mai
faxin gaske sai ta ga wani xan qarfe da ta lura
wataqila an yi shi ne domin kamawa a hau a zuba
ruwa, ta fara shawarar ta hau qarfen ta shiga cikin
tankin, sai kuma ta yi tunanin za a iya hango ta.
Da ta ji kamar motsi ana nufo inda take sai ta daxa
gyara mavoya ta kasa kunnuwa tana sauraron daga
inda ake tahowar. Ta waiga dama da hagu da
bayanta yayin da ta hangi wata siririyar hanya da
ta yi tsammanin za ta iya kai ta bayan gida, sai
kawai ta shafa a guje cikin sanxa da xaga qafa
sosai ta nufe ta.
Hanyar ta miqe fetal zuwa wasu rukunin
xakuna da ta lura suna jere kusa da katangar
gidan, sai kuma ta ji kamar motsi a xaya daga
cikin xakunan, ta samu gindin wata bishiyar
maina da ke kusa da wasu tarin shuke-shuke ta
dakata a nan gabanta yana faxuwa. Zuwa can sai
Gawa ta qi rami
140 A.M. Xanzaki
aka buxe qofar da take jiyo motsin don haka sai ta
bi lafiyar shuke-shuken ta yi kwance kamar ba rai
a jikinta tana saurare.
Mutum biyu ne suka fito daga xakin suna
magana, xaya siriri ne sanye da ‘yar shara da
dogon wando kansa da hula havar kada yayin da
xayan ya kasance lukuti mai manyan kumatu
tamkar an hura balan-balam. Suka nufi sashen da
ta baro.
Ta ji siririn yana cewa; “wanne irin sakaci ne
za ka ce ka bar qofar a rufe? Idan fa yarinyar nan
ta yi laya wallahi kashinmu ya bushe.”
“Haba yo idan ma ta gudu ina za ta je? Ai
kafin ta yi nisa mun qare mata gudu mun kama
‘yar banza,” lukutin ya ba shi amsa.
Suka wuce suna surutansu yayin da ta fito
daga mavoyarta tana kallon xakunan ko za ta
samu wurin tserewa, tabbas idan ba ta yi da gaske
ba dama xaya gare ta, idan kuma ta bari ta suvuce
mata har ta sake shiga hannunsu to kuwa za su
tsaurara tsaro a kanta. Ta dubi tsawon katangar ta
ga akwai wasu qarafa da aka saka masu tsini gami
da wasu tarin wayoyi da aka sassarqa a tsakani
waxanda take zargin an jona su ne da wutar
lantarki saboda tsaro, ta waiga baya ta ga ba ta
Gawa ta qi rami
141 A.M. Xanzaki
ganin alamun lukutin mutumin da siririn. ‘Ki yi
maza ki tsere kafin su gane ba kya xakin.’
Ta yi maza ta zagaya bayan xakunan inda ta
tarar da tazarar da ke tsakanin bayan xakunan da
katangar gidan ba ta fi taku xaya ba, kamar buxar
ido sai kawai ta ga tsani a jingine a jikin katangar.
Gabanta ya ba da das! Jikinta ya xauki sabuwar
karkarwa tamkar ana kaxa mata gangi, ta matsa ta
jawo tsanin da qyar saboda nauyinsa ta jingina shi
a jikin katangar ta gyara xaurin da ta yi wa rigarta
ta kama tsanin kamar qadangaruwa ta fara hawa,
taku xaya, biyu, uku a na huxu sai ta jiyo motsin
mutanen nan suna dawowa, don haka sai ta qara
azama ta jefa qafarta wadda ta fara sagewa saboda
rashin sabo da wahala, sai a sannan ne ta sake
ganin abin da ya ba ta tsoro, wayoyin da suke jikin
qarfen su suka qara razana ta amma sai ta daure a
karo na barkatai ta miqa hannu ta tava cikin
dabara, da ta ga babu alamar wutar lantarki a jiki
sai ta janye wayoyin ta kurxa da wuyanta ta
tsakanin wayoyin sannan ta tura gangar jikinta
kamar kyanwa ta kurxa, kamar wasa sai ta ga ta
wuce, ta yi ajiyar zuciya da ta kalli qasa ta hangi
ashe wani gidan gonan ne a baya.
Gawa ta qi rami
142 A.M. Xanzaki
Ta shiga shawarwarin yadda za a yi ta dira,
wata zuciyar na gaya mata ta koma baya, amma da
ta ji sautin mutanen nan sun dawo kuma ta ji wani
a cikinsu na cewa; “Ga ta can.” Sai kawai ta dira
tare da tsarabar qananan qujewa a gadon bayanta
da wani sashe na sharavarta. Ta yi sa’a ta dira da
gwiwoyinta, ta saurara suka qarasa amsawa kafin
ta miqe ta shara a guje.
***
Sani Tahir ya kammala cin abincinsa na safe
ya wanke hannunsa sannan ya fita waje daga
vangarensa da ke boy’s quarter ya tsaya a
qofar xakin nasa yana qarewa motocin da ke cikin
rumfar da ke daura da xakin nasa kallo. Babu
mota xaya a wurin wanda hakan ya tabbatar masa
Alhaji ne ya fita da sassafe, kuma idan ya fita sai
wajen yamma yake dawowa ko kuma ya wuce
wurin aikinsa. Da ma maigidan nasa ya saba irin
wannan fitar ba tare da ya nemi taimakonsa ba.
Yakan ce gidan gonarsa yake zuwa don duba
yadda yaransa ke kula da wurin.
Sani ya yi imanin akwai wani abu da
maigidan nasa ke yi a voye kuma yana zargin
akwai rashin gaskiya a ciki. Idan bai manta ba yau
shekarunsa kusan huxu da fara aiki a gidan a
Gawa ta qi rami
143 A.M. Xanzaki
matsayin direba. Hajiya Abu ce ta sa aka kawo shi
daga qauyen Malammadori kasancewarsa qanin
qawar qawarta wadda kuma tasu ta zo xaya. Tun
daga wannan lokacin yake a matsayin direba har
zuwa yanzu. Idan ya auna daxewar da ya yi yana
aiki da maigidan nasa tabbas ya bauta masa sosai,
amma har yanzu babu wata tsiya da ya tara, duk
da cewa ba ya rasa ci da sha da sauran buqatun
rayuwa na yau da kullum. Rabon da ya kai ziyara
garin su Malammadori yau wata guda. Yana
buqatar ya ga mahaifiyarsa da qannensa biyu mata
da su kaxai suka rage masa a rayuwarsa ta duniya.
Ya nemi wuri ya zauna yana tunanin
makomarsa a rayuwa, a yadda lamarinsa ke tafiya
jikinsa yana ba shi kamar komai ya kusa zuwa
qarshe, amma bai san yaushe ba ne, kuma ta yaya.
A wannan satin ya kamata ya nemi alfarmar
Alhaji ya tafi Malammadori don ya gaisa da ‘yan
uwa da mahaifiyarsa Lami. Kai! Ai lokaci ma ya
yi da ya kamata ya daina duk wata bauta ya gina
kansa shi ma. Amma wannan zai faru ne idan har
ba a yi masa butulcin xan adam ba.
Ya tashi tsaye ya nufi wajen maigadi don su
yi hira idan kuma ya ga miskilin maigadin ba ya
Gawa ta qi rami
144 A.M. Xanzaki
son hirar to sai ya fita waje don ya miqe qafa
zuwa cikin gari.
Kamar yadda ya zata Ado maigadi na zaune
yana sauraren shirin kowanne gauta na Freedom
radio suka gaisa sama-sama hankalin Ado yana
kan radiyo yayin da Sani ya xaga masa hannu
alamar zai dawo sannan ya tura ‘yar qaramar
qofar da aka tanada ya fita waje.
Unguwar shiru babu mutane sosai duk da
kasancewar safiya ce, ba tare da wata tantama ba
Sani ya doshi sashen hagu ya ci gaba da tafiya, bai
yi nisa da barin gidan sosai ba sai wani babur mai
qafa uku ya biyo titin da yake bi, ya qaraso a
hankali ya tsaya a gefen Sani. Sani ya waiga ya
kalli babur xin, haka kawai sai ya ji gabansa ya
faxi.
Mutum uku ne a babur xin; biyu a baya sai
kuma direban da ke zaune ya rufe fuskarsa da
mayani, kai ai da ma Sani ya lura duka mutanen
da ke baya sun rufe fuskarsu da mayani. Bello ne
da abokan aikinsa Tuguji da Xantala.
Sani ya qara xaga qafa don bai yarda da
mutanen ba, amma sai Bello ya yi hanzarin fitowa
daga motar kamar wanda aka harbo da kibiya ya
damqi wuyan Sani ya cusa shi a cikin babur xin.
Gawa ta qi rami
145 A.M. Xanzaki
Xantala da ke gidan baya ya sa wani hankici ja
mai qunshe da wata farar hoda ya toshe masa
hanci.
Sani ya shiga haure-haure da yunqurin yin ihu
amma sai ihun ya maqale a maqogwaronsa don
haka sai jikinsa ya saki, suka zauna da shi a
tsakiyarsu suka kama hanya tamkar sun xauko
maras lafiya.
Gawa ta qi rami
146 A.M. Xanzaki
__________BABI NA 7__________
un lokacin da aka kulle Bilkisu da
Hannatu a cikin gidan da ke tsakiyar
dajin suke ta faman kuka bayan
farfaxowarsu.
Bilkisu ce ta fara farkawa sannan ta dubi
Hannatu wadda ke cikin mayen hodar da aka fesa
musu ta hanyar na’ura, sannan idanuwanta suka yi
bulaguro zuwa cikin xakin. Babu komai a xakin
duk da kasancewarsa babba in ka xauke
shimfixexiyar dardumar da ke malale a tsakiyar
xakin sai kuma wasu tsofaffin kujeru masu zaman
mutum uku guda biyu da masu zaman mutum biyu
guda uku da ke kewaye da xakin, Akwai qofofi
guda biyu, xaya ta shigowa xakin xaya kuma
wadda su Bilkisu ba su san ta mece ce ba tana
daga can ciki nesa kaxan da inda suke zaune.
Hannatu ta wartsake ta dubi ‘yar’uwarta
sannan qwaqwalwarta ta dawo mata da abubuwan
da suka faru da su sa’anni kaxan da suka wuce, ta
dubi xakin, ba ta buqatar tambaya ta tabbata sato
su aka yi. Ko dai qungiyar matsafa ce ko kuma
masu satar mutane ne da neman kuxin fansa.
T
Gawa ta qi rami
147 A.M. Xanzaki
Ta zabura ta tashi zaune cikin ximuwa, “Mun
shiga uku, sato mu aka yi,” nan take ta rushe da
kuka wurjanjan! ‘Yar uwarta ta shiga taya ta. Sun
tabbata sun shiga matsala ba qarama ba. Yanzu
haka Hajiya tana can tana neman su, ko kuma tana
jiran a kira ta a waya a nemi kuxin fansa. A yadda
take jin labarin masu satar mutane ta tabbata ba
qaramin kuxi za su caji Hajiya ba. Tunanin haka
ya sake karyar musu da zuciya. Suka jingina da
bango suka ci gaba da kuka a tare cikin tashin
hankali.
A daren Bilkisu ta yi qoqarin miqewa ta
kama qofar xakin ta jijjiga da qarfi tana kiran a
buxe . Da ta fahimci aikin banza take yi wai jefa
agwagwa a ruwa sai ta dawo ta zauna kusa da ‘yar
uwarta ta faxa a tunanin makomarsu. Zuwa can
aka buxe qofar xakin. Lawurje ya shigo yana zare
idanuwa yana kallon su xaya bayan xaya.
“Ku kwantar da hankalinku, ba wani abu za
mu yi muku ba, Oga yana son ganin ku yanzu. Za
ku ci abinci?”
Suka girgiza kawuna, Bilkisu ta ce, “Ba ma
jin yunwa don Allah ku qyale mu, munfi son ku
mai da mu gida. Me muka yi muku?”
Gawa ta qi rami
148 A.M. Xanzaki
Lawurje ya vata rai, “Ku bari Oga ya zo duk
sai ku yi masa waxannan tambayoyin, mu ‘yan
cika aiki ne kawai,” daga nan ya juya ya fita, “bari
na sanar da shi kun farfaxo ko?” ya kama qofa ya
buxe ya fita. Bilkisu ta matso da zafin nama za ta
bi shi, kamar yana ganin ta ta baya ya yi wani juyi
a murxe ya harba mata qafafu har ya same ta a
qirji, numfashinta ya xauke ta sulale ta faxi qasa.
“Kada ki sake qoqarin biyo ni, don ba imani
ne da ni ba,” ya faxa sannan ya yi waje yana vata
rai.
Bilkisu ta daxe daga zaman ‘yan borin da ta
yi, har zuwa sadda jikinta ya egama amsawa ta
gyara zama.
Hannatu ta girgiza mata kai, ‘Waxannan
mutanen mugaye ne idan muka yi wasa kashe mu
za su yi ko su yi mana dukan tsiya.”
Suka xan yi shiru suna tunani har zuwa sadda
Hannatu ta ce; “Wai wane ne Ogan da na ji yana
faxa ne?”
Bilkisu ta girgiza kai, “Ni ma ban sani ba,
amma mu dage da addu’a tabbas qofar Allah a
buxe take, amma duk da haka muna da wani
yunquri da za mu iya yi.”
Gawa ta qi rami
149 A.M. Xanzaki
Hannatu ta kalli xaya qofar da ke ciki ta miqe
ta nufe ta yayin da Bilkisu ta bi ta da kallo.
“Me za ki yi?”
Ba tare da Hannatu ta ba ta amsa ba ta kama
qyauren ta tura da qarfi, ashe qofar a buxe take
hakan kuma ya sa ta ji ta faxa ciki babu shiri.
Ashe banxaki ne. ta qare masa kallo kafin ta dawo
da baya.
“Banxaki ne ko?” Bilkisu ta tambaya.
Ba tare da ta amsa ba ta gyaxa kai.
Suka zauna yayin da abubuwa masu yawa
suka ci gaba da zuwa qwaqwalwar Bilkisu. Ina
A’isha da Binta da aka xauko su tare? Tana tuna
haka sai ya ji gabanta ya faxi, an ce ‘yan yankan
kai suna warewa duk wanda suka kama ranakun
yin layya da su? To ko dai an fara ta kan su A’isha
ne da Binta kafin su ma tasu ranar ta zo? Ta tuna
taron fatin da aka yi, yanzu ko ina ragowar
qawayensu suke? Mai yiwuwa kowacce ta tafi
gidan iyayenta yayin da ita da ‘yar uwarta ke
hannun wasu azzalumai marasa imani.
A daren babu wanda ya zo neman su haka
kuma sun kasance a wannan hali na damuwa ba
tare da sun yi barci ba har gari ya waye. Ba a ta
Gawa ta qi rami
150 A.M. Xanzaki
batun yunwa wadda kwata-kwata ma ba sa jin ta.
Fargaba da tashin hankali sun maye gurbin
yunwar.
Kusan Asuba barci ya yi nasarar xauke su.
Motsin buxewar qyaure ne ya farkar da su a daidai
lokacin da ba su san qarfe nawa ba ne amma sun
tabbatar gari ya waye don akwai alamun ketowar
hasken rana. Alhaji Lado ya shigo xakin daga shi
sai doguwar riga da wando a bayansa Lawurje ne
sanye da baqaqen qananan kaya riga da wandon
jins kansa da hula hana sallah ita ma baqa.
“Alhaji sun farka,” ya faxa yana qare musu
kallo.
Alhaji Lado ya kalli xakin ta ko ina sannan ya
juyo ya harari Lawurje, “Me ya sa ba ka ba su
abinci jiya ba?”
“Cewa suka yi ba sa jin yunwa.”
“Yanzu je ka kawo musu abin karyawa.”
Lawurje ya rusuna alamar girmamawa, “An
gama Sir.” ya fita daga xakin.
Alhaji Lado ya dawo da hankalinsa kan su
Bilkisu waxanda suka yi zuru-zuru suna kallonsa
ya xauko wayarsa ya duba agogo.
Gawa ta qi rami
151 A.M. Xanzaki
“Yanzu qarfe tara na safe, ina so zan koma
cikin gari amma kafin na tafi ina son magana da
ku, Lawurje ya gaya muku ai tun jiya ko?”
Suka ci gaba da kallon sa suna qoqarin tuna
inda suka san wannan mutumin, tunaninsu ya
gimtse, tabbas ba su san shi ba, domin ko a
abokan hulxar Hajiya mahaifiyarsu wannan
baquwar fuska ce, amma duk ta inda ya fito babu
alkhairi tare da shi.
Ya zaro musu idanuwa, “Ku tashi zaune mana
kafin a kawo muku abinci, kun tsaya kuna wani
kallo na kamar kun ga wani mugun mutum.”
Suka tashi zaune suna kallon sa, kowaccensu
da abin da take qissimawa a zuciyarta. Ya samu
kujera kusa da qofa ya zauna ya xora qafa xaya
kan xaya yana qare musu kallo.
“Sunana Alhaji Lado, kuma na sa an kawo ku
nan ne bisa umarnin maigidana, haka kuma bai ba
ni iznin na yi muku wani abu ba illa na ba ku
kulawa tamkar ‘ya’yana,” ya xan dakata da
magana yana nazarin ko xan abin daya faxa ya
shiga jikinsu.
“Babu wanda zan cutar ko na sa a cutar daga
cikinku matuqar ba ku sava umarnina ba,umarnin
Gawa ta qi rami
152 A.M. Xanzaki
kuwa da zan ba ku ba za su wuce guda uku ba; na
farko kada wata ta yi qoqarin guduwa daga gidan
nan ko ku duka; abu na biyu duk abin da kuke so
ku qwanqwasa qofa Lawurje zai zo ya kawo
muku; na uku za ku kasance a nan tsawon kwana
uku ne kawai. Maigida shi zai zo ya yanke
hukuncin yadda za a yi da ku.”
“Bawan Allah me muka yi muku?” Bilkisu ta
tambaya.
Ya yi dariya, “Yaro man kaza, ba ku yi mana
komai ba mu