Showing 15001 words to 18000 words out of 39022 words
Chapter 6 - Gawa Taki Rami Book Complete Writing By Ayuba Muhammad Danzaki.pdf
kai, “Ko xaya, ya dai bi ta
wata hanyar ya sani.”
Bilkisu ta musa, “To idan ba ke ba ce yaya
aka yi kika san shi ne ya zo? Hakan na nufin kin
san da zuwansa ke nan,”
Ta girgiza kai, “Ko kaxan, kawai dai rabu da
abin da mutum ke so…”
Bilkisu ta harare ta, “So kuma?”
Gawa ta qi rami
74 A.M. Xanzaki
Hannatu ta juya ta kalli Jibo, “Ka ce masa
tana zuwa.”
“Haka na ce?” Bilkisu ta katse ta.
Jibo ya juya ya nufi qofa yayin da Bilkisu ta
miqe tsaye, “Bari na je na ji da wacce ya zo.”
“Hakan dai ya fi,” cewar Hannatu sannan ta
mayar da kai ga kallon ta ga fim xin yayin da wata
budurwa a fim xin ke bin wani saurayi tana ba shi
haquri bisa laifin da ta yi masa.
Bilkisu ba ta ce komai ba ta xauki mayafi ta
fita.
A can qofar gida ta tarar da Nasiru tare da
Abbas a jikin motar. Nasiru sanye da farar riga
shet mai dogon hannu haxi da wandon jins baqi
kansa akwai hula hana-sallah baqa ya taje sumar
kansa yana murmushi.
Abbas na zaune a kan kujerar motar yayin da
qofar motar ta kasance a buxe yana kaxa
makullan motar. Shi kuma yana sanye da rigar
qwallo mai gajeren hannu gami da farin wando
iyaka qwauri (tiri-kwata) ya sunkuyar da kansa
qasa.
Duk waxannan abubuwa Bilkisu ta kula da su
ne yayin da take qarasowa kusa da su.
Ta yi musu sallama suka amsa mata.
Gawa ta qi rami
75 A.M. Xanzaki
“Ku ne masu nema na?” Ta tambaya.
Nasiru da Abbas suka kalle ta, “Kamar da
qasa, in ji mai ciwon ido,” in ji Nasiru, “ko ba a yi
murna da zuwanmu ba ne?” Ya qarasa maganarsa
da tambaya.
“Baqo babu sallama mugu ne, ya kamata ku
sanar da ni za ku zo, yanzu da a ce kun daki gurbi
yaya za ku yi?”
“Sai mu koma gwiwa a sanyaye, kin ga kuwa
ai dole mu yafewa kanmu,” in ji Abbas.
Ta yi ajiyar zuciya sannan ta tsaya tana
fuskantar su yayin da Abbas ya fito daga motar ya
kulle qofar tare da yin tsayuwar gwamen jaki a
gaban ta.
“In kuma ba a yi maraba da zuwanmu ba mu
koma inda muka fi wayo,” wannan maganar
Abbas ne ya faxe ta.
“Ni dai ba ka ji daga bakina ba,” in ji Bilkisu.
Daga nan suka yi dariya tare kafin shiru ya
maye gurbin dariyar tasu zuwa can Abbas ya nuna
Nasiru ya ce; “Kin ga wanda ya matsa sai mun zo
wurin ki nan, ni niyya ta filin qwallo na nufa ya
roqe ni Allah Annabi na taimaka na rako shi
domin yana da wani muhimmin saqo da yake son
sanar da ke.”
Gawa ta qi rami
76 A.M. Xanzaki
Bilkisu ta yi murmushi ba tare da ta kalle su
ba ta ce; “Ai ya kyauta.”
Daga nan ba ta qara cewa komai ba.
Nasiru da Abbas sun san halin Bilkisu na
wajen rashin son yin magana ko kuma miskilanci
don haka sai suka qi kawaita ga shirun ta.
“Kada fa ki ce mun kawo miki ziyara babu
sanarwa akwai muhimmin saqo kamar yadda na
gaya miki da farko.”
Bilkisu dai ba ta ce komai ba yayin da Nasiru
da Abbas suka kalli juna.
Nasiru ya gyara tsayuwa, “Gaskiya Bilkisu
akwai abubuwa da yawa da na voye miki a tun
farkon mu’amala ta da ke, na tsinci kaina a yawan
kai-kawon zuci game da abin da ke zuciyata, haka
nan kuma na sha fama da kuvucewar tunani duk
domin ki, har sai da na ga tura ta kai bango tana
neman ture bangon, in ma ba ta ture ba na yanke
shawarar gaya miki gaskiya don ki taya ni na fitar
da A’i daga rogo,” ya yi shiru ya numfasa sannan
ya ci gaba, “ba na zaton zan xauki lokaci mai
tsawo daga zarar na kammala karatuna za a yi
mini aure, a kullum burin Hajiya na kawo mata
wadda za ta kalla a matsayin surukarta, idan har
buqatata ba ta biya ba ina mai takaicin ba wa
zuciyata haquri tare da dangana har Allah Ya yaye
Gawa ta qi rami
77 A.M. Xanzaki
mini damuwata,” daga nan ya yi shiru yana kallon
Bilkisu cike da shauqi da faxuwar gaba.
Bilkisu dai ba ta ce komai ba har yanzu,
wanda hakan ya haddasa shirun su su ma suna
jiran amsa.
“Ko mu bar ki ki yi tunani?” Abbas ya katse
shirun.
Girgiza kai ta yi sannan ta yi wani murmushi,
“Na ji dukkanin abin da ka ce.”
“Hakan na nufin kin amince ke nan,” Nasiru
ne ya faxa tare da yin ajiyar zuciya sannan ya
xaga hannunsa sama yana godiya ga Allah.
“Allah na gode maka da ka yi mini baiwa da
haka. Yaushe za mu je gida ki ga Hajiyata ku
gaisa?”
“Ba yanzu ba,” ta ba da amsa kai tsaye.
Suka ci gaba da tattauna batutuwa masu yawa
musamman game da gobensu a rayuwa da
makomar karatun su, daga qarshe dai suka ajiye
ranar Talata za su je gidan daga zarar an tashi
daga makaranta, domin a wannan rana suna da
qarancin lacca.
Sai da aka fara kiran sallar Magriba sannan
suka yi sallama suka tafi.
Gawa ta qi rami
78 A.M. Xanzaki
Bayan sun tafi ne har Bilkisu ta shiga gida
sun shiga wasu sabgogin ita da Hannatu sai ga
Hajiya Abu ta dawo daga unguwar da ta tafi.
Babu wanda ya mayar da hankali ya ba ta
labarin zuwan Nasiru gidan da abin da ya kawo
shi, ba wai sun yi haka ne don tsoro ba sai dai don
ba su ga fuskar yin hakan ba.
Hajiya Abu ba ta son vacin ran su ko kaxan.
Gawa ta qi rami
79 A.M. Xanzaki
________BABI NA 4________
ikin kwanaki kaxan al’amura suka
canza a rayuwar Bilkisu, yawan yin
waya, tunani da samun kai a wani
yanayi na soyayya suka taru suka rikixa rayuwar
ta. Ranar Lahadi bayan an gama laccan qarfe biyu
na rana Nasiru ya xauke ta a motarsa suka wuce
gidan mahaifiyarsa bayan sun yi wa Hannatu
qirqirarriyar qarya.
Nasiru ya sassauta tuqi sannan ya sauqa gefen
hanya ya gangara zuwa qofar wani gida mai
babbar qofa ya yi ham sau biyu.
Ba a jima ba aka turo qofar gidan daga ciki
sannan ya danna hancin motarsa zuwa cikin gidan,
maigadin, wani siririn buzu mai rama kamar sillen
kara ya mayar da qofar ya rufe.
Gidan faffaxa ne qwarai, haka kuma akwai
qofofi guda biyu xaya tana fuskantar qofar shiga
gidan yayin da xayar ke kallon gefe da barandarta.
Ya tsayar da motar a wurin adana motoci suka
fito.
Nasiru na sanye da farar riga shet mai dogon
hannu yayin da Bilkisu ke sanye da rifa da siket
‘yan kanti sannan akwai hijabi da ta lulluve jikinta
kamar wata ustaziya.
C
Gawa ta qi rami
80 A.M. Xanzaki
Nasiru ya kulle motar suka nufi qofar shiga
gidan. Tun kafin su qarasa aka buxe qofar.
Bilkisu ta yi kwalli da wata mata fara mai jiki
sosai haka kuma tana da yawan fara’a, kamar ta
xaya da Nasiru, hakan ya alamta mata cewa ita ce
mahaifiyarsa Hajiya Nadiya. Bilkisu ta yi
mamakin zumuxin matar maimakon ta jira a
qaraso har ta yi gajen haquri haka, hakan ya
tabbatar mata Nasiru xan gatan Hajiya ne kuma
Hajiyar ta san da zuwan ta a wannan lokacin,
murmushin fuskarta kaxai ya isa shaida.
Tana sanye da atamfa kalar makuba riga da
zani da xankwali, akwai alamun himma tare da
ita.
“Har kun qaraso ke nan,” Hajiya Nadiya ta
faxa yayin da take kallon Bilkisu sama da qasa.
Nasiru ya yi murmushi kawai, ko ba a faxa ba
ya san Bilkisunsa za ta samu karvuwa a wurin
mahaifiyarsa.
Ta juya ta koma ciki.
Bilkisu ba ta san ta samu tarba mai kyau ba
sai da suka shiga falon gidan, qamshi ya cika
gidan, qamshin turaren xaki da qamshin abinci
kala-kala wanda ke ajiye a kan teburin cin abinci.
Bilkisu ta qarewa falon kallo ta girgiza kai, ta
san komai ya ji abin ba magana.
Gawa ta qi rami
81 A.M. Xanzaki
Hajiya Nadiya ta nemi Bilkisu ta zauna a kan
kujera.
Bilkisu ta gaishe da surukarta cikin ladabi.
Nasiru ya ajiye wayarsa bisa tebur yayin da
ya wuce xakinsa don ya watsa ruwa ya bar Bilkisu
da mahaifiyarsa a falon.
“Taso ki ci abinci ‘yata,” Hajiya Nadiya ta
faxa.
Kunya ta kama Bilkisu, “Mhm!” kawai ta ce.
“Ko kunya ta kike ji? Kada fa ki yi fulatanci,”
ta shawarci Bilkisu.
Bilkisu ta yi murmushi ta tashi ta zauna bisa
kujera daura da teburin cin abincin, Hajiya ta zuba
mata a filet. Da qyar ta fara ci.
Da Hajiya Nadiya ta fahimci dai Bilkisu ba ta
saki jikinta ba sai ta ba ta wuri.
“’Yata bari in ba ki wuri ko?”
Ba ta daxe da tafiya ba sai ga Nasiru ya fito
daga xaki ya musanya kayan jikinsa da wata farar
shadda da ta sha koren aiki daga sama har qasa.
Saura kaxan cokali ya suvuce daga hannun
Bilkisu saboda yadda ta shagala da kallon sa.
Ya samu wuri ya zauna ya jawo filet ya zuba
abincin son ransa sannan ya kalle ta bayan ya yi
cokali biyu.
“Ya ya kika ga Hajiya?”
Gawa ta qi rami
82 A.M. Xanzaki
Bilkisu ta gyaxa kai, “Tana da kirki qwarai.”
“Ba ki ga kirkin ta ba yanzu, tana matuqar so
na saboda ni kaxai ne mallakin ta a duniyar nan.”
“Me kake nufi da haka?” ta tambaye shi.
Ya yi murmushi yayin da ya tsikari
haqarqarin kaza da cokali mai yatsu ya kai
bakinsa, “Wata rana zan gaya miki.”
Ta gyaxa kai yayin da ta ture filet xin abincin
ta jawo takardar goge baki (toilet paper) .
Ya kalle ta da sauri, “Kada dai ki ce mini kin
qoshi. Haba Bilkisu tare muka dawo daga
makaranta fa ni kaina yanzu na fara cin abincin
nan. Don Allah ki matso mu qarasa.”
Ta tura kujera baya tana gyaxa kai.
Ya buxe lemon kwali mai sanyi ya tsiyaya a
kofi, “Na ga alama har yanzu ba ki saki jikinki da
gidanmu ba. Za ki sha mamakin Hajiya, tun kafin
ki zo na ba ta labarin ki kuma ta ga hotunan ki da
yawa a wayata, ta daxe da yabawa da yadda kike
tana shauqin ganin ki, lokacin kuma da ta gan ki
bai kamata a ce ki nuna mata halin ki na
miskilanci ba.”
Ta yi masa wani kallo, “Ashe da ma duk
kallon miskila kuke yi mini ko? Gara da Allah Ya
matsi bakinka ka faxa.”
Gawa ta qi rami
83 A.M. Xanzaki
Ya girgiza kai, “Ko kaxan, ai ke xin ce wani
lokacin kamar tayar keke kike sai a rasa gane
gaban ki da bayan ki.”
Ta yi murmushi, “Kamar yadda ku ma maza
idan mace ta bari kuka gane ta ta shiga uku a
hannunku.”
“Ba dai Nasiru ba Bilkisu.”
Haka suka ci gaba da hira har Nasiru ya cika
tumbinsa yayin da Hajiya ta fito. Bilkisu kuma ta
ce gida za ta koma domin kada Hajiya ta riga ta
komawa.
Hajiya Nadiya ta miqa wa Bilkisu wani abu a
cikin kwali nannaxe da leda mai qyalli.
“Da wuri haka? To ungo wannan kyauta ce ta
musamman zuwa ga surukata na gode da ziyara.”
Bilkisu ta karva cikin matuqar jin kunya,
domin ta fuskanci rayuwar gidan ta wayayyun
mutane ne waxanda idanuwansu suke a buxe
tangaran.
Da haka suka yi sallama da Hajiya Nasiru ya
yi alqawarin kai ta har layin gidansu saboda ta yi
masa qorafin ba ta son Hajiya ta san ta je wani
wuri.
Hajiya kuma ta gargaxi Nasiru, “Ka tuqa ta a
hankali ban da gudu.”
Gawa ta qi rami
84 A.M. Xanzaki
Sun isa unguwar Nassarawa daga Kabuga a
mintunan da ba su wuce talatin ba, haka kuma
Nasiru ya sauke Bilkisu a kwanar layinsu a daidai
lokacin da wata mota Honda kalar makuba ta gifta
su kaxan ta tsaya a can gabansu a cikin layin. Jim
kaxan kuma sai motar ta qarasa cikin layin ta
tsaya a qofar gidan Hajiya Abu.
Nasiru ya miqa wa Bilkisu kuxaxe masu
yawa amma ta qi karva. A dole ya haqura ya
mayar da abinsa suka yi sallama.
Bilkisu ta tako da qafarta ta iso qofar gida. A
daidai lokacin da ta dafa qyauren gidan ne qofar
motar nan ta buxe Hajiya Abu ta sauqo daga cikin
motar.
Bilkisu ta waigo a tsorace ta yi ido huxu da
Hajiya mahaifiyarta.
“Daga ina kike, kuma wancan wane ne ya
sauqe ki a mota?”
Tambayar ta yi wa Bilkisu dirar guduma a
kan uwar maqera amma a can cikin zuciyarta.
***
“Ashe ban gargaxe ku akan amincewa da
wani mutum a wannan rayuwa ba?” Bilkisu ta
samu kanta mahaifiyarta tana gaya mata haka a
Gawa ta qi rami
85 A.M. Xanzaki
falo, bayan Jibo Maigadi ya buxe musu qofa sun
shiga.
Ganin an fara yi wa Bilkisu faxa sai Hannatu
wadda ke faman danna waya tun da suka shigo ta
tashi ta shige uwar xaki.
Hajiya ta nuna ta da yatsa, “Bilkisu ke ce
babba ke ya kamata ki ja kunnen qanwarki a duk
lokacin da kika ga za ta sava wa maganata amma
abin mamaki ke ce da kanki yau da tsallake
sharaxina, na gargaxe ku a kan barin wani wanda
ba da iznina ba ya san gidan nan. Shi xin wanda
ya sauqe ki a mota wane ne shi?”
Sai a lokacin Bilkisu ta numfasa domin tun
lokacin da aka tambaye ta wane ne ya sauke ta a
mota ta kasa ba da amsa har suka shigo gidan, ga
shi a matuqar tsorace take.
“Mama xan ajinmu ne ya rage mini hanya,
malamin da yake yi mana lacca ne bai zo da wuri
ba ya makara saboda an kwantar da mahaifiyarsa a
asibiti shi ne ya ce lallai mu tsaya ya yi mana
laccar.”
Hajiya ta kalle ta kurum, ko ba a faxa maka
ba ka san ji dai ya zama dole a wurin Hajiya
amma yarda kam ba ta yarda ba.
Gawa ta qi rami
86 A.M. Xanzaki
“To ya kamata dai ku kiyaye, akwai abubuwa
da yawa da ba ku sani ba amma in lokacin sanin
ya yi za ku sani. Kin ci abinci?”
Bilkisu ta gyaxa kai alamar e.
“A wanne Hotel kuka ci?”
Wannan karon Bilkisu sai ta xaga kai da sauri
ta kalli Hajiya wadda ba ta saurari amsar da za a
ba ta ba ta juya ta nufi uwar xaki.
Bilkisu ta yi ajiyar zuciya sannan ta miqe ta
nufi xakinsu inda ta taras Hannatu tana faman
danne-danne a waya. Bilkisu ta zauna gefen gadon
ta sannan ta fito da kwalin da Hajiya ta ba ta farke
ledar sai ga shi ta yi kwalli da wata sarqar gwal
mai masifar tsada.
Kyawu da qyalqyalin sarqar ya garzayo ya
fizgi hankalin Hannatu ta qura wa sarqar ido kafin
ta xago kai ta kalli Yayar tata.
“Nasiru ne ya ba ki?”
Ta girgiza kai tana kallon sarqar, “Hajiyarsa
ce ta ba ni.”
Ta miqa wa Hannatu sarqar ta karva tana
dubawa, “amma kamar Hajiya tana zargi na ko?”
Hannatu ta dawo mata da sarqar bayan ta
gama gani, “Ai ba zargi ba ne ke ma kin yi sakaci
da kika bari ta gan ki tare da shi.”
Gawa ta qi rami
87 A.M. Xanzaki
Da haka soyayyar Nasir da Bilkisu ta fara tun
Hajiya ba ta fahimci komai ba har ta ganehalin da
‘yarta take ciki kuma ta shiga bincike akan wane
ne Nasiru, a qarshe dai ta samu amsa cewa Nasiru
xan wani tsohon babban soja ne a qasar nan
wanda ahalinsa suka more duk wata alfarma da
ake nema, haka kuma suke da tarin dukiyar da ta
zame wa magadanta abin alfahari.
Da fari Hajiya ta so ta hana amma ganin
yadda suka zo gab da kammala karatun su na
makaranta ya sa ta qyale su da nufin cewa da zarar
sun kammala karatu za a yi maganar aure.
Qawance mai zurfi ya qullu tsakanin Hajiya
Abu da Hajiya Nadiya har ta kai xaya takan kai
wa xayar ziyara ko da ba ta nan kuma ta yi yadda
ta ga dama a gidan xayar.
‘Yayansu suka zama tamkar ahali guda.
Waxannan abubuwan sun faru ne a qasa da
watanni huxu.
***
A cikin wata na biyar an samu qarin abubuwa
masu yawa, domin har an fara maganar auren
Bilkisu da Nasir.
A kuma daidai wannan lokaci ne Hannatu ta
qulla kyakkyawar alaqa da Abbas, a da abin nasu
da dabi ya fara amma daga baya sai ya rikixe ya
Gawa ta qi rami
88 A.M. Xanzaki
zama soyayya, irin soyayyar nan mai farawa da
qarfinta.
Arziqin Hajiya Abu na ci gaba da bunqasa ta
yadda take samun riba mai yawa daga
kasuwancinta na Saudiyya da Hajiya Hindu ke
gudanar mata. Ta sayi motoci da baburan A-
daidaita-sahu ana yi mata haya kuxaxe suna
shigowa. Ta mallaki filaye da kadarori masu yawa
ta yadda a cikin shekara guda arziqinta ya yi
tashin gwauron zabo daga qaramar miloniya zuwa
babbar miloniya.
Akwai wani abu da ke xaure wa mutanen da
ke kewaye da Hajiya Abu kai; wato duk wannan
bunqasar da ta samu ba ta yarda ta fito da kanta an
san ta ba sai dai ta dinga buxe kasuwanci da
sunayen wasu mutane dabam.
Wannan shi ake kira vadda sawu ko kuma
iya-taku. Ko mene ne dalilinta na yin haka?
Wannan wani abu ne da za a iya cewa lokaci zai
nuna.
***
A lokacin da ake cikin tsananin hunturun
sanyi ne garin ya haxe ya yi duhu, mutane sun yi
qaranci a babban titin zuwa jami’ar BUK wata
mota baqa ta tsaya a qofar wani gida mai qatuwar
Gawa ta qi rami
89 A.M. Xanzaki
qofa, haka nan kuma ta daxe