Showing 27001 words to 28793 words out of 28793 words
Chapter 10 - TAFARKIN TSIRA Book Complete by Sarkin Marubutan Yaki .pdf
attajiri idan ya tsinci kanshi a
wannan fada dole ya tabbatarwa kanshi cewa GABA DA GABANTA aljani ya taka wuta, a
wannan lokaci fadar ta cika maƙil babu masaka tsinke duk inda mutum ya kalla kawunan
bil'adama ne rututu babu masaka tsinke, a kowacce kusurwa a dakarun tsaro ne shirye cikin
gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro suna ta kai komo domin tabbatar da
cikekken tsaro.
Bisa wani zagayayyen tudu mai matattakala bakwai a ƙasan shi anan aka ajiye wata
ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'anta ta da ƙarfen zubar daju aka yi mata feshi da koren
lu'ulu'u, wani shirgegen mutum ne tamkar giwa, ƙasumba da sajen shi baƙaƙe siɗik! Sune suka
tona asirin kyawun surarshi, kuma suturun dake jikinshi suka dace da shi, kallo ɗaya za ka yi
mashi ka fahimci cewa ya cika GWARZON MAYAƘI mai ƙarfi na Allah ya isa, a wannan lokaci
fadar ta yi tsit tamkar mutuwa ta kawo ziyara, kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga wani
mutum ya bayyana tsulum! A tsakiyar fadar tamkar an aiko shi daga sama, mutumin yakasance
gajere baki wuluk! Fuskarshi mummuna ce tamkar bai taɓa dariya ba, jikinshi cike yake da gashi
buzu-buzu da layi, da guraye na sihiri babu kyawun gani tamkar wani tsohon mahaukaci, babu
wani tufafi a jikinshi face bante na fatar damisa da ya suturce al'amuran shi, a hannunshi na
hagu yana dogare da wata SANDAR TSAFI, kaico! Haƙiƙa babu wani mahaluki a doron ƙasa da
zai yi arba da wannan mutum ba face ya firgice, ba wani ba ne face boka kaddad.
Sannu a hankali kaddad ya yi tattaki da ƙafafuwanshi yana mai dogara sandarshi ya durfafi inda
karagar mulki take, lokacin da ya rage saura kamar taku goma ya isa sai ya zube ƙasa ya
kwashi gaisuwa cikin girmamawa,
Cikin annuri fuska mutum dake zaune bisa karagar ya ƙarɓi gaisuwar ta hanyar gyaɗa kai
sannan ya buɗe baki cikin kakkausar murya mai kama da saukar aradu ya ce "Lale marhabun
da Dodon bakoye hadari malafar duniya, lafiya na gan ka a wannan lokaci da baka saba zuwa
ba ? Koda jin wannan tambaya sai boka kaddad ya buɗe baki a karo na farko cikin murya mai kama
da haushin kare ya ce "Ya shugabana ka ji sani cewa bakomai na ya kawo ni gare ka sai domin
na sanar da kai wani abin farin ciki, bincike da na gudanar bisa halarar tsafi na ya bayyana mini
maganin da zai warkar da gimbiya da cutar makanta da take damun ta, shi ne wani ALLON
TSAFI, dake ajiye a ƙarƙashin tekun Baharul-Saljir a cikin wani masifaffen kada,
Ya kai Hulaifu ka yi sani cewa a halin yanzu a duniya babu wata dabba dake rayuwa a cikin teku
da ta kai kadan ƙarfin damtse da na sihiri,
Za a warkar da gimbiya ne idan aka karanta ɗalasiman tsafin dake jikin Allon sannan a shafa
mata a fuska take idanuwanta za su buɗe garau!"
Koda jin wannan jawabi daga bakin boka kaddad sai sarki Hulaifu ya cika da matuƙar farin
ciki maral-musaltuwa fuskarshi ta faɗa da murmushi ya dube shi ya ce "Ya masanin ilimin tsafi
tsawon lokaci za mu ɗauka kafin tafiya nemo wannan ALLON TSAFI?
Boka kaddad ya bushe da dariyar mugunta sannan ya ce "Ai a gobe za mu yi wannan tafiya
domin masu iya magana na cewa da zafi-zafi akan daki ƙarfe, kuma a bari ya huce shi ke kawo
rabon wani, sai dai dole ne tafiyar sai an tafi da gimbiya domin kuwa Allon yana da wani sharaɗi
idan har aka fito da shi daga gadan idan har ya huce tsawon sa'a ɗaya ba ayi amfani da shi ba
zai lalace kaga kenan an sha wahalar banza".
Koda jin wannan batu daga bakin boka kaddad sai sarki Hulaifu ya cika da matuƙar farin
maral-musaltuwa, take kaddad ya sake ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba, sarki ya tashi
daga faɗa ya shiga izuwa cikin gidan sarauta, kowa ya watse ya kama gaban shi.
Mu haɗu a TAFARKIN TSIRA 12 Domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
TAFARKIN TSIRA 12
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
Littafan Marubucin
Kogon Annoba
Sarautar Mutuwa
Kangin Bauta
Jaruman Duniya
Takobin Ɗaukaka
Ƙarshen Zalunci
Fataucin Bayi
Sarkin Sadaukai
Goga Sha Fama
Tafarkin Tsira
Ƙarya Da Gaskiya
Gasar Sarauta
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
Kashe gari tunda duku-dukun safiya bayan shugaban 'yan fashin duniya sadauki
Fitinatul-Amir ya yi kalaci ya caɓa ado sai nufi fada domin ganawa da sarakunan da zasu
gabatar da haraji. Bayan kowa ya hallara sarki ya hakimce bisa karaga 'yan majalisa sun
kammala mika gaisuwa,
Lokacin da sarakuna birane ashirin da uku suka gurfana a gaban sadauki Fitinatul-Amir sai
sarki na farko da ake kira da suna Madsur ibn Zauhil ya faɗi ya yi gaisuwa sannan ya buɗi baki
cikin ladabi kanshi a sunkuiye ya ce "Ya sarkin sarakuna, GOBARAR DAJI mai share abokan
gaba, KAIFIN TAKOBI mai raba tsakanin masoya, kai ne SARKIN SADAUKAI GOGA SHA
FAMA dake saukar da ANNOBA ƊARI, gani tafe da ɗan abin da bai taka kara ya karya ba ina
roƙon a ƙarba domin na kai ba".
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Madsur sai Fitinatul-Amir ya bushe da dariyar farin
ciki maral-musaltuwa bisa kirarin da ya yi mashi, sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar
an aiko mashi da SAƙON MUTUWA ya dube shi cikin taƙama da BAƘAR IZZA ya ce "Yakai
Madsur haƙiƙa dukkan abin da ka faɗa gaskiya ne saboda haka dukkan abin da ka kawo an
karɓa tafi abin ka".
Cikin matuƙar farin ciki dakarun sarki Madsur suka gabatar da dinaren harajin dake cikin
waɗansu akwatu na baƙin ƙarfe, sannan sarki ya ja ya koma ya gefe guda
Sarki na biyu mai suna Ashrum dake mulkin birnin Darul-Zabub ya faɗi ya kwashi gaisuwa ya
buɗi baki ya yi gyaran murya kanshi a sunkuiye ya ce "Ya shugabana gani tafe da dukkan abin
da aka buƙata, ina fatan dukiyata za ta zamo fansa gare ni da al'ummata"
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Ashrum sai Fitinatul-Amir ya fusata ainun ya daka mashi
tsawa wacce ta sanya hantar cikinshi Ashrum ta kaɗa jikkunansu suka kama ƙyarma, cikin
matuƙar fushi Fitinatul-Amir ya dube shi "Ya kai Ashrum shin wace dukiya gare ka da zata
fansar da Jinin al'ummarka? Haƙiƙa ka yi Furuci mafi muni a gare mu da wajibi ne sai mun
ganar da kai kuskuren ka,
Koda jin wannan batu daga bakin Fitinatul-Amir sai sarki Ashrum ya faɗi ƙasa yana neman
gafara yana mai cewa "Ina tuba ya shugabana tabbas na yi kuskure....,
Kafin ya gama rufe bakinshi Fitinatul-Amir ya dako wawan tsalle daga kan karagarshi tamkar an
harbi shi daga cikin baka ya shammaci Ashrum ya kirɓa mashi wawan naushi a wuya, saboda
ƙarfin naushin nan take wuyan ya yi ƙara ya karye ji kake ruƙus! Ƙas jini ya yi tsartuwa gangar
jikin ta faɗi ƙasa rikica! Nan waɗansu zaratan dakaru a fadar suka ɗauke gawar sarki Ashrum
suka goge jikin da ya zuba, sannan suka tusa ƙeyar jama'ar shi izuwa kurkuku.
Sa'adda sauran sarakunan suka ga abin da ya faru ga sarki Ashrum sai cikinsu ya ɗuru ruwa
domin sun san cewa a kodayaushe ɗayan su zai iya baƙuntar barzahu,
Bayan Fitinatul-Amir ya koma bisa kan karagarshi ya hakimce sai aka hango yara biyu mace da
namiji sun shigo fadar sun durfafo inda karagar mulki take, ba wasu ba ne face Yaro Usaiba mai
hatimin takobi tare 'yar uwarshi Hairat, lokacin da yazamana tazarar dake tsakanin su da
karagar mulki bata huce taku goma kawai sai aka ga sarki Fitinatul-Amir ya miƙe tsaye tsam!
Daga kan karagar mulki fuskarshi cike da annuri ya je ha tare su yaja hannayensu har izuwa
kan karagar mulki suka zauna a tare.
"Wannan shi ne masu iya magana ke cewa idan rabo ya rantse... Kaico! Rashin sani wai
Kaza ta kwana akan dami, haƙiƙa Fitinatul-Amir ya tafka babban kuskure da ya riƙi wannan yaro
a matsayin magajin shi, shin ko bai gano cewa yaron shi ne Usaiba mai hatimin takobi
SAIFUL-ZAYYAD da yake farauta dare da rana ba" Wani daga cikin sarakunanne ya yi wannan furuci a cikin ranshi batare da ya bayyana ba,
Ana cikin wannan hali ne wani badakare ya matso daf da karagar mulki ya risina ya kwashi
gaisuwa ga sarki ya ce " Ya shugabana an lissafa harajin sarki Madsur kuma tuni dakaru sun
nufi Baitul-Mali domin su kai dukiyar domin haka sarki Madsur ta tawagar shi za su iya tafiya,
Koda jin wannan batu daga bakin badakaren sai Fitinatul-Amir ya gyaɗa kai alamar gamsuwa.
Nan take Madsur da tawagarshi suka miƙe tsaye suka durfafi ƙofar fita daga fadar, amma koda
suka zo giftawa ta gaban Fitinatul-Amir sarki Madsur ya haɗa idanu da yaro Usaiba sai suka
ƙurawa juna idanu, nan take Madsur ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi tsoro ya kama shi.
Jim kaɗan bayan ficewar su daga fadar sai yaro Usaiba ya dubi Fitinatul-Amir ya buɗi baki cikin
alamun matuƙar damuwa ya ce "Ya abbana wannan sarki da ya fita daga wannan fadar ya
shirya maka wata mummunar gadar zare ka sani cewa dukiyar da ya kawo maka a matsayin
haraji bakomai ba ce face sinadaran tsafi, wadanda matsawar ka haɗa su da dukiyar ka dukkan
abin da ka mallaka zai lale za ka dawo sarkin da ya fi kowa talauci a duniya"
Koda jin wannan batu daga bakin yaro Usaiba sai Fitinatul-Amir ya cika da matuƙar mamaki
ainun ya dubi Usaiba ya ce "Ya aka yi kasan da hakan ya ɗana?
Usaiba ya ce "Ya abbana ka duba idan har ka tabbatar da abin da na faɗa ba gaskiya ba ne na
yarda cewa na yi kuskure".
Koda jin wannan batu sai Fitinatul-Amir ya zira hannunshi a aljihunshi na riga ya ɗauko
madaidaicin madubin tsafi ya shafe shi da hannun shi na hagu ya shiga gudanar da bincike,
Nan take ya gano gaskiyar abin da yaro Usaiba ya faɗa game da mugun tanadin sarki Madsur.
Koda ganin wannan al'amari sai Fitinatul-Amir ya taƙarƙare ya kurwa wawan ihu da ya
ɗimauta duk wata halitta dake fadar.
Mu haɗu a ƘARYA DA GASKIYA Domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071