Showing 24001 words to 27000 words out of 39022 words

Chapter 9 - Gawa Taki Rami Book Complete Writing By Ayuba Muhammad Danzaki.pdf

gidan na matsi sai Hajiya ta ji
wayarta ta yi qara ta yi sauri ta koma gefe ta xaga
bayan ta gane mai kiran.
“Hello Bello aiki ya kammala ko?”
Aka amsa daga xaya vangaren, “Hajiya an
samu matsala sosai.”
Ta gyara tsayuwa tare da yin waige-waige
don tabbatar da babu mai jin ta.
“Matsala wacce iri kuma?”
“Mun iso wurin ba mu same su ba.”
“Kamar yaya? Me ya sa kuka bari lokaci ya
qure muku wannan ce damar da nake son yin
amfani da ita, idan na bari ta suvuce wata irinta za
ta yi mini wahalar samu.”

Gawa ta qi rami
123 A.M. Xanzaki

Daga xaya vangaren wani ya amshi wayar,
“Tun xazu nake taraddadin sanar da ke abin da ya
faru, gaskiya akwai gagarumar matsala Hajiya.”
Ta nutsu tana saurare, “Me ya faru kuma?”
“Mun iso wurin taron kamar yadda kika
umarce mu amma sai muka tarar har an tashi sun
fito waje, a kan idonmu wani ya xauke su a mota
ya fita da su, mun yi qoqarin bin su amma sai
motar tamu ta samu matsala ta taka qusa.”
“Me? Kuna nufin an xauke su?” ta faxa
kamar da tsawa wanda yin hakan ya janyo
hankalin wani yaro da ya fito yin fitsari a
makwarara, “Affale kuna da hankali kuwa? Na
shiga uku shikenan.”
“Hajiya kin san waxanda suka xauke su ne?”
Affale ya tambaya.
Hankalin Hajiya a tashe take magana, “Ban
sani ba amma ina mai tabbatar muku an tafka
babban kuskure, su kaxai ne makamin da za a yi
amfani da su a ga bayana, wallahi idan abin da
nake zato ya tabbata ni kam zan yanke qauna da
rayuwa.”
“Idan dai muna nan babu abin da zai faru
Hajiya.”

Gawa ta qi rami
124 A.M. Xanzaki

“Bana son zancen banza, kuna ina aka xauke
su? Kuma har kake da bakin gaya mini cewa akan
idonku, yanzu duk wani shiri da nake yi zai
ruguje, kun san me satar su Bilkisu ke nufi a gare
ni kuwa? Ko kun san su ne kaxai makaman da
suka rage da zan yi amfani da su wajen kare kaina
ko kuma yaqar maqiyana? Idan ba ku fahimta ba
to su kaxai ne kuma raunina.”
“Ai na ce miki Hajiya…”
Ta katse shi, “Ka bar wannan maganar idan
ka san ba za ku iya samo su kafin safiya ba.”
Tun kafin ya yi magana ta katse wayar wanda
yin hakan ya alamta masa matsalar tata ta kai
matuqa.
Cikin sauri ta danna lambar Bilkisu amma ta
ji a kashe haka ma layin Hannatu shi ma ba labari,
hankalinta ya qara tashi sai take ganin kamar
alqiyamarta ce ta kusa tsayawa.
Hajiya ta yi tsaye nan tana kallon hasken farin
wata, take ta ji duk wata gajiya da barci sun
qaurace mata, haka nan sai take ji gwiwoyinta sun
yi sanyi matuqa, akwai buqatar ta zurfafa tunani
don tuna daga inda ta fara samun matsala. Nan
take wani tunani ya zo mata.

Gawa ta qi rami
125 A.M. Xanzaki

Wani tunani ya zo mata, ta xan zurfafa shi
wanda yin hakan ya sa ta samu amsar daga inda
matsalarta take. Ya kamata ta yi gaggawar yi wa
hanci tufka tun kafin wankin hula ya kai ta dare.
Ta juyo ta koma inda mahaifinta yake, wanda
bayan tashinta da mintuna kaxan ya fuskanci
wayar ba ta qare ba ce sai kawai ya koma xakinsa
ya kara qofa ya yi kwanciyarsa.
Da ta rasa takamaimai abin yi sai ta koma
xakin da ta san shi ne masauqinta a duk sadda ta
zo ta nemi wuri ta kwanta amma barci ya gagara
zuwa.
Ta yi ta sake jarraba kiran wayoyin Bilkisu da
Hannatu amma kamar dai xazu, wayoyin ba sa
shiga. Ta san kwara ruwa kawai take a bayan
agwagwa, amma ba za su xaga kiran ba, tana yin
kiran ne kawai don ta rasa takamaimai abin yi
bayan tunani. Bayan ta gaji da kiran wayoyin tana
kwance cikin duhu tana tuna rayuwarta ta baya da
mijinta sai wayar tata ta yi qara.
Da sauri ta kai mata wawura ta duba, ta so ta
yi tsaki amma sai ta xaga wayar ta fara amasawa.
“Wa’alaikas salam Hajiya lafiya kuwa?”

Gawa ta qi rami
126 A.M. Xanzaki

Hajiya Nadiya ta amsa daga xaya vangaren,
“Babu lafiya Hajiya ba ki ji abin da ya faru ba
ne?”
***
Da Assalatun fari ta yi miqa, ba miqar tashi
daga barci ta yi ba sai miqar gajiya da kwanciya
domin tun jiya da misalin qarfe sha xaya da rabi
na dare da aka sanar da ita labarin vatan ‘ya ‘yanta
ta shiga ximuwa fiye da wadda ta same ta yayin
jin labarin mutuwar Tanko.
Ta matsu gari ya waye ji take kamar ta yi
tsuntsuwa ta tashi ta koma Kano a daren ko kuma
ta sa manjagara ko wata doguwar sanda ta jawo
Alfijir ya keto ko Ladanai za su tashi su sanar da
waxanda za su hana ta tafiya cewa Asuba ta yi.
A gurguje ta xaura alwala ta bi wani
masallaci sallah, ana sallamewa ta fita waje ta
matsa mavalli motar ta buxe ta shiga ta tashe ta ta
fara ba ta wuta.
Qarar tashin motar ne ya katsewa Malam
Kalla mahaifin Hajiya Abu lazumin da yake yi a
cikin masallacin qofar gidan bugu da qari shi ne
limamin masallacin haka kuma a qa’ida idan ya
fara wannan lazumin ba ya fitowa sai rana ta yi.

Gawa ta qi rami
127 A.M. Xanzaki

Ya fito riqe da carbinsa rafkeke wanda ya sha
adon tutoci ya nufo wurinta yana tafiya a
durqushe. An ce tun yana yaro ba a tava samun
wanda ya tsere masa a noma ba, kafin su yi kunya
xaya shi ya shiga ta uku. Haka ya kasance har
tsufansa, wataqila wannan ne ya durqusar da
gadon bayansa.
“Yau addu’ar uku fa, tun yanzu za ki tafi ba
za ki bari gari ya daxa wayewa ba?” ya tambaya
ba tare da ya daina jan carbin ba kuma bakinsa bai
daina motsawa ba.
“Baba akwai matsala ne a can wallahi, amma
zan dawo kafin bakwai.”
Ita kanta ta san qarya take yi, domin ita da
dawowa sai bayan ta san halin da ‘ya’yanta suke
ciki.
Tsohon ya ci gaba da nazartar ‘yar tasa, nan
take ya ga matsalar qarara a fuskarta kamar ma ta
xan rame daga daren jiya zuwa yau. Kai duk
yadda aka yi ba ta yi barci ba, domin tun da ta
koma gefe ta amsa waya ta dawo ta zauna ya leqo
ya fuskanci wani labari maras daxi ne ya same ta.
“Allah Ya tsare amma dai a dinga addu’a.”

Gawa ta qi rami
128 A.M. Xanzaki

Ta gama ba wa motar wuta ta fito waje
sannan ta zura hannu ta xauko jakarta ta buxa ta
xauko damin xari biyar-biyar guda biyu ta miqa
masa, “Xaya a ba wa mahaifiyar Tanko sai a yi
masa addu’a wannan kuma ku yi amfani da shi a
gida.”
Dattijon nan ya zage tsakani da Allah yana ta
faman runtuma mata addu’a.
Ba tare da ta ce komai ba ta shiga mota
sannan ta leqo ta taga, “Sai na dawo Baba,” ta sha
kwana ta kama bin hanyar da za ta fitar da ita daga
qauyen.
Malam Kalla ya tsaya ya qurawa danjojin
motar idanu har suka vace sannan ya cusa
damman kuxin a aljihun tsohuwar malum-malum
xinsa ya faki ido ya koma cikin masallaci ya ci
gaba da lazimi.
***
A daidai lokacin da Hajiya take barin qauyen
Xansarai ne da sanyin safiyar, Alhaji Haruna
Tinqwal ya danna ham sau biyu Maigadi ya taso
da sauri ya buxe qofar.
Alhaji Haruna ya fita daga gidan ya hau titi.

Gawa ta qi rami
129 A.M. Xanzaki

Maigadi ya bi motar da kallo, ba al’adar
Alhaji ba ce fita da Asuba amma yau me ya sa ya
yi wannan fitar saurin haka? Wani lokacin sai ya
kai qarfe goma na safe bai fita ba kai wani lokacin
ma sai ya yi sallar Azahar amma yau, ya duba
agogon hannunsa, qarfe shida saura kwata na safe
ina za shi?
Duk wannan tunanin Maigadin ne yake faman
yi lokacin da yake bin motar Alhaji Haruna da
kallo. Ya gyaxa kai ya juya bayan rasa amsoshin
tambayoyinsa.
Alhaji Haruna ya miqe ya ci gaba da tafiya
kamar zai bar garin, ya hau titin Northwest cikin
lokacin da ba su wuce mintuna talatin ba,
kasancewar safiya akwai qarancin ababen hawa a
titunan garin.
Ya isa gidan hutawarsa a cikin mintuna
hamsin, babu vata lokaci aka buxe masa qofa ya
shiga ya samu wuri ya ajiye motar sannan ya fito
daga wurin ya nufi wasu xakuna kevavvu a gefe.
Jagwado da ke tsaye yana jiran sa ya buxe
masa qofa sannan ya yi masa ishara da cewa tana
ciki.

Gawa ta qi rami
130 A.M. Xanzaki

Alhaji ya shiga xakin babu alamar rahama a
fuskarsa yayin da ya yi tozali da Alawiyya zaune
bisa wata tsohuwar kujerar qarfe, ga wanda ya san
ta zai iya fahimtar tana cikin matuqar damuwa.
Bayan wayar da ta yi da Zahira ne ta yi
qoqarin killace kanta daga sharrin abin da aka
gargaxe ta a kansa. Kamar abin tsautsayi qarfe
uku na dare wayarta ta fara qara, a da kamar ba za
ta xaga ba amma sai ta xaga kiran.
“Kina ina ne?” ta ji muryar wata qawarta a
nan maqwabtansu mai suna Ta’iba.
“A ina kike tsammanin gani na a daren nan
idan ba a gida ba?” ta ba ta amsa.
“Don Allah taimaka ki zo ki same ni a gida
wallahi ni kaxai ce a gidan kuma motsi nake ji,”
Ta’iba ta ce mata haka.
Alawiyya ta tashi zaune, “Motsi kuma wanne
iri Ta’iba? Ki kunna wuta mana.”
“Don Allah idan za ki zo ki zo, kin ga
wallahi…”
Alawiyya ta sauqo daga kan gadon sannan ta
nufo waje riqe da waya sanye da takalmi Faxe a
qafarta.

Gawa ta qi rami
131 A.M. Xanzaki

“Ke kin faye raki wallahi, to ga ni nan zuwa.”
Ta buxe qofa sai da ta leqa ta tabbatar babu
mai ganin ta sannan ta fito waje ta nufi qofa,
kasancewar qofar gidansu ba wata babbar qofa ba
ce ba ta vata lokaci ba wajen zare sakatar gidan ta
sa qafa ta fita. Shaf ta manta da gargaxin da
Zahira ta yi mata, sai da ta fara tafiya ke nan za ta
tsallaka titi sai ta ji gabanta yana faxuwa kuma
tamkar wani yana kallon ta.
Ta tsallaka qaramin titin da ya raba gidansu
da gidan su Ta’iba ta isa qofar gidan cike da tsoro.
Ta qwanqwasa qofa karon farko ke nan za ta
sake qwanqwasawa sai ta ji wani tafkeken hannu
ya zagayo ta baya ya rufe mata fuska. Kafin ta yi
qoqarin yin ihu sai ta ji kanta yana juyawa
idanuwanta suka rufe sannan sai jikinta ya saki
gaba xaya kamar wata ‘yar maye. Daga nan ba ta
farka ba sai a wani xaki mai duhu ta duba wayarta
ba ta gan ta ba, sai a sannan ne ta san ta shiga
mugun hannu.
Tsawon mintuna kafin ta ji jikinta ya yi qarfi,
sannan a lokaci guda ta lura safiya ce. Tana cikin
tunani ne sai ta ji an turo qofa a sannan ne kuma ta
ga mutumin da take zargi da sato ta. Wato Alhaji
Haruna Tinqwal.

Gawa ta qi rami
132 A.M. Xanzaki

Alhaji Haruna ya qaraso gabanta yana qare
mata kallo daga sama har qasa sannan ya yi tsaye
a kanta yayin da Jagwado da ke biye da shi ya
tsaya qerere a bayansa tamkar xan gadinsa.
“Alawiyya Surajo ko?”
Kallon sa kawai ta yi ta gyaxa kai.
“Aikinki yana kyau, sai dai bana sa an kawo
ki nan ba ne don na wulaqanta ki ko na cutar da ke
ba a’a na sa an kira ki ne domin kawai ki sanar da
ni wanda ya saka ki aiki a kaina da har kike yi
mini binciken qwaqwaf! Idan kika aikata abin da
na ce shikenan za mu rabu cikin aminci, ba cuta ba
cutarwa amma idan kika yi mini taurin kai to za ki
tilasta ni aikata abin da ban yi niyya ba. Wane ne
ya saka ki bincike a kaina?”
Ta kalle shi ta kawar da kai, “Ni bana bincike
a kanka, ka rabu da ni na tafi ni xaliba ce wadda
take ajin qarshe a makaranta don Allah kada ka
vata mini shekaruna na karatu su tafi a banza. Na
yi maka alqawarin ba zan sanar da kowa ba.”
Alhaji ya yi murmushi, “Ai sai kin fita daga
nan za ki yanke wannan hukuncin, idan kuwa ba
haka ba to ina tabbatar miki ciranin karatunki a
nan zai qare. Ina so in san wanda ya saka ki

Gawa ta qi rami
133 A.M. Xanzaki

wannan aikin. Sannan mene ne haxinki da matata
da aka gan ku tare a mota shekaranjiya?”
Alawiyya ta zazzaro idanuwa tana kallon sa.
“Kina mamaki ne? To ko kaxan bai kamata ki
yi mamaki ba domin ke xalibar jami’a ce a ajin
qarshe wadda ake sa ran samun wayewa daga gare
ta. Au! Kin san ba ki shirya faxan ba kika tare
shi?”
Ya fara zagaya ta, “Ina mai ba ki shawarar ki
sanar da ni gaskiya na yi miki alqawarin babu abin
da zai same ki.”
Alawiyya ta kalle shi a matuqar tsorace, “Zan
gaya maka gaskiya amma don Allah ka fara kunce
ni kuma ina buqatar ruwan sha.”
***
Hajiya Abu na zaune bisa kujera yayin da
Bello ke tsaye a gabanta cikin faxuwar gaba.
Hajiya ta kalle shi, “Wanne qoqari ka ce ka
yi?”
Bello ya gyara tsayuwa, “Na samo wani
mutum wanda zai iya bin sawun wayoyinsu domin
samun cikakken bayani game da inda suke.”

Gawa ta qi rami
134 A.M. Xanzaki

Ta kalle shi da mamaki, “Daga nan sai a yi
yaya?”
Ya yi shiru yana kallon ta, “Sai a sanar da
‘yan sanda.”
Ta xaga masa xan yatsa tana karkaxawa
alamar a’a, “Ka bi abin a hankali bana so ‘yan
sanda su sani.”
“Akwai wanda kike zargi ke nan ranki ya
daxe?”
Ta gyaxa kai tana kallon sa da idanun tabbaci,
“Qwarai kuwa, sai dai yin hakan ya sabbaba muku
wani aikin, ina so ku bincika min gidan Alhaji
Haruna Tinqwal ku tabbatar direbansa ya shiga
hannunmu nan da kwana biyu.”
“Hajiya mene ne haxin ki da direban Alhaji
Haruna Tinqwal?”
Ta xaga masa hannu, “Kada wannan ya dame
ka, da sannu za ka san komai matuqar ka iya
bakinka. Kai dai ka yi abin da na ce.”
Bello ya xan yi tunani sannan ya kalle ta, “An
gama Hajiya, ai kin yi min komai a rayuwa, ni
kuwa na xauki alqawarin babu abin da za ki nema
a wurina ki rasa.”

Gawa ta qi rami
135 A.M. Xanzaki

Hajiya ta kalle shi ta keve baki.
Ya miqe ya nufi qofa ya fita yayin da ta bi shi
da kallo.
Hajiya ta shiga tunanin yadda aka yi ta samu
matsala a shirin da ta daxe tana yi, duk yadda aka
yi wani yana nan ya maqe a bayan labule yana
kallon duk wani motsinta, a saninta kuwa babu
wanda ya san wasu sirrika nata idan ba Sani ba,
amma kuma ba ta jin zai iya cin amanarta. Kai!
Xan adam fa wuyar sha’ani ne da shi, babu
mamaki ya sauya bayan tsawon lokaci da ba su
haxu ba. to ko da ya sauya a ina ya samu qarfin
gwiwar sanyawa a sace mata yara? Wayewarsa da
buxewar idonsa bai kai ya aikata haka ba, ta ba wa
kanta amsa.
Tana iya yiwuwa masu satar mutane ne suka
xauke su, nan ma ta yi saurin kawar da wannan
tunanin, tunanin tuhumarta ya sake garzayawa ta
gayyato Sani a cikin lamarin, sai dai ta san ba za
ta tava samun amsa cikakkiya ba matuqar ba shi ta
samu ido da ido ba. A yadda ta ba wa Bello kwana
biyu rak ta tabbata zai iya samo Sani a kwana
biyu.

Gawa ta qi rami
136 A.M. Xanzaki

Ta yi ajiyar zuciya sarqar tunaninta ta tsinke a
daidai lokacin da wayarta ta xauki qara ta sa
hannu ta xauka.
Hajiya Nadiya ce ta kira ta.
“Hello! An dace kuwa?”
“Ina fa aka dace? Wani mugun ya sace mini
yara.”
“Ko kiran waya ba a yi ba har yanzu?”
“Babu wanda ya kira,” ta ba da amsa kai
tsaye.
“Allah Ya kiyaye, na yi waya da mataimakin
I.G mai kula da shiyyar nan ya yi alqawarin kawo
xauki don gano varayin.”
Gyaxa kai kawai Hajiya ta yi cikin sanyin
jiki, “Ai kuwa da ya taimake ni,” kawai ta iya
cewa.
“Sai dai nan da mintuna zai iya turo jami’ai
zuwa gidanki domin ki taimaka musu da wasu
bayanai.”
“Wannan babu matsala, shirye nake a
kowanne lokaci.”
Daga nan ta kashe wayar bayan sun gama
tattaunawa ta zauna zaman jiran zuwan wakilan

Gawa ta qi rami
137 A.M. Xanzaki

‘yan sanda masu shirin yi mata tambayoyi a
hanyar binciko varayin ya’yanta.
***
Alhaji Haruna Tinqwal ya qarewa Alawiyya
kallo bayan ta gama ba shi labari.
“Kin tabbata abin da kika faxa gaskiya ne?”
Hawaye suka kwararo daga fuskarta, “Ka
taimaka ka kunce ni sannan ka sa a kawo mini
ruwa.”
Ya xaga murya ya kira yaronsa, “Kawo mata
ruwa ta sha.”
Har aka kawo mata ruwa ta sha kallon xakin
take sake yi tana tunanin hanyar guduwa don ta
samu sanar da ‘yan sanda abin da yake faruwa,
hakan ya sa ba ta san lokacin da Alhaji Haruna ya
fita daga xakin ba.sai xaga kai ta yi ta ga wayam!
‘Wannan dama ce a gare ki da za ki iya
tserewa’ ta ji zuciyarta na raya mata haka. Ta
saurara don ta ji alamar motsin mutane a kusa da
xakin, ina ma ita vera ce ko kyanwa da ta sakaxa
ta qaramar qofar tagar da ke can sama ta sulale
abinta. Ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login