Showing 3001 words to 6000 words out of 39022 words
Chapter 2 - Gawa Taki Rami Book Complete Writing By Ayuba Muhammad Danzaki.pdf
tsarabar bagaruwa da dabinon makka
wanda ta saya a masauqin alhazai na Kano (Hajj
Gawa ta qi rami
17 A.M. Xanzaki
camp) wani lokaci takan ba wa maza jallabiya da
hula tashi-ka-faye-naci, mata kuma ta ba su
haqoran makka da sauran kayan kwalliya da suka
shafe su.
Zuwa yamma aka bar ta ta sarara, a kuma
wannan lokacin ne ta samu sararin ganawa da ‘ya
‘yanta Bilkisu da Hanne.
Bilkisu ce babba haka kuma shekarunta
ashirin da biyu daidai yayin da Hanne ta kasance
qarama, mai shekaru goma sha takwas. Bayan hira
da tambayar yadda ta bar su sai ta sanar da su abin
da ke tafe da ita a wannan lokacin.
“Shiryawa za ku yi mu tafi birni, domin zuwa
na yi na koma da ku.”
Bilkisu ta kalle ta, “Umma a wannan
lokacin?”
“Qwarai kuwa mai sunan Mama ko ba ki son
komawa ne? Ai da ma na kawo ku ne domin
rayuwa na xan wani lokaci domin barin ku a nan
haxari ne matuqa ina jiye muku sharrin sa ne.”
“To kuma yaya za mu yi da karatunmu?”
Hanne ce ta yi wannan tambayar.
“Akwai makaranta da zan saka ku a can ku ci
gaba da karatu, sai dai ina son ku sani, bana son
kowa ya san inda kuke a can, domin unguwar da
Gawa ta qi rami
18 A.M. Xanzaki
na zava muku ina buqatar ku yi voyayyiyar
rayuwa ne, na sayi gida da dawowa ta.”
Gaba xayansu suka cika da farin cikin abin da
mahaifiyarsu ta faxa, domin da ma suna fama da
tsangwamar mutanen garin ‘yan gaza-gani (da ma
maganar da ake yaxawa a garin ana cewa
dukkansu shegu ne, mahaifiyarsu ce ta je birni ta
yi cikin shege ta haife su, shi ne ta kawo su qauye
ta ajiye su) yana matuqar qona musu rai.
Hanne ta kalli mahaifiyarsu Hajiya Abu,
“Umma na ji xazu kin ce kina jiye mana sharrinsa,
wane ne?”
Hajiya Abu ta yi wani guntun murmushi mai
kama da yaqe, “Ku bar maganar kawai, idan
lokacin ku sani ya yi za ku sani.”
Bilkisu ta ce, “Wane ne mahaifin namu?”
Hajiya Abu ta vata rai, “Ban cika son yawaita
tambayoyi ba, ko me kuke son sani ku bari idan
mun koma birni, zan yi muku bayani,”
Xakin ya yi shiru na xan wani lokaci sannan
Hanne ta kalli Hajiya Abu.
“Umma yaushe za mu koma?”
*********
Cikin dare yayin da sahu ya xauke a faxin
qauyen ba ka jin komai sai kukan gyare da sauran
qwarin da ke fitowa da daddare, akwai alamun
Gawa ta qi rami
19 A.M. Xanzaki
hasken farin wata da ke nuna cewa watan ya yi
nisa a lissafin kwanakinsa, haka kuma ragowar
hasken nasa da ya maqale a sararin Subhana shi ne
yake haska garin sama-sama.
Hajiya Abu ta miqe zaune a kan tsohon gadon
katakon da aka ba ta gami da wata tsohuwar
yamusasshiyar katifa wadda ta ji jiki, ko kaxan ba
ta jin daxin kwanciya a kan gadon, ta saba
kwanciya a katifar da ta fi wannan laushi haka
kuma da isasshen wurin da za ta yi ta mirgin-
mirgin ba irin wannan gadon mai kama da makara
ba. Tun da ta kwanta bayan mutane sun sarara
mata sannan bayan ta gama ganawa da manyan
‘ya yanta ta kasa barci sai juye-juye take yi kamar
wadda kuxin cizo ke ciza.
A karo na barkatai ta duba agogon gwal xin
da ke hannunta siriri, wanda ya sha adon zaiba;
qarfe xaya na dare. Yanzu ne ya kamata ta yi
magana da Tanko kamar yadda ta shaida masa ya
zo ya same ta a qofar gidan da qarfe xaya na dare.
Ta miqe tsaye sannan ta kalli xakin daga
bango zuwa wani bangon, ginin xakin da aka yi
wa yave da sumunti aka qaga masa ‘yar taga daga
can saman xakin kusa da qofa babu komai a
cikinsa in ka xauke motsattsen gadon da take kai
da kuma wata tsohuwar randa da aka cika da
Gawa ta qi rami
20 A.M. Xanzaki
ruwan daxi xazu sai kuma wani tsohon teburi da
babu komai a kan sa sai akwatin da ta dawo da ita
wanda ya qunshi suturunta na sakawa da sauran
kayayyakinta. Ta dubi daven xakin ta hanyar
haskawa da siririyar tocilan xin da ke hannunta,
daven xakin ya fara rumurmushewa, mai yiwuwa
ba a yi shi da ingantaccen sumunti ba.
Ta matsa kusa da qofa ta kama ta ja a hankali,
qofar ta langa-lamga ce da aka yi wa da’ira da
katako mai qarfi, ta leqo waje, sai da ta tabbatar
babu kowa a tsakar gidan mai matuqar faxi
sannan ta sa qafa ta fito a hankali, sannan kamar
wadda aka yi wa allura sai ta nufi qofar gidan da
sassarfa.
Qofar gidan ba ta ba ta wahala wajen buxewa
ba musamman da ta kula dutse kawai aka sa aka
kare domin sakatar ta lalace, sannan ta fito waje ta
nufi gindin bishiyar mainar da suka yi alqawarin
haxuwa da Tanko.
Ta daxe a tsaye, duk mintuna biyu sai ta duba
agogo sannan ta fara hango duhu-duhun mutum
yana tunkaro inda take, ta tabbata Tanko ne don
haka ta gyara tsayuwa tana sauraro.
Matashin ya qaraso inda take saida ya
tabbatar ya shaida ta sannan ya gaishe ta.
“Barka da dare Hajiya,” ya faxa qasa-qasa.
Gawa ta qi rami
21 A.M. Xanzaki
“Yaya aka yi ka vata lokaci haka? Ka san ba
zama na zo yi a garin nan ba.”
Tun kafin ya yi magana sai ta sake kallon sa,
“Shige mu je.”
Tanko ya shige gaba zungui-zungui kamar
mai raka amarya suka doshi bayan garin a tare.
Bayan aqalla tafiyar yadi arba’in sai suka isa
gindin wata tsohuwar bishiyar kuka. Tanko ya
tsuguna qarqashin bishiyar ya ciro wani xan buda
daga aljihunsa ya fara haqar rami.
Tsawon mintuna yana haqa ita kuma tana
tsaye tana kallon sa tare da haska masa da siririyar
fitilar da ke hannun ta ba tare da wani ya yi
magana a cikinsu ba.
Tanko ya xago da sauri ya kalle ta, fuskarsa
duk ta yi sharkaf da gumi.
“Ha… Hajiya ina ji na manta ramin kamar ba
nan ba ne,” ya miqe tsaye.
Hajiya ta kalle shi sosai, “Sake dubawa dai,
ko dai ba wanan bishiyar ba ce?”
Ya girgiza kai yana share gumi da gwiwar
hannun rigarsa.
Ita ce Hajiya kafin na kawo nan sai da na
tabbatar babu mai tsaurin idon da zai iya zuwa nan
a irin wannan lokacin ballantana ya yi wani abu.”
Gawa ta qi rami
22 A.M. Xanzaki
“Ni ma bana tunanin wani ya zo ya xauka, na
fi zaton mantawa ka yi.”
Tanko ya matsa ya ci gaba da duba wani wuri,
zuwa can sai ya yi murmushi sannan ya yi saurin
xauko xan budansa ya ci gaba da haqa wani wuri.
Zuwa can sai ya xago ya kalle ta yana murmushin
gajiya.
Hajiya ga ajiyar mu nan a nan muka ajiye
ashe,” ya ciro wani qunshi a cikin wata jakar fata
ruwan qasa ya miqa wa Hajiya.
Hajiya ta karva ta buxe ciki, nan take hasken
abubuwan suka haska qarqashin bishiyar kukar
har zuwa kan fuskar Hajiya.
Hajiya ta yi ajiyar zuciya sannan ta kalli
Tanko tare da rungume dukiyarta da hannunta.
“Tabbas ita ce Tanko. Na gode, yanzu sai mu
koma gida ko?”
Tanko da Hajiya suka kamo hanya tinkis-
tinkis suka taho gida.
Har suka isa mararraba babu wanda ya yi wa
wani magana, sai da za su rabu ne Hajiya ta kalle
shi, “Da safe ka zo ina son ganin ka kafin na koma
birni, wannan karon ka zo a idon kowa domin
voye-voye ya qare, tun da na karvi ajiyata, sannan
ina so a daren nan ka manta da waxannan
abubuwan da suka faru har abada.”
Gawa ta qi rami
23 A.M. Xanzaki
Tanko ya gyaxa kai, “Hajiya ai kin yi min
komai a rayuwa, ba kowa ne zai kula da ni ya yi
min abin da kika yi mini ba sai uwa ga xanta.”
***
Da safe Tanko ya zo kamar yadda ta umarce
shi, haka kuma ta yi masa kyautar wasu maqudan
kuxaxe a idon mutane, har wasu suka yi mamakin
dalilin kyautar, duk da cewa ta yi irin wannan
kyautar ga wasu daga cikin dangin ta da
maqwabta na kusa.
Zuwa rana Hajiya ta gama kintsawa, haka
kuma ta tattara ya-nata-ya-nata tare da ‘ya’yanta ta
xebe su suka nufi birni.
Sun sauqa da misalin qarfe huxu na yamma a
unguwar Nassarawa da ke birnin Kano. Sun tarar
da wani mutum lukuti qaqqarfa a tsaye a qofar
gidan yana muzurai daga shi sai ‘yar shara da
bujen wando da kuma hula wadda ya lanqwasa ta
gefe, hular ta sha wahala, ga alama mai ita tsohon
xan dako ne. da ganin mutumin ya fi kama da
tsofaffin ‘yan daban nan da ta qare musu. Wani
lokacin yana da shegen surutu.
Ya durqusa ya gaisa da Hajiya cikin ladabi.
Hajiya ta kalle shi da murmushi, “Jibo ka ga
na daxe ban iso ba ko?
Gawa ta qi rami
24 A.M. Xanzaki
“E Hajiya ai har na yi tsammanin ma ko kin
xaga dawowar ne kamar yadda kika saba.”
Ta girgiza kai, “Ko xaya kawai dai abubuwan
ne ka san sai da ‘yan dabaru,” ta nuna masa su
Hanne da Bilkisu, “ka gan su nan, ‘ya’yana ne
wannan sunanta Bilkisu ita ce babba, wannan
xayar kuma sunanta Hanne ita ce ‘yar autata.
Jibo ya kalle su, Ina kwanan ku?”
Suka amsa. Jibo ya miqa mata curin makullai
sannan Hajiya ta ja musu gora suka shiga gidan.
“An gyara famfon nan kuwa?” ta shiga
tambayar sa, haka suka xan zagaya cikin gidan
tana tambayar sa, shi kuma yana ba ta amsa a inda
ake buqatar amsa inda kuma ake buqatar bayani
sai ya tsaya ya yi mata har suka gama karaxe
gidan gaba xaya daga qarshe suka ya da zango a
babban falon gidan.
Jibo ya xebo musu ruwan sanyi da lemo a
tafkeken firjin gidan ya dire musu a tebur suka sha
suka huta.
“Hajiya in babu wani abu zan iya komawa
aiki na?”
Ta yi ajiyar zuciya, “Za ka iya komawa Jibo,
idan da wani abu zan kira ka.”
Har ya juya ya fara tafiya Hajiya ta kira shi,
“Au ba ka ji ba.”
Gawa ta qi rami
25 A.M. Xanzaki
Ya waiwayo.
“Ai ina jin watan da saura ko?”
Jibo ya tsaya yana sosa qeya, “E Hajiya
amma dai da ina son yin aike qauye domin Innata
tana kwance ba lafiya ga kuma…”
Ta dakatar da shi ta hanyar xaga masa hannu,
“Kada ka damu na san matsalar, in an jima kafin
mu yi barci sai ka zo ka karvi wani abu amma ba a
cikin albashinka ba.”
Jibo ya rusuna, ‘Godiya nake Hajiya Allah Ya
qara nisan kwana. Allah Ya ba ki abin da kike
nema duniya da lahira Allah Ya kawo miji da
gag…”
Hajiya ta daka masa harara wanda hakan ya
sa ya yi waje da sauri har yana tuntuve.
Hajiya ta kalli Bilkisu, “Mu je in nuna muku
xakin kwanan ku.”
Suka miqe kusan a tare suka shiga xakuna
Hajiya tana nuna musu.
“Ke Hanne ga naki nan ke ma Bilkisu ga inda
ya kamata ki dinga kwana nan ba kuma na so na ji
wata fitina.”
Suka tsaya turus!
“Ko kun fi son ku dinga kwana a tare?”
Gawa ta qi rami
26 A.M. Xanzaki
Hanne ta haxe kafaxarta da kanta, “Gaskiya
Mama ni tsoro nake ji, bana so na dinga kwana ni
kaxai.”
Hajiya ta yi murmushi, “To shikenan duka
xaya ne xaya xakin sai ku mayar da shi xakin
ajiyar litattafanku da sauran kayayyakinku.”
Hajiya ta jawo qofar ta kulle ta miqa musu
makullayen xakunan. Yayin da suke dawowa
falon ne Hajiya ke cewa; “Ranar Litinin za ku je
makarantar don a yi muku ganawa (enterview).”
Suka dawo falo da murna suka zauna. Hajiya
ta kira Jibo ta umarce shi da ya tayar da injin ba da
wutar lantarki na gidan.
Ba a jima ba haske ya wadaci gidan, Hajiya ta
xauki linzamin Talabijin da na tashoshin waje ta
kunna musu suka shagala da kallo har aka kira
sallar Magriba.
Bayan idar da sallah Hajiya ta umarci Bilkisu
da ta shiga kicin ta shirya musu abinci.
Bilkisu da taimakon Hajiya suka kammala
girki cikin dabara Hajiya na koyar da ita yadda
ake sarrafa madafi mai gas, ta yi sa’a akwai
qwaqwalwa tare da ita don haka a lokacin qanqani
ta xauke komai.
Bayan kammalawar su da cin abincin dare ne
Hajiya ta kira su taro na gaggawa a falon gidan
Gawa ta qi rami
27 A.M. Xanzaki
inda aka kashe talabijin, Hajiya ta shiga yi musu
bayani game da yadda zaman gidan zai kasance.
“Kada wani a cikinku ya kuskura ya yi wani
abu ba tare da ya tuntuve ni ba kodayaushe ku
zama a qarqashin kulawata. Wannan ne ya sa zan
xauko ‘yar aiki ta zo ta dinga rage muku ayyuka,
bana son hidimar gidan ta shafi karatun ku kun ji
ko?”
Suka amsa.
“Mama yaushe ne babanmu zai zo?” Hanne
ce ta yi wannan tambayar.
Hajiya ta xan yamutsa fuska.
Bilkisu ta kula Hajiya ba ta fiya son a yi mata
maganar mahaifinsu ba don haka sai ta yi qoqarin
sauya akalar zancen, amma duk da haka sai Hajiya
ta ce da Hanne.
Kada ku damu da sanin wane ne mahaifinku
tun yanzu, lallai za ku gan shi wata rana da
idanuwanku. Ina so ku kwantar da hankulanku ku
yi karatu kamar yadda na umarce ku, tun da har na
yi sa’a kun kammala Sakandire xorawa a kai abu
ne mai sauqi. Ilmi shi ne darajar ‘ya mace a
wannan zamanin, na san ba za ku fahimci
maganata yanzu ba amma a hankali za ku gane
azancina saboda abin da babba ya hango yaro ko
Gawa ta qi rami
28 A.M. Xanzaki
ya hau turmi ba zai hango ba, shikenan za ku iya
tafiya ku kwanta da safe za mu yi wata magana.”
Cike da farin cikin zama a sabon waje, sabon
gida, sabon wurin kwana, kai sabuwar rayuwa ma
gaba xaya suka koma xakunan da aka ba su a
matsayin xakunan barcin su.
Sun tarar da komai da xan adam zai buqata na
rayuwa an tanadar musu, tun daga gado na
alfarma, katifa lallausa da matashin kai, banxaki
na zamani da kayan qawa gami da qaramar
akwatin talabijin ta bango qarama.
Nan suka kwanta a kan tangamemen gadon da
zai ci aqalla mutum goma. Ba a jima ba barci ya
kwashe su.
***
A daidai lokacin da Hanne da Bilkisu ke
barci a kan gadonsu Hajiya kuma ta falo tana
danne-dannen waya bayan ta shiga yanar gizo ta
hanyar manhajar whatssap misalin qarfe tara na
dare, a lokacin ma har Jibo ya zo ta sallame shi, a
can wata unguwa kuma a wani gida sannan a wani
tangamemen falo da ya lanqwame wani xakin
barci, a cikin xakin barcin Zahira ce zaune da
na’ura mai qwaqwalwa a gabanta tana latse-latse
tare da kofin shayi a gabanta da wani qaramin
filas.
Gawa ta qi rami
29 A.M. Xanzaki
Zahira doguwa ce siririya fara kyakkyawa,
sai dai sirantar tata ta taimaka wajen ayyana
kyawun fasalin qirar jikinta. Shekarunta Talatin da
takwas. Ko da yaushe ta fi son saka riga da siket
matsattsu na yadin shadda musamman masu duhu
domin suna taimakawa wajen fito da hasken
fatarta. A kullum idanuwanta ba sa rabuwa da
farin tabarau siriri saboda yawan kallon na’ura
mai qwaqwalwa da ta zame mata tamkar ibada a
rayuwarta. Tana da kafiya da naci akan abin da ta
sa a gaba kamar yadda take da qulafuci da nacin
gano abu matuqar ta so gano shi.
Daga can xakinta ta ture na’urarta gefe ta cire
tabarau tana goge fuskarta sannan ta miqe ta nufo
falon inda mijinta ke zaune, domin tana gab da
kwanciya barci domin ta samu damar tashi da
daddare don yin wani bincike na musamman akan
dodon koxi wanda yau makon ta guda da farawa.
Tsayawa ta yi cak tana qarewa Alhaji kallo,
yau ma yana aikin da ya saba, ta tabbata ba zai
daina ba, idan ban da qaddara ma me zai kai ta
auren mutumin da ta yi imanin auren cike-gurbi ya
yi da ita?
A irin wannan lokacin idan ya kammala cin
abinci bayan dawowar sa daga kamfaninsa ba shi
Gawa ta qi rami
30 A.M. Xanzaki
da wani aiki sai kallon hotuna. Allah kaxai Ya san
me yake saqawa a ransa.
Alhaji Haruna Tinqwal ya tava yin aure a
baya ya so matar irin son da bai tava yi wa wata
mace ba. ba ya manta yadda zaman su ya kasance,
tana son sa yana son ta. Sun zauna zaman amana
da soyayya, ya aure ta auren da za a ce ba don
yana da kuxi masu sunan kuxi ba da babu yadda
za a yi ta yarda ta aure shi domin tana da matuqar
kyawun da ya jaza mata farin jini, shi kuma farin
jinin ya tara mata dandazon samarin da kayar da
su sai da qarfin naira. Kuma ita ta yi tasiri har
Alhaji Haruna ya aure ta.
Ba su haihu ba kamar yadda shekarun su biyu
da aure mummunan hatsarin mota ya xauki ranta.
Tun da ta tafi aka matsa wa Alhaji da maganar
aure, bai samu yin auren ba sai bayan shekaru
biyu da yin wafatin ta sannan ya nemi ‘yar wani
abokinsa mai suna Zahira wadda ta kammala
masters amma babu miji.
Zahira ta amince ta auri Alhaji Haruna ne
saboda ganin ba shi da wani magaji qwaqqwara
da zai gaji dukiyarsa sai mahaifiyarsa kaxai da ke
zaune a qauyen Kamaye wadda ta yi fafur ta qi
zaman birni, a cewar ta yahudanci ne taf a zuciyar
Gawa ta qi rami
31 A.M. Xanzaki
mutanen birni, a dole ya gina mata gida a qauyen
ya qawata shi ta ci gaba da rayuwarta a can.
Ta taka