Showing 12001 words to 15000 words out of 39022 words

Chapter 5 - Gawa Taki Rami Book Complete Writing By Ayuba Muhammad Danzaki.pdf

a qufule ya qura wa littafin da
ke gabansa idanu amma a zahiri ba karatu ko

Gawa ta qi rami
60 A.M. Xanzaki

kallon littafin yake yi ba, tunani yake yi na yadda
zai sama wa kansa mafita bisa abin da ke shirin
samun sa. A kan idonsa Bilkisu ta samu Bashir
suka tattauna har ya ba ta wata kyauta a leda, haka
kuma a kan idonsa Bashir ya hau mota ya tafi.
Yanzu haka Bilkisu za ta yi masa? Me ya sa
za ta ajiye shi ta tafi wurin wani? Ko ba ta san
yana son ta ba ne? Wani sashen na zuciyarsa ya ce
masa; ‘laifinka ne Nasiru ko ka tava gaya mata
kana son ta?”
‘A’a ban tava ba, amma ai ita ba yarinya ba
ce da za ta gaza gane duk alamun da nake nuna
mata.’
‘Ba lallai ba ne, idan kuma miskila ce
yarinyar fa?”
‘Ai kuwa tabbas haka ne, Bilkisu ta fi kama
da miskilan matan nan masu halin ko-in-kula da
al’amura, a mu’amalar da ya fara da ita ya fahimci
haka a lokuta da dama, sannan ba ta da yawan
magana.
Waxannan tunane-tunanen su suka gallabi
zuciyar Nasiru a irin wannan lokaci, har bai san
lokacin da abokinsa Abbas ya zo ya same shi ya
dafa kafaxarsa ba.
“Me kake yi a nan ga shi har Malam ya shiga
lacca?”

Gawa ta qi rami
61 A.M. Xanzaki

***
Tun da yammacin Lahadin ake rugugin
hadarin da ya taso amma ba a fara ruwan saman
ba sai misalin qarfe takwas na dare, waxansu sun
ce wai an dakata da fara ruwan ne har sai an
kammala sallolin Magriba da Isha wannan ranar,
amma shi Ubangiji ikonsa ba shi da alaqa da ibada
ko rashin ibadar bayinsa, yakan saki ruwansa a
duk sadda Ya so.
A irin wannan lokaci magidanta da yawa na
zaune a gidajensu, waxansu suna aikin taren ruwa
saboda zubar da xakunansu ke yi yayin da
waxansu ke kwance a xakunansu cikin kwanciyar
hankali suna daddanna wayoyinsu cike da nishaxi.
Alawiyya ta san an fara ruwa duk da
kasancewar gilasan tagarta a rufe suke haka kuma
tun da ta dawo da yamma ta shige xakinta take
faman tunani a bisa binciken da ta fara game da
abin da ya shafi rayuwar qawarta Zahira.
A yadda ta san Zahira da matsanancin kishi
zai yi wahala ta iya tarayyar xa namiji da wata
mace a duniya, ballantana wannan abin da a wurin
ta zai zama tamkar shashanci ne.
Ruwan saman ya ci gaba da sauqa yayin da
take kallon sa ta cikin katangar gilas xin da ta yi
mata hijabi da shi, a irin wannan lokaci na ruwan

Gawa ta qi rami
62 A.M. Xanzaki

sama Alawiyya ta fi samun nutsuwa da tunani mai
kyau. Labarin da qawarta ta ba ta game da zargin
da take yi game da Alhaji da tsohuwar matarsa ya
yi matuqar girgiza ta haka kuma ya saka ta a
kogin ximuwa maras misaltuwa, tsawon kwana
biyu da samun labarin amma ta rasa zaren da za ta
kama don fara gudanar da bincike a yadda aka
umarce ta.
Alawiyya na kwance ne a kan gado amma
wannan karon sai ta tashi zaune tana tunani.
A yadda ta san Alhaji mijin qawarta mutum
ne da mata ba su dame shi ba, haka nan kuma
babu wata xabi’a maras kyau da ta bayyana daga
gare shi har mutane suka san ta. To in haka ne ta
yaya wata mace za ta shiga ransa har ta kai bayan
ta mutu ya dinga tunanin ta, Alawiyya ta ji
zuciyarta na saqa mata cewa waxansu matan fa ko
a mata dabam ne, wataqila tana cikin su, wata
zuciyar kuma ta saqa mata cewa ba lallai haka ne
ba, sai kawai ta ji ita ma ta fara tunani irin na
qawarta kuma aminiyarta Zahira.
Yana da kyau ta fara bincike gobe da safe ta
ofishin Alhaji kuma Alhajin za ta tattauna da shi.
Ta jawo wayarta ta nemo lambar Zahira ta kira,
babu jimawa ta xaga wayar.

Gawa ta qi rami
63 A.M. Xanzaki

“Hello qawata yaya aka yi ne, an samu wani
cigaba ne?”
Ta yi murmushi, “Na tunani ko? Adireshin
ofishin Maigida nake son ji.”
Zahira ta xan yi shiru a wayar kafin ta yi
magana, “Binciken ne sai an je ofishin nasa?”
“Ta inda aka hau ta nan ake sauqa Zahira,
dole idan ana neman masaniya game da ita ta
hannunsa za a san bayanan.”
“A me za ki je masa?” Zahira ta tambaya.
“Ai na san bai san ni ba, ke dai ki sanar da ni
komai game da yadda za a yi na haxu da shi.”
“Me zai hana ki zo nan gidan sai in haxa ku?”
Alawiyya ta girgiza kai kamar Zahira tana
ganin ta, “A’a hakan ba zai yiwu ba don bana son
ya san alaqata da ke, in dai aka samu akasi kika
gan mu tare kada ki kuskura ki nuna kin san ni.”
Zahira ta xan yi tunani, ‘Shegiya na gane me
kike son yi, ki bi dai a hankali domin Alhaji yana
da basira maqura. Zan turo miki adireshin ta
waya.”
***
“Na amince da duk maganganun da muka yi
da ke a baya,” Hajiya Hindu ce ke gayawa Hajiya
Abu haka washegarin ranar da suka haxu a Hotel.

Gawa ta qi rami
64 A.M. Xanzaki

Suna zaune ne a falon gidan Hajiya Hindu
suna fuskantar juna.
“Da kyau tawan, na san za ki iya.”
“Amma ina da wani sharaxi.”
Hajiya Abu ta nutsu da murmushi a fuskarta,
‘Wanne sharaxi ne kuma? Faxe shi na ji.”
“Duk haxarin da na faxa za ki fitar da ni.”
Hajiya Abu ta yi dariya, “Haba Hindu, kada
ina yabon ki sallah ki kasa alwala mana, wanne
haxari kike tunanin za ki shiga ne? Da ma kin saki
ranki kamar tsumma a randa, duk saboda yanzu za
ki fara ne kike jin fargaba, amma da zarar kin fara
harkar nan tamu na tabbata sai kin fi mai kora
shafawa, da kanki za ki zo kina ba ni labari.”
Hajiya Hindu ta gyaxa kai, “Bayan haka
kuma…” ta ci gaba, “kason da za ki ba ni zai tashi
daga kaso ashirin cikin xari zuwa kaso arba’in.”
Hajiya Abu ta yi mata wani kallo, “Kada
kuma ki zaqe da yawa mana. Ko kin san ribar
nawa nake samu a wata a harkar nan kuwa?”
“Ai ba aikin albashi kika xauke ni ba,” in ji
Hajiya Hindu.
“Duk xaya, makaho ya yi dare, ke dai abin da
nake so ki saki jikinki ki yi abin babu fargaba, zan
mayar da ke kaso Talatin bisa xari. Ya yi?”

Gawa ta qi rami
65 A.M. Xanzaki

Hajiya Hindu ta gyaxa kai da murmushi,
“Hakan ya yi. yanzu sai ki ba ni duk wani abu da
nake buqata domin farawa.”
Hajiya Abu ta ce, “A ina za ki samo mana
miliyan biyu rance, ko da a kadarorinki ne?”
Hajiya Hindu ta yi mata wani kallo, “Ki ce
jari zan zuba ba aiki zan yi miki ba? miliyan biyu
fa kika ce? To in dai ba filaye da gidajen ‘ya’yana
zan siyar su koma haya ba ina na ga miliyan xaya
ma ajiyayya?”
Hajiya Abu ta xaga mata hannu, “Ya isa haka
don Allah uwar raki, na ji zan bayar da komai da
komai sai mu fara shirin komawar ki can, bayan
shekaru biyu ni ma zan biyo ki.”
Hajiya Hindu ta buxe baki cikin mamaki,
“Haba Hajiya shekaru biyu fa kika ce? Har yaushe
zan zauna a can shekaru biyu ga shi Alhaji
Mu’azzam ya matsa mini da maganar aure? Kuma
ma ban da abin ki muna da tabbacin za mu kai
shekaru biyu masu zuwa ne?”
Hajiya Abu ta gyara zama, “Abin da ya sa na
ce shekaru biyu shi ne, kin ga a lokacin ne nake sa
ran su Bilkisu da Hannatu sun kammala karatun su
na kwaleji, da zarar sun fara karatu a jami’a idan
na saita su sai in taho ni ma. Sannan don Allah in
muna magana ki daina tuna min da batun mutuwa

Gawa ta qi rami
66 A.M. Xanzaki

don yana sawa na dinga tuna wani abu da ya faru a
baya.”
“Na mutuwar mijinki ko? Ai duniya ta daxe
da sanin haka, ke dai saki ranki mu yi harka
kawai. Yaushe zan tashi?”
***
Baqar matar kakkaura mai jiki ta bi sawun
adireshin wanda ya zame mata jagora ta hanyar
duba wayarta har ta isa kamfanin, sau biyu ta
danna hon kawai aka taso aka buxe mata
wangamemiyar qofar kamfanin Alhaji Haruna
Tinqwal.
Harabar kamfanin cike take da jama’a ana ta
hada-hada, waxansu na faman loda kaya a mota,
wasu na kwaso kaya daga wani suto suna kawowa
gindin motar suna ajiyewa, yayin da wasu ke
qoqarin jera kayan a saman motar, mafi yawansu
matasa ne ‘yan bana-bakwai.
Akwai wurin ajiye motoci na musamman a
qarqashin wata tafkekiyar rumfa, a nan Alawiyya
ta samu wuri ta ajiye motarta, ta daxe a ciki tana
saqe-saqe kafin ta fito ta danna linzamin kulle
motar da ke haxe da curin makullan da ke
hannunta sannan kai tsaye ta nufi qofar da za ta
sada ta da ofishin Director General na kamfanin.
Ta bi wani dogon korido sannan ta isa qata qofa

Gawa ta qi rami
67 A.M. Xanzaki

mai yalwar farfajiya ta shiga ta daxe tana magana
da wani mutum kafin ya nuna mata ofishin a hawa
na xaya na benen da ke farfajiyar.
Alawiyya ta gyara riqon jakarta sannan ta
nufi matattakar benen da za ta sada ta da ofishin
wadda ke killace qasan benen. Ta qure mataki na
farko ta sake hawa mataki na biyu sannan ta riski
ofisoshi guda biyu amma xaya a rufe yake. Ta
kalli saman ofishin inda ta ga an rubuta Director
General ta qwanqwasa qofa.
Wata mata fara sanye da farar riga ‘yar kanti
ta leqo da kanta babu xankwali, tana sanye da
siket baqi akwai maxaurin wuya a tattare da rigar
jikinta daga sama, ta qare wa Alawiyya kallo sama
da qasa.
“Wa kina nema?” sai yanzu Alawiyya ta gane
kamar Hausa ba ta ishi matar ba, har take ganin
baiken matar da ta dage sai ta yi Hausa maimakon
ta yi turanci tun da ba Bagwariya ‘yar uwarta ta
taras ba.
“I want to talk to D.G,” ta ba ta amsa cikin
harshen Turanci. Ma’ana ina son yin magana da
D.G ne.
Matar ta yi gatsine ta nuna wa Alawiyya wata
kujera fara a nan barandar ofishin.

Gawa ta qi rami
68 A.M. Xanzaki

“Ok seat here, he is busy with his visitors.”
Ma’ana ‘ki zauna a nan, yana ganawa da baqinsa
ne.’
Ba ta daxe da zama ba sai ga Alhaji Haruna
Tinqwal ya fito daga ofis tare da waxansu mutane
yana cike da fara’a, suka yi musabaha ya sallame
su suka nufi qasan bene.
Har ya juya zai koma ciki sai matar (wadda
Alawiyya ta fahimci kamar ita ce Sakatariyarsa) ta
yi masa magana ta nuna masa Alawiyya.
Ya juyo ya kalli Alawiyya, kallonsa ta juye
zuwa kallon rashin sani, ya yamutsa fuska sannan
ya yi wa Alawiyya alama da ta shigo.
Mintuna kaxan da faruwar hakan sai ga
Alawiyya zaune cikin wani ofis mai faxi ba laifi.
Alhaji Haruna Tinqwal ya kalli Alawiyya
sannan ya gyara zama, “Daga ina haka kuma har
kike son gani na a irin wannan lokacin?”
Alawiyya ta kalle shi, “Ina fata kai ne Alhaji
Haruna.”
“Faxi ki qara, Tinqwal uwar daka ba,” ya ba
ta amsa ta hanyar tabbatar mata.
“Xaliba ce ni a sashen binciken halayyar xan
adam, kuma ina matakin rubuta project ne akan
wata matsala da ta shafi damuwa saboda rasa wani
abu, a binciken da na yi na samu labarin

Gawa ta qi rami
69 A.M. Xanzaki

gudunmawar da za ka iya ba ni na qarasa aikina
wanda ya rage kaxan.”
Alhaji Haruna Tinqwal ya nutsu yana
sauraren ta ta hanyar yin tagumi da hannunwansa
guda biyu, zuwa can ya yi ajiyar zuciya sannan ya
raba hannayensa da havarsa ya kalli Alawiyya
sosai.
“Baiwar Allah ke kuwa wa ya ba ki labarina
har kike sa ran samun wani abu daga wurina a
fannin bincikenki, kuma hakan ya bayu ga ki tako
takanas-ta-kano zuwa ofishina don neman wasu
bayanai?”
Alawiyya ta gyara zama ta ce; “Ina son sanin
bayani game da matarka marigayiya.”
Irin kallon da Alhaji Haruna ya yi mata ya
razana ta amma sai ta da ke ta ci gaba da magana,
“Ka yi haquri Alhaji kai ne wanda nake sa ran za
ka iya ba ni gudummawa na qarasa wannan aikin,
wallahi ba su fi kwanaki kaxan na miqa
sakamakon binciken nawa ba,”
Ya cije leve ya murza gashin baki yana mai ci
gaba da kallon ta, “Har yanzu ba ki ba ni amsar
tambayata ba, wane ne ya ba ki labarina?”
Ta gyara zama, “Haba Alhaji, mutum sananne
kamar ka mashahurin xan kasuwa a qasar nan a ce
ba a san ka ba, kuma ba a san yadda kake matuqar

Gawa ta qi rami
70 A.M. Xanzaki

son matarka ba, ai abu ne mawuyaci, wai gurguwa
da auren nesa. Ka tuna fa a lokacin mutuwarta
labarin halin da ka shiga sai da ya karaxe garin
nan.”
Alhaji ya gyaxa kai, “Haka ne. me kike son
sani?”
Ta fito da abin rubutu da xan littafinta na
ajiyar bayanai ta xora a kan tebur sannan ta gyara
zaman tabaranta, “Yaya kake ji game da mutuwar
matarka?”
“Har yanzu na kasa manta ta a rayuwata, ina
matuqar jin takaici game da yadda na rasa ta haka
kuma da yadda har yanzu nake kewar ta, shin kin
tava gamuwa da wani mutum iri na da ya rasa
matarsa da yake matuqar so amma ya iya jurewa
ba tare da ya samu tavin qwaqwalwa ba na wasu
shekaru?”
Ta rubuta dukkan bayanan da ya yi sannan ta
xago ta girgiza kai, “To Alhaji yaya ake ciki
yanzu? Kana jin za ka samu wata matar da ta
wuce matarka nagarta da halin kirki kuwa?’
“Babu,” ya yi saurin ba ta amsa.
Ta kuma yin rubutu sannan ta kalle shi,
“Yanzu da a ce za ta dawo duniya za ka so haka
ke nan.”

Gawa ta qi rami
71 A.M. Xanzaki

Wannan karon maimakon ya ba ta amsa sai
kawai ya qura mata idanuwa yana kallon ta, har
sai da ta kai ta tsargu da kallon da yake yi mata
hantar ta ta kaxa amma duk da haka sai ta da ke
tana mai ci gaba da kallon sa.
“Mutane da yawa da nasu suka mutu da a ce
za su dawo za su yi murna da hakan. In tambaye
ki mana; wani naki ya tava mutuwa da kika kasa
manta shi? Kin tava cin karo da xacin zuciya irin
wanda na fuskanta a rayuwa kuwa?” ya girgiza
kai, yayin da qwalla ta fara qoqarin zubowa daga
idanuwansa.
“Yi haquri Alhaji,” ta bi shi da rarrashi,
yayin da take tattare kayan rubutunta tana
mayarwa a cikin jaka bayan ta kammala rubuta
bayanansa na qarshe.
“Alhaji zan so ka sanar da ni inda garin ita
matar taka yake domin na samu qarin wasu
bayanai daga can, bayanan da nake nema sun
danganta ne da yadda mutum kan ji yayin da ya
rasa wani masoyinsa na gaskiya.”
Ya xaga mata hannu, ‘Kada ki damu zan
sanar da ke. Allah Ya taimaka.”
Ta dawo da abin rubutun hannunta ta xora
biron a bisa takarda yayin da ya fara ba ta
cikakken bayani akan asalin matarsa da garin da ta

Gawa ta qi rami
72 A.M. Xanzaki

fito da yadda aka yi suka haxu, bayanan nasa suka
bi ta kunnuwan Alawiyya suka zagaya
qwaqwalwarta suka shiga zuciyarta daga nan suka
bi jini zuwa hannunta suka bayyana a zahiri cikin
qayatattun kalmomi bisa takarda.
Har zuwa lokacin da ta fita ta bar shi bai
dawo daga tunanin da ya shiga ba, haqiqa ta daxa
yi masa fami akan ciwon da ya daxe yana
qwazzabar zuciyarsa, sai dai kuma akwai lam’a a
tattaunawar sa da matar da ta fita.
Ya jawo wayarsa ya daddanna lambobi ya
saka a kunne ya xan saurara.
“Hello! Wata yarinya ce baqa mai jiki…”
“…E yanzun nan ta fita daga ofishina…”
“…Ban yarda da ita ba ne kawai, ta zo tana yi
mini wasu tambayoyi wai akan mutuwar tsohuwar
matata, kai ka ji wata fitina don Allah…”
“…A’a kada a yi mata komai, kawai a bi ta
har a gano inda take kuma sannan a tabbatar an
san wanda ya saka ta wannan aikin…” “…Yauwa
ka gane me nake nufi ke nan, domin yin shirinmu
zai iya sakawa liqi ya valle…”
Ya ajiye wayar yana huci, “Shashasha ni za ki
rainawa hankali.”
Ya yi qwafa sannan ya qura wa taga ido yana
tunani.

Gawa ta qi rami
73 A.M. Xanzaki

***
Misalin qarfe biyar na yammacin Lahadi
Bilkisu da Hannatu na zaune suna kallon wani fim
na Indiya a falon gidansu bayan kammala jingar
da aka ba su a makaranta sai ga Jibo Maigadi ya
shigo da sallama ya xan sunkuya ya gai da su suka
amsa.
“Ana sallama da Bilkisu,” ya faxa yana kallon
su.
Gaba xaya ya karkato da hankulansu gare shi
suka dakata da kallo suna sauraren sa.
“Wane ne?” in ji Hannatu.
Waxansu ne su su biyu, xaya dogo fari…”
Tun kafin ya qarasa Hannatu ta katse shi ta
hanyar kallon Bilkisu da mamaki, “Nasiru ne.”
Bilkisu ta yi mata kallon zargi, “Ke kika
kwatanta musu gidan nan ke nan.”
Hannatu ta girgiza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login