Showing 9001 words to 12000 words out of 39022 words

Chapter 4 - Gawa Taki Rami Book Complete Writing By Ayuba Muhammad Danzaki.pdf

mu tsaya kallon ruwa kwaxo ya yi mana
qafa,” cewar Hajiya Tabawa.
“Abin da ni ma na gani ke nan, tuni na shirya
mana haxuwa a gobe ko za ki samu damar zuwa?”
Hajiya Abu ta tambaya.
Hajiya Tabawa ta xan yi shiru daga xaya
vangaren kafin ta ce; “Gaskiya kin san idan Alhaji

Gawa ta qi rami
46 A.M. Xanzaki

yana gari bana son yawace-yawacen nan, amma
kwanan nan zai koma domin kin san zave ya
gabato a irin wannan lokacin kuwa idan ya lula ya
tafi yawon yaqin neman zave sai Baba ta gani, ku
dai yi abin da ya kamata.”
“To shikenan babu matsala, za ki ji ni ko ta
whatssap ne.”
Ta kashe wayar sannan ta kishingixa bisa
kujera tana tunanin matakin da ya kamata ta xauka
don gudun yin kitso da kwarkwata.
***
Tana sanye da shadda shuxiya mai duhu da
tabarau fari, a halin yanzu tana zaune a barandar
falon gidan mijinta da ke saman benen gidan bisa
farar kujerar roba tana duba na’urarta mai
qwaqwalwa.
A hankali siririn hannunta ya kai kan
mavallan na’ura mai qwaqwalwar sannan ta
lalubo abin da take nema ta ci gaba da latsawa
tana nazarin wani qaton hoton Fara da ke kan
allon na’urar sannan ta xauko biro da takarda ta yi
rubutu ta ajiye a gefe.
Agogon allon na’urar ya nuna qarfe huxu da
rabi na yamma.
Daga inda take tana iya hangen farar qaramar
motar da ta shigo gidan bayan maigadi ya buxe

Gawa ta qi rami
47 A.M. Xanzaki

mata qofa, ta shaida motar amma sai ta kanne ta ci
gaba da kallon ta daga saman benen.
Motar ta tsaya a rumfar da aka tanada don
adana motoci sannan aka xan yi jinkiri kafin qofar
motar ta buxe.
Wata baqar mace mai ‘yar qiba ta fito daga
motar tana sanye da atamfa shuxiya mai duhu
xinkin riga da siket, ta yafa wani siririn gyale fari
wanda za a ce da shi gara babu, ita ma kamar
Zahira akwai tabarau a fuskarta sai dai baqi ne,
kanta akwai xankwali kalar atamfar sai kuma wani
takalmi mai tudun dunduniya ta ratayo wata jaka
baqa tana taunar cingam. Akwai babbar waya a
hannunta kamfanin Ipad mai faxin gaske.
Zahira ta qura wa budurwar ido tana qare
mata kallo daga sama har qasa, kamar an ce ta
xaga kanta sai budurwar ta xago kai ta kalli saman
barandar benen, wataqila idonta ne ya ba ta ana
kallon ta. Murmushi ya suvuce a levvanta sannan
kamar wasa sai ta xaure fuska.
Zahira ta kawar da kai ta ci gaba da danna
na’ura mai qwaqwalwarta, idan har ta ji daxin
zuwan baquwar tata to fuskarta ba ta nuna ba.
Bayan giftawar wasu daqiqu masu auki sai
baquwar ta fito ta bayan Zahira da ke zaune
wanda hakan ya nuna ta san gidan ciki da bai.

Gawa ta qi rami
48 A.M. Xanzaki

Zahira ba ta waiga ba kamar yadda baquwar
ba ta ce komai ba sai kawai ta ja kujera ta zauna ta
saka hannu a jaka ta xauko cingam guda huxu ta
vare biyu ta jefa a baki ta xora biyu a kan na’urar
da ke gaban Zahira ta ci gaba da tauna tana kallon
ta.
Zahira ta yi ajiyar zuciya ta ture na’urar gefe
ta cire farin tabaran fuskarta ta kalli baquwar tata,
“Alawiyya yaya ake ciki ne? Ai na daxe a nan ina
jiran ki.”
“Kina jira na ko kina sana’ar taki da kika
saba?” in ji baquwar da aka kira Alawiyya.
“Yanzu dai mu ture batun wasa, wata matsala
ce nake so mu tattauna da take damu na.”
Alawiyya ta jawo na’urar ta fara dubawa.
Zahira ta kalli na’urar sannan ta kalli
Alawiyya, “Wato al’amarin tsohuwar matar Alhaji
ne yake damu na.”
Alawiyya ta tura na’urar da sauri gaban
Zahira ta cire tabaran fuskarta, “What? Yake
damun ki kamar yaya? Ba ta riga ta mutu ba, ko
dawowa ta yi?”
Zahira ta yamutsa fuska, “A wurinmu ne ta
mutu ko in ce a wurin kowa amma ban da wurin
sa, kullum ba shi da aiki in ya dawo daga nema

Gawa ta qi rami
49 A.M. Xanzaki

face ya zauna yana kallon hoton ta, abin ya zame
masa tamkar wazifa.”
“To ke mece ce matsalar ki da hakan? Sanin
kan ki ne wanda ya mutu ba zai dawo ba, kuma ko
ba jima ko ba daxe zai daina tuna ta, yau da gobe
fa ta fi qarfin wasa.”
Zahira ta tashi tsaye ta je kusa da makarin
qarfe da ke barandar benen ta sa hannu ta riqe
makarin barandar tana kallon qasa, “Ba zai daina
ba Alawiyya, sam ba zai daina ba, da a ce zai
daina tun shekara xaya da ta wuce ya bari, ki tuna
fa tun yana yi a voye har ya bayyana savon nasa,
yanzu qarara yake fitowa yana yi, na yi qoqarin
taka masa burki amma ya qure maleji.”
Alawiyya ta bi ta da kallo kawai yayin da take
waxannan jawaban, a hankali kuma sai ta taso ta
zo kusa da qawarta ita ma ta dafa makarin qarfen
tana kallon qasa kamar qawarta, ba tare da ta kalle
ta ba ta ce; “Yanzu mene ne takamaimai dalilin
kira na da kika yi?”
Zahira ta juyo ta fuskance ta sosai, “Yauwa
shawara za ki ba ni domin ina tunanin game da
matar nan ta Alhaji akwai lauje cikin naxi
Alawiyya, don me Alhaji zai damu da ita haka?”
Alawiyya ta tuntsure da dariya har ta fara ba
wa Zahira haushi.

Gawa ta qi rami
50 A.M. Xanzaki

“Ni fa shawara na kira ki ki ba ni ba raina
mini hankali da dariyar ki maras daxi ba.”
Alawiyya ta yi magana ba tare da ta gimtse
dariyar tata ba, domin kalaman tan a yanzu sun
fito tare da dariyar ne kafin kalaman su haxiye
dariyar, “Qawata ki ce kishi kawai kike yi, ai da
kin gaya mini haka da na taho miki da manta-
uwa,”
Zahira ta komar da kanta tana kallon tsakar
gidan ta hanyar dafa makarin barandar, “Na ga
alama wasa kika xauki maganar, domin ba ki
hango abin da na hango ba.”
Alawiyya ta goge qwalla daga idonta, “To ai
ke ce da abin mamaki, ki tafi kai tsaye ga topic kin
tsaya kina gwalangwason magana. Me kike tunani
ne?”
Zahira ta kalle ta, “Akwai wani voyayyen
dalili da ya sa Alhaji yake nanata kallon hoton nan
kullum, dalilin nake so a binciko min?”
“Me kike nufi?”
“Ina nufin a binciko min asalin wace ce ita a
ina ta rayu kuma a ina ta mutu, ina son bayanin
rayuwar ta da duk mutanen da suka taka rawa a
cikin ta.”
Alawiyya ta ja baya, “Wonderful! Na ga
alama kin fara samun matsala qawata. Da gawar

Gawa ta qi rami
51 A.M. Xanzaki

za ki yi kishi? Duk me ya kawo maganar a nemo
bayanai a kanta haka? Raya ta za ki yi ko litttafin
rayuwarta za ki rubuta? Don Allah mu bar
maganar nan daga ni sai ke domin wani zai yi
tsammanin tavuwa kika yi.”
Zahira ta girgiza kai, “Ba za ki gane ba amma
in lokacin ya yi za ki gane, ina zargin akwai
kitimurmura game da mutuwar matar nan tasa, ba
mutuwar Allah da Annabi ba ce.”
“To ke ina ruwan ki.”
“Da ruwana har da tsakina, kin manta ban
auri Alhaji ba sai don na mori abubuwa da yawa a
tare da shi? Kuma mafi yawan dukiyarsa tana
hannunta kafin ta bar duniya. Ke dai in za ki yi
min aiki kawai ki yi min, domin da ta tashi
mutuwa ba ita kaxai ta mutu ba, ta tafi lahira da
dukiyar Alhaji mai ximbin yawa.”
Alawiyya ta fara yi wa Zahira wani irin kallo,
“Me hakan ke nufi?”
Zahira ta yi murmushi, “Zauna in ba ki labari,
abokin cin mushe ai ba a voye masa wuqa.”
***
Rana ta sunkuya qasa sosai wanda hakan ke
nuna alamar farkon shigar dare. Mafi yawan
mutane a wannan lokaci sun dawo daga harkokin
su, waxansu suna kan hanyar zuwa gida yayin da

Gawa ta qi rami
52 A.M. Xanzaki

wasu suka isa gida tuntuni. Waxansu kuwa da
wataqila bariki suka saka a gaba sun zarce
wuraren shaqatawa suna sharholiyar su. Kamar
sauran wuraren shaqatawa da ke birnin Kano inda
ta zama matattarar ‘yan birni da Alhazai gami da
qadangarun bariki wanda aka fi kira da Central
Hotel wani babur mai qafa uku xauke da wata
mata ya tsaya a gefen titi kusa da wurin.
Wata mata kakkaura fara mai xan tsawo da
kyawun fuska da jiki sanye da doguwar shuxiyar
riga har qasa, baqar safar hannu da qafa sannan
da baqin niqabi ta fito daga babur xin, ba tare da
ta yi magana da mai babur xin ba sai ta miqa masa
kuxinsa ya shiga laluben canji amma sai ta yi
masa alama da ya riqe canjin, ya yi kwana cike da
farin ciki ya bar wurin.
Matar ta janye niqabin wanda ya bayyanar da
idanunta kaxai sannan ta fara raba idanuwa tana
qarewa mutanen wurin kallo. Idanuwanta suka
qare a kan wani faffaxan teburin roba inda wata
mata ke zaune ita ma sanye da kaya kamar nata sai
dai ita fuskarta a buxe take in ban da takunkumi
(face mask) da ta sakawa fuskar tata. Akwai lemo
a gabanta da kofuna guda biyu sannan da
tafkekiyar jakarta bisa teburin gami da wayoyinta

Gawa ta qi rami
53 A.M. Xanzaki

guda biyu babba da qarama. Kujera guda tana
fuskantar ta ba tare da kowa a kan ta ba.
Kai tsaye wurin ta matar da ta sauqa a babur
ta taho fuskarta ba yabo ba fallasa.
Har ta qaraso suna qarewa juna kallo daga
nesa, ga alama akwai daxaxxiyar sanayya a
tsakanin su kuma da ganin su ka san an daxe ba a
haxu ba.
Sallama ta yi sannan ta zauna bisa kujerar da
ke fuskantar matar sannan a hankali sai ta yaye
niqabin suka haxa idanu. Murmushi ya suvuce a
fuskokinsu.
“Ko ke fa Hajjaju, amma da kin lulluve fuska
tamkar buzuwa,” cewar matar da aka tarar a
zaune.
Hajiya Abu ta gyara zama, “Ke ma dai Hajiya
Hindu ai kin san babu yadda na iya ne, abin ne sai
da iya-taku idan ba haka ba sai ta kwave maka, ai
tamkar bariki ce da aka ce alalen gero ce.”
“Me kike so a kawo miki na sha?” Hajiya
Hindu ta kawar da zancen.
Hajiya Abu ta fito da madaidaiciyar jakarta da
ke cikin doguwar baqar rigarta ta ajiye a kan
teburin sannan ta xauko wayarta ta fara dannawa
sannan ta xaga wa Hajiya Hindu yatsa xaya,
“Ruwa kawai.”

Gawa ta qi rami
54 A.M. Xanzaki

Hajiya Hindu ta kira mai kula da baqi ya
kawo musu ruwan roba mai sanyi ya ajiye, Hajiya
Hindu ta biya shi kuxi ya karva ya juya ya tafi.
Hajiya Abu ta ajiye wayarta ta tsiyaya ruwa a
kofi ta kurva sannan ta kalli Hajiya Hindu ta ce;
“Ina sauraren ki, kika ce Hajiyar Birni ma tare
kuka dawo?”
“Qwarai kuwa, ai an sha taqaddama da mu
kafin su yi nasarar kama mu, kin san muna
Sharamansoor suka yi mana dirar mikiya,
askarawa ne sun fi mutum talatin suka abka mana,
da qyar Alhaji Audu Xangwal ya sha.”
Hajiya Abu ta yi shiru tana sauraren labari
daga qawarta, har zuwa sadda qawar tata ta yi
shiru.
Hajiya Abu ta kalle ta, “Gaskiya akwai
babbar matsala, akwai fa matsala Hajiya Hindu.
Kadarorina da kuxaxena da suke hannun jama’a
nake ji, ga shi yanzu amana ta yi qaranci. Na
tabbata tun da Hajiyar Birni ta dawo wallahi ta
gama kwave mana, wai malaman ta ba su duba
mata taurarinta ba ne wannan karon da har ta yi
sake haka ta same ta?”
Hajiya Hindu ta yi hucin takaici, “Ni ma ban
sani ba, kin san Malam Xangaske da ke yi mata
aiki daga nan ya rasu, yanzu xansa ne ya gaje shi

Gawa ta qi rami
55 A.M. Xanzaki

kin san kuwa Hausawa na cewa Magaji magajiyi.
Nisan aikinsa da Malam Xangaske akwai tazara
sosai.”
Suka xan yi shiru ba tare da wata ta yi
magana a cikinsu ba har zuwa sadda Hajiya Hindu
ta buxe baki, “Amma ina da wata mafita guda
xaya, mu ganganxa mu san yadda za mu yi mu
koma ko da ta kama mu sayar da filaye da
gidajenmu ne.”
Hajiya Abu ta girgiza kai, “Sam wannan ba
mafita ba ce, ina zan kai ‘ya’yana yanzu? Na
gama yi musu tanadi, so nake sai sun zama
mutane sosai in kwashe su mu koma can. Ba zan
iya barin Hanne da Bilkisu a nan babu mai kula da
su ba.”
Hajiya Hindu ta xan yi tunani kafin ta ce, “E,
kina da gaskiyar ki a nan, amma ta yaya dukiyar
da kike tunqaho da ita za ta dawo hannunki cikin
salama? Kina da wani amintacce ne?”
“Ba ga ki ba,” in ji Hajiya Abu.
“Ni kuma?” Hajiya Hindu ta tambaya da
mamaki, “a’a ki canza shawara amma ba wai na qi
ba ne, sai don sanin harka irin taku sai ku, ni
yaushe zan iya?”
Hajiya Abu ta yi dariya, “Haba, kada ki ba da
mata mana tawan, lamuran nawa fa sai da ke, zan

Gawa ta qi rami
56 A.M. Xanzaki

yi miki bayanin yadda komai yake filla-filla, in
Shaa Allahu ma ba za a samu matsala ba, zan yi
miki komai na aiki ki koma, na yi miki alqawarin
kina da kaso ashirin a cikin ribar da na samu.”
Hajiya Hindu ta yi shiru tana tunani. Kaso
ashirin fa kuxi ne masu yawa musamman idan aka
yi la’akari da tarin dukiyar da Hajiya Abu ta tara.
“Ko in bar ki ki yi shawara?” Hajiya Abu ta
katse mata tunani.
Hajiya Hindu ta xauki ruwa ta kurva ta ce;
“Da dai ya fi.”

Gawa ta qi rami
57 A.M. Xanzaki


_____________BABI NA 3_____________
l’amura sun ci gaba da tafiya a
makarantar share fagen shiga jami’a ta
Kano (C.A.S.) kamar yadda suka fara
ga rayuwar Bilkisu da Hanne. Nasiru ya ci gaba da
bibiyar rayuwar Bilkisu wadda da kanta ta fahimci
son ta yake yi amma ya kasa furta mata.
Yau ma kamar kullum misalin qarfe goma na
safe bayan sun fito daga laccar farko suna zaune
bisa wata kujerar sumunti da aka tanada don
zaman xalibai da yin nazari a qarqashin wata
bishiya.
Nasiru sanye da kot baqa mai haxe da
falmaran da maxaurin wuya yana duba wani littafi
da biro a hannunsa yayin da Bilkisu ke zaune
kusa da shi tana nazarin wani littafi. Lokaci-lokaci
yakan xago kai ya kalle ta ya tambaye ta wani abu
ita kuma ta yi masa qarin bayani.
A haka suka daxe kafin lokacin da A’isha ta
zo ta same su, “Bilkisu an zo neman ki.”
Ta xago kai da sauri tana kallon qanwar tata,
“Wane ne ya zo nema na?”
Nasiru ya dakata da karatu yana qarewa
A’isha kallo.
A

Gawa ta qi rami
58 A.M. Xanzaki

A’isha ta kalle shi ta kau da kai, “Wani ne a
mota.”
Bilkisu ta tashi da sauri ta bi bayan A’isha
bayan ta ce wa Nasiru, “Ka jira ni kaxan ina
zuwa.”
Sai da suka fara tafiya sannan Bilkisu ta kalli
A’isha, “Me ya sa kika daxe haka? Wallahi har na
qagaita na bar wurin, ni kuma bana so na yi masa
abin da zai ji kamar na yi masa wulaqanci, qiris ya
rage na yi tsuntsuwa na tashi.”
“Ai kuwa da na ara miki fukafukina, domin
babu amfanin da zan yi da su, domin tsuntsun
soyayyata da ya sauqa a sheqar Bashir babu ta
yadda za a yi ya tashi.”
Bilkisu ta harare ta, “Shi ne ya zo ke nan shi
ya sa kika shanya ni.”
“To a tsammanin ki shugaban qasa ne zai zo
na tsaya kallon sa idan ba Bashir ba? Ai tun da ya
zo muka dasa hira sai da ya tambaye ni kina ina
sannan na tuna kin ce da zarar kin yi minti goma
da Nasiru na zo na kira ki, yanzu ma zuwa za mu
yi ki gaisa da shi.”
Bilkisu ta samu Bashir mai fara’a da
barkwanci yana da daxin hira, a haka suka
tattauna batutuwa da dama. A qarshe ya xauko
wata leda ya ba wa Bilkisu kyauta,

Gawa ta qi rami
59 A.M. Xanzaki

“Ga wannan don Allah a ci gaba da yi mini yaqin
neman zave.”
Bilkisu ta yi murmushi, “Ai ka gama cin garin
da yaqi, kai dai ka saki ingarmanka ka yi ta
sukuwa a filin yaqin babu kowa sai kai kaxai.”
Bashir ya yi dariyar jin daxin kalaman ta suka
yi sallama ya hau motarsa ya tafi.
Bashir Isa matashin xan kasuwa ne da ke
neman auren A’isha, domin a gidan su A’ishar ma
an san da maganar sa kuma har an kai kuxi, yana
harkar shigo da kaya ne da fita da su a qasashen
qetare (import and export) mafi yawan harkar sa a
qasar Dubai ne. ya mallaki dukiya da kadarori
masu yawa haka kuma ya san manyan mutane
kama daga kan ‘yan siyasa zuwa kan jami’an
gwamnati masu riqe da madafun iko. Akwai
abokinsa a makarantar su A’isha wanda yake a
matsayin malami, kuma da qarfafar gwiwarsa ne
Bashir ke samun shiga makarantar a duk sadda ya
buqaci ganin A’isha idan ba haka ba kuma yakan
kai mata ziyara har gida musamman ranar Juma’a
da yamma.
A lokacin da su Bilkisu ke qoqarin komawa
aji a wani vangare na makarantar Nasiru ne a
zaune ya yi tagumi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login