Showing 18001 words to 21000 words out of 28793 words

Chapter 7 - TAFARKIN TSIRA Book Complete by Sarkin Marubutan Yaki .pdf

sarakai, wani irin
daddaɗan ƙamshi na tashi a jikinshi,
Haƙiƙa shigar ta yi matuƙar fito da tsantsar kyawunshi, domin babu wata mace da za tayi arba
da shi a cikin wannan yanayi face ta kamu da matuƙar ƙaunarshi,
Yayin da Rusayyat tayi arba da shi sai miƙe tsaye tsam! Ta tare shi suka rungume juna na
tsawon daƙiƙa goma, sannan Fitinatul-Amir ya janye jikinshi daga nata, sannan ya ja hannunta
har izuwa inda teburin abincin yake suna zaune a bisa kujerun,
Ba tare da wani jinkiri ba suka shiga kimtsa cikinsu suna fira cikin nishaɗi da tsantsar soyayyar
juna, cikin matuƙar farin ciki Rusayyat ta ɗauki kofin da ta zuba wannan banju a cikin shi ta
sanya wa mai gidanta a bakinshi ya shiga kwankwaɗar ruwan har sai da ya sha ya ƙoshi,
Bayan sun kammala kalacen ne Rusayyat ta lura idanuwan mai gidanta sun fara lunshewa, sai
ta dube shi cikin tattausan murmushi mai ɗimauta zuciyar masoya ta ce "Ya uban 'ya'yana lafiya
kuwa na ga alamun ɓarci a fuskarka?
Koda jin wannan tambaya sai Fitinatul-Amir ya yi murmushi a gare ta sannan yace " kwarai
kuwa zancenki duste ya abar kaunata, haƙiƙa ina jin barci mai nauyi sosai, koda gama faɗin
hakan sai ya miƙe tsaye tsam! Ya kama hannun Rusayyat suka nufi wani ƙasaitaccen gado a
turakar ya kishingiɗa akai, kafin Rusayyat ta yi wani yunƙuri har ya fara aikin rago idanuwanshi
sun rufe,
Cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa Rusayyat ta miƙe tsaye zumbur! Ta fice daga turakar,
Kai tsaye turakar su yaro Usaiba ta nufa, duk inda ta gifta a gidan sarautar sai dai kaga dakaru,
kuyangi, da bayi ba zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa,
Lokacin da ta shiga turakar ta su sai ta iske har yanzu barci suke yi ba su farka ba, cikin
matuƙar farin ciki ta ɗauki garin magani na farko ta buɗe gadon bayan yaro Usaiba ta shafa
masa, nan take zanen hatimin takobin Saiful-zayyad ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa wanzuwa ba,

Sannan ta buɗe bakinta ta karanta dalasiman tsafi ta tofa akan garin magani na biyu wanda
shine kaɗai zai iya ƙarya shirin zanen hatimin takobin ya bayyana, tana gama rufe bakinta garin
maganin ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
A sannanne ta ja wata doguwar ajiyar zuciya, kuma ta ƙurawa Yaro Usaiba da 'yar uwarshi
Hairat idanu hawayen farin ciki suna kwaranyo mata,
Domin a halin yanzu ta samu nutsuwa a zuciyarta tun da ta tseratar da rayuwar yaro Usaiba
mai hatimin takobi daga sharrin mai gidanta shugaban'yan fashin duniya dake farautar shi dare
da rana domin ya hallaka shi,
Wannan shi ne abin da ya faru da Jaruma Rusayyat da mai gidanta Sadauki Fitinatul-Amir.


Lokacin da lokacin birnin Zainul-Ansar suka ɗauki sarki Nu'umanu bisa ƙasaitaccen gadon
marasa lafiya suka shiga da shi izuwa cikin gidan sarauta, sai suka huce kai tsaye da shi izuwa
turakarshi suka shimfiɗe shi suka shiga duba lafiyar shi, suka ɗinke duk wani rauni dake jikinshi
aka sanya masa magani, wani abu da ya bawa likitocin mamaki shine, duk da sarki Nu'umanu
yana cikin halin jinya amma bakinshi bai gushe ba wajen ambaton Allah da yiwa annabin shi
Salati.
Cikin abin da bai gaza daƙiƙa hamsin likitocin suka kammala aikin su, kawai sai wani dattijo
ma'abocin haiba daga cikin likitocin ya ɗauki wani ruwan magani dake cikin kofin azurfa ya
sanya hannunshi ɗaya ya tashi kafaɗun sarki domin ya ba shi maganin, amma sai sarki ya
dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu da yake yi mashi nuni ya dakata, sannan ya buɗi
baki muryarshi na sarƙewa ya ce " Ya kai likita sha'aban kayi sani cewa bana buƙatar a shayar
dani maganin da zai sanya ni barci domin lokacin sallah ya yi har a alfijir ya keto,
Zai fi kyau a ƙyale shi sai na yi sallah sai na sha,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki sai likita sha'aban ya gyaɗa kai yana jin ƙaunar sarki a
zuciyarshi domin kuwa ya tabbata cewa shi shugaba ne abin koyi,
Batare da wani ɓata lokaci ba sarki ya yi kabbara ya tayar da sallah yana da kwance, yana mai
rufe idanuwanshi gami da ɓudewa kuma bakinshi yana motsi alamun cewa ya fara gabatar da
sallar, jin kaɗan ya ya sallama, sannan likita sha'aban ya ba shi ruwan maganin a baki ya kurɓe,
Har wani daga cikin likitocin wani kyakkyawan saurayi ya buɗi baki cikin matuƙar mamaki domin
ya ce wani abu amma sai sha'aban ya tari numfashi shi ya dube shi fuskarshi cike da annuri ya
ce " Yakai Sultan ka yi sani cewa na san ba wata tambaya kake da bukatar kayi mani ba face
yadda sarki ya gudanar da inadarshi, To ina so ka yi sani cewa addini ya sanya sallah ta zamo wajibi ga dukkan Musulmi matsawar
hankalinshi bai gushe ba, a kowa ne irin yanayi mutum zai iya yin Sallah, saboda muhimmancin
sallah Annabi SAW da Sahabbanshi a yaƙi suka yi sallah, ka ga kenan da Allah zai ɗaukewa
wani da ya ɗaukewa Annabin shi SAW da Sahabbanshi", Koda jin wannan bayani daga bakin likita sha'aban sai Sultan ya jinjina kai alamar gamsuwa,
Ana cikin wannan hali ne aka jiyo motsi na kusanto turakar cikin hanzari kowa ya waiga domin
aga ko wane ne, kawai sai aka yi arba da gimbiya lawisat,
Domin sai likita sha'aban da muƙarrabanshi suka juya suka fice daga turakar cikin hanzari,
A dai-dai lokacin lawisat ta iso daf da gadon da sarki ke kwance fuskarta cike da alamun
matuƙar damuwa.
Wannan shi ne abin da ya wakana a cikin gidan sarautar birnin Zainul-Ansar.

BABI NA SHA HUƊU

Al'amarin waziri Yazid kuwa tun sa'adda ya ɓace ɓat! Bayan ya kammala fafata BAƘIN
ARTABU da sarki Nu'umanu, bai bayyana a ko ina ba sai a cikin gidan sarautar a cikin wata
ƙasaitacciyar turaka sarki Rakibu, cikin hanzari likitoci suka taru a kan shi domin ba shi
taimakon gaggawa, cikin abin da bai gaza daƙiƙa talatin ba likitocin suka kammala aikin su, jim!
Kaɗan da ficewar likitocin sai sarki Rakibu da sarkin yaƙi suka shigo turakar suka samu kujeru
suka zauna dake fuskantar waziri Yazid fuskokinsu cike da matuƙar damuwa tsawon daƙiƙa
goma babu wanda yace ƙala a cikin su,
Sai daga can sarki Rakibu ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar buɗe baki ya ce " Ya waziri
shin mene ne mafita ? Ga shi yanzu haƙan mu bai cimma ruwa ba duk shirin da mu ka yi akan
sarki Nu'umanu da jama'ar ya tashi a banza",
Koda jin wannan batu daga bakin Rakibu sai waziri cikin sarƙewar murya ya ce " Ya ku manyan
abokai na ku yi sani cewa ba a san MAZAN JIYA da tsoro ba, rashin nasara akan abu shi ne ke
nuna alamun nasarar, domin rashin nasara shi ne zai sanya ka gyara kusakuren da ka aikata,
ku yi sani cewa matuƙa kuka bi waɗansu sharuɗɗa da zan gindaya tabbas nasara ta same mu. Da farko dai wajibi ne mu nemo ZARATAN JARUMAI da suka ƙware ainun a leƙen asiri da
za su dinga kawo mana rahoton shirin abokan gabarmu,
Sannan zan sihirce wani hadimana domin ya kasance mai sura irin tawa zai tafi zuwa ga sarki
Nu'umanu a matsayin cewa ni ne, wannan wata hanya ce da zata ɗauke hankalin sarki
Nu'umanu da sauran al'ummarsa akan gano cewa da ni za a ci amanar su,
Sannan zamu nemi taimakon waɗansu daga cikin GWARAZAN JARUMAI na jin MUTUM DA
ALJAN,
Sa'adda sarki Rakibu da sarkin yaƙi suka ji wannan dogon jawabi daga bakin waziri sai suka
cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa,
Amma Rakibu ya buɗi baki ya dubi waziri ya ce "To amma ba ka tunanin cewa idan aka samu
gawarwakin dakarunmu za a gano cewa mu ne muka kai MAMAYAR BAZATO ?,
Da jin wannan batu sai dariya ta suɓucewa waziri ya dube shi ya ce " Ya kai Rakibu ban da abin
ka ai lokacin da muka ɓace daga birnin Zainul-Ansar bayan ARTABU ai tare da gawarwakin
dakarunmu muka tawo,
Lokacin da yazo nan a zancen shi sai mayar da duban shi ga sarkin yaƙi sannan ya ɗora da
cewa,
Kai kuma sarkin yaƙi za ka koma birnin Zainul-Ansar ka zauna tare da sarki Nu'umanu a zahiri
za ka nuna kana tare da shi amma a baɗini ba haka ba ne za ka dinga bawa 'yan leƙen
asirinmu bayanai ne kawai,
Da jin wannan ƙarin bayani sai dariyar farin ciki ta suɓucewa sarki Rakibu,
Ba tare da ɓata lokaci ba waziri ya ƙwallawa hadimin sa kira, jim kaɗan! Ya bayyana gare shi ya
zube ƙasa ya kwashi gaisuwa,
Kawai sai waziri ya nuna shi a ɗan yatsanshi na hagu tare da karanta waɗansu dalasiman tsafi
yana gama rufe bakinshi nan take siffar hadimin ta koma san! Ta waziri Yazid tamkar an tsaga
kara, su kansu su sarki Rakibu sai da tunanin su ya dagule suka kasa tantance waziri na
gaskiya da na bogi,

Faruwar hakan ke da wuya sai waziri ya sake nuna hadimin da yatsanshi na hagu a karo na
biyu take ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Sannan ya yi nuni izuwa ga bangon turakar sai ga taswirar turakar sarki Nu'umanu ta bayyana
yana kwance bisa gadon sarauta uwar gidansa Lawisat na zaune a gefen shi cikin alamun
matuƙar damuwa, suna cikin wannan hali ne wannan hadimi mai ɗauke da siffa irin ta waziri ya
shigo turakar hankalin shi ya yi matuƙar DUGUNZUMA, Koda ganin wannan taswira sai sarki Rakibu, Sarkin yaƙi da waziri Yazid suka bushe da dariyar
mugunta har da ƙyaƙyatawa.


Al'amarin gimbiya Nuwairat kuwa tun sa'adda ta suɓuce daga hannun muridi Zabratul-ukub
cikin halin suma, wannan hadimin aljani ma'abocin kyawun sura ya ɗauke ta bai tsaya ko ina sai
birnin MADINATUL-AFNAN,
Lokacin da sarki Rayyan ya ga halin da gimbiya ta ke ciki sai hankalinshi ya DUGUNZUMA
ainun ya tura wata kuyanga ta kirawo mashi liktar masarautar mai suna karima,
Karimat ta bayyana a gare shi tare da mataimakanta suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa cikin
girmamawa,
Cikin hanzari karima da sauran likitocin suka nufi gadon da aka kwantar da gimbiya suka shiga
ƙoƙarin ceto rayuwarta, koda ganin hakan sai sarki Rayyan ya ɗauke jakar dinaren dake ajiye
ajiye a gefen Nuwairat ya juya ya fice daga turakar cikin alamun matuƙar damuwa,
Kai tsaye harabar turakarshi ya nufa ya dinga kai-komo ya kasa zaune,
Yana cikin wannan hali ne sarkin yaƙi Zubairu ibn Saiful-Zaman ya bayyana a gare shi,
Sarkin yaƙi yakasance GWARZON ƘARNI mai tarwatsa DANDAZON MAYAƘA a FILIN FAMA,
kyakkyawa ne na gaban kwatance wanda ganin farko zai ɗimauta zuciyar duk wata 'ya mace
mai hankali, ya gaji sarautar sarkin yaƙi ne a wajen mahaifinshi Barde Huburul-zaman,
Ya jagoranci yaƙoƙi guda ashirin da uku kuma duk ya samu nasara,
Bisa wannan dalili yasanya sarki Rayyan ya ja shi a jikinshi duk wani abu nashi ya ke sanya shi
a ciki,
Tsakanin sarkin yaƙi da gimbiya Nuwairat akwai soyayya mai ƙarfi sai dai sun gaza bayyanawa,
Sarkin yaƙi ya yi sallama irin ta ma'abota addinin Musulunci gami da risinawa ƙasa ya kwashi
gaisuwa,
Sarki Rayyan ya amshi gaisuwar tare da miƙa mashi hannu suka yi musabaha, kuma ya ja
hannunshi har izuwa bisa kan wata ƙasaitacciyar kujera suka zauna tare sannan ya dube shi
cikin nutsuwa ya ce " Ya kai dirkar birnin MADINATUL-AFNAN kayi sani cewa bakomai ya
sanya na kirawo ka nan ba sai domin na bayyana maka cewa gimbiya Nuwairat ta samu
nasarar ɗauko jakar dinaren dake hannun abokin gabarmu sarki Lamsarul-Azlam gani tare da
shi ya kare batun yana miƙa mashi jakar ya ƙarba sannan ya ɗora da cewa " Wannan nasara da
muka samu ba za ta saka mu saki jiki ba, domin a kowa ne lokaci abokan gaba za su iya kawo
mana MAMAYAR BAZATO, domin haka wajibi mu tanadi dakarun kar-ta-kwana",
Koda jin wannan jawabi daga bakin sarki Rayyan sai sarkin yaƙi ya buɗe baki cikin ladabi ya yi
gyaran murya ya ce " Ya shugabana na ji dukkan bayanin ka kuma da yardar Allah SWT za a
aiwatar da komai yadda ka buƙata, sai dai ranka ta daɗe shin ko a wane hali gimbiya take ciki?
Ya ƙare batun cikin alamun damuwa,

Sarki Rayyan ya yi murmushi mai taushi a gare shi ya dafa ƙafadunshi da hannayenshi biyu ya
ce " Kar ka damu ta ɗan samu buguwa ne a kan ta likitoci suna can suna bata kulawa zata
samu lafiya",
Da jin amsar wannan tambaya sai Zuhairu ya risina ga sarki ya miƙe tsaye ya fice daga harabar
hannunshi ɗauke da wannan jakar dinaren.
Wannan shi ne abin da ya faru a can birnin MADINATUL-AFNAN bayan farin hadimin aljani
ya samu nasarar ceto gimbiya Nuwairat daga hannun muridi Zabratul-ukub.

TAFARKIN TSIRA 8
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071





ELEGANT ONLINE WRITER'S



Littafan Marubucin

Kogon Annoba
Sarautar Mutuwa
Kangin Bauta
Jaruman Duniya
Takobin Ɗaukaka
Ƙarshen Zalunci
Fataucin Bayi
Sarkin Sadaukai
Goga Sha Fama
Tafarkin Tsira
Gasar Sarauta
Kundin Al'ajabi




BABI NA SHA BIYAR

A can gidan sarautar shugan 'yan fashin duniya sadauki fitinatul-Amir kuwa, lokacin da yaro
Usaiba mai hatimin takobi da 'yar uwarshi Hairat suka farka daga barci sai kuyangi suka shiga
da su kewaye suka yi masu wanka suka sanya masu tufafi masu tsadar gaske, bayan an shirya
masu abin kalaci sun kimtsa cikinsu sai Rusayyat ta ɗauke su a bisa wani ƙayataccen keken
doki ta shiga da su izuwa lambun shaƙatawa ta zaunar da su ƙarƙashin wata itaciya mai
manyan rassa,
Lambun ya ƙawatu da nau'ikan shuke-shuken furanni masu kyawun launi da ƙamshi, ƙoramu na
gudana da ruwa garai-garai, waɗansu irin tsuntsaye masu kyawun launi da kuka mai daɗin
saurare ya shawagi a rassan bishiyu,
Wohoho! Haƙiƙa wannan lambu ya cika aljannar duniya, domin babu wata halitta a doron ƙasa
MUTUM DA ALJAN da za su tsinci kansu a wannan waje face sun ƙwadaitu da su kasance a
lambun har ƙarshen rayuwar su.
Shiru ne ya wanzu a tsakanin su na ɗan lokaci daga bisani Yaro Usaiba ya katse shirun da
wanzu ta hanyar ɓudar baki ya yi gyaran murya ta ce " Ya ummun mu kin yi mana alkawari
cewa za ki bamu labarin rayuwarki?.
Koda jin wannan tambaya sai ƙwalla ta zubo daga idanun Rusayyat,
Al'amarin da ya yi matuƙar DUGUNZUMA hankalin Usaiba da 'yar uwarshi kenan ya dube ta
cikin alamun matuƙar damuwa ya ce " Ya ummina ki yi mini afuwa idan tambayar da nayi miki ta
ɓata maki rai",
Rusayyat ta yi guntun murmushi a gare shi ta buɗi baki a karo na farko ta ce " Ko kaɗan
tambayar ka bata ɓata mini rai ba, kawai dai ta tuna mini da labarin uƙubar da na sha a
rayuwata,
Yanzu sai ku gyara zama domin ku ji yadda labarin nawa ya kasance.
Rusayyat ta fara labarin kamar haka:-

A wani zamani can baya mai tsawo da ya shuɗe a yankin ƙasashen Larabawa an yi wani
ƙasaitacciyar birni da ake yiwa laƙabi da Hairul-Mazwar,
Birnin Hairul-Mazwar ya bunƙasa ya bunƙasa a arziƙin noma da kiyo, suna da ZARATAN
JARUMAI masu juriya a FILIN DAGA, har su fatake ke kiran sunan da suna BIRNIN
SADAUKAI,
Sarkin dake mulkin birnin ana yi mashi laƙabi da Hubru ibn Kamsil,
Sarki Hubru yakasance dattijon mutum mai tausayi da jin ƙari, GWARZON MAYAKI ne mai
tarwatsa DANDAZON JARUMAI a filin fama,
Bisa wannan dalili yasanya sarakunan dake maƙwabtaka da shi suke matuƙar shayin shi, Ni da
mahaifana muna zaune ne a ƙauyen da ke wannan birni, kasancewar mu talakawa hakan
yasanya bana samun wani jin daɗin rayuwa sosai,
Mahaifina yakasance makaho, mahaifiyata kuwa gurguwa ce bata da ƙafafu, a kowa ce
hudowar rana ni da mahaifana sai mun shiga izuwa cikin birni mun yi bara, abin da muka samu
da shi za mu yi kalaci, duk ranar da ba mu samu ba kuwa sai dai mu kwana da yunwa.
Wata rana ni da mahaifana muna bara a cikin kasuwa ina riƙe da sandarshi, sai mu ka zo
hucewa ta rumfar wani attajiri,

Attajirin yakasance garjejen ƙato, fuskarshi mai matuƙar gwarjini ce yana da idanuwa jajur!
Tamkar garwashi ya tara ƙasumba da gemu mai tsawo da ya shimfiɗo har bisa ƙirjinshi, kanshi
a salsale yake babu ɗigon gashi ko ɗaya sai ƙyalli yake yi tamkar sabuwa tasa,
Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci cewa yana da ƙarfi na Allah ya isa, kuma ya tara dukiya
mai tarin yawa saboda surutan dake sanye a jikinshi irin na hamshaƙan sarakai ne, kai ! Ko
takalmi da kwamitin dake hannunshi abin kallo ne,
Har mun huce ta gaban attajirin sai ya kirani na zo na ƙarɓi sadaka, cikin matuƙar farin ciki ya ja
sandar mahaifana da nufin na koma da baya domin tun da muka baro gida babu wanda ya
bamu koda dinare guda amma bisa mamaki sai na ji mahaifana ya tsaya can! Ba tare da motsa
daga inda yake ba, a tunani na ko bai fahimci abin da nake nufi ba ne sai kawai na ƙyale shi
anan tsaye na nufi inda wannan attajiri ke hakimce a cikin rumfarshi,
Tun kafin na iso gare shi ya ƙura mini idanu ko ƙiftawa ba ya yi, kuma fuskarshi cike da annuri
tamkar wanda aka bawa SARAUTAR DUNIYA,
Lokacin da na isa gare shi sai ɗebo dinare mai tarin yawa a cikin wata jakar fata ya miƙa mini
cikin ladabi hannayena na kyarma saboda mamakin yawan dinaren wanda sai mu shekars
muna bukatunmu da shi na durƙusa na ƙarɓa, sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login