Showing 6001 words to 9000 words out of 39022 words

Chapter 3 - Gawa Taki Rami Book Complete Writing By Ayuba Muhammad Danzaki.pdf

a hankali ta matso kusa da shi yayin
da ya yi nisa a kogin tunani da wataqila begen
tsohuwar matarsa ne (a tunanin Zahira). Ta tsaya a
kusa da shi.
Jin motsinta ne ya sa ya juya firgigit! Sannan
lokaci guda ya kife hoton a kan teburin ya yi
gaggawar xora littafinsa a kai. Sai dai ya makara
domin sai da ta qarewa hoton kallo sannan ya
ankara.
Ya qaqaro murmushi sannan ya kalle ta,
“Lokacin barci ya yi ko?”
“Me kake voye min?” ta zagayo ta zauna
kusa da shi, “har yanzu ba ka daina tunaninta ba
ko?”
Alhaji Haruna ya yi hamma ya xauki hoton ya
saka a aljihun babbar rigarsa ya miqe tsaye, “Kina
buqatar ki kwanta ki huta haka nan, domin na
tabbata kin daxe a xaki kina karatu.”
Ta bi shi da kallo kawai har ya bar falon ya
nufi xakin barcinsu.
Ta yi ajiyar zuciya ta qura wa gurbin da ya
ajiye hoton idanu, bai kamata ta bar abin nan ya
dinga tafiya haka sasakai ba tare da ta xauki
mataki ba. Babu ta yadda za a yi tana tare da

Gawa ta qi rami
32 A.M. Xanzaki

mijinta ya dinga tuna wata a ransa har abin ya
zame masa kamar ibada. a ranta sai ta sha
alwashin gano ko mene ne mijin nata ke voye
mata, haka kawai sai ta ji ba ta yarda cewa
tsananin so ko bege ko zafin rabuwa yake
sanyawa kullum yana maqale da hoton tsohuwar
matarsa ba. lallai akwai wani abu a qasa.
Mene ne wannan kuwa? Aikin da za ta saka a
gaba ke nan har sai ta cim masa. Ta miqe ta nufi
xaki da nufin fara gudanar da shirin ta a wannan
daren, domin Hausawa sun ce ba a bori da sanyin
jiki kuma a bari ya huce shi ke kawo rabon wani.
***
Gajimaren da ya fito tun da sanyin safiya bai
iya voye hasken rana ba domin a koyaushe
sassarfa yake yi yana wucewa, kasancewar damina
ta gabato babu abin da mutane ke sa ran gani
tamkar ruwan sama.
A yanzu da qarfe xaya na rana ta yi gajimaren
ya washe haka nan kuma rana ta fito qwanyar.
Bilkisu da Hanne da ke riqe da ‘yan
litattafansu suka biyo dodo-dodon yuyar xaliban
da ke fitowa daga makarantar C.A.S da ke kan
titin hawa da sauqar jiragen sama da ke Kano
bayan kammala laccar qarfe xaya na rana wadda

Gawa ta qi rami
33 A.M. Xanzaki

ita ce laccarsu ta qarshe a wannan wunin. Suka
fito waje suka dakata a gefen titi suna jira.
Tarin mutanen da ke qofar makarantar gami
da cunkoson ababen hawa da ke wucewa a kan
titin ya sanya dole suka koma gefe inda wata
bishiya take suka zauna suna hutawa.
Bilkisu ta kalli Hanne, “Karvo mana askirim
mana da ragowar canjin wurin ki.”
Hanne ta tashi ta tafi wurin wani mai keke da
ke tsaye yana sayar da askirim ta karvo musu
madara guda biyu ta kawo musu suka ci gaba da
tsotsa suna hira.
Tun da suka zo da safe aka tantance su suka
fara departmental aka shigar da sunayensu a jerin
sunayen xaliban makarantar aka buxe musu
kundaye sai ta koma ta kuma gaya musu daga
zarar an tashi za ta zo da kanta ta tafi da su kafin
su saba.
Bilkisu da Hanne sun tsinci kawunansu a
wata sabuwar rayuwa musamman gogayya da
xalibai da suka qunshi yaruka daban-dabam, mafi
yawan xaliban matasa ne masu qananun shekaru,
Babu wadda tasu ta zo xaya a ajin da suka fara
zama kamar wata yarinya A’isha Hamisu sai wani
matashi wanda shi ne shugaban xaliban ajin mai
suna Faisal Hisham. A haka suka wuni a ajin suka

Gawa ta qi rami
34 A.M. Xanzaki

samu sabo da A’isha Hamisu wadda ta ce musu ita
ma sabuwar zuwa ce satin ta xaya, haka kuma
tana zaune ne a unguwar Badawa.
Ba su daxe da fara sha ba sai ga wani babur
mai qafa uku ya tsaya a gefen titin tare da Hajiya
Abu a ciki fuskarta a rufe da niqab kamar yadda ta
kawo su da safe fuska a lulluve, direban babur xin
wani siriri mai qaramin jiki, idanuwansa a loko ya
fito yana rarraba idanuwa kamar bawan da ya yi
wa Sarki qarya.
Hanne ta tava Bilkisu ta nuna mata direban,
“Kin gan shi can ya zo, bari mu yi masa magana.
La kin ga har da Hajiya ma.”
Direban mai suna Iro Indabawa ya xauko
wayarsa ya buxe yana duba wani abu yayin da ya
jingina da babur xin.
Hanne ta qaraso wurin da fara’arta tana
kallon fuskar Hajiya, ta gaisa da direban.
“Ku shigo mu tafi. Ina Mamana?”
Bilkisu ta qaraso wurin ta gai da Hajiya
sannan suka shiga babur xin a tare suka zauna. Iro
ya shiga ya ta da babur xin suka miqe titi suka
nufi unguwar Nassarawa.
A kan hanya Hajiya ta kalli su Bilkisu, “Yaya
makarantar, ta yi dai ko?”
Suka gyaxa kai dukkansu.

Gawa ta qi rami
35 A.M. Xanzaki

“A’a idan ba ta yi ba ku yi magana na canza
muku wata, in dai Kano ce makaranta sai kun
gaji,” idonta ya qare akan Hanne, “ke mai
tambayar yaya za ku yi da karatun ku.”
Hanne ta yi murmushi, “Mama wallahi ta yi,
komai ya ji.”
“Ke fa Mamana?”
Bilkisu ta gyaxa kai, “Ta yi, sai dai monitan
ajinmu ne yake matsa mini da kallo koyaushe na
juya sai na ga yana kallo na.”
Hajiya ta yi murmushi, “A hankali zai daina,
kin san yadda baqo yake a wuri. Yauwa, ga Iro
nan shi zai dinga kai ku yana dawo da ku, a
koyaushe ku tsaya a gindin bishiyar nan da na gan
ku yau kafin nan gaba na sayi mota.”
Hanne ta yi murmushi, jin an ce za a sayi
mota.
Hajiya ta kalli Iro yayin da ya ci burki a danja
bayan ya fahimci tab a da alamar launin ja, jerin
gwanon motoci da Babura suka yi masa qawanya
ta gefe da gefe.
“Iro waxannan ne yaran nawa da nake faxa
maka don Allah ka dinga zuwa da wuri kana
xaukar su kuma ka tabbata qarfe xaya ta yi maka
a qofar makarantar.”

Gawa ta qi rami
36 A.M. Xanzaki

Iro ya gyaxa kai yayin da danja ta nuna
alamar kore, Iro ya miqe titi ya ci gaba
da tafiya.
A cikin abin da bai gaza mintuna arba’in ba
suka isa gida ya sauqe su sannan ya juya ya koma
kan titi.
“Idan ka dawo za mu yi lissafi,” in ji Hajiya.
Hannu ya xaga mata kawai ya danna hon
yayin da Jibo ya qaraso yana yi mata sannu da
zuwa.
Suka shige cikin gidan suka zarce falon gidan
inda kowaccensu ta shiga xakinta ta canza kaya ta
yi wanka ta dawo falon, hajiya ta zubo musu
abinci daga wani fulas, da ma tun safe an tanada.
Bayan gama cin abinci Hajiya ta saka su a
gaba sai da suka yi bitar abin da aka koya musu ta
tabbatar ya zauna a kan su sannan ta qyale su suka
shiga wata sabgar.
Ga alama Hajiya ta shirya inganta rayuwar
‘ya‘yanta.

Gawa ta qi rami
37 A.M. Xanzaki

__________BABI NA 2__________

BAYAN SHEKARA XAYA

n samu sauyin rayuwa a abubuwa da
dama, waxansu mutane sun kuxance
waxansu sun talauce, an haifi wasu,
wasu sun mutu, waxansu sun hau mulki, waxansu
sun sauqa daga mulki sun ba wa wasu, waxansu
sun yi aure yayin da wasu suka saki matansu,
aurarraki da yawa sun mutu yayin da aka sanyawa
wasu ranar auren, kowanne mutum a wannann
lokaci ya samu qarin shekaru biyu a rayuwarsa, a
cikinsu akwai Bilkisu da Hannatu tare da Hajiya
Zainab.
A cikin makarantar C.A.S da su Bilkisu ke
matakin qarshe na karatun su misalin qarfe goma
na safe bayan an kammala lacca an fito sai suka
wuce cafeteria domin cin abinci ko shan abin sha.
Faisal Hisham na zaune a kan kujera tare da
abokansa su biyu; Abbas Manga da Nasiru Ado
suna kallon qwallo a wata tasha da ke wurin.
Faisal baqi ne mai madaidacin tsayi, zai kai
shekaru ashirin, mahaifinsa shahararren
matsakaicin xan siyasa ne da ke da iyayen gida
A

Gawa ta qi rami
38 A.M. Xanzaki

manya a siyasa, tsohon shugaban qaramar hukuma
haka kuma kwamishinan lafiya mai ci a yanzu.
Abbas gajere ne fari yana da bille a fuskarsa,
shekarunsa za su iya zama daga sha takwas zuwa
ashirin, xa ne ga qwararren ma’aikacin jami’in
tsaro a hukumar shige da fice wanda ya yi ritaya a
matsayin Controller general haka kuma mutumin
da ya yi wa siyasa shigar shantun qadangare.
Nasiru yana da hasken fata ba laifi, haka
kuma dogo ne a siffa. Xa ne ga Hajiya Nadiya
matar da ta gaji dukiya daga tsohon attajirin da ya
yi sharafi tun zamanin mulkin soja, haka kuma
babban abokin dogarin wani tsohon shugaban
qasa. Nasiru yana da xaurin gindi da gata da
shagwava daga mahaifiyarsa kasancewar shi kaxai
ta mallaka.
Abbas ya xaga kai ya kalli su Bilkisu da
Hanne da waxansu ‘yan mata ya nuna wa Faisal
su, “Ka ga mutuniyarka can tare da gayyar ta.”
Faisal ya harba qwayar idanunsa inda su
Bilkisu ke zaune suna shan askirim ya vata rai,
“Kai dai bari Abbas, wallahi yadda na tsani
yarinyar can kamar na shaqe ta ta bar duniya.”
Nasiru ya kalle shi da mamaki, “Kullum na
tambaye ka me ya sa ka tsane ta kai ma kakan ce
ba ka sani ba, an tava yin qiyayya ko soyayya

Gawa ta qi rami
39 A.M. Xanzaki

babu dalili? Ni kam ban tava ganin yarinyar da
take burge ni a makarantar nan kamar ta ba.”
Faisal ya harare shi, “Ai kai da ma ungulu ne
ba ka tarar nama, yanzu ba qaramin abu ba ne a
wurin ka ka lallava wurin ta don ka kashe
gobara.”
Nasiru ya jinjina kai, “Ko kaxan ni ba nufi na
ke nan ba, amma kai kanka ka san irin matan da
nake kulawa, Bilkisu ba ta cikin ‘yan matan da
zan yaudara kawai dai Beb xin ce tana burge ni
saboda ga ta gentle shiru-shiru da ita. Ko ka tava
ganin abokin faxan ta?”
Abbas ya gyaxa kai, “Ni ma ban ga wani aibu
tare da ita ba, amma tun da kai ka yaba Nasiru me
zai hana ka shiga?”
“Ya shiga ina?” Faisal ya tari maganar, “ai
wallahi ya kuskura ya fara mu’amala da ita zan
raba gari da shi.”
“To sai me?” Nasiru ya amsa, “kana zaton ina
jin tsoron ka ne da akan abin da nake so zan ji
tsoron mu rabu?”
Faisal ya xan yi shiru yana jinjina
maganganun Nasiru a ransa, tabbas Nasiru ne
amininsa na sirri a makarantar haka kuma tare
suke yin duk wata harqalla da ta shafi rashin
gaskiya, kama daga shaye-shaye zuwa neman ‘yan

Gawa ta qi rami
40 A.M. Xanzaki

mata, yawon kulab da bin gidajen caca
musamman na zamani, bugu da qari Nasiru ya san
sirrin gidan su Faisal kamar yadda Faisal ya san
sirrin gidan su Nasiru kasancewar unguwarsu
xaya. A halayya ne kawai suka samu xan
bambanci, Nasiru na da sassauqan ra’ayi akan
mata haka kuma ba ya tarar budurwa ko ‘yar gidan
talaka ce yayin da Faisal sai ya tsefe ya taje ya
kitse yake neman mace, Nasiru na da dabarun
yaudara a voye yayin da Faisal ke fitowa varo-
varo ya bayyana ra’ayinsa.
Idan kuwa haka ne lallai akawi buqatar Faisal
ya bi a hankali wajen raba yarinyar nan da
abokinsa ba tare da sun samu savani ba, domin
alaqar sa da ita ba komai zai ja wa Faisal ba sai
kusanci da yarinyar, shi kuwa ko za a yi yaqin
duniya na uku, kai ko cutar Corona za ta dawo ba
zai bari haka ta faru ba.
Nasiru ya miqe tsaye yana kallon su Bilkisu
yayin da ya ga sun miqe za su tafi aji kasancewar
lokacin komawa ya kusa.
“Ba dai tun yanzu za ka fara gwada
makaminka ba?” Abbas ya tambaye shi.
“To kai me ya shafe ka?” Nasiru ya mai da
masa tambaya da tambaya.

Gawa ta qi rami
41 A.M. Xanzaki

“Amma ba ka ganin tare take da qawayenta?
Kada fa ta dizga ka.”
“To ni me ya shafe ni da qawayenta? Ita nake
ra’ayin yi wa magana.”
Faisal ya kalli Nasiru, “Qyale shi ya je, ina
tsammanin Alqiyamarsa ce ta kusa tsayawa.”
Nasiru ya gyara tsayuwa ya saka hannu a
aljihu, “Alqiyamar kowa ma sai ta tsaya in dai
akan Bilkisu ce.”
Ya nufi wurin ta kai tsaye yayin da abokansa
suka bi shi da kallo.
“Da gaske yake fa,” Abbas ya tabbatar.
“Kai don Allah qyale shi, ya je ya yi idan tusa
za ta hura wuta za mu gani,” cewar Faisal.
Abbas ya kalli Faisal, “Wai me ya sa ba ka
son yarinyar nan ne?”
Faisal ya kalle shi kawai, “Ra’ayina ne haka,
kuma ko da babu dalili ina da damar na so wanda
na so a lokacin da na so ko da zuciyar wani ba ta
so.”
***
A kan hanya kuma a cikin babur mai qafa uku
yayin da suke komawa gida Hanne ta kalli Bilkisu,
“Wai me ya haxa ki da wannan Nasirun xazu har
muka koma aji na ga kun daxe kuna magana?”

Gawa ta qi rami
42 A.M. Xanzaki

Bilkisu ta kalli waje ta qofa ta murguxa baki,
“Wata magana yake yi min wai yana so ya san
gidanmu zai dinga zuwa muna gaisawa, wai kuma
ba ya gane darasin lissafi sosai.”
Hanne ta yi dariya, “Ki ce ya kamu kawai.”
Bilkisu ta vata rai, “Ya kamu da me?”
“Kawai ki ce kin samu saurayi daga zuwa, ai
idan kika ga namiji yana yawan kallon ki to da
walakin. Sai dai ban ji daxin yadda yake so ya fara
zuwa gidanmu ba.”
Bilkisu ta ce, Saboda me?”
Hanne ta riqe baki, “Tab! Mama fa ta ce kada
mu sanar da kowa gidanmu ko mu qulla hulxa da
wani har mu ba shi adireshinmu. Ina fata ba ki
gaya masa ba.”
Bilkisu ta kalli Hanne kawai.
***
Qarar wayar sadarwa ta tashi Hajiya Abu
daga barci, ta buxe idanuwanta waxanda suka
sauqa akan agogon bango da ke fuskantar gadon
da take kwance, agogon ya nuna qarfe xaya da
rabi na rana, sannan idanuwan nata suka yi
bulaguro zuwa kan wayarta da ke ta faman ruri a
gefen matashin da ta ta da kai da shi.
Ta sa hannu ta xauki wayar ta duba sannan
kamar wadda aka tsikara sai ta tashi zaune zumbur

Gawa ta qi rami
43 A.M. Xanzaki

ta sake qurawa fuskar wayar idanu kamar ba ta
shaida abin da ta gani a kan allon gilashin wayar
ba.
Ta xauki wayar ta kai kunnenta tana share
fuskarta da xaya hannun.
“Hello Hajiya Hindu, yaya na ga kin kira ni
da lambar Najeriya, kada dai a ce kin dawo?”
Daga xaya vangaren aka amsa mata, “Na
dawo Hajiya, mhm! Ke dai bari akwai labari. Kina
ina ne in zo in same ki?”
“Don Allah kada ki ce min ke ma kamo ki aka
yi?” cewar Hajiya Abu.
“Na daxe da samun labarin abin da ya faru da
ke a wurin Hajiyar Birni, muna cikin yunqurin
nema wa kanmu mafita abin ya ritsa da mu.”
Hajiya Abu ta miqe zaune cike da mamaki,
“Kada dai ki ce ita ma an kamo ta.”
“Tare muka dawo. Jiya-jiyan nan jirginmu ya
sauqa, ke dai ki bari na zo ki sha labari. Kina ina
ne?”
Hajiya Abu ta xan yi tunani, “Sai dai mu yi
wata mahaxa guda xaya mu haxu a can.”
“To shikenan na gane manufar ki, ni ma akan
wannan qadamin nake. A ina za mu haxu?”
“Kin san gafiya ba ta da wurin vuya da ya
wuce ramin ta,” cewar Hajiya Abu.

Gawa ta qi rami
44 A.M. Xanzaki

“To shikenan na gane, sai ki sa mana lokaci.’
Hajiya Abu ta xan yi tunani, “Gobe da
yamma gab da Magriba.”
“Allah Ya kai mu,” daga nan suka kashe
wayoyinsu.
Hajiya Abu ta yi ajiyar zuciya ta fara qoqarin
lalubo wata lamba ta same ta ta kira, har ta katse
ba a xaga ba. Ta sake kira, wayar ta qaraci vurarin
ta ba a xaga ba. ta yi jifa da wayar kan gado.
“Wai me yake damun Hajiya Tabawa ne? Da
zafi-zafi fa akan bugi qarfe.”
A daidai lokacin ne kuma su Bilkisu suka yi
sallama suka shigo xakin nata.
Ta miqe tsaye tana kallon su, “Yaya na ga
yau kamar kun daxe?”
“Babur xin ne ya xan ba da matsala,” in ji
Bilkisu.
“Bari in shiga wanka in fito, akwai abinci a
kicin sai ku zuba ku ci.”
Ta nufi banxaki tana zancen zuci, ya dai
kamata na sayi mota ko ‘yar qarama ce saboda
zirga-zirgar tana nema ta yi yawa, ga matsalolin
yau da kullum.’
Mintuna kaxan ta fito daga wanka ta yi
kwalliya ta canza tufafi sannan ta xauki wayarta ta
sake kiran lambar Hajiya Tabawa, ta saurara har

Gawa ta qi rami
45 A.M. Xanzaki

wayarta ta gama kwarmaton shigar kira sannan ta
katse.
Ta yi tsaki ta ajiye wayar ta shiga tunani.
Zuwa jimawa wayar tata ta fara yin qarar amsar
saqo ta xauka ta saka a kunne.
“Hello Hajiya Tabawa wanne irin abu ne
wannan ina kiran ki ba za ki xaga ba?”
Hajiya Tabawa ta amsa daga can vangaren,
“Ki yi haquri Alhaji yana gida ne shi ya sa kuma
wayar tana silent, yanzun nan ya fita wallahi.”
“Ko da na ji, xazun nan na yi waya da Hajiya
Hindu take gaya mini cewa ta dawo daga
Saudiyya ita ma.”
“Mun shiga uku! Ta yaya za mu iya warware
matsalar nan ne?”
“Wallahi ba ki ga yadda na shiga ximuwa ba
da ta sanar da ni abin da ya faru,” in ji Hajiya
Abu.
“Ya kamata mu haxu a yi abin da ya kamata
kada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login