Showing 12001 words to 15000 words out of 28793 words
Chapter 5 - TAFARKIN TSIRA Book Complete by Sarkin Marubutan Yaki .pdf
tunani mai zurfi domin samun mafita, Bayan shuɗewar daƙiƙa ashirin ta samu
mafitar, Sai dai mafitar na da matuƙar wahalar gaske abin da za ta yi shi ne dole ta ɗauko wani
garin magani dake ajiye a turakar mai gidanta,
Garin magani na farko zata yi amfani da garin maganin wajen shafawa Usaiba a gadon
bayanshi domin ɓatar da zanen hatimin takobin,
Garin magani na biyu kuwa shi ne zai bayyana zanen hatimin idan aka shafa shi,
Nan fa hankalin ta ya sake ɗugunzuma ta sake zurfafa cikin Kogin tunani domin samun hanyar
da zata shiga turakar mai gidannata har ta ɗauko garin maganin cikin sirri ba tare da asirin ta ya
tonu ba,
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin shugaban'yan fashin duniya Sadauki Fitinatul-Amir tare
da uwargidanshi jaruma Rusayyat.
BABI NA GOMA
Dakaru ne shirye cikin gagarumar shigar yaƙi su kimanin ɗari biyu riƙe da miyagun makamai
suna tafe cikin hanzari, kallo ɗaya zaka yi masu ka fahimci cewa sun kasance azzalumai n
gaban kwatance, Abin da zai tabbatar maka da hakan shi ne idan ka yi duba da fuskokin su sai
ka yi tsakanin basu taɓa dariya ba. Kai tsaye kasuwar birnin suka durfafa wacce ta cika maƙil da jama'a, duk inda mai kallo ya
kai duban shi babu abin da zai gani face masu siye da siyarwa na yi, Duk wajen da dakarun
suka durfafa a cikin kasuwar sai dai ka ga jama'a na dare suna buɗe masu hanya tare da tattare
kotsan su tamkar sun hango mutuwar su, Haka dai dakarun suka ci gaba da kutsawa saƙo da lungu na kasuwar suna muzurai tamkar za
su ci babu, Sai da suka shafe tsawon daƙiƙa hamsin suna tafiyar sannan suka iso wani
ƙasaitaccen gida mai girma da faɗin gaske da aka yi ginin shi da zallar duwatsun wuta masu
ƙwarin gaske, Ba tare da wani jinkiri ba wani garjejen ƙato daga cikin mayaƙan ya matsa daf da
ƙofar ya ƙwanƙwasa har sau uku da ƙarfi.
Jim kaɗan da faruwar hakan sai ƙofar ta buɗe kwatsam! sai ga wani dattijo ma'abocin cikar
kamala ya fito daga cikin gidan hannunshi riƙe da wata jakar fata, Sannu a hankali har iso izuwa
inda dakarun suke ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa ga wani Sadaukai daga cikin dakarun
wanda da alama shi ne shugaban su, Cikin matuƙar fushi shugaban dakarun ya saka mashi tsawa da ta sanya hantar cikin shi ta
kaɗa ya dube shi ya ce "Ya kai Isham shin ina harajin mai girma Lamsarul-Azlam da ka saba
bayarwa?,
Cikin dattijon na tsuma ya ajiye jakar dinaren da ke hannun shi muryar shi na sarƙewa ya ce
"Ka.. ga..far ce ni ya shuga.. bana bisa jinkirin fi..to..wa na tare ku har ku..ka iso nan".
Shugaban dakarun mai suna Shahral ya bushe da dariyar mugunta sannan daga bisani ya
murtuke fuska cikin kakkausar murya ya dubi wani Barde dake tsaye a hannun shi na dama ya
ce "Ya kai Ruhaizu yi hanzari ka lissafa mani dinaren da ke cikin wannan jaka.
Kafin shugaba Shahral ya gama rufe bakin shi Barde Ruhaizu ya tsugunna ƙasa ya shiga
lissafa dinaren, jim kaɗan ya dubi shugaba Shahral cikin ladabi ya ce "Dinaren ya cika yadda
ake bukata ya shugabana".
Ko da jin wannan batu sai Shahral ya gyaɗa kai alamar gamsuwa sannan ya dubi dattijon
ya ce "Sai ka kasance cikin shiri domin a koda yaushe zamu iya dawo wa domin sake ƙarbar
wannan haraji.
Yana gama ya juya ya shige gaba sauran dakarun suka mara ma shi baya suka sake nausa
wa cikin kasuwar suna tafiya cikin hanzari,
Suna cikin wannan tafiya ne kwatsam! bazato babu tsammani sai suka hango wata tsaleliyar
kyakkyawar Budurwa tana sanye cikin fararen tufafi masu yalwa a gadon bayanta ta na rataye
da wata sharɓeɓiyar takobi a cikin kubenta, ta tunkaro inda dakarun suke babu alamun tsoro a
tare da ita,
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa dakarun mamaki kenan kuma ya ɗaure masu kai, domin tun
da suke fitowa wannan ran-gadi hakan bai taɓa faruwa ba, da alamu wannan budurwa baƙuwa
ce, amma koma dai baƙuwa ce ai ya kamata ace kwarjinin su ya firgita ta ?,
Amsar tambayar da dakarun suka kasa bawa kan su kenan,
Sa'adda da ya zama tazarar dake tsakanin su bata huce taku goma sai dakarun suka ja suka
tsaya aka fara kallon-kallo tsakanin su da budurwar.
Daga can sai budurwar ta taka da ƙafafuwanta ta durfafi inda dakarun ke tsaye batare da
fargabar komai ba, kafin dakarun su farga ta shammace su ta daga wawan tsalle ta dira a daf
da wani badakare ta warce jakar dinaren dake hannunshi ta rataya a gadon bayanta, sannan ya
dunƙule hannayenta biyu ta gabza mashi wawan naushi a wuya, nan take wuyan na shi ya
ƙarye ya yi ƙara ruƙus! Ƙas, take ya faɗi ƙasa ko shurawa bai yi ba,
Ko da dakarun suka yi arba da abin da ya faru da Barde Ruhaizu sai suka firgita ainun,
zukatansu suka kama tafarfasa tamkar za su ƙone.
Abin da ya firgita su ɗin shi ne shin ya aka yi budurwar ta samu irin gagarumin ƙarfi da ta
kashe ɗaya daga cikin su bayan cewa tun da suke fitowa wannan ran-gadi hakan bai taɓa
faruwa ba,
Abin da ya fusata su ɗin shi ne ta ya ya za a mace guda ɗaya jal! ta bayyana a gare su kuma
har ta yi GABA DA GABA da su,
Lokacin da dakarun suka zo nan a tunanin su sai sai shugaba Shahral ya buɗe su ya dakama
su tsawa dake nuna basu umarni su afkawa budurwar,
Cikin matuƙar fushi dakarun suka yi ɗauki izuwa gare ta suna ihu da kururuwa mai firgitarwa,
Ko da ganin hakan sai budurwar ta dunƙule hannayenta biyu ta gwara tsayuwa domin fafatawa,
Al'amarin da ya sanya shugaba Shahral ya bushe da dariyar mugunta kenan bisa ganin cewa
budurwar ta yi wauta da ta kusanci mayakan ba tare da ta riƙe wani makami ba.
Lokacin da aka haɗu sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, Ban tsoro
gami da tashin hankali,
Dakarun suka wanzu suna kai Budurwar sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da
bajinta,
Ita kuwa ta wanzu ta na zillewa hare-haren su cikin zafin nama gami da mayar da martani ta
hanyar zabgawa dakarun naushi a sassan jikkunan su,
Duk inda ta nausa ɗin sai ka ga jini ya taru idan a baki ko hanci ne sai kaga yana yoyon jini,
Nan fa dakarun suka suka dinga zubewa ƙasa magashiyan.
Wohoho! Haƙiƙa duk wanda Allah ya ba shi jarumtaka ya more, kuma gaskiyar masu iya
magana da suka ce "Duk wanda ya isa ya huta" inda a ce mutum yana tsaye a wannan waje
lokacin da budurwar ke ragargazar dakarun tamkar tana sassabe a gonar audiga dole ne ya
jinjina mata ya tabbatar da cewa ta cika JARUMAR ASALI. Cikin abin da bai gaza daƙiƙa hamsin dakarun Shahral suka hargitsa kasuwar, domin duk
sa'adda suka kaiwa budurwar hari da takubban su idan ta zillewa harin duk abin da takubban su
suka sauka a kai sai ka ga ya yi bindiga ya tarwatse,
Rumfunan kasuwa kuwa a dinga rushe su ana bazar da su a ƙasa,
Nan fa jama'a suka shiga yin guje-guje gami da ifice-ifice domin TSIRA DA RAYUKAn si,
Lokacin da ya zamana an shafe tsawon rabin sa'a ana wannan ɗauki ba daɗi sai ya zamana
budurwar ta samu nasarar hallaka fiye kaso ɗaya bisa biyu na dakarun.
Sa'adda sadauki Shahral ya ga irin gagarumar ɓarnar da budurwar ke yi mashi sai ya fusata
ainun ya dakawa sauran dakarun suka ja da baya, kawai sai ya dako wawan tsalle sama tamkar
an harbo shi daga cikin baka yana saman ya zare waɗansu waɗansu zaratan takubba a gadon
bayan shi ya kaiwa budurwar wawan hari da nufin tsinke mata wuya, Cikin baƙin zafin nama zare takobinta ta kare harin,
Sannan suka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, firgici da tashin hankali, Ana
cikin wannan fafatawa ne sauran dakarun suka saci jiki suka fice daga kasuwar a bisa
dawakansu suka kunna kai cikin gari tafiyar daƙiƙa hamsin kacal suka yi suka iso fadar birnin.
Fadar ta kasance ƙasaitacciya da aka ƙawata ta da nau'ikan kayan more rayuwa, Gaba ɗaya
ginin fadar an yi shi ne da waɗansu irin duwatsu masu ƙyalli tamkar gilashi, A wannan lokaci
fadar ta cika maƙil da jama'a 'yan majalisa na zaune bisa ƙayatattun shimfiɗu na alfarma,
kuyangi, Hadimai, Barori haɗe da dakaru na kai komo suna hidima. Zaune bisa wata ƙasaitacciyar karagar mulki sarki Lamsarul-Azlam ne ya hakimce sanye
ya ke cikin ƙayatattun tufafi na alfarma ya ɗora ƙafa ɗaya-kan-ɗaya ana gudanar da sha'anin
mulki cikin annashiwa,
Sannu a hankali dakarun Sadauki Shahral suka shigo fadar lokacin da ya zamo tazarar dake
tsakanin su da karagar mulki bai huce taku goma ba sai suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa
wani cikin su ya buɗi baki cikin ladabi kanshi a sunukye ya yi gyaran murya ya ce " Ya
shugabana bayan mun samu nasarar ƙarɓo jakar dinare daga hannun Sarkin kasuwa Isham
kamar yadda muka saba sai mu ka yi gamo da wata hatsabibiyar jaruma har ta samu nasarar
kwace jakar daga gare mu,
Kafin badakare ya gama rufe bakin shi Sarki Lamsarul-Azlam ya nuna badakaren da yatsan shi
na hagu nan take wata irin gagarumar wuta ta kama ci a jikin shi nan badakaren ya shiga ihu da
kururuwa, kafin cikar daƙiƙa ashirin ya ƙone ƙurmus,
Lamsarul-Azlam ya taƙarƙare ya kwarara ihu, daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko
mashi da Wasikar Mutuwa,
Sannan ya buɗe bakinshi ya shiga karanta waɗansu dalasiman tsafi, Ya na gama furta
dalasiman sai ga wani shirgegen muridi ya bayyana a fadar,
Shi dai muridin yakasance mai matuƙar tsawo, kauri da kauri, yana da rafkeken kai mai ɗauke
da manyan idanu jajaye tamkar garwashi, ƙofofin hancin shi manya ne tamkar mazirarin iska,
Gaba ɗaya jikinshi cike yake da gashi buzu-buzu tamkar wani tsohon mahaukaci,
Haƙiƙa komai dakewar zuciyar mutum idan ya yi arba da muridin dole ya ɗimauce,
Sa'adda jama'a suka yi arba da muridin sai suka firgita ainun, amma saboda matuƙar tsoron
sarki Lamsarul-Azlam sai kowanne ya zauna a wajen zaman shi cikin tashin hankali, Su kansu
dakarun fadar a matuƙar razane suke,
Maridin ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa, Sarki Lamsarul-Azlam ya dube shi
ya ce "Ya kai Zabratul-ukub ka yi sani cewa bakomai ne ya sanya na kirawo ka nan ba sai
domin ina so ka tafi izuwa kasuwar dake cikin birni na inda dakaruna ke fafata yaƙi da wata
jaruma ka dauko mani jarumar ina so ka kawo mani ita cikin ƙoshin lafiya". Ko da jin wannan umarni daga bakin Lamsarul-Azlam sai maridi Zabratul-ukub ya ɓarke da
wata irin mahaukaciyar dariya wacce ta bayyana wargatsattsun haƙoran shi marasa kyawun
gani har wani irin taririn baƙin hayaƙi na fita daga cikin su,
A lokaci guda ya turɓune fuska cikin wata irin kakkausar murya mai kama da saukar aradu ya
ce "Ya shugabana ai wannan aiki tamkar shaƙar numfashi ne a waje na na rantse da girman
halarar tsafin ka zan kawo maka jarumar cikin ƙoshin lafiya,
Ko da gama faɗin hakan sai ya ɓace ɓat! tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Sarki Lamsarul-Azlam sai ya shiga ɓaɓɓaka dariyar mugunta tamkar ba zai daina ba.
Lokacin maridi Zabratul-ukub ya ɓace daga fadar sarki Lamsarul-Azlam bai bayyana a ko ina
sai a wajen da shugaba Shahral ke fafatawa da kyakkyawar Budurwar nan,
A wannan lokaci budurwar ta samu nasarar hallaka haɗawa shugaba Shahral jini da majina sai
layi ya ke yi jiri na ɗibar shi tamkar wanda ya sha barasa,
Sa'adda jama'a suka yi arba da maridi Zabratul-ukub sai suka fara cika wandon su da iska suna
zurawa da gudun tsiya wasu har da sakin fitsari a wando saboda matuƙar tsoro, Kai hatta
dakarun dake wajen ba a bar su a ba ya su ma dafe ƙeya suka yi suka sura da gudu domin a
zaton su sarki Lamsarul-Azlam ya aiko da wata musiba domin ta hallaka kowa, Kafin ƙiftawar ido babu kowa a filin kasuwar sai wannan kyakkyawar Budurwa,
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin ta da Zabratul-ukub,
A iya tsawon rayuwar Budurwar bata taɓa ganin halitta mai muni da kwarjini tamkar wannan
maridi ba, kawai dai ƙarfin hali ne irin na JARUMAR ASALI.
Sai da daƙiƙa talatin ta shuɗe ana wannan kallon-kallo tsakanin su tamkar ba za su afkawa
juna ba,
Kawai sai Zabratul-ukub ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu da ya firgita duk wata halitta dake
birnin gidaje suka dinga rushe suna faɗawa kan al'umma suna hallaka, ba shiri kyakkyawar
Budurwar ta sanya hannayenta ta tsohe kunnuwanta, tsawon daƙiƙa talatin ana cikin wannan
hali sai daga bisani ne Zabratul-ukub ya tsuke bakinshi sannan komai ya samu dai-dai ta, Kawai sai ya kaiwa budurwar cafka da hannunshi, cikin wani irin baƙin zafin nama budurwar ta
daka tsalle gefe guda ta zillewa harin, abu kamar wasa sai ga shi budurwar ta tsallake harin shi
fiye da goma,
Al'amarin da ya fusata shi kenan ya ce a cikin ran shi yanzu ace GWARZON ƘARNI tamka ta
halitta guda ɗaya ta gagare ni tabbas wannan abun kunya ne,
Ko da ya zo nan a tunanin shi sai ya kawai ya shammaci budurwar ya ƙirɓa mata wani wawan
naushi a fuska, saboda ƙarfin naushin sai da ta yi sama tamkar an janye ta da ƙungiya sannan
daga bisani ta faɗo ƙasa tim! a matuƙar galabaice hancinta da bakinta na yoyon jini, har a
wannan lokaci jakar dinaren da ta ƙarɓa daga hannun dakarun tana goye a gadon bayanta. Ko da samun wannan gagarumar nasara sai maridi Zabratul-ukub ya bushe da dariyar
farin ciki ya sanya hannunshi ɗaya ya ɗauki budurwar tamkar bil'adama ya ɗauki tuffa a tafin
hannunshi, sannan ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Abin tambaya a nan shi ne daga ina wannan budurwa ta fito kuma mene ne dalilin da ya sanya
ta kwace jakar dinaren dake hannun dakarun sarki Lamsarul-Azlam suka karɓo a wajen dattijo
Isham,
Dalilin hakan kuwa shi ne Kamar haka:-
Mu haɗu a littafi na 6 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga Mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubuta Littattafan yaƙi
08137237071
TAFARKIN TSIRA
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaki
Wthapp Number
08137237071
BABI NA SHA ƊAYA
MADINATUL-AFNAN
Ƙasaitaccen birnin ya bunƙasa ainun a ƙarfin tattalin arziki, yawan al'umma gami da zaratan
mayaƙa masu juriya a filin fama,
Gaba ɗaya jama'ar birnin suna da kyawawan halaye da mu'amala mai nagarta, hakan ya samo
asali ne saboda kasancewar su ma'abota addinin musulunci,
Wannan al'amari ya janyo hankalin fatake daga sassan nahiyoyin duniya zuwa birin domin yin
hulɗar siye da siyarwa, domin haka sai ya zamo tattalin arzikin birnin yana bunƙasa cikin
ƙanƙanin lokaci kuma birnin ya zamo zarra a nahiyar,
Al'amarin da ya sanya biranen dake nahiyar suka kwallafa ran su akan ginin bayan birnin daga
doron ƙasa amma Ubangiji baya ba su nasara.
Sarkin dake mulkin birnin yakasance dattijo ma'abocin kamala da sadaukantaka mutum ne
mai son cigaban al'ummar shi ana kiran shi da suna RAYYAN IBN HUSSAIN Yana da matar
aure guda ɗaya wacce ta haifa ma shi wata kyakkyawar 'ya da ake yiwa laƙabi da NUWAIRAT,
Tabbas masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce barewa ba za ta yi gudu ba ɗanta ya yi
rarrafe,
Kamar yadda Sarki Rayyan yakasance GWARZON ƘARNI haka 'yarshi gimbiya NUWAIRAT ta
kasance, domin a gaba daya birnin MADINATUL-AFNAN bayan sarki Rayyan babu jaruma
tamkar ta, hatta kyawun halaye da tausayin al'umma Nuwairat ta gaji mahaifinta.
Tsakanin Sarki Rayyan da Sarki Lamsarul-Azlam ba a ga maciji ga juna, Lamsarul-Azlam ya
zo ya kaiwa Rayyan harin bazato fiye da arba'in domin ya ga ya tunɓuke shi daga kan karagar
mulki ya mallaki tarin arzikin dake birnin MADINATUL-AFNAN,
Wata rana sarki Rayyan na kwance a bisa gadon sarauta sai ya yi mugun mafarki daya sanya
ya kasa rintsawa abin da ya gani a mafarkin shi ne sarki Lamsarul-Azlam ya na haɗa wani
sinadarin tsafi wanda da zarar ya kammala zai samu nasara akan shi, sinadarin zai yi amfani da
dukiyar da sarki Rayyan ke amfani da ita, Bisa wannan dalili ya sanya sarki Rayyan ya umarci gimbiya NUWAIRAT ta tafi zuwa kasar
Darul-Ashmar domin ta hana dakaru karɓar dinaren dake hannun sarkin kasuwa Isham,
Kuma a halin yanzu dinaren da gimbiya Nuwairat ta kwace daga hannun dakarun sune kaɗai
suka rage wa sarki Lamsarul-Azlam ya mallaka domin kammala sinadarin tsafin.
***
Sa'adda Rusayyat uwar gidan shugaban 'yan fashin duniya sadauki fitinatul-Amir ta zurfafa
izuwa kogin tunani domin samun mafita akan hanyar da zata shiga turakar mai gidanta ta ɗauko
garin magani na sihiri, Domin ta tseratar da rayuwar Usaiba mai hatimin takobi, Sai ta shafe
tsawon daƙiƙa talatin a cikin wannan hali ba tare da ta samu mafita ba, Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin ta kenan ta shiga damuwa ainun, Haka dai ta
cigaba da nazarin daga bisani ne ta samu mafitar, ko da samun mafitar sai kawai ta miƙe tsaye
zumbur