Showing 33001 words to 36000 words out of 39022 words

Chapter 12 - Gawa Taki Rami Book Complete Writing By Ayuba Muhammad Danzaki.pdf

ne?” ya tambaya yana kallon
qwayar idanunta.
Ta xan rusuna alamar girmamawa, “E Alhaji
Tanko ne tare da Alhaji Bara’u suke son shigowa.

Gawa ta qi rami
168 A.M. Xanzaki

Ya kalle ta a razane sannan ya yi ajiyar
zuciya, cikin qarfin gwiwa da tattara nutsuwarsa
wuri guda ya ce mata, “Ki ce musu su shigo.”
Ta qara rusunawa sannan ta koma ta bar shi
cikin tunanin abin da ya kawo su a wannan lokaci,
duk da ba ya mamakin zuwan su amma bai tava
zaton a wannan lokacin za su zo ba. Da fitarta da
shigowarsu ya faru ne a cikin abin da ya gaza
minti guda.
Suka nemi wuri suka zauna suna masu
qarewa ofis xin kallo.
Alhaji Tanko ya kalle shi, “Qarshen tika-tika
dai aka ce tik! Mun samu marigayiyar matarka da
ta yi maka qaryar ta mutu.”
Duk da qoqarin da ya yi na voye razaninsa
amma sai da zuciyarsa ta nemi bugawa sakamakon
abin da Alhaji Tanko ya faxa, yayin da Alhaji
Bara’u ya bi shi da kallo yana nazarin sa.
Ji ya yi kamar kansa na juyawa a wannan
lokacin, hatta fankar sama gani yake yi a tsaye
take cak ba ta motsi, ya qura wa Alhaji Tanko ido
yana kallo.
“Alhaji ka san me kake faxa kuwa?”

Gawa ta qi rami
169 A.M. Xanzaki

Alhaji Tanko ya gyara zama cikin fushi, “Ka
bi a hankali mu yi magana kada ruxewa ta sa ka
rasa abin yi tun kafin tafiya ta yi nisa,” ya kalli
Alhaji Bara’u, “ko ba haka ba Alhaji?”
Alhaji Bara’u ya xauke idanuwansa daga
kallon Alhaji Haruna, “Qwarai kuwa,” ya gyara
zama ya kalli Alhaji Haruna.
“Wato mun daxe muna bincike bisa abin da
ya faru na mutuwar matarka in da muka fahimci ta
shirya mutuwar qarya ne don cimma wata manufa
tata, mun sanya yaranmu sun yi aiki a kanta sosai,
har suka gano manaqisar da ta shirya, inda ta yi
doguwar tafiya zuwa Saudiyya, har can Saudiyyar
muka bi ta aka kawo mana rahoton irin rayuwar da
take yi a can. Kuma yaran namu sun yi aiki yadda
ya kamata har zuwa sadda aka kamo ta zuwa nan
ta hanyar makircinmu tare da xana mata tarko. A
taqaice dai muna sanar da kai cewa matarka tana
raye yanzu haka…”
Alhaji Haruna ya zaro idanuwa cikin
kokwanto, “Wacce irin magana ce wannan? Alhaji
kun tava ganin wanda ya mutu ya dawo? Ni da
kaina aka kai ni qabarinta na yi mata addu’a bayan
na farfaxo daga dogon suman da na yi, kuma duk
waxanda suka halarci jana’izarta sun tabbatar mini

Gawa ta qi rami
170 A.M. Xanzaki

da cewa ita aka binne,” ya girgiza kai, “wannan
labarin akwai qura a cikinsa, ya kamata ku
tabbatar da sahihancinsa kafin ku ba da shi.”
Suka kalli juna.
Alhaji Bara’u ya muskuta, “Kana buqatar
shaida ke nan?” Ya kalli Alhaji Tanko, “tabbatar
masa da shaida domin muna gaggawar ci gaba da
aikinmu.”
Alhaji Tanko ya saka hannu a aljihu ya xauko
wayarsa ya buxe ta ya shiga zaqulo wasu hotuna
da bidiyo da ya adana sannan ya miqa wa Alhaji
Haruna wayar.
Alhaji Haruna ya karvi wayar jiki a sanyaye
ya fara kallon hotunan yayin da yake jin kamar an
yi masa dukan tsiya, su kuma suka bi shi da
idanuwa suna kallon sa.
Tabbas! Hajiya Abu ce matarsa, haka nan
‘ya'yan da ya sani tare da ita sun girma sun zama
‘yan mata sosai. Hajiya ta yi qiba ta samu jin daxi.
Wani abu a can cikin zuciyarsa na nan na yi masa
yawo akan matakin da ya kamata ya xauka na
gaba tun kafin shirinsa ya wargaje shi ma.
Alhaji Bara’u ya miqa masa hannu, “Ba ni
wayar.”

Gawa ta qi rami
171 A.M. Xanzaki

Alhaji Haruna ya miqa masa wayar jiki a
sanyaye yana girgiza kai, “wannan al’amarin ya
xaure mini kai matuqa, a ce mutum ya mutu ya
dawo? Anya kun bincika ba wata mai kama da ita
kuka samu ba kuwa?”
Suka yi murmushi dukkansu.
“Tabbas ita ce, kuma muna da labarai masu
yawa a kanta, kai dai kwantar da hankalinka
komai ya kusa zuwa qarshe,” in ji Alhaji Tanko.
Suka miqe tsaye.
“Da ma mun zo ne domin mu tabbatar da abin
da muke zargi daga gare ka, mun kuma samu, illa
dai qwararan hujjoji da suka fi waxannan muke
buqata domin kawo qarshen zamba cikin aminci a
lamarin,” cewar Alhaji Bara’u.
Da wannan maganar suka fice daga ofis xin.
Alhaji Haruna ya zabga tagumi cike da tunani
iri-iri a zuciyarsa, qarshe dai ya xauki waya ya
kira wata lamba. Sau biyu tana qara ba a xaga ba.
Hankalin Alhaji ya tashi.
A kira na uku saura kaxan ta katse sai aka
xaga.

Gawa ta qi rami
172 A.M. Xanzaki

“Alhaji Lado kana ina ne? Liqi fa ya valle,
mutanen nan sun gano matar nan ba ta mutu ba,”
ya xan saurara. “kun tabbatar kun samu inda take
kun xebo yaran nan nata, kun yi garkuwa da
su?…” “…A’a ku bi komai a hankali bana so a
samu wata varaka…” “ …Ok to shi ke nan, idan
komai ya kammala ku kira ni ku sanar da ni,” ya
kashe wayar yana hucin tashin hankali.
Ya girgiza kai, “An yanka ta tashi ke nan .”
Ya xauki wayarsa ya kira lambar Sani direba
domin a yadda aiki ya jiqe masa ba ya tsammanin
zai kwana a gida yau ko kuma ya iya tuqi, dole ne
ya nemi ganawa da yaran da aka tabbatar masa an
kama.
Wayar Sani a kashe, ransa ya vaci, ashe bai
gargaxi Sani akan kashe waya ba? ya kira lambar
Ado maigadi don ya haxa shi da Sani. Lokacin da
Ado direba ya xaga wayar sai Alhaji ya yi magana
a fusace.
“Kai ina Sani ya shiga ne nake kiran wayarsa
a kashe?”
“Ranka ya daxe ni ma ban sani ba tun safe da
ya fita bai dawo ba kuma ma…”

Gawa ta qi rami
173 A.M. Xanzaki

Bai tsaya ya ji qarshen maganar Ado ba ya
kashe wayar cikin damuwa ya shiga sabon tunani.
‘Lallai yau zai hukunta Sani.’
Wayar tasa ta sake yin qara ya sa hannu ya
xauka sai ga kiran wani daga cikin yaransa na
gidan gona.
“Me ya faru kuma Jagwado?”
Muryar Jagwado na rawa ya amsa, “Yallavai
yarinyar nan ce ta gudu.”
Bai san lokacin da ya tashi tsaye ba cikin
wata sabuwar fusata, “Wanne irin iskancin banza
ne haka? Ta gudu kamar yaya?”
“Ranka ya daxe haurawa ta yi ta katanga.”
“Ku kuma kuna me a lokacin? Yaya zan sa ku
kula da mutum ku zo mini da labarin wai ya gudu?
To wallahi ku nemo ta duk inda ta shiga, idan
kuka same ta ku kashe ta.”
Ya kashe wayar yana huci. Yau me ya sa tun
da ya tashi da sassafe al’amura suke zo masa a
birkice ne? Duk wani tanadi da ya daxe yana yi
marmashewa yake yi kamar busassun furannin da
suka sha rana iska kuma ta kaxa su.

Gawa ta qi rami
174 A.M. Xanzaki

Babu mafita illa ya kira malaminsa ya sake
kai wa wayar raruma ya xauka ya danna lambobi.

Gawa ta qi rami
175 A.M. Xanzaki

___________BABI NA 8____________
SP Abdulhakim baqi ne mai
madaidaicin tsayi a tsaye, dirarre
kamar ingarman doki, sanye yake da
kakin ‘yan sanda, alamar matsayi tana
nuna shi a matsayin ASP ya qurawa Alawiyya ido.
“Kin tabbatar labarin da kika sanar da ni
gaskiya ne?”
Ta gyaxa kai, “A dalilin me zan yi maka
qarya? Ko sadda kake fafutukar neman soyayyata
ban yi maka qarya ba sai akan wani abu?”
Ya girgiza kai, “Ba ina nufin in qaryata ki ba
ne amma labarin ne na ji shi tamkar almara, ta
yaya za a yi mace Bahaushiya ta iya shirya
wannan lalatar?”
Ta yi masa wani kallo, “Ai kuwa ga shi ya
faru.”
Ya xan yi tunani sannan ya kalle ta, “Yanzu
za ki iya gane gidan gonar da suka kai ki?”
Ta girgiza kai, “Gaskiya ba zan iya ba saboda
da daddare ne amma na lura da wata alama da zan
iya ganewa.”
A

Gawa ta qi rami
176 A.M. Xanzaki

“Da kyau!” ya faxa sannan ya miqe tsaye ya
yafuto wani xan sanda mai sanye da kaki irin nasa
mai muqamin sajen.
Xan sandan, wanda tun da suka samu
Alawiyya a qofar gidan yayarta ya ajiye motarsu
ya buxe qofar motar tare da kunna wayarsa yana
sauraren daddaxar waqa daga wayarsa ya yi sauri
ya kashe wayar ya taso ya zo gaban maigidansa ya
sara masa.
“Sir!”
“Mu je gidajen gona na titin Northwest
yanzun nan, akwai suspect a can.”
Xan sandan ya juya ya buxe qofar motar,
Maigidansa ya shiga tare da Alawiyya, akwai ‘yan
sanda a bayan motar masu muqamin kofur suna
zaune riqe da bindigoginsu.
Alawiyya ta shiga nuna musu hanya yayin da
direban ke bin umarninta.
***
Misalin qarfe biyar na yamma a gidan Hajiya
Abu tana zaune tana danna waya yayin da ta
lalubo wata lamba ta kira.
“Hello! Hajiya Hindu.”

Gawa ta qi rami
177 A.M. Xanzaki

Aka amsa daga xaya vangaren, “Hello!
Hajjaju akwai wani abu ne?”
Hajiya Abu ta gyara zama, “Abubuwa da
yawa ma, wallahi wani shirina ne yake neman
wargajewa don haka ina ganin zan yi shiri na biyo
ki kwanan nan.”
“Bilkisu da Hannatu fa?”
“Suna nan qalau ke dai ki shirya mini komai
na dukiyata kafin na iso, domin wannan karon
idan na samu yadda nake so to tabbas idan na
dawo Najeriya a matsayin matacciya zan dawo.”
“Me kike nufi da haka? Basaja za ki yi ko
me?”
“Kwantar da hankalinki, idan na zo za ki ji
komai, ke dai ki yi abin da na ce domin wallahi
akwai qura.”
“To Hajiya yadda kika ce haka za a yi sai kin
zo.”
Suka kashe wayar gaba xaya.
Hajiya Abu ta girgiza kai, “Yanzu kam na
shirya, komai ta fanjama fanjam!”
Hajiya Abu ta miqe tsaye amma sai wayata ta
yi qara wanda hakan ya tilasta mata komawa ta

Gawa ta qi rami
178 A.M. Xanzaki

zauna ta xauki wayar tana dubawa, voyayyiyar
lamba ce. Sanin cewa akwai abin da ta taka ya sa
ta xaga wayar ta kai kunnenta.
“Ke ce Hajiya Abu?”
“E, mene ne?”
“Muna buqatar ganin ki a inda ‘ya’yanki
suke.”
“Wane ne kai?” ta tambaya.
“Sanin wane ne ni ba shi zai ceci ‘ya’yanki
daga hallaka ba,” aka ba ta amsa.
“Me zan ba ka ka qyale su su yi tafiyarsu?”
“Ba ki da abin da za ki bayar na fansa ki cece
su, idan kina son kuvutar da su ki kawo kanki.
Zan turo miki adireshin wurin”
Aka kashe wayar.
Hajiya Abu ta yi zugum da wayar a hannunta
tana tunani. Wane ne ya kira ta, kuma a ina ya
samu lambarta? Ba kowa ne yake da lambarta ba.
Ba ta da wata mafita sai kawai ta shirya ta tafi
inda aka ce mata. Ba ta gama tunani ba saqo ya
shigo wayarta.
***

Gawa ta qi rami
179 A.M. Xanzaki

Rana ta sunkuya, garin ya fara nuna alamun
shigowar almuru a daidai lokacin da Tsigi da
Qabusu ke zaune a qofar gidan bisa wani dutse
suna shan wiwi. Tun lokacin da Alhaji Lado ya
umarce su da su karvi aikin gadin Bilkisu da
Hannatu daga wurin Lawurje suke zaune a wurin
suna zuqar wiwinsu.
Tsigi ya yi wa wata doguwar wiwinsa ja
wadda ta kai tsayin rula ya kalli qwal kwabon da
ke kan Qabusu a cikin hasken farin watan.
“Wai me ka fahimta game da ‘yan matan nan
ni fa wallahi sai na yi budurwa a cikinsu.”
Qabusu ya harare shi, “Bana son rainin
hankali ka ji, Kai da ka ga mace sai ka bi ka wani
rikice kamar wanda ya ga kuxi.”
“Bambancina da kai ke nan; kai mayen kuxi
ne ni kuma mayen mata ne, ka ga ni da kai za ni
ce ta tad da mu je mu, wai yaqin ruwa ya tad da
sakaina.”
Qabusu ya ja wiwinsa shi ma ya yi wani shan
yaji ya kalli abokinsa ya ce; “Ta yaya aka yi
muka zama xaya? Mata kashe ka za su yi yayin da
kuxi kuma kai za ka kashe su.”

Gawa ta qi rami
180 A.M. Xanzaki

Tsigi ya haxa yatsunsa biyu ya xaga masa,
“A’a biyu ne, na tava ji wani masanin falasafa ya
ce abubuwa biyu idan ka ji an ce ka faye son su to
raina ka aka yi; kuxi da mata.”
Qabusu ya kuma jan wiwinsa, “To na ji don
Allah kada ka ishe ni, kai dai tun da ka yi sa’a an
ba mu gadin su ka tashi ka tafi uzurinka amma ka
bi a hankali kada ka jawo mana salalar tsiya.”
Tsigi ya yi wa wiwin hannunsa wata doguwar
zuqa ya qure maleji har ta kusa qona shi, hayaqi
ya turnuqe wurin yayin da ya jefar da ragowar ya
miqe yana karkaxe wandonsa.
“Bari in je da ma lokacin kai musu abinci ya
yi.”
Qabusu ya harare shi, “Tun xazu ba ka tuna
ba sai da biyar na yamma ta kusa.”
Ya yi murmushi, “Sha’afa na yi wallahi,
kuma ma ai ka san ba a kawo musu abincin da
wuri ba,” ya juya ya tafi.
Qabusu ya bi shi da kallo har ya shiga cikin
gidan shi kuma ya gyara zama ya ci gaba da
bushe-bushensa.
***

Gawa ta qi rami
181 A.M. Xanzaki

Hannatu ta kalli ‘yar uwarta Bilkisu a cikin
xan hasken fitilar qwan da ta rage musu., “Lokaci
fa ya yi, ya kamata mu fara shiri.”
Bilkisu wadda take zaune zaman dirshan ta
kalli Hannatu irin kallon da ake yiwa xanwaken
da babu yaji, “Wai ke kina ganin wannan dabarar
za ta ci kuwa?”
Hannatu ta miqe tsaye, “Bari ki gani, da
jarrabawa jirgin sama ya tashi,” ta fara qoqarin
cire rigarta yayin da Bilkisu ta bi ta da kallon
mamaki.
“Wai da gaske kike?”
“Ahaf! Naki wasa ne,” ta kammala cire riga
da zanenta daga ita sai shimi da wani dogon siket
har qasa. A sannan ne kuma aka fara qoqarin
qwanqwasa qofa don shigowa a kawo musu
abincin rana wanda tuni ya yi sanyi ga alama.
Hannatu ta yi murmushi, “Muna zuwa za mu
buxe.”
Ta yi wa Bilkisu alama da ita ma ta shirya.
Bilkisu ta miqe ta cire riga da zanin da ke jikinta
ta koma daga ita sai wata after dress sannan ta nufi
qofar banxaki ta buxe ta shiga.

Gawa ta qi rami
182 A.M. Xanzaki

Hannatu ta rataya rigarta a kafaxa ta doshi
qofar ta sa hannu ta buxe ta tsaya cak tana kallon
sa sannan sai ta fara qoqarin sanya rigar da ke
qafaxarta.
Tsigi da ke tsaye riqe da kular abinci ya bi
qirjin Hannatu da kallo yayin da take qoqarin
rufewa, “A’uzu billahi da ma kai ne?”
Ya daka mata harara, “E ni ne an canza mai
kawo muku abinci ne,” sannan ya sa makulli ya
kulle qofar xakin ya zura ‘ya’yan makullan a
aljihunsa yana yi yana kallon ta ya ture ta ya shige
ciki, a wannan lokacin kuwa ta ba shi dama ya
gama kallon jikinta.
Ya ajiye kular a tsakiyar xakin yana waige-
waige kamar yana neman wani abu, Hannatu
kuma ta fara qoqarin sanya rigar jikinta.
Ya kalle ta ya vata rai, “Ke ina ‘yar uwarki?”
yana magana murya a karye sannan yana bin
sauran jikinta da ya kasance a buxe da kallo.
Ta nuna masa banxaki, “Tana ciki wanka take
yi, ni ma fa wankan zan shiga shi ne ka shigo,
bayan haka kuma zafi yana damun mu.”
“To ina ruwana?” ya faxa yayin da ya nufi
banxakin kai tsaye.

Gawa ta qi rami
183 A.M. Xanzaki

“Da mutum fa a ciki, na gaya maka wanka
take yi,” ta faxa cikin shagwava.
Ya juyo ya kalle ta, “Na sani, so nake yi na
tabbatar,” sai kuma ya tsaya cak yana kallon ta
yana haxiyar yawu.
Hannatu ta yi masa fari da idanu. Nan take
gogan naka ya ximauce ta kuma yin qasa da
idanuwanta.
Tsigi ya lashe levvan bakinsa da ya ji sun fara
bushewa sannan ya matso gabanta. A wanan
lokacin ne kuma Bilkisu ta fito daga banxakin
xaure da tawul a qirjinta wanda ta samu a
banxakin.
Tsigi ya kalle ta daga sama har qasa ya qara
rikicewa.
“Yan matan biyu Ya da qanwa suka rikita
bawan Allahn nan ya rasa wurin wa zai je.
“Kai kada ku raina mini hankali mana, da ma ku
ma ashe hakan take ?”
“Matuqar za ka yi mana abin da muke so to
duk abin da ka nema a wurinmu za ka samu,” in ji
Hannatu.
“Me kuke so?” ya yi saurin faxa yana kallon
su xaya bayan xaya.

Gawa ta qi rami
184 A.M. Xanzaki

“Za ka ba mu makulli mu xan zagaya cikin
gidan nan, mun gaji da zama a nan.”
Ya kalli kullalliyar qofar kamar yana gudun
kada wani ya ji abin da yake qullawa da ‘yan
matan, “Amma sai kun ba ni mintuna goma tare
da ku.”
Ya qara matsowa kusa da su.
Hannatu ta nemi xaya daga cikin kujerun da
ke wurin ta kishingixa tana yi masa murmushi.”
Tsigi ya doso wurinta cike da nishaxi.
Akwai wani dogon katako mai faxi da ke
jingine a gefe wanda zai kai tsawon Bilkisu, da shi
ta yi amfani ta rangaxa masa duka a qeya har jini
ya fara zuba.
Tsigi ya juyo a fusace zai yi magana a lokacin
ne kuma Hannatu ta shure shi da qafarta da
dukkan qarfinta a marainansa.
Tsigi ya qwala ihu ya yi taga-taga zai faxi ya
daure ya miqe ya nufo Bilkisu ya kai mata raruma.
Bilkisu wadda ke cike da tsoro kamar za ta
fashe da kuka ta dage ta kuma dukansa da katakon
a tsakiyar kansa nan take ya baje a qasa. Hannatu
ta xaga qafarta ta taka masa qirji.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login