Showing 30001 words to 33000 words out of 39022 words
Chapter 11 - Gawa Taki Rami Book Complete Writing By Ayuba Muhammad Danzaki.pdf
ma umarni ne aka ba mu kuma muka
kammala aikinmu, daga yanzu kuma ba za ku sake
gani na ba, da ma don kada na bar ku a duhu ne ya
sa na zo na yi muku bayani.”
Hannatu ta kalle shi da fuskar tausayi, ‘Ku
faxi ko nawa kuke so a ba ku wallahi Hajiya za ta
ba ku don ku sake mu.”
Ya daka mata tsawa, “Ke rufe mana bakinki
da wata maganar Hajiya maciyiyar amana kawai,
wadda ba ta jin kunyar yin qarya, ku a tunaninku
qaunar ku take yi? To amfani take so ta yi da ku
don ta tara dukiya, amma ba za ku gane ba, ko kun
san a jiya ta shrya xauke ku ta yi daga wurin da
kuka taru da sunan fati?”
Gawa ta qi rami
153 A.M. Xanzaki
Gaba xaya suka kalli juna cikin mamaki suka
sake mayar da hankalinsu kansa.
Aka turo qofa, Lawurje ya shigo xauke da tire
da kofunan shayi da fulas gami da wani qaton
mummuqi a wata babbar leda ya ajiye a gaban su
Hannatu.
Alhaji Lado ya bi shi da kallo, “To fice ka ba
mu wuri, kai ma a yau za ka bar gidan nan ban
yarda da kallon da kake yi wa ‘yan matan nan ba.”
Lawurje ya sa qafa ya fita.
Alhaji ya sake kallon su, “qwarai kuwa
Hajiya ta yi niyyar xauke ku ne daga wurin domin
ta salwantar da rayuwarku a bisa wani qudiri nata,
duk na san komai,” ya sake xauko waya ya duba
lokaci sannan ya nuna musu shayin da ke gabansu,
“au! Na manta ga shi nan ku karya yayin da kuke
karyawa zan ci gaba da magana idan na kammala
sai ku yi tambaya, lokaci yana qurewa” ya faxa
musu haka a wani yanayi na malamin da ke gaban
xalibansa yana yi musu darasi.
Suka kalli farantin da kayan shayin ke kai
sannan suka kalle shi.
Ba tare da ya damu ba ya ci gaba da magana,
“Ba ku muke nema ba Hajiyarku muke nema ta
Gawa ta qi rami
154 A.M. Xanzaki
kawo kanta nan sannan sai mu sake ku, muna sa
ran haka zai faru daga yau zuwa jibi.”
Ya miqe tsaye, “sauran bayani idan Maigida
ya zo zai yi muku ni zan tafi gari, idan kun gama
karyawa ku ci gaba da jira ku qara jira, matuqar
ba ku sava umarnina ba za ku bar nan lafiya yayin
da Hajiya ta zo hannu.”
Ba tare da ya qara cewa wani abu ba ya juya
ya fita amma sai suka ji ya sa makulli ko kwaxo
ya kulle qofar daga waje. Sai a lokacin ne suka ji
yunwa ta kawo musu ziyara suka kalli abincin da
ke gabansu suka haxiyi yawu.
Hannatu ta jawo farantin gabanta.
Bilkisu ta ture farantin, “Ba ki da hankali ne?
Mutanen da ba sa qaunar mu za su ba ki abu ki ci?
Wallahi gara yunwa ta kashe ni,” ta qarasa da
shan alwashi.
Hannatu ta qara jawo farantin gabanta ta
xauki fulas xin ta fara tsiyaya shayin a kofi, “Idan
ma ba ki ci ba yunwa za ta kashe ki, da wuya ta
kashe ni gara daxi ya kashe ni,” ta gutsuri burodi
ta kai bakinta ta fara tauna.
Bilkisu ta qura mata ido, don ita a
tsammaninta akwai guba a cikin abincin.
Gawa ta qi rami
155 A.M. Xanzaki
Hannatu ta yi nisa da fara shan shayin sai
kuma ta yi shiru da tauna tana tunani.
“Me ya faru kuma?” Bilkisu ta tambaye ta.
“Wani tunani ne ya faxo mini ko in ce wata
dabara ce ta zo mini.”
“Ta me?” ta tattara hankalinta a kan Hannatu.
“Kin lura tun da wannan mai baqaqen kayan
ya shigo yake kallon mu sama da qasa?”
“E to mene ne kuma? Kina jin zai taimake mu
ne mu tsere?”
Ta yi murmushi, “Ba za ki gane ba ‘yar
uwata.”
***
Tun lokacin da Alawiyya ta dira ta bayan
gidan gonar Alhaji Haruna sai kawai ta ci gaba da
gudu har ta doshi wani wuri da take tsammanin a
nan qofar fita daga wurin take. Ta lura, wannan
ma wani tsohon gidan gona ne da ya daina amfani.
Da ta tabbatar ta yi nisa da gidan Alhaji Haruna
Tinqwal sai ta dakata tana haki tare da nazarin
inda take cikin nutsuwa.
Wurin ya fi kama da jeji sai dai qaramar
katangar da ta zagaye wurin mai shegen faxi ba ta
Gawa ta qi rami
156 A.M. Xanzaki
ba ta damar ganin qarshen katangar ba a faxi
amma ba ta da tsayi sosai. Akwai tsoffin gine-
gine da suka fara vavurewa a wurare daban-
dabam, tabbas nan tsohon gidan gona ne da aka
daina amfani da shi haka rumbunan ajiyar kayan
abinci ne a wurin sun fi talatin da aka daina
amfani da su. Daga can nesa tana iya jiyo kukan
motoci wanda ya tabbatar mata tana kusa da bakin
titi.
Da ta fahimci babu motsin wani bil’adama a
wurin sai kawai ta ci gaba da tafiya abinta har
zuwa lokacin da ta fara jin haushin karnuka.
Ba ta san lokacin da ta tsaya cak cike da
faxuwar gaba ba sannan gumi ya yanko mata duk
da kasancewar sanyin safiya ce. Ta tabbata
mutanen da ke neman ta ne suka xebo karnukansu
don su taya su kama ta. Tunanin haka ya sa ta
shafa a guje ta nufi inda take jiyo kukan motocin.
Ba ta kwashe mintuna biyar tana gudun ba sai
kawai ta gan ta ta fita bakin titi, haka nan kuma
ashe wawagegen gidan gonar da ta fito daga
cikinsa ba shi da qofa sai wata rusasshiyar katanga
da ta ga an rubuta EFCC under investigation wato
alamar filin ya shiga komar bincike ta hukumar
yaqi da cin hanci da rashawa.
Gawa ta qi rami
157 A.M. Xanzaki
Babu wadatar motoci a titin kasancewar
safiya ce amma hakan bai hana ta dinga ganin
Babura masu qafa uku suna giftawa jefi-jefi ba.
Wani matashin mai babur da bai wuce shekaru
ashirin da biyar ba da tarin sumarsa a ka kamar
sheqar ungulu ya tsaya kusa da ita yana qare mata
kallo.
“Hajiya ina za ki je ne?”
Ta faxi sunan unguwar da gidanta yake.
“Hau mu je Hajiya, ni ma yaran uwarxakina
zan je na kai makaranta kafin lokaci ya qure.”
Ta shige babur xin da sauri yayin da ya ja
suka tafi, ta waiga ta kalli gidan gonar sannan ta yi
ajiyar zuciya.
Mintuna kaxan suka isa qofar gidan ya dakata
ta sauqa sannan ta kalle shi, “Ina zuwa,” ta nufi
cikin gidan.
“Hajiya ai ba ki ba ni cittar ba.” ya faxa, ga
alamu bai ji abin da ta ce ba.
“Na ce maka ina zuwa,” ta maimaita ba tare
da ta waiwayo ba.
Ya kashe babur xin ya kifa kansa a kan
sitiyarin babur xin ya zauna zaman jiran ta.
Gawa ta qi rami
158 A.M. Xanzaki
Alawiyya ta shiga cikin gidan da sauri ta
shige xakinta ta nufi inda ta ajiye wayarta ta
xauka ta duba sai ta ga ma ashe wayar babu caji,
saboda ba kwanan gida ta yi ba ta tabbatar sun
kawo wutar sun xauke. Ta nemi power bank
(ma’ajiyar wuta)ta xauko ta haxa da wayar sannan
ta laluba ma’ajiyar kuxinta ta xauko dubu xayan
da ta rage mata ta fito waje da sauri ta rufe ko ina
na gidan tana yi tana waiwaye, domin in har
waxanda suka xauke ta suka san gida ta nufo to
tabbas kuwa za su kuma biyo ta.
Da sauri ta nufi inda mai babur yake ta shiga
ta zauna, “Kai ni Kwanar Xiso,’ta ambata ba tare
da ta kalle shi ba.
“Hajiya nan fa kika ce na kawo ki, kuma na
gaya miki…”
“Na sani ai,” ta katse shi.
Ya gyaxa kai yayin da ya kunna babur xin,
“Kuxinki ya qaru.”
Ta shuna masa dubu xayan da ta xauko, ya
karva ya saka a aljihu ya ba wa babur xin wuta ya
miqe titi.
A cikin babur xin Alawiyya ta saka wayarta a
jikin ma’adanar wuta (power bank) ta kunna ta jira
Gawa ta qi rami
159 A.M. Xanzaki
har wayar ta gama laqaqinta ta kawo wuta. Ba tare
da ta vata lokaci ba lokacin da mai babur ke quga
wuta a kan titi ita kuma tana laluben lambar
Zahira.
Ta saka a kunne ta jira har aka xaga, “Hello
kina ina ne Alawiyya? Kin sa hankalina ta tashi
tun jiya nake kiran ki.”
Ta kalli mai babur xin sannan ta yi qasa da
murya, “Ina cikin tashin hankali Zahira, wallahi
sace ni aka yi jiya.”
Mai babur ya kalle ta ya zaro harshe ya ci
gaba da tuqi yana tunani.
“Sata kuma?” Zahira ta xaga murya har ta kai
mai babur xin yana jin me take cewa.
“Yanzu kina ina?”
“Na nufi gidan Aunty Fatima.”
“Ai na gaya miki ki kiyaye, zan zo gidan na
same ki.”
Daga nan ta kashe wayar har suka qaraso
qofar gidan sannan ta sauqa.
Sai dai kuma tun kafin ta biya mai babur xin
kuxinsa numfashinta ya tsaya cak! Sakamakon
Gawa ta qi rami
160 A.M. Xanzaki
ganin qofar gidan a kulle da qaton kwaxo. Ta
tsaya tana tunani
Mai babur ya kalle ta, “Hajiya ko mayar da
ke za a yi ne?”
Ta girgiza kai, “A’a ka je kawai na gode.”
Ya ba wa babur xin wuta, “Canjinki fa?”
Ta sake girgiza kai, “Ka je kawai na gode.”
Ya yi murmushi, “Allah Ya biya Hajjaju, na
gode. Allah Ya kare mana ke Aunty.”
Ko kula shi ba ta yi ba har ya bar wurin, ita
dai ta nemi wuri ta zauna a kan dakalin qofar
gidan tana qoqarin kiran wayar Yayar tata. Har
wayar ta gama qara ba a xaga ba, ta tabbata
hatsabiban mutanen nan ba za su bar ta ba ko don
kada asirinsu ya tonu za su yi mai yiwuwa wajen
ganin sun kama ta. Shin za ta tsaya jiran Zahira ne
ko kuwa?
Wayarta ta yi qara da sauri ta xauka sa ta ga
sunan yayar tata, “Lafiya kike damu na da kira da
sassafe?”
“Aunty ina cikin wani hali na zo gidanki na
tarar a kulle,” ta ba ta amsa.
Gawa ta qi rami
161 A.M. Xanzaki
“Wanne irin hali kuma ni ‘ya su? Mun yi
tafiya Katsina tun jiya, muna Dutsin Ma yanzu
haka.”
“Maganar ba ta waya ba ce, ki bari sai kin
dawo.”
Ba ta ba ta damar sake magana ba ta katse
wayar a daidai lokacin da saqo ya shigo, ta yi
saurin dubawa sai ta ga ashe kuxi ne Zahira ta turo
mata gami da wani saqo a rubuce.
‘Ki gaggauta shiryawa ki bar garin nan yanzu,
ga kuxin mota nan na turo miki za mu yi waya
daga baya.’
Ta karanta saqon a gaggauce sannan kamar
wadda aka tsikara sai ta ji ta tashi tsaye ba shiri
tana tunanin mafita. Ko me Zahira ta gani ta turo
mata wannan saqon? Akwai matsala gaskiya.
Yanzu yaya za ta yi? Abdulhakeem ya faxo mata a
rai, wani jami’in tsaro ne mai muqamin ASP da ke
ta nacin ta miqa masa soyayyarta amma ta yi
qememe. Ya sha nuna mata zai iya yin komai a
kanta kuma zai iya xaukar kowanne irin mataki
akan duk wanda ya tava masa ita ko ya nemi shiga
tsakaninsu. Mutumin kirki ne amma a vangaren
soyayyarta ba shi da mutunci, shi mahaukaci ne da
ya haukace a dajin ruquqin soyayyarta ya zauce
Gawa ta qi rami
162 A.M. Xanzaki
ya ximauce. Shin ko zai iya zame mata mafita a
wannan tsaka mai wuyar da ta tsinci kanta? Ko
babu komai shi kaxai ya rage mata a wannan
lokacin, tun da Zahira da ta zama silar saka ta
binciken ita ma ba ta shawarar gudu take yi.
Ta sake xaukar wayarta ta kira lambarsa,
bugu na xaya a na biyu sai ya xauka.
“Lafiya yau ake nema na kuma?”
Ta raunana muryarta ta fara kuka, “Ka
taimake ni don Allah waxansu mutane ne suke bi
na.”
“What?” yadda ya yi tambayar sai ta ji kamar
ta toshe dodon kunnenta, “waxanne banzaye ne
waxannan? Kina ina dai yanzu?”
“Ina gidan Aunty Fatima barin garin zan yi
yanzu ka zo ka kai ni tasha.”
“Tasha kuma? Babu inda za ki je ki jira ni na
zo yanzun nan.”
Tana ji a waya yana ba wa wani umarni, “Yi
kwana ka juya.”
***
Misalin sha biyu na rana a barandar asibitin
mutane sun fara cika, ma’aikatan lafiya na faman
Gawa ta qi rami
163 A.M. Xanzaki
zirga-zirgar kula da marasa lafiya. Yayin da ake
shiga da wasu ake fita da wasu, waxansu kuma na
cikin xakunan jinya ana ba su kulawa, yayin da
adadin masu ziyara ke qaruwa duk bayan wasu
mintuna.
A’isha da Binta na zaune a barandar bisa
benci suna jiran likita ya dawo yayin da Nasiru ke
zaune kusa da su cike da damuwa.
A daren da abin ya faru ne labari ya samu
iyayen A’isha cewa an sace ta daga wurin fati tare
da amarya, hakan ya xaga wa Alhaji Salisu
mahaifinta da Hajiya Hauwa mahafiyarta hankali
ya yi mugun tashi, suka shiga nema ido rufe, a
daren babu wanda ya iya barci, bayan sun kai
rahoto ofisoshin yan sanda ne suka dawo misalin
sha biyu na dare tun kafin su shiga gida suka
hangi wata mota baqa ta tsaya nesa da su kaxan
sannan sai aka buxe qofar motar aka jeho mutum
biyu qasa, sannan motar ta ja ta tafi a guje tamkar
zuciya.
Alhaji Salisu ya zabura ya fita daga motar ya
nufi wurin da mutanen suke a qasa, jikinsa yana
ba shi cewa abin da ya faru yana da alaqa da abin
da suke nema.
“Kada ka je,” Hajiya Hauwa ta shawarce shi.
Gawa ta qi rami
164 A.M. Xanzaki
“Kada ki damu, alheri ne,” Yana murmushi
ya faxa. A yadda ta ji muryarsa akwai yaqinin
kyakkyawan zato, don haka sai ta zura masa ido
tare da yin addu’a a zuciyarta.
Alhaji Salisu ya isa gare su sai ya tarar ‘yarsa
A’isha ce da qawarta Binta, amma suna cikin wani
yanayi. Da sauri ya kama hannuwansu ya kawo su
gindin motar, wadda tun kafin ya qaraso Hajiya
Hauwa ta buxe qofar ya saka su a ciki ya dawo da
sauri ya kunna motar.
Tun kafin ta yi magana ya riga ta, “Asibiti za
mu je, Allah Ya sa da sauran shan ruwansu.”
A daren a asibiti aka kwana ana duba
lafiyarsu. Likita ya tabbatar babu abin da ya same
su duk da hodar sa barci da aka yi amfani da ita
don a bugar da su. An ba su magunguna sannan an
kira ‘yan sanda sun yi musu tambayoyin da suka
kamata. Qarfe huxu na Asuba ‘yan sanda suka
kammala xaukar rahoto suka ce za su dawo gidan
Alhaji Salisu da safe.
Da sassafe Nasiru ya samu labari to shi ne ya
taho don ya ji waqa daga bakin mai ita.
“Jiki da sauqi,” A’isha ta ba shi amsa.
Gawa ta qi rami
165 A.M. Xanzaki
Binta ta ce, “Ka yi haquri Yaya Nasuru
wallahi sun tafi da Bilkisu da Hannatu, mu ma
Allah ne Ya sa suka dawo da mu,” ta fashe da
kuka.
Ya xaga mata hannu cikin qarfin hali,
“Qaddara ce. Allah Ya yi sai hakan ta faru, kada
ki ji komai su ma za su dawo. Haka Hajiyata ta ce
mini jiya. Mafi yawan qwarin gwiwata daga
wurinta nake samu. Me ‘yan sanda suka ce?”
“Suna kan bincike har yanzu kuma sun ce za
su same mu har gida. Ka san abokin Babana DPO
ne.” In ji A’isha.
Ya gyaxa kai sannan ya kalli Binta, “Tun da
kun ji sauqi ko zan mai da ke gida?”
Ta girgiza kai, “A’a ai a gidan Yayana nake
kuma ba ya nan shi da matarsa don haka nake
kwana a gidan su A’isha, don ba zan iya kwana ni
kaxai ba.”
Ya gyaxa kai, “Na fahimta babu damuwa.
Amma yaya aka yi suka san gidanku?”
“Tambayar mu suka yi muka yi musu
kwatance,” in ji A’isha.
Ya yi shiru yana tunani.
Gawa ta qi rami
166 A.M. Xanzaki
“Ina tsammanin mutanen nan ba varayin
mutane ba ne kawai.”
***
Sani Tahir ya gyara zama yana kallon fuskar
Hajiya Abu yana qyaqqyafta idanuwa kamar
varawon akuya. Tun da aka kawo shi misalin
qarfe goma na safe Hajiya ta sa su Bello suka
kunce masa mayanin da aka xaure masa fuska da
shi yake so ya san wanda ya kawo shi nan da
kuma dalilin kawo shi.
An kawo masa abinci wai ya ci amma fargaba
ta hana shi ci. Zuwa misalin sha xaya na rana sai
ga Hajiya Abu ta sauqo daga sama inda ta zauna
tana fuskantar sa a falon tana qare masa kallo.
“Hajiya ai da kin aika na zo ma zai fi.”
“Na sani, amma ina son labarin xauke ka ya
isa kunnen maigidanka ne.”
“Me kike nufi da haka?” ya tambaya.
“Tava makaho na yi don ya san ana ganin sa,
an xauke Hannatu da Bilkisu kuma ina zargin
maigidanka da aikata haka.”
Gawa ta qi rami
167 A.M. Xanzaki
Ya tsuguna ya fara magana cikin karayar
murya, “Don Allah don Annabi ki yi haquri,
wallahi ba ni da masaniya akan abin da ya faru.”
“Na sani,” ta kuma faxa, “ina son tauna
tsakuwa ne don aya ta ji tsoro.”
“Amma ni mene ne nawa a ciki?”
Ta nuna masa abinci, “Ka karya ne kafin ka
fito na ga ko tava abincin ba ka yi ba?”
Ya kalli abincin ya kuma kallon ta, “Hajiya ki
qyale ni in tafi, ban san komai ba wallahi.”
“Ka san komai Sani, kada ka munafunce ni,
kai dai ka ba da haxin kai a duk abin da zan gaya
maka.”
***
Alhaji Haruna Tinqwal na zaune a ofis yana
danna na’ura mai qwaqwalwa sakatariyarsa
Hauwa ta yi sallama ta shiga. Ya xaga kai ya kalle
ta.
“Wani ya zo