Showing 24001 words to 27000 words out of 28793 words
Chapter 9 - TAFARKIN TSIRA Book Complete by Sarkin Marubutan Yaki .pdf
ya mallaki ALLON SIHIRIn,
Wannan shi ne abin da yasanya boka kaddad ya yi wannan dariyar farin ciki,
Tun daga wannan rana kaddad ya fara shirye-shiryen tafiya domin mallakar hular Lauhul-Sihir.
Wannan shi ne abin da faru da boka kaddad bayan ya tura hadimin aljanin shi domin farauto
mishi yaro mai hatimin takobi.
BABI NA GOMA SHA TAKWAS
Al'amarin shugaban 'yan fashin duniya sadauki fitinatul-Amir kuwa, tun sa'adda uwar gidanshi
Rusayyat ta shayar da shi hodar banju domin ta samu nasarar tseratar da rayuwar yaro Usaiba
mai hatimin takobi. Sai ya shafe tsawon kwana ɗaya a cikin wannan hali sannan ya farka ta
hanyar buɗewa idanuwanshi ya yi miƙa gami da hamma, kuma ya ji kanshi na juya mishi, Kawai sai ya ƙwalla wa wata kuyanga kira,bayan ta bayyana gare shi ta zube ƙasa ta kwashi
gaisuwa sai ya dube ta ya ce "Ya ke mushlaira shin har tsawon wane lokaci na ɗauka ina barci
kuwa?
Koda jin wannan tambaya sai Mushlaira sai ta buɗi baki cikin ladabi ta ce "Ya shugabana ai yau
tsawon kwana ɗaya kenan ka shafe kana barci"
Sa'adda fitinatul-Amir ya ji wannan batu sai ya cika da matuƙar mamaki da al'ajabi, har buɗe
baki da nufin yace wani abu sai ya ji alamun ɓuɗe ƙofar turakar don haka sai mayar da duban
shi izuwa ga wajen domin ya ga wane ne ke tafe.
Aikuwa sai ya yi arba da uwar gidanshi Rusayyat ta caɓa ado mai ƙayatarwa fuskarta cike da
annuri,
Koda Mushlaira ta yi ga cewa gimbiya ta shigo sai ta miƙe tsaye zumbur! Ta durfafi ƙofar fita
daga turakar,
Sannu a hankali Rusayyat tana takawa da ƙafafuwanta har ta iso inda mai gidanta yake ta
zauna a daf da shi har suna jin numfashin juna,
Cikin tattausan murmushi mai ɗimauta zuciya Rusayyat ta ce "Barka da wannan lokaci ya
JARUMIN JARUMAI farin cikin zuciyata", fitinatul-Amir ya mai da mata da martanin murmushin,
wanda ya fi kama da yaƙe sannan yayi gyaran murya ya ce "Ya uwar'ya'yana wai shin tsawon
wane lokaci na ɗauka ina wannan barci ne? Da jin wannan tambaya sai Rusayyat ta ce "Ya abin ƙaunata ai baka huce tsawon sa'a ɗaya ba,
ko ka manta ne cewa ɗazun nan ba jimawa muka yi kalaci yanzu kuma da farka ai lokacin fita
faɗa ne",
Koda jin amsar wannan tambaya sai tunanin fitinatul-Amir ya rikice yace a cikin ranshi, shin
tsakanin matata da kuyanga Mushlaira wane ne ya raina mini hankali? Tabbas duk wanda na
samu da laifin hakan sai na yanke mishi hukunci mai tsanani",
Koda gama tunanin hakan sai ya miƙe tsaye ya nufi kewaye, jim! Kaɗan ya fito bayan ya
tsaftace fuskarshi ya riƙe hannun Rusayyat suka durfafi ƙofar turakar, suna fita waɗansu
zaratan dakaru masu jajayen sulke ɗauke da miyagun makamai suka mara masu baya,
Duk wajen da suka durfafa a cikin gidan sarautar sai ka ga dakaru, kuyangi da hadimai na
zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa cikin girmamawa, yayin da aka iso daf da turakar Rusayyat
sai suka yi bankwana fitinatul-Amir da sauran dakarun kuma sai suka ci-gaba da tafiya,
Tafiyar daƙiƙa arba'in kacal! Suka yi aka iso fadar birnin,
Ita dai fadar ta kasance ƙasaitacciya da aka yi mata ado da nau'ikan kayan ƙawa da alatun
more rayuwar duniya, gaba ganin fadar an yi shi ne da zallar jauhari da zubar-daju,
Masana da masu hasashe sun tabbatar da cewa babu wata faɗa da ta kai ta ƙawatuwa,
waɗansu daga cikin masana na kiran fadar da suna ALJANNAR DUNIYA.
Kai tsaye fitinatul-Amir ya nufi inda karagar mulki take ya taka matattakalar fadar, a lokacin
da gaba ɗaya jama'ar fadar suka miƙe tsaye domin girmamawa a gare shi,
Bayan Fitinatul-Amir ya hakimce bisa karagar mulki sai suka dinga tashi daga wajen zamansu
suna zuwa gare shi suna kwasar gaisuwa, talakawa ne suka fara tasu gaisuwar sannan attajirai,
sai 'yan majalisar sarki, su dai 'yan majalisar sun kasance GWARAZAN JARUMAI da
Fitinatul-Amir ke amfani da su domin kai farmaki zuwa wata ƙasa, don FATAUCIN BAYI da
ganimar dukiya, mutum shida daga cikin 'yan majalisar sun kasance GWARAZAN SARAKAI
saboda matuƙar tsoron Fitinatul-Amir ya sanya suka haƙura suka bar sarautar suka koma
KANGIN BAUTA a ƙarƙashin shi. Shiru ne ya wanzu a fadar na tsawon lokaci tamkar an yi ruwa
an ɗauke, sai daga bisani ne wani garjejen ƙato mai ƙirar samudawan farko daga cikin 'yan
majalisar ya buɗi baki cikin ladabi da ƙasƙantar da kai ya buɗi baki ya ce "Ya shugabana yau
tsawon kwanaki uku kenan Ayarin sarakuna guda ashirin suna so su gana da kai domin su
bayar da harajin su kamar yadda suka saba"
Koda jin wannan batu daga bakin ɗan majalissar sai Fitinatul-Amir ya sake cika da matuƙar
mamaki ya dube shi ya ce "Ya kai Haibatu shin yau har na kai tsawon kwanaki uku ban fito fada
ba?,
Haibatu ya ce "Kwarai kuwa ya shugabana"
Shin yanzu wane ne ya raina mini hankali uwar gidana, kuyanga Mushlaira ko kuwa Haibatu?,
Amsar tambayar da Fitinatul-Amir ya kasa bawa kanshi kenan, sannan ya sake bude baki a a
karo na biyu yana duban Haibatu ya ce " Ka sanar da sarakunan cewa ba zan samu damar
ganawa da su a yau ba dai zuwa gobe",
Daga wannan batu ne ya yi shiru aka cigaba da gudanar da sha'anin mulki kamar yadda aka
saba.
Mu haɗu a littafi na 10 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaki
Wthapp Number
08137237071
TAFARKIN TSIRA 3
Littafin Yaki
Rubuta Labari
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
Littafan Marubucin
Kogon Annoba
Sarautar Mutuwa
Kangin Bauta
Jaruman Duniya
Takobin Ɗaukaka
Ƙarshen Zalunci
Fataucin Bayi
Sarkin Sadaukai
Goga Sha Fama
Tafarkin Tsira
Gasar Sarauta
Kundin Al'ajabi
Turbar Ajali
Farautar Mazaje
Littafin kudi ne ₦300
Za'a biya kudin ta wannan account
0084279025
Usman Umar Mansur
Accces bank
Sai a tura shaidar biya ta wannan Number
08137237071
BABI NA SHA TARA
A can birnin Zainul-Ansar kuwa sai da aka shafe tsawon kwanaki uku ana bawa sarki
Nu'umanu kulawa sosai ya warke sumul. A iya tsawon waɗannan kwanaki wannan hadimi mai
ɗauke da siffa irin ta waziri Yazid shi ne ke lura da dukkanin wani sha'ani na masarauta, kuma
duk bayan wani lokaci sai ya ziyarci turakar sarki ya ga a wane hali yake ciki a sirrance batare
da wani ya gane shi ba.
A ɓangaren sarkin yaƙi lauzar kuwa shi ma ya gudanar da aiyukan da waziri ya umarce shi
batare da wata matsala ba.
A safiyar wata rana ne sarki Nu'umanu ya aike wa da dukkan 'yan majalisar shi da saƙon
zaman majalisar zartarwa,
Sa'adda sarki ya ga cewa kowa ya hallara a fadar kuwa an yi shiru sai ya yayi gyaran murya ya
ce "Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki bisa iko da ya bamu na halartar wannan taro
mai albarka, tsira da amincin shi su ƙara tabbata ga Manzon tsira, bayan haka ya ku dattawam
wannan masarauta tamu mai albarka bakomai ne ya sanya na tara ku a anan ba sai domin
tattaunawa akan abin da ya faru a wannan birni namu na harin bazato daga maƙiya, shin yanzu
wa ake tunanin ya kawo mana farmakin, sannan wane mataki ya dace mu ɗauka domin kare
afuwar hakan?
Sa'adda sarki ya zo dai-dai nan a jawabin shi sai fadar ta yi tsit babu wanda yace ƙala
tsawon daƙiƙa talatin sai daga bisani ne wani kyakkyawan saurayi ma'abocin kwariji wanda shi
ne magatakarda ya yi gyaran murya ya ce "Ya 'yan uwana dattawam wannan masarauta mai
albarka ku yi sani cewa abin da bincike ya tabbatar mini a harin bazato da aka kawo mana
tabbas anyi amfani da shiri,
Hujja ta farko shi ne masu ba su ƙyale wata alama da zamu iya bincike akai ba tun daga
gawarwakin dakarunsu, takobi ko tufafi,
Hujja ta biyu lokacin da na hallaka wani ɗan MAMAYAR BAZATO naga hatimin wata masarauta
a jikin sulkenshi sai dai ban tsaya na lura da na wace masarauta ba ne,
Waɗannan hujjoji da na zayyana za su tabbatar mana da cewa waɗanda suka kawo farmakin
sun kasance ma'abota bautar wanin Allah,
Ta wata fuskar zan iya cewa da alamu akwai wani munafuki a cikinmu da labartawa sarki
Rakibu tattaunawar zaman da mu kayi a makon da ya gabata".
Lokacin da magatakarda ya zo dai-dai nan a zancen shi sai kowa ya sha jinin jikinshi kuma ya
zurfafa izuwa kogin tunani, wannan hadimi mai ɗauke da siffa irin ta waziri da sarkin yaƙi Lauzar
kuwa sai suka ji hantar cikinshi ta kaɗa da ƙarfi suka dinga yiwa junansu inkiya ta wutsiyar
idanu batare da wani ya lura da su ba. Shugaban Baitul-Mali yayi gyaran murya sannan ya ce "Hakiƙa abin da magatakarda ya faɗi
zai iya zamowa gaskiya, domin kuwa idan bamu manta ba Ubangiji ya faɗa a cikin littafinshi mai
tsarki cewa kar mu riƙe kafirai a matsayin masu jiɓintar lamuran mu, domin su na yin umarni ne
da hanyar shaiɗan... Kafin ya gama rufe bakinshi magatakarda ya tari numfashi yana mai cewa "Ban katse ka ba ta
kai ma'aji amma kafi kowa sanin cewa ba ma da wata hujja da za mu iya tuhumar sarki Rakibu
bisa zargin da muke yi mishi, sannan kar ka manta cewa shi ne sarki da yafi kowa kyautata
zumunta da zaman lafiya tsakanin mu da shi a kaf masarautun dake wannan nahiya tamu.
Shawarar da zan bamu anan ita ce tsaurara matakan tsaro domin a fahimta ta sakacin dakaru
masu tsaron ƙofa shi ne ya haifar da MAMAYAR BAZATO, wannan ita ce shawarata Allah ya
taimake ka".
Lokacin da waziri Yazid yazo nan a zancen shi sai zauren majalissar ya sake yin shiru a karo na
uku tsawon daƙiƙa talatin ana cikin wannan hali babu wanda ya ce uffan, koda ganin hakan sai
sarki Nu'umanu ya miƙe daga kan karagarshi yayi gyaran murya a karo na biyu sannan ya buɗi
baki ya ce "Ya ku 'yan majalissata ku yi sani cewa tun da bamu tsayar da magana ɗaya ba, ya
zama wajibi mu sake dogon nazari domin nemo bakin zaren, amma kafin wannan lokaci ba
shiru za mu yi ba dole ne mu ƙara ƙarfin mayaƙanmu dodon tsaurara matakan tsaro, sannan
akwai buƙatar mu yawaita idanuwansu a cikin al'umma domin samun bayanan sirri, da wannan
batu nake yi maku fatan alheri sai Ubangiji maɗaukakin SARKI ya sake haɗa fusakun mu".
Koda gama faɗin hakan sai ya sauko ƙasa yana takawa da ƙafafuwanshi ya durfafi wata ƙofa
ta musamman dakaru ma'abota fararen tufafi suka mara mishi baya har sai da suka ƙule izuwa
cikin ƙofar, sannan taron ya watse kowa ya kama gabanshi.
Wannan shi ne abin da ya wakana a can birnin Zainul-Ansar bayan harin sumane daga dakarun
haɗin gwiwa.
Dukkan abin da ya wakana a wannan tattaunawa da sarki Nu'umanu ya yi da 'yan majalisar
shi, sarki Rakibu da waziri Yazid sun gani a cikin madubin tsafin waziri a lokacin da suke zaune
a wani lambun shaƙatawa, koda ganin wannan al'amari sai hankalin sarki Rakibu ya
DUGUNZUMA ainun ya dubi waziri cikin matuƙar damuwa ya ce "Ya abokina tabbas a yanzu
muna halin TSAKA MAI WUYA idan har sarki Nu'umanu ya gano cewa mu ne muka kai mishi
MAMAYAR BAZATO".
Koda jin wannan batu sai waziri ya yi shiru yana mai juya al'amarin a cikin ranshi, daga bisani
ya tattare hankalin shi waje guda ya dubi Rakibu ya ce "Ya kai babban aminina Kabul sani cewa
koda ace sarki Nu'umanu ya gano shirin mu wannan ba zai sanya mu janye aniyar mu ta kawar
da shi daga doran ƙasa ba, babban abin da nake ganin zai iya haifar mana da matsala shi ne
ma'aji Kulairu,
Na fi kowa sanin wane shi domin mutum mai naci da juriya akan dukkan abin da ya sanya a
gaba sai ya cimma nasara, ya zama wajibi a gare mu mu gana da shi a wannan dare, sannan
za mu nufi birnin Zainul-Ansar ta dakarun yaƙin mu amma ba zamu kai farmaki ba sai lokacin
da alfijir ya keto za a gudanar da sallar asuba, ina mai tabbatar maka da cewa zamu samu
gagarumar nasara a wannan karon".
Lokacin da waziri ya zo dai-dai nan a zancen shi sai sarki Rakibu ya cika da matuƙar farin ciki
maral-musaltuwa.
Wannan shi ne abin da ya wakana tsakanin waziri Yazid na gaskiya da sarki Rakibu bayan
sun ga dukkan tattaunawar sarki Nu'umanu da 'yan majalisar shi.
Mu haɗu a Littafin TAFARKIN TSIRA 11 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
TAFARKIN TSIRA 11
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
ELEGANT ONLINE WRITER'S
Littafan Marubucin
Kogon Annoba
Sarautar Mutuwa
Kangin Bauta
Jaruman Duniya
Takobin Ɗaukaka
Ƙarshen Zalunci
Fataucin Bayi
Sarkin Sadaukai
Goga Sha Fama
Tafarkin Tsira
Gasar Sarauta
Kundin Al'ajabi
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Rayyan sai jama'a suka samu ƙarfin gwiwa dukkan
fargaba,
Lokacin da yazamana tarar da ke tsakanin rundunonin biyu bai huce taku talatin ba sai
kowanne ya ja ya tsaya aka yi kallon-kallo na tsawon daƙiƙa hamsin daga bisani sai sarki
Lamsarul-Azlam ya ƙatse shirun da wanzu ta hanyar bushewa da dariyar mugunta sannan daga
bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da SAƙON MUTUWA ya buɗi baki cikin
kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce "Ya kai tsohon abokin gaba kuma sarki mai
taurin kai wajen biyayya a gare mu ka yi sani cewa yau ita ce rana ta ƙarshe da zan shafe
tarihin ka daga doron ƙasa, domin kai ganau ne ba jiyau ba kuma ko ba a gwada ba linzami ya
fi ƙarfin bakin kaza, kuma wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, ba za ka iya ja dani domin har
abada ruwa ba sa'an kwando ba ne..."
Kafin ya gama rufe bakinshi sarki Rayyan ya tari numfashin shi yana mai daka mashi tsawa ya
dube shi ya ce "Karya kake ya tsahon mafi amana ka yi sani cewa komai matuƙar yawan
rundunarka bazai firgita ni ba domin Ubangiji shine mai bayar da nasara, sannan har abada
ƘARYA DA GASKIYA ba sa haɗuwa waje guda guda face gaskiya ta yi RINJAYE.
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Rayyan sai Lamsarul-Azlam ya fusata ainun gashin
jikin shi ya mimmiƙe kawai sai ya zare wata sharɓeɓiyar Adda mai matuƙar KAIFI DA TSINI ya
sakarwa dokinshi linzami yana ihu da kururuwa mai firgitarwa ya durfafi sarki Rayyan, koda
ganin hakan sai shi ma ya yi koyi da shi ta hanyar zare takobinshi ya yi ɗauki kanshi yana ƙwala
kabbara, lokacin da suka zo daf da juna sai Lamsarul-Azlam ya kai mishi wawan sara a kafaɗa,
cikin matuƙar zafin nama Rayyan ya sanya garkuwarshi ya kare harin sannan suka ruguntsume
da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, suka yi KARON BATTA irin na
GWARAZANA JIYA.
Lokacin ɓangarorin biyu suka ga cewa jagororin su sun ruguntsume da artabu sai suka ɗaga
makaman su suka yi ɗauki kan juna kafurai na ihu da kururuwar banza, musulmi na kabbara
lokacin da aka haɗu sai aka rincaɓe da BAƘIN ARTABU ƙarar karafniyar ƙarafa haɗe ihu da
kururuwar mazaje ta cika dodon kunne. Haƙiƙa yaƙi shine matattarar dukkan wata musiba da zata samu ɗan Adam a doron ƙasa,
domin yaƙi shine ke raba uwa da ɗan ta, asarar dukiya da rayuwa ma baki ɗaya.
Kaico! Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da kofatun dawakai ke kartar ƙasa
suna tayar da ƙura, Hargowar aljanu da bil'adama JINI DA KASA suka cakuɗe waje guda
MUTUWAR MAZAJE ta fara gudana dole ya ɗimauce.
Wannan shi ne abin da ya faru a lokacin da sarki Lamsarul-Azlam da rundunarshi suka isa
izuwa birnin MADINATUL-AFNAN.
BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA
Al'amarin shugaban'yan fashin duniya sadauki fitinatul-Amir kuwa lokacin da ya baro fada
cikin matuƙar fushi bisa ga amsar tambayar da ɗan majalisa Haibatu ya faɗa mashi akan cewa
yau tsawon kwanaki uku bai fito zaman fada ba, sai ya huce kai tsaye izuwa turakar su yaro
Usaiba domin ya tabbatar da zargin da zuciyarshi take yi, lokacin da ya isa masu gadi suka
buɗe mashi ƙofar turakar ya kunna kai izuwa ciki sai ya tarar da suna sharar barci a bisa kan
gado, domin haka sai ya isa bakin gadon cikin hanzari ya sanya hannunshi ya ɗage jigar dake
jikin Usaiba ya duba gadon bayanshi, aikuwa sai ya ga wayam babu zanen hatimin takobin
SAIFUL-ZAYYAD, domin haka sai ya juya ya fice daga turakar zuciyarshi cike da matuƙar
mamaki ainun,
Abu na farko da ya bashi mamaki shine shin mene ne yasanya zuciyarshi take bugawa da ƙarfi
a duk lokacin da ya yi arba da yaro Usaiba,
Anya kuwa uwargidanka Rusayyat ba zata ci Amanar ka ba ta tseratar da rayuwar yaron.
Wata zuciyar kuma ta ce da shi ta ya ya kake tsammanin zata ci amanar ka bayan cewa za ta fi
kowa burin ace ta samu haihuwa domin samun magaji. Lokacin da yazo dai dai nan a tunanin
shi sai hankalin shi ya kwanta ya ji ya gamsu cewa yaro Usaiba ba shine mai hatimin takobi ba.
Wannan shi ne abin da ya faru da sarkin 'yan fashin duniya sadauki fitinatul-Amir.
Fadar ta ƙawatu ainun da nau'ikan kayan ƙawa gami da alatun jin daɗin rayuwar duniya har
da abin da idanu ba su taɓa gani ba, duk ƙasaitar BASARAKE ko