Showing 6001 words to 9000 words out of 28793 words

Chapter 3 - TAFARKIN TSIRA Book Complete by Sarkin Marubutan Yaki .pdf

cikin rayuwata ka
yi sani cewa tabbas magana ta babu jayayya akan ta, Duk sa'adda na samu nutsuwa zan ba ku
labarin domin ku tabbatar, Yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne ku kwanta ku huce gajiyar da eh tare da ku,Ko da jin
wannan batu sai farin ciki ya mamaye zukatansu,
Kawai sai usaiba ya koma bisa wata ƙasaitacciyar kujera ya kwanta ita kuma Hairat sai ta
kishingiɗa a bisa wani ƙayataccen gado,
Ko da ganin hakan sai Rusayyat ta miƙe tsaye ta nufi Kofar fita turakar tana mai waigen su tana
sakar masu ƙayataccen murmushi mai cike da tsantsar so da kauna a haka har ta fice baki
ɗaya dakarun masu tsaro suka janyo ƙofar suka rufe rufe.
wannan shi ne abin da ya faru da baƙuwar jaruma da ta ceto rayuwar waɗannan yara biyu daga
sharrin zaki da kuma dakarun sarki Lamsarul-Azlam, wato jaruma Rusayyat uwar gidan
shugaban 'yan fashin duniya Sadauki Fitinatul-Amir.

TAFARKIN TSIRA 4
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaki
Wthapp Number
08137237071

BABI NA BAKWAI

sa'adda waziri Yazid, sarkin yaƙi lauzar da sarki Rakibu suka kammala shirya rundunar
MAYAƘAn su sai da suka bari dare ya tsala sannan suka durfafi hanyar da zata kai su zuwa
birnin Zainul-Ansar.
Tafiyar rabin sa'a kacal suka yi suka iso domin haka sai suka yiwa birnin ƙawanya,
Waziri Yazid ya yi gyaran murya ya ce "Ya ku dakarun haɗin gwiwa ku yi sani cewa yaƙin ku
da dakarune kawai ba jama'ar gari ba da kuma duk wanda ya yi yunkurin kawo maku tazgaro
domin ku isa zuwa turakar sarki Nu'umanu,
Yana zuwa nan a zancen shi sai ya umarci masu kibbau suka ɗana bakansu sannan suka harba
shi izuwa dakarun dake tsaron ƙofa,
Sannan suka afkawa birnin suka hau dakaru da sara da suka, ihun Mazaje da kururuwar su shi
ne abin da ya fara sauka akan kunnuwan jama'ar birnin.
Nan fa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro,
Ɓangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da
bajinta irin ta MAZAN JIYA masu juriya a filin fama,
A wannan lokaci babu abin da kunne ke ji face ihun mazaje da ƙarar karafniyar ƙarafa gami da
haniniyar dawakai, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya aka fara yiwa ƙasa ado da jini, sassan
jikkunan bil'adama suka fara shawagi a sararin samaniya suka zubowa ƙasa tamkar ana ruwan
su ne daga saman, Nan fa gari ya hautsi ne sakamakon guje-gujen al'umma gami da ifice-ificen su.
Bayan waziri Yazid ya yi umarni an afkawa birnin Zainul-Ansar da yaƙi sai kawai ya tuntse
Idanuwanshi ya karanta ɗalasiman tsafi, Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce
"Tabbas "Makashin ka yana tare da kai" kuma tabbas ba a gane mutum a fuska, Inda a ce
mutum yana tsaye a lokacin da waziri Yazid ke karanta ɗalasiman tsafin sai ya rantse ya ce bai
Kasance musulmi ba,
Ko da gama rufe bakinshi sai ya shafi wani guru a damtsen shi na hagu na ɓace ɓat! tamkar bai
taɓa wanzuwa ba.
Wannan shi ne abin da ya faru da su waziri Yazid da sarki Rakibu bayan sun kammala tara
rundunar MAYAƘA domin kai farmakin Bazato birnin Zainul-Ansar domin hamɓarar da sarki
Nu'umanu daga kan karagar mulki.
Al'amarin shugaban dakarun sarki Lamsarul-Azlam kuwa wato Sadauki Hukaiza tun sa'adda
aka fyaɗa shi da ƙasa sakamakon yunƙurin da ya yi na gudanar da bincike game da yaro
Usaiba mai hatimin takobin Saiful-zayyad da jaruma Rusayyat ta ceci rayuwar shi sai ya yi
yunƙurin miƙe wa tsaye amma sai ya ji ya kasa, Ko da sauran dakarun suka fahimci cewa ya kasa miƙewa tsaye sai suka zaburi dawakansu
suka yunƙura izuwa inda ya ke,
Ko da ukaiza ya fahimci aniyar su sai kawai ya dube su ya daka masu tsawa cikin matuƙar fushi
ya ce da su "Ya ku waɗannan dakaru ku yi sani cewa a halin yanzu ba zai yiwu a ina tashi tsaye
akwai buƙatar na ɗauki tsawon lokaci a wannan waje kafin jikina ya samu lafiya,
Abin da na ke so ku yi kawai shi ne ku koma izuwa ga mai girma Lamsarul-Azlam ku labarta
masa abin da ya wakana gare mu, domin ko da ba ku koma gare shi yana ba za ku iya tsere
mashi ba".

Ko da jin wannan batu daga bakin Ukaiza sai hankulan dakarun ya yi mummunan tashi
Suka ce a cikin zukatansu tabbas a halin yanzu muna cikin tsaka mai wuya kuma gaban mu
tsini ne baya siyaki.
Wani garjejen ƙato daga cikin mayakan ya buɗi baki cikin ƙarfin hali ya ce "Ya shugabana sanin
kanka ne cewa matsawar mu ka je da wannan mummunan labari ga mai girma Lamsarul-Azlam
to hukuncin kisa ya tabbata a gare mu",
Ukaiza ya ce "Ai ko da baku koma zuwa gare shi sanin kanku ne cewa zai iya tura wata
Annobar da zata hallaka ku ku yi mutuwar wulakanci,
Saboda haka yanzu shawara dai ta rage ga mai shiga rijiya".
Sa'adda Ukaiza ya zo nan azancen shi sai jikin dakarun ya yi sanyi kawai sai suka sakarwa
dawakansu linzami suka durfafi wani ɓangare a dajin suna masu tsala gudu zukatansu cike da
matuƙar tsoro.

***
'yar gajeriyar tafiya Rusayyat ta yi a cikin gidan sarautar ta iso wata ƙasaitacciyar turaka da
aka cika ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, kai tsaye ta kunna kai
izuwa ciki,
Zaune ta same shi ya tafka wani uban tagumi ta isa gare shi ta zauna daf da shi ta sanya
hannayenta biyu ta dafa kafaɗunshi, Haka ne ya sanya ya dawo daga duniyar tunanin da ya yi
fana'i a ciki,
Sannan ta dube shi fuskarta cike da annuri ta ce "Ya uban 'ya'yana shin ina dalilin wannan
tagumi na ka ?.
Ko da jin wannan batu sai Fitinatul-Amir ya mayar mata da martanin murmushin da ƙara wa
fuskar shi kwarjini ya yi gyaran murya ya ce "Ya abar bege na dare da rana ki yi sani cewa
bakomai ne ya sanya ni a cikin wannan hali sai bisa rashin samun Magaji,
Babban abin da ke dugunzuma hankalina shi ne yadda har yau na gaza gano inda yaro mai
hatimin takobin Saiful-zayyad yake wanda shi kaɗai ne ya matsala wajen burina namu.
Ko da jin wannan batu sai Rusayyat ta yi murmushi a karo na biyu har kyawawan haƙoranta
suka bayyana farare ƙal!, Cikin zazzaƙar murya mai daɗi tamkar sarewa ta ce " Ya muradin
raina ka kwantar da hankalinka tamkar tsimma a randa ka yi sani cewa a yau na samo wata
gagarumar tsintuwa da zata maye gurbin rashin magaji a gare mu. Cike da alama matuƙar mamaki Fitinatul-Amir ya dube ta ya ce " Ya farin cikin rayuwata shin
wace irin tsintuwa ce kika yi da zata maye mana gurbin magaji?
Da jin wannan tambaya sai Rusayyat ta miƙe tsaye tsam! daga kan kujerar ta durfafi ƙofar fita
daga turakar tana mai yafito Fitinatul-Amir da hannu tana nuna cewa ya biyo bayanta,
Ba tare da bata gardama ba ya miƙe tsaye ya yi ko yi da ita,
Lokacin da suka fice daga turakar sai suka wanzu suna tsara saƙo da lungu a gidan sarautar,
duk inda suka gifta sai ka ga dakaru, barori, dakaru haɗe da bayi na zubewa ƙasa suna kwasar
gaisuwa cikin girmamawa.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin Jaruma Rusayyat da mai gidanta Sadauki
Fitinatul-Amir.

***

Dukkan abin da ya wakana tsakanin Jaruma da Rusayyat da shugaban dakaru sadauki
Hukaiza,
Sarki Lamsarul-Azlam ya gani a cikin madubin tsafin shi a lokacin da yake zaune a cikin
ƙasaitacciyar turakar shi ta shaƙatawa,
Ko da ganin wannan al'amari sai ya cika da matuƙar baƙin ciki maral-musaltuwa ya buɗi baki
cikin kakkausar murya yana mai cewa "Haƙiƙa jaruma Rusayyat ta aikata laifi mafi muni a gare
ni da ba zan taɓa yafe mata ba face ta miƙo mani yaro mai hatimin takobi,
Ko da yazo nan azancen shi sai ya sake baje alƙalumman sihirin ya sake nutsawa cikin halarar
tsafin domin ya ga irin wainar da duniya ke toyawa,
Abin da ya gani abinciken shi ne ba shi da wani aiki da ya huce ya ga ya gano sabuwar hanyar
mallakar yaro mai hatimin takobi.

***
Lokacin da aljani Lattul-kifas ya tsala da matsanancin gudu a sararin samaniya sai ya wanzu
yana ratsa giza-gizai,
Tafiyar daƙiƙa hamsin kacal ya yi ya iso wani ƙasaitaccen gida mai girma da tsawo tamkar gari
guda,
Ko da ya yi arba da gidan sai kawai ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuh! ya sauka a turba
nesa ƙaɗan da inda gidan ya ke, Nan take ya kama kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan ƙauye
ya shigo birni,
Wani abu da ya ba shi mamaki game da gidan shi ne yadda aka yi ginin shi da zallar waɗansu
irin duwatsu masu ƙyalli tamkar gilashi, an yiwa dukkan katangun gidan ado da wani irin hatimin
sarauta gami da turanni mabanbantan launuka masu kyawun gani da ƙamshi,
Duk inda mutum zai taka a harabar gidan an yi daɓe da koren yaƙutu,
Wohoho! haƙiƙa babu wani attajiri ko BASARAKE da zai yi arba da wannan gida face ya
tabbatar wa da kanshi cewa GABA DA GABANTA, kuma sawun Giwa ya take na raƙumi,
Iya tsawon rayuwar aljani Lattul-kifas bai taɓa gani ko jin labarin gida mai ƙawatuwa tamkar shi
ba,
Na rantse da gemun kakana boka Zamzarul-Dayyan ko wane ne mai mallakin wannan gida
yakasance mutum mai girman matsayi a tsakanin duniyar mutane da aljanu domin wannan gida
na shi a iya kiran shi da suna aljannar duniya",
Lattul-kifas ne ya yi wannan furuci a cikin ran shi ba tare da ya bayyana ba.
Ko da kammala furuci sai ya yunƙura ya durfafi gidan domin ya ganewa kwarkwatar
idanunshi, domin masu iya magana na cewa gani ya kori ji, Ai kuwa sai ya hango waɗansu irin
gabza-gabzan dakaru na jinsin MUTUM DA ALJAN ɗauke da miyagun makamai bila-adadin
masu matuƙar barazana ga duk wata halitta mai numfashi, Sa'adda ya yi arba da su sai firgita ainun tsoro ya kama shi duk da kasancewar gwarzon mayaƙi
mai dakakkiyar zuciya,
Amma abin da ya ba shi mamaki shi ne dakarun ko ɗaga kai ba su yi ballantana su yi yunƙurin
afka mashi,
Shin ko dakarun ba sa iya gani na ne ?,
Amsar tambayar da ya kasa bawa kanshi kenan kawai sai ya takaici Idanuwansu ya falfala da
gudu domin ya shiga zuwa gidan batare da sun gan shi ba.

Kaico! haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce "kifi na ganin ka mai jar koma" ya
yin da ya rage saura taku uku ya ketare katangar gidan sai dakarun suka yi ɗauki kan shi suka
yi masa ƙawanya saboda girman dakarun da yawan su sai aljani Lattul-kifas ya zamo tamkar an
ajiye kwanya guda ɗaya a gaban dubban karnuka, Tamkar haɗin baki a lokaci guda dakarun suka afka masa da dukkan ƙarfin su suna ihu da
kururuwa mai firgita ZARATAN JARUMAI komai matuƙar yawan su,
Kaico! haƙiƙa komai dakewar zuciyar jarumi da rashin tsoron shi idan ya ga yadda dakarun ke
kururuwar suna ɗaga makamansu izuwa sama dole ne ya ɗimauce,
Ko da ganin hakan sai Lattul-kifas ya yi wuf! ya zare wata sharbebiyar takobi a damtsen shi ya
tare su aka kacame da masifaffan artabu mai matuƙar muni daban tsoro, ƙarar karafniyar ƙarafa
gami ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne.
Wannan shi ne abin da ya faru da aljani Lattul-kifas da boka kaddad ya tura domin ya ɗauko
mashi yaro mai hatimin takobin Saiful-zayyad.

***
Al'amarin waziri Yazid kuwa tun sa'adda ya ɓace cikin alƙalumman sihiri bayan ya yi umarni
an farmaki birnin Zainul-Ansar da yaƙi bai bayyana a ko ina ba sai a tsakiyar gidan sarauta,
Ko da bayyanar shi sai ya zare wata sharbebiyar takobi a gadon bayanshi ya afkawa dakarun
gidan da sara da suka yana kutsawa cikin gidan sarautar.
Sa'adda Sarki Nu'umanu ya ji gidan sarautar ya kaure da guje-guje gami ifice-ificen jama'a
sai kawai ya ruga zuwa turakarshi, jim kaɗan sai ga shi ya fito shirye cikin matsananciyar shigar
yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, fararen sulken ya saka haɗe da koren rawani, ya rataya
waɗansu zaratan takubba biyu a gadon bayanshi, Kawai sai ya durfafi turakar uwar gidan shi lawisat, Ya na isa dakarun suka wangame kofa ya
kunna kai ciki,
Sa'adda lawisat ta yi arba da maigidan ta a cikin wannan hali sai kawai ta faɗa kan ƙirjin shi ta
rungume shi ta fashe da kuka mai tsuma zuciya,
Da ga can sai sarki ya janye jikinshi daga na ta suka fuskanci juna,
"Shin ina dalilin wannan hawaye na ki ya Sarauniyar zuciyata?,
Ko da jin wannan tambaya sai lawisat ta buɗi baki cikin alamun damuwa ta ce "Ya uban
'ya'yana ka yi sani cewa na ji a jikina cewa wannan yaƙi da zaka fita ba alkairi ba ne, ma'ana shi
ne zai zamo ajalinka.
Ko da jin wannan batu sai sarki Nu'umanu ya sanya hannayenshi ya share mata hawayen
dake kan fuskarta ya dube ta cikin alamun tsantsar tsantsar so da ƙauna ya ce "Ya Annurin
kalbina ki yi sani cewa RAYUWA DA HALAKA duk a hannun Allah (SWT) suke komai zai
kasance wajibi ne a gare ni na fita na kare rayukan al'ummata, Kada ki manta cewa muna kan bisa TAFARKIN TSIRA abokan gabar mu kuwa suna bisa
TURBAR AJALI, Domin haka da yardar Ubangijin halitta za mu samu nasara a wannan yaƙi
kuma na dawo gare ki cikin ƙoshin lafiya,
Fatana shi ne ki Kasance mai yi mani fatan alheri da nasara, idan kuma ta Allah ta kasance ki
roƙa mani gafara a wajen Ubangiji".
Lokacin da Sarki yazo nan azancen shi sai lawisat ta sake fashewa da kuka a karo na biyu,
Dakyar da siɗin goshi ya samu ya lallashe ta ya fice turakar suna masu zubar da hawayen
rabuwa da juna.

Yana fitowa ya falfala da azababban gudu zuwa cikin gidan sarautar ba tare da ya haye bisa
doki ba.
Wannan shi ne abin da ya faru a birnin Zainul-Ansar bayan waziri Yazid ya kai farmakin
Bazato zuwa birnin.

***
A can ƙasar Darul-Ashmar kuwa sarki Lamsarul-Azlam ya shafe tsawon kwanaki biyu yana
gudanar da bincike domin ya gano hanyar da zai hallaka yaro mai hatimin takobin
Saiful-zayyad,
Abin da ya gano shi ne ɗin shi ne ba zai iya hallaka yaro mai hatimin ba face a ranar da sadauki
Fitinatul-Amir ya gano cewa yaro Usaiba shi ne wanda yake farauta tsawon shekaru,
Sa'adda ya ga wannan al'amari sai ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa,
Shin mene ne dalilin da ya sanya sarki Lamsarul-Azlam ke farautar yaro usaiba mai hatimin
takobi dalilin hakan kuwa shi ne.
Sarki Lamsarul-Azlam ibn Rauzil ya kasance GWARZON BASARAKE kuma gawutaccen
mayaƙi da ya yi shura a ilimin tsafi, daɗin daɗawa kuma ya kasance azzalumi na gaban
kwatance,
Gaba ɗaya jama'ar birnin Darul-Ashmar babu wnada yake jin daɗin mulkin shi face fadawa shi
kaɗai,
Saboda matuƙar zaluncin shi ne ya sanya ya mamaye birane da ƙasashen da ke makwabtaka
da shi sun yi MUBAYA'A a gare shi ta ƙarfin tsiya, Bisa wannan dalili ne ya sanya ya zamo babu
mashahurin sarki tamkar shi a kaf nahiyar.
Wata rana da sulu-sainin dare sarki Lamsarul-Azlam na zaune a cikin turakarshi ya baje
alƙalumman sihirin yana gudanar da bincike domin ganin halin da duniya ke ciki,
Yana cikin wannan hali ne sai kawai ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu da ya mamaye gidan
sarautar ya amsa kuwwa izuwa ko ina, Al'amarin da ya yi matuƙar janyo hankalin dakarun gidan
kenan suka zare makaman su suka rugo izuwa turakar,
Ba wani abu ne ya sanya shi wannan ihu ba face wani al'amari da ya gani a madubin tsafin shi,
Abin da ya gani ɗin shi ne wani yaro mai shekaru tara dake ɗauke da zanen hatimin takobin
Saiful-zayyad a gadon bayanshi da zai zamowa sarakunan duniya ƙadangaren bakin tulu kuma
ciwon idanu, zai kawo ƙarshen mulkin duk wani azzalumi a doron ƙasa kuma zai samu ɗaukaka
fiye da kowa ne sarki a duniya, Yaron yakasance ɗa ne ga wani wani sarki da ake kira da suna Hidyal na birnin Baitul-Hazwar
dake yamma maso gabashin duniya a gaban tekun baharul-sawara,


BABI NA TAKWAS

Lokacin da dakarun suka iso turakar sai suka yi turus! ba wani abu suka gani ba face dakarun
dake gudanar da tsaro alamun dake bayyana cewa babu wani al'amari da ya gudana mara
kyawu,
A lokaci guda sarki Lamsarul-Azlam ya tsuke bakinshi daga sannan ya ƙwalla wani hadimin shi
kira mai suna Hukaiza ya bayyana a gare shi, sarki ya dube shi ya ce "Ya kai Hukaiza ina so ka

jagoranci MAYAƘA izuwa birnin Baitul-Hazwar dake iyaka da gabar tekun baharul-sawara ku
hallaka duk wata halitta dake ciki koda kiyashi kada ku bari a raye,
Cikin matuƙar ladabi Hukaiza ya miƙe ya fice daga turakar ba tare ya ce uffan ba.
Wannan shi ne dalilin da ya sanya sarki Lamsarul-Azlam ke farautar yaro usaiba mai hatimin
takobin Saiful-zayyad.
Sarki Lamsarul-Azlam na zaune a bisa KARAGAR MULKI cikin suturu na alfarma irin na
hamshaƙan sarakai yana sanye da kambun Sarauta a kanshi a hannunshi yana riƙe da kwagiri
na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login