Showing 1 words to 3000 words out of 28793 words
Chapter 1 - TAFARKIN TSIRA Book Complete by Sarkin Marubutan Yaki .pdf
TAFARKIN TSIRA
RUBUTA LABARI
MANSUR USMAN SUFI
SARKIN MARUBUTAN YAƘI
Wthapp number
08137237071
Babi na ɗaya
A wani zamani can baya mai tsawo daya shuɗe an yi wani birni a yankin ƙasashen larabawa
mai suna ZAINUL ANSAR.
Birnin zainul-Ansar ya tara manyan kabilu iri daban -daban suna da arzikin noma, kiwo da
tattalin arziki,
Duk da kasancewar su mabanbanta ra'ayi amma suna zaune lafiya babu tashe-tashen hankula.
Wannan ya samo asali ne saboda bisa kyakkyawan shugabanci da sarkin birnin ke zartar wa,
wannan sarki ana kiransa da suna nu'umanu.
Sarki Nu'umanu yakasan ce mashahurin sadauki kuma JARUMIN JARUMAI kuma masani a
fagen ilimin addinin musulunci,
A rayuwar Sarki Nu,umanu babu abinda ya ke dugunzuma hankalin shi sama da abu biyu,
Na farko shi ne rashin Haihuwar matar shi mai suna lawisat, Tun suna saurayi da budurwa su
ka yi aure amma har girma ya fara kama su basu samu haihuwa ba.
A bu na biyu shine akwai wata ƙasa ta kafurai dake makwabtaka dasu suna da mu'amala
mai karfi ta zaman amana atsakanin su,
Tun zamanin mahaifin sarki nu'umanu yake ta ƙoƙarin ya ga cewa sun ƙarbi musulunci amma
har ya mutu basu daina bautar gumaka ba,
Hawan Sarki Nu'umanu ne ya yi tunanin cewa zai nemi duk hanyar da ya kamata domin ya ga
cewa sun ƙarbi musulunci koda kuwa yaƙi zai faru tsakanin su.
Bisa wannan dalili ne yasanya ya tara dukkanin yan majalissar shi domin tattaunawa bisa
wannan al'amari.
Ko da sarki Nu'umanu ya ga cewa dukkanin 'yan majalissar shi sun hallara a ɗakin taron
kuma shiru ya wanzu sai ya miƙe tsaye ya yi gyaran murya a karo na farko bayan ya gabatar da
salati ga Manzon Allah (s.a.w)
Kana daga bisani ya cigaba da cewa "Ya ku 'yan majalissa ku yi sani cewa bakomai ne yasanya
na tara ku a nan ba sai domin mu tattauna game da al'amarin Sarki Rakibu,
Sanin kanku ne cewa mahaifin sarki Rakibu amini ne a wajen mahaifina, Abbana ya yi ƙoƙari
domin ya ga cewa sarki Zaidur ya karbi addinin musulunci amma hakan ya faskara akwana a
tashi yanzu ni ne a bisa KARAGAR MULKI shin yanzu haka zamu zuba idanu ana bauta wanin
Allah SWT?. Sa'adda sarki Nu'umanu ya zo nan azancen shi sai daƙin taron ya yi shiru a karo biyu,
Tsawon daƙiƙa ashirin babu wanda ya ce uffan daga bisani waziri Yazid ya yi gyaran murya a
karo na farko ya ce "Allah ya taimaki sarki ina ganin ba ya cikin tsarin addini da koyarwar
magabata a tilas mutum shiga musulunci face shi da kan shi ya ga Yakamata ya shiga,
Ina ganin kyauta ta mu'amalar mu da su shi n zai sake zaburo da zuciyar su zuwa ga addinin
Allah SWT.
Sa'adda waziri ya zo nan a jawabin shi sai zuciyar sarki Nu'umanu ta harzuƙa ainun Amma
sai ya bar abin a ran shi, ko da cewar maganar waziri ta na kan TURBAR GASKIYA,
Sarkin fada wanda ake kira da kizalu shine ya miƙe tsaye ya yi gyaran murya ya ce "Ya
shugabana ina ganin abin da ya kamata a yi shi ne a tura wasiƙa zuwa ga sarki Rakibu a
kwaɗaita ma shi musulunci da irin garaɓasar da zai samu idan ya shiga tare da jama'a shi,
Tun da tsakanin mu da shi akwai fahimtar juna matuƙa da wahala ya yi watsi da tayin da muka
yi ma shi,
Duba da cewa mun zame ma shi tamkar garkuwa, kuma mune karfin tattalin arzikin su baki
ɗaya daga mu ne suke samun ingantaccen tsaro, kayan masarufi".
Lokacin da sarkin fada kizalu ya zo nan a jawabin shi sai sarki Nu'umanu ya cika da matuƙar
farin ciki domin yana da tabbacin kizalu ya kawo shawara mai kyau.
Shugaban baitul-mali ne ya miƙe tsaye ya fara magana a karo na farko tun shigowar shi
ɗakin taron ya ce "Allah ya taimaki waziri ya shugabana kada ka manta cewa tsawon shekaru
muna kyauta ta mu'amalar mu da mutanen sarki Rakibu amma ga shi ɗayan su bai shiga
addinin Musulunci ba ina ganin shawarar sarkin fada ita ce mafita, idan ma har suka karɓi
karɓar tayin da muka yi masu a cikin wasiƙar za mu yanke duk wata hulɗar kasuwanci tsakanin
mu, wannan shi ne ra'ayi na Allah ya taimaki waziri".
Sa'adda shugaban baitul-mali ya zo nan a zancen shi sai ɗakin taron ya sake yin shiru a
karo na uku,
A wannan lokaci sai da aka shafe tsawon lokaci babu wanda ya ce uffan.
Ko da ganin hakan sai sarki Nu'umanu ya yi gyaran murya a karo na biyu ya ce " Na ji
dukkan shawarwarin ku yanzu abin da ya dace shi ne za mu sake taro a nan a mako mai zuwa
domin na yi nazari akan hakan na bar ku lafiya wassalam".
Ko da sarki nan a zancen shi sai ya miƙe tsaye ya ci wata 'yar siririyar hanya da ke da zata
sada shi da gidan sarauta waɗansu ZARATAN DAKARU masu jajayen tufafi suka mara ma shi
baya, take ɗakin taron ya watse kowa ya kama gaban shi.
BABI NA BIYU
Ayarin fatake ne da adadin su ya kai ɗari tara da ɗoriya, tafiya suke wasu akan dawakai,
raƙumi, wasu a ƙafa, su dai wannan ayari ana iya kiran su da 'yan GUDUN TSIRA, domin kuwa
kallo ɗaya za ka yi masu ka fahimci hakan dalilin yara, mata da tsofaffi
Ayarin suna tafiya ne a cikin dokar daji ma'abocin dogayen bishiyu, duwatsu da
kwazazzabai, Hakan ne ya sanya duhu ya mamaye dajin, sai da ayarin suka iso tsakiyar dajin
kwatsam! bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu ZARATAN MAYAƘA suna yin fitar bdaga
cikin duhuwar bishiyun dajin suna yi masu ƙawanya, Ko da bayyanar dakarun sai kawai suka ce da wa Allah ya haɗamu sai suka afkawa ayarin da
azababban yaƙi, nan take waje ya kaure da koke-koken yara ƙanana, mata da tsofaffi.
Abin tambaya a nan shi ne daga ina waɗannan ayari suke? Kuma ina suka nufa?.
Su dai ayarin sun fito ne daga wata ƙaramar alkarya da ake kira da kira da suna
Baitul-Hazwar.
Birnin Baitul-Hazwar ya bunƙasa a noma, kiwo da kasuwanci, dadin daɗawa kuma sun tara
MAZAN JIYA masu juriya a filin fama,
Sarkin dake riƙe da kambun Sarautar birnin ana yi masa lakabi da Hidayal,
Sarki Hidayal yakasance dattijo ma'abocin kwarjini da haiba shekarun sun haura hamsin
alamun tsufa sun fara riskar shi amma duk da hakan ya kasance gwarzon mayaƙi kuma
JARUMIN JARUMAI,
A rayuwar Sarki Hidyal babu abin da ya tsana fiye da zalunci da cin zarafi bisa wannan dalili ya
sanya ya ke gudanar da mulkin shi bisa adalci,
Al'amarin da ya janyo ma shi daraja da ƙima a idanun sarakunan dake makwabtaka da shi
kenan suke ɗaukar shi a matsayin ubansu, kuma suka ƙulla hulɗar kasuwanci tsakanin su da
shi, al'amarin da ya sanya tattalin arzikin birnin shi ke bunƙasa kenan da sauran biranen.
A rayuwar Hidyal babu abin da ya ke ƙauna kamar 'ya'yanshi yarima Usaib da gimbiya
Haifar,
Usaib da Hairat sun kasance kyawawa na gaban kwatance, tun suna da shekara biyar a duniya
suke nuna abubuwan al'ajabi,
Lokuta da yawa idan sarki ya fito rangadi tare da su idan gungun 'yan fashi da makami suka
gan su sai kaga sun tarwatse zuwa cikin daji sun cika wandonsu da iska, idan kuwa muguwar
dabbar daji ta haɗa idanu da su Usaib sai ka ga ta sunkuyar da kanta ƙasa cikin ladabi ta juya
ta shige zuwa cikin daji. Lokacin da usaib da 'yar uwar shi Hairat suka cika shekaru goma da haihuwa sai suka rinƙa
shiga cikin daji suna farauto namun daji irin su zaki, ƙura, damisa da sauran su, wani abu da
yafi ɗaurewa mutane kai shi ne koda zabirar aski ba su taɓa riƙe wa ba ballantana su fita yaƙi,
Akwai wata rana da wani hatsabibin dodo ya bayyana a birnin domin ya hallaka duk wata halitta
da ke ciki, har dakarun yaƙi sun fita da nufin su afkawa dodon kawai sai aka hango su yarima
Usaib sun fito daga dajin birnin sun tunkaro inda dodon yake,
Cikin matuƙar kaɗuwa sarki Hidayal ya zaburo dokin shi ya tunkari inda suke yana mai ƙwala
masu kira yana cewa "Ya 'ya'yana kada ku iso inda wannan dodon yake.
Al'amarin dodon kuwa sa'adda ya ji takun sawaye a bayan shi sai ya waiga domin ya ga ko
mene ne aikuwa koda ya yi arba da su Usaib sai a ka ga ya durƙusa ƙasa bisa gwiwoyin shi
cikin ladabi.
Usaiba ya taka da ƙafafuwanshi har zuwa inda dodon yake ya dafa kanshi, kawai sai aka ga
dodon ya miƙe tsaye ya ruga izuwa cikin daji ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Nan fa jama'a suka cika da matuƙar mamaki da murna suka ɗauki Usaib da Hairat suka shiga
da su cikin birnin suna masu kirari da jinjina sun masu cewa tabbas sarki Hidayal ya haifi yara
'yan baiwa,
Nan fa labari ya watsu a birnin Baitul-Hazwar da ƙasashen da ke nahiyar akan abubuwan
al'ajabi da su Usaib ke bayyanawa,
Wasu ma suna cewa anya kuwa waɗannan yara bil'adama ne?.
Bayan mako guda da faruwar wannan al'amari da la'asar sakaliya jama'a na gudanar da
aiyukan su cikin annashiwa da jin daɗi, sarki na zaune a fadarshi ana gudanar da sha'anin mulki
kamar yadda aka saba,
Kwatsam! bazato babu tsammani sai aka ji gari ya kaure da guje-guje gami da ifice-ificen jama'a
cikin hanzari aka buga kugen yaƙi, dakaru suka dinga kwaso makaman yaƙi suna rugawa izuwa
bakin ƙofar gari domin tarar abokan gaba, har wandu Barada sun yunƙura da nufin su buɗe
ƙofar birnin sai kawai aka ga ƙofar ta karye, Kafin ayi wani yunƙuri ta danne dakaru masu tarin
yawa sun sheƙa barzahu.
A lokacinne dakarun birnin Baitul-Hazwar suka yi arba da wata irin ƙasaitacciyar rundunar
MAYAƘA, Nan fa suka firgice suka ɗimauce,
Ba komai ne ya firgita su ba sai bisa ganin tsananin kwarjinin rundunar nan fa su ka ji tamkar su
koma da baya,
Ita dai rundunar ta kasance mai matuƙar yawa idan mutum ya kalle ta sai ya ga tamkar sun
tokare da gajimare saboda matuƙar yawansu, makaman yaƙin su kuwa gasu nan birjik
bila-adadin, wasu suna zaune a bisa dawakai, raƙuma, toron giwa har da dabbar da idanu ba su
taɓa gani ba, Kaico! haƙiƙa komai dakewar zuciyar jarumi idan ya yi arba da rundunar dole ya ɗimauce.
Ana cikin wannan hali ne aka hango sarki Hidyal tare da muƙarraban shi sun tunkaro wajen
zaune bisa dawakai shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro zaune
bisa dawakai ɗauke da malamai,
Yayin da ya iso ne ya ga halin da jama'ar shi ne ciki sai buɗe baki cikin murya mai ƙarfafa
gwiwa ya ce "Ya ku jama'ata ku yi sani cewa wannan yaƙi mun fito shi ne domin kare rayukan
iyalanmu, duniyoyi gami da martani birninmu domin haka babu gudu babu ja da baya".
Ko da gama faɗin wannan jawabi sai sarki Hidyal ya zare takobinshi ya ɗaga sama ya zaburi
dokinshi ya ruga zuwa kan abokan gaba,
Take dakarun shi suka yi koyi da shi suna ihu da kururuwa mai firgitarwa aka afkawa abokan
gaba.
Nan take waje ya kaure da ƙarar karafniyar ƙarafa gami ihun Mazaje, ƙura ta turnuƙe sararin
samaniya tamkar dare ya kawo kai, Sassan jikkunan bil'adama suka dinga shawagi a sararin
samaniya suna zubowa ƙasa, dawakai suka dinga dudufniya kofatunsu na kartar ƙasa suna
tayar da ƙura, jini ya na kwaranya, tsartuwa yana malala a ƙasa tamkar an buɗe kan fanfo, Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya ana wannan ƙazamin artabu babu sassauci yazamana cewa
rundunar abokan gaba sun hallaka kaso huɗu bisa shida na dakarun birnin Baitul-Hazwar,
Sa'adda yazamana sa'a biyar ta shuɗe a dai-dai wannan lokaci ne abokan gaba suka hallaka
baki ɗaya sarki Hidyal da dakarun shi babu ɗaya da ya tsira da rayuwar shi.
Ko da samun wannan gagarumar nasara ne sai wani kyakkyawan saurayi daga cikin abokan
gaba ya zira hannunshi a aljihun shi na riga ya ɗauko madubin tsafin shi ya shafe shi da
hannunshi na hagu ya shiga gudanar da bincike,
Jim kaɗan bayan kammala hakan sai ya juya ya dubi wani barde dake tsaye a hannun shi na
dama cikin kaɗuwa ya ce da shi "Yakai Huzlan haƙiƙa binciken da na gudanar a yanzu ya
tabbatar mani da cewa a lokacin da muke fafata yaƙi da jama'ar birnin Waɗansu a cikin su sun
yi gudun hijira, Domin haka wajibi mu bazama domin nemo yaro mai hatimin takobin saiful-zayyada ina so ka
haɗa da dakaru mutum dubu ashirin,
Ko da jin wannan batu daga bakin Saurayin sai Barde Huzlan ya yi wa wasu dakaru inkiya ta
wutsiya idanu, take su ka shiga yin wani sahu na musamman a bayan shi suna fuskantar wani
ɓangare,
Kawai sai wannan kyakkyawar saurayi ya zaburi dokinshi ya nausa zuwa cikin daji take Barde
Huzlan da dakarun dubu ashirin suka mara mashi baya,
Take sauran tawagar abokan gabar suka shiga kwashe gawarwakin 'yan uwan su, bayan sun
kammala suka nausa zuwa wata hanya ta daban a dajin suna tsala azababban gudu a bisa
dawakan su.
Kaico! inda mutum yana tsaye a wannan lokaci zai ga yadda gawarwakin yara da mata da
mazaje ke kwance cikin jini dole tausayi ya kama shi ya zubar da hawayen baƙin ciki, kuma ya
tabbatar da cewa haƙiƙa yaƙi shi ne mafakar dukkan wata musiba a doron ƙasa.
Wannan shi ne dalilin da yasanya waɗannan ayarin 'yan gudun hijira ke yin gudun tsira a
cikin wannan daji.
Lokacin da wannan runduna ƙarƙashin jagorancin Sadauki Hukaiza suka afkawa ayarin
fataken da azababban yaƙi, sai jini ya dinga kwaranya tamkar an ɓalle teku, rayuka suka dinga
rabuwa da gangar jiki suna shawagi a sararin samaniya suna zubowa ƙasa tamkar ana ruwan
su ne daga saman, ƙarar karafniyar ƙarafa gami ihun Mazaje ta cika dodon kunne. Kaico! Nan fa dakarun suka shiga hallaka rayukan su babu wanda suke tausaya wa
tsakanin yara da mata,
Inda ace mutum ya ba tsaye a wannan waje lokacin da dakarun ke aiwatar da wannan rashin
imani dole ne tausayi ya kama shi ya zubar da hawaye.
Kafin shuɗewar daƙiƙa ɗari huɗu sun hallaka baki ɗaya ayarin sun zubar da gawarwakin su
ƙwance cikin jini babu kyawun gani.
Bayan ƙura ta lafa ne Waɗansu ZARATAN MAYAKA suka shiga bincike gawarwakin domin
su gano yaro mai hatimin takobin Saiful-zayyad a gadon bayanshi.
Jim kaɗan bayan sun kammala sai suka tabbatarwa da shugaban su cewa babu yaro mai
hatimin takobin Saiful-zayyad a cikin gawarwakin,
Ko da shugaban ya ji wannan batu sai hankalinshi ya dugunzuma ainun ya dubi dakarun cikin
matuƙar damuwa ya ce "Ya ku 'yan uwana dakaru sanin kanku ne cewa mai girma
Lamsarul-Azlam bai tura mu hallaka ayarin 'yan gudun hijirar ba sai domin mu hallaka yaro mai
hatimin takobin Saiful-zayyad, kuma ya faɗa mana cewa yaron yana cikin birnin Baitul-Hazwar, To kenan hakan ya tabbatar da cewa lokacin da muka tare waɗannan ayari ke nan yaron ya yi
gudun tsira,
Ina so ku sani cewa farautar yaron shi ne zai sanya dukkan ruhikan mu su kuɓuta daga
TSANANI DA UKUBA ta mai girma Lamsarul-Azlam.
Ko da shugaban ya zo nan azancen shi sai dakarun suka kasu gida biyu, na farko su ka yi
yamma bisa jagorancin Sadauki Hukaiza, na biyu bisa jagorancin Barde Huzlan, suka sukwani
dawakan su izuwa cikin daji.
BABI NA UKU
Gidan sarautar ya yi matuƙar ƙawatuwa da nau'ikan abubuwan jin daɗin rayuwar duniya har da
ma abin da idanu ba su taɓa gani ba,
Duk ƙasaitar BASARAKE ko attajiri idan ya tsinci kanshi a cikin wannan gida dole ne ya raina
kanshi ya tabbatar da cewa GABA DA GABANTA,
Idan mai kallo ya yi duba ga wani ɓangare a gidan zai yi arba da wata turaka da ta ƙawatu
ainun da kayan ado fiye da ko wane waje a gidan.
Idan mai kallo ya ƙara nazari sosai zai yi arba da waɗansu ƙayatattun kujeru zaune a bisa
kan su waɗansu ZARATAN JARUMAI ma'abota mulki sanye cikin ƙayatattun tufafi suna masu
fuskantar juna shiru ne ya wanzu tsakanin su na wani lokaci.
Daga can sai waziri Yazid ya yi gyaran murya ya fara magana a karo na farko ta hanyar buɗe
baki ya yi gyaran murya ya ce " Ya kai Rakibu ka yi sani cewa bakomai ya sanya na kawo maka
wannan ziyara ba face saboda na sanar da kai wani al'amari da yake shirin faruwa gare ka,
wanda idan har baka bani goyon baya zaka rasa sarautar ka da jama'ar ka baki ɗaya". Cikin alamun rashin fahimta sarki Rakibu ya