Showing 21001 words to 24000 words out of 28793 words
Chapter 8 - TAFARKIN TSIRA Book Complete by Sarkin Marubutan Yaki .pdf
ya koma izuwa inda a bana ke tsaye na
riƙe sandar jagora mu ka cigaba da tafiya, Muna cikin wannan tafiya ne na waiga izuwa inda wannan attajiri yake aikuwa sai na ga har
yanzu bai ɗauke idanuwanshi daga kaina ba,
Nan take n tambayi kaina a cikin raina na ce shin wannan attajiri tsananin tausayin da yake yi
mana ne yansa shi wannan murmushi ko kuwa? Kuma na lura da yadda fuskar abbana ta
canza a cikin ƙanƙanin lokaci,
Amsar tambayar da ba kasa bawa kaina kenan,
Kawai na dubi mahaifina cikin alamun matuƙar damuwa na ce " Ya abbana shin ina dalilin
wannan fushi na ka? Shin baka farin ciki bisa wannan sadaka da muka samu da za ta iya
magance mana dukkan matsalolinmu na rayuwa ?
Koda jin wannan tambaya sai abbana ya sake murtuke fuska al'amarin da ya sanya na sha jinin
jikina keman,
Daga bisani ya yi ajiyar zuciya ya dube ni ya ce " Ya cikar muradin rayuwa ta kiyi sani cewa da
ace kin san abin da na sani da ba kiyi gangancin ƙarbar sadakar wannan attajiri ba, domin babu
wani alkairi a tare da shi,
Ina mai baƙin cikin sanar da ke cewa a halin yanzu rayuwarmu na cikin halin TSAKA MAI
WUYA wajibi ne a gare mu mu yi hijira daga su tafi izuwa wata nahiyar domin shirya wa kan mu
sabuwar rayuwa",
Koda jin wannan batu sai hankalina ya DUGUNZUMA ainun na dubi mahaifana cike da matuƙar
mamaki na ce " Ya abbana shin mene ne sharrin da ka sani a tare da wannan attajiri da har zai
sanya mu yi hijira ?,
Mahaifina ya gyaɗa kai cikin takaici ya ce " Ya 'yata ki yi sani cewa a halin yanzu babu lokacin
da zan iya bayyana miki ko wane ne attajiri Kulbus, sai dai na yi miki alkawari bayan mun samu
matsugunni a can wata nahiyar daban zan bayyana miki wane Kulbus, ya cikar farin ciki na ki yi
sani cewa sirrin da muka daɗe ni da mahaifiyarki muna ɓoye miki duka ya tattara ne akan attajiri
Kulbus, ba domin ƙaddara ta sake haɗa mu da shi ba ko da sunan shi bana so kunnuwana su
sake saurare har ajali ya riske ni",
Koda jin wannan batu daga bakin mahaifana sai ƙwalla ta zubo daga idanuna kuma na fahimci
cewa haƙiƙa na aikata babban kuskure ga mahaifana na karɓar sadakar attajiri Kulbus,
Mahaifina ya sake duba na a karo na biyu ya ce "Sai ki yi hanzari mu isa izuwa gida kar duhun
dare ya riske mu a hanya"
Koda jin hakan sai na riƙe sandar mahaifana muka cigaba da tafiya cikin hanzari suka fice daga
kasuwar har muka nausa izuwa cikin daji,
Muna cikin tafiyar ne a cikin daji wanda mun saba huce ta cikin shi ba tare da wata fargaba ba,
Kaico! Haƙiƙa rashin sani ya fi dare duhu, kuma tabbas tashin hankali ba a sa masa rana,
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai mu ka ji an ɓarke da wata irin mahaukaciyar dariya mai
kama da haniniyar doki, jim! Kaɗan sai ga waɗansu zunzurutun samudawan dakaru na ratsowa
daga cikin duhuwar bishiyun dajin,
Dakarun suna shirye cikin wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro,
suna ɗauke da miyagun makamai masu barazana ga rayuwar MUTUM DA ALJAN,
Komai dakewar zuciyar jarumi da rashin tsoron shi idan ya yi arba da Waɗannan dole ne ya
ɗimauce,
Kafin mu yi wani yunƙuri dakarun sun yi mana ƙawanya suna muzurai tamkar za su ci babu,
koda ganin hakan ban san lokacin da hawaye suka kwaranyo daga idanuna ba na riƙe hannun
mahaifina.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai mu ka ji an bushe da wata mahaukaciyar dariya mai
matuƙar ban tsoro, daga can sai sautin dariyar ya ɗauke, kawai sai dakarun dake ɓangaren
yamma suka dare suka samar da wata 'yar siririyar hanya da mutum biyu za su iya jeruwa,
kwatsam! Sai ga attajiri Kulbus ya ratso ta hanyar ya durfafo inda muke tsaye yana mai taka
ƙafafuwanshi cikin ƙasaita fuskarshi a murtuke babu annuri, kuma a wannan lokaci yana shirye
cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, tun da nake a rayuwata ban taɓa
ganin sadauki mai kwarjini tamkar attajiri Kulbus ba,
Ya yin da yazamana cewa tazarar dake tsakanin mu da shi ba ta huce taku goma ba sai kawai
ya ja ta tsaya cak! Yana mai ƙura mana idanu ko ƙitawa ba ya yi,
Al'amarin da sanya tsoro ya sake kama ni ainun kenan jikina ya kama ƙyarma!,
Tsawon daƙiƙa talatin muna cikin wannan hali sai daga bisani ne attajiri Kulbus ya sake
bushewa da dariya a karo na biyu sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi
da sakon mutuwa ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai ban tsoro ya dubi abbana ya ce " Ya
kai makaho Zafiyar ka yi sani cewa tsawon lokaci ina farautar ka a cikin wannan birni amma ban
samu nasara ba sai a yau, ko ka manta cewa na faɗa maka indai kere na yawo zabo na yawo
wata rana sai sun gamu",
Koda jin wannan batu daga bakin Kulbus sai mahaifana ya fusata ainun ya daka mashi tsawa
ya ce " Ya kai babban maci amana kuma mayaudari ka yi sani cewa har abada ƙarshen maci
amana mutuwar wulakanci, ina yi maka albishir da cewa yau zan hallaka ka".
Ko da jin wannan batu daga bakin abbana sai Kulbus ya bushe da dariya ya ce " Ya kai
Zariyar ka fi kowa sanin cewa ko ba a gwada ba linzami ya fi ƙarfin bakin kaza, kar ka manta
cewa a halin yanzu kai makaho ne idanuwanka ba sa gani, kuma tsufa ya fara kama ka ba ka
da jarumtakar da za ka yin KARON BATTA da ni ba, sannan wannan 'ya taka ba ta da ƙarfin da
za iya kare ka daga ka ba".
Kafin Kulbus ya gama rufe bakinshi na tari numfashin shi ina mai daka ma shi
tsawa na na buɗe baki da nufin na furta wani abu amma sai mahaifana ya dakatar da ni ta
hanyar ɗaga mini hannu, kawai ya ɗaga sandarshi ya shammaci Kulbus ya make takobin sa ke
hannunshi ya taƙarƙare ya gabza mashi wawan naushi a fuska da dukkan ƙarfin shi,
Saboda ƙarfin naushin sai da Kulbus ya yi taga-taga zai faɗi ƙasa amma sai ya turje ya shafa
fuskarshi da hannunshi na hagu take ya ji jini na zuba a hancinshi,
Al'amarin da ya yi matuƙar bani mamaki kenan kuma ya ɗaure mini kai, domin a iya sani na
mahaifana ko da wuƙar yankan tuffa bai iya riƙewa, amma ya ya aka yi ya samu wannan
gagarumin ƙarfi haka? Amsar tambayar da na kasa bawa kaina kenan,
Shi kuwa attajiri Kulbus sai ya fusata ainun ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu da ya firgita duk
wata halitta dake dajin, yana gama rufe bakin shi sai dakarunshi suka zare makamansu suka yi
ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA a FIKIN DAGA, suka ɗauki izuwa kan
mahaifina, Koda jin hakan sai mahaifana ya daka wawan tsalle tamkar an harba shi daga cikin baka ya
sauka a daf da dakarun tamkar yakasance mai gani ba makaho ba, ya shammaci mutum huɗu
a cikin su ya gabza masu wawan naushi a fuska a lokaci guda suka zube ƙasa magashiyan
suna nishin wahala. Lokacin da Jaruma Rusayyat ta zo dai-dai nan a labarin da take bawa su yaro Usaiba sai
hawaye suka kwaranyo daga idanuwanta, sannan cigaba da cewa
BABI NA SHA SHIDA
Sa'adda na ga an kacame da azababban yaƙi tsakanin mahaifina da dakarun sai na ruga
izuwa bayan wata bishiya na rakaɓe ina leƙen abin da ke wakana zuciyata cike da matuƙar
mamakin jarumtaka irin ta abbana duk da kasancewar shi makaho,
Wani ɓangaren a zuciyata kuwa cike yake da tsoro akan abin da zai iya biyo baya idan attajiri
Kulbus ya samu nasara akan abbana, wani tunani da ya faɗo mini a rai ya dungunzuma
hankalina shi ne mahaifyata da baro a gida shin ko a wane hali take ciki,
Sa'adda na zo nan a tunanina sai hawaye suka kwaranyo mini,
Duk inda abbana ya sanya a gaba sai dai ka ga dakaru na zubewa ƙasa matattu tamkar ana
karkaɗe busassu ganyeyya kin bishiya a lokacin hunturu, sassan jikkunan bil'adama suka dinga
shawagi a sararin samaniya suna zubowa ƙasa, jini ya dinga kwanya, tsartuwa yana malala a
ƙasa, Nan da karafniyar ƙarafa da ihun MAZAJE ta cika dodon kunne,
Wohoho! Haƙiƙa jarumtaka baiwa ce da zaɓi na Ubangiji dukiya ko mulki ba sa bayar da ita,
Komai hassadar mutum idan ya ga yadda makaho Zafiyar ke ragargazar dakarun dole ne ya
jinjina mashi ya tabbatar da cewa ya shiga MURUCIN KAN DUTSE..,
"Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya ana wannan Baƙin ARTABU babu sassauci,
Kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA yafi SARKIN ƘARFI sai dakarun
Kulbus suka fara galabaitar da mahaifana suka haɗa mashi jini da majina har ta kai cewa ya
faɗi ƙasa magashiyan yana numfashi da ƙurar! Al'amarin da sanya ni zubar da hawayen baƙin
ciki kenan, Koda samun wannan gagarumar nasara sai attajiri Kulbus ya bushe da dariyar mugunta sannan
daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da sakon mutuwa ya zare wata sharɓeɓiyar
takobi a damtsenshi daga cikin kubenta ya taka da ƙafafuwanshi har izuwa inda mahaifana ke
kwance ya sanya KAIFIN TAKOBI ya yi wa abbana yankan rago ya yi jifa da gawarshi gefe
guda".
Lokacin da Jaruma Rusayyat ta zo dai-dai nan a labarin rayuwarta sai ta fashe da matsanancin
kuka mai tsuma zuciya hawaye suna kwaranyo daga idanuwanta, al'amarin da ya sanya yaro
Usaiba da yar uwarshi Hairat su ka fara zubar da hawayen saboda matuƙar tausayin ta,
Tsawon daƙiƙa talatin suna cikin wannan hali sai daga bisani ne Rusayyat ta share hawayenta
ta dube su a lokacin da idanuwanta suka kaɗa suka yi jajur ta ce " Ya ku 'ya'yana ku yi sani
cewa wannan labari nawa da na ba ku ba a ɗauki kaso ɗaya bisa biyar ɗin shi ba, kuma wanda
zan ba ku anan gaba ya fi shi ban tausayi da takaici". Koda jin wannan batu daga bakin Rusayyat sai yaro Usaiba ya dube ta cikin alamun matuƙar
damuwa ya ce " Ya ummina haƙiƙa attajiri Kulbus ya cika baƙin azzalumi marar tausayi, shin ta
ya aka yi kika kuɓuta daga hannun shi sannan mene ne abin da ya faru da mahaifiyarki?, Koda
jin waɗannan tambayoyi sai ƙwalla ta zubo wa Rusayyat ta dube shi ta ce " Ya ɗan abin alfahari
na ka yi sani gaba ɗaya amsar tambayoyin da ka yi mini suna cikin ƙasashen labarina, yanzu za
mu koma izuwa gida domin lokacin yin kalaci ya yi, zuwa gobe zan cigaba daga in da na tsaya".
Koda gama faɗin hakan sai Rusayyat ta riƙe hannayen su suka tashi tsaye ta ɗora su a bisa
wannan keken doki, ta hau ta zauna ta bisa dokin keken ta sakar ma shi linzami suka fara tafiya
suna durfafar hanyar da zata sadasu da harabar gidan sarauta.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin jaruma Rusayyat uwar gidan shugaban'yan fashin
duniya sadauki fitinatul-Amir tare da su yaro Usaiba mai hatimin takobi.
Mu haɗu a Littafin TAFARKIN TSIRA 9 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa lakabi da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaki
Wthapp Number
0813723771
TAFARKIN TSIRA 9
Littafin Yaƙi
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
Littafan Marubucin
Kogon Annoba
Sarautar Mutuwa
Kangin Bauta
Jaruman Duniya
Takobin Ɗaukaka
Ƙarshen Zalunci
Fataucin Bayi
Sarkin Sadaukai
Goga Sha Fama
Tafarkin Tsira
Gasar Sarauta
Kundin Al'ajabi
BABI NA SHA BAKWAI
Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin sadauki ukaiza shugaban dakarun sarki
Lamsarul-Azlam da ke farautar yaro mai hatimin takobi tare da dakaru dake tsaron ƙofar birnin
Baitul-Ashmar, sai yaƙin ya zamto abin tsoro gami da tashin hankali, yawan dakarun ya zamo a
banza domin ukaiza ya wanzu yana aika rayukan su izuwa barzahu KAIFIN TAKOBInsa ya
dinga ratsa sassan jikkunan su JINI DA ƘASA suna cakuɗuwa da juna,
Kaifin shudewar daƙiƙa hamsin ukaiza ya hallaka fiye da rabin dakarun, al'amarin da ya razana
sauran kenan domin tun da suke gadin wannan ƙofa ba a samu GWARZON MAYAKI da ya
samu nasara akan su na shin wane ne wannan sadauki? Amsar tambayar da suka kasa bawa
kansu kenan, Ana cikin wannan ARTABU ne wani tunani ya faɗo wa ukaiza tunanin kuwa shi ne, idan har ka
bari aka ɗauki wani lokaci ba tare da ka yi nasara ba to dakarun dake cikin gari za su samu
rahoton abin da ke faruwa domin haka za a tsaurara matakan tsaro,
Sa'adda Ukaiza ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya dinga amfani da hikima ya na kashe fitilun
dake wajen , yayin da ya fahimci cewa wajen ya yi dubu dunɗum! Sai kawai ya shammaci
dakarun ya kunna kai izuwa cikin birnin, ya bar dakarun suna ta ƙoƙarin kunna fitilun, kai tsaye
gidanshi ya nuna domin ya ga wane hali iyalinshi ke ciki, Lokacin da isa sai ya tarar ƙofar gidan a buɗe kuma ko wane waje a ciki haskake yake da fitilar
ice, al'amarin da ya yi matuƙar ba shi mamaki kenan, kuma zuciyarshi ta buga da ƙarfi, amma
sai ya kunna kai izuwa ciki yana sanɗa hannunshi dafe da kuben takobinshi domin shirin kar ta
kwana, ya yin da ya yi kamar taku shida a zauren gidan sai kawai ya ji an gabza ma shi wani
wawan naushi a ƙeyarshi saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da ya yi katan-tanwa sai uku sai ya
faɗi ƙasa tim! A matuƙar galabaice yana mai kurma ihu, kafin ya yi wani yunƙuri waɗansu irin
samudawan dakaru ma'abota jajayen tufafi sun ɗaure shi tamau da wata irin murtukekiyar igiya
sannan ɗaya daga cikin su ya ɗauke shi ya ɗora shi a kafaɗarshi ya nufi ƙofar fita daga gidan,
sauran dakarun mutum shida suka yi koyi da shi, suna fita kai tsaye suka durfafi wata hanya da
zata sadasu da kurkukun birnin suna tafiya cikin hanzari.
Wannan shi ne abin da ya wakana tsakanin sadauki ukaiza da dakarun sarki
Lamsarul-Azlam.
Al'amarin boka kaddad kuwa tun sa'adda ya tura aljani Lattul-kifas domin farauto mishi yaro
mai hatimin takobi sai ya shafe tsawon kwanaki biyu bai ji ɗuriyar shi ba, yayin da ya fahimci
cewa wankin hula zai kai shi dare sai kawai ya yanke shawarar ya gudanar da bincike bisa
halarar tsafin shi domin gano abin da ke wakana, Sa'adda ya gudanar da bincike nan take ya ga dukkan abin da wakana tsakanin Lattul-kifas da
dakarun dake gadin gidan sarkin 'yan fashin duniya sadauki fitinatul-Amir, koda ganin hakan sai
ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu, sautin ihun ya amsa kuwwa har izuwa cikin dajin ya tashi ha
hankulan tsuntsaye dake kan bishiyu suka bazama wajen canja sheƙunansu, Tsawon daƙiƙa ashirin yana cikin wannan hali sai daga bisani ne ya murtuke fuska an aiko mishi
da sakon mutuwa,
Sannan ya sake baje alƙalumman sihirin shi ya cigaba da gudanar da bincike, yana cikin
wannan hali ne kuma sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar farin ciki,
Ba wani abu ne ya sanya shi wannan dariya ba sai domin ya gano cewa har abada ba zai taɓa
cimma burin shi na shan jinin yaro mai hatimin takobi ba kuma har ya kawar da Jaruma
Rusayyat da mai gidanta ba face ya mallaki wata hula da ake yiwa laƙabi da Lauhul-Sihir,
Hular Lauhul-Sihir ta kasance mallakin sarkin bokayen aljanun duniya wanda a ƘARNI UKU
bayan yaƙin duniya na farko ba a samu GWARZON MAYAKI tamkar shi ba,
Binciken masana da masu hasashe ya tabbatar da cewa boka ƙaddamul-Barzahu yana iya
yaƙar gari guda shi ƙadai ya cinye shi da yaƙi b zai bar koda ƙiyashin birnin a raye ba,
Kuma an ce ya shafe tsawon shekaru ɗari bakwai yana sana'anta hular Lauhul-Sihir bayan ya
kammala ne ya shiga yaƙar sarakunan duniya yana mayar da su izuwa ƙarƙashin ikon shi, wata
ƙasa ce ta ma'abota addinin musulunci kawai ta zamo mishi cikas wajen cimma burin shi na
BAUTAR SARAKAI na duniya, bisa wannan dalili yasanya masana ke yi masa laƙabi TARKON
SARAKAI,
Daga cikin amfanin da hular Lauhul-Sihir shi ne duk mahalukin da ya mallake ta zai mulki
dukkan sarakunan duniya,
Tana ɗauke da sirrkan tsafi guda miliyan biyu da babu wanda zai same su face wanda ya
mallaki hular,
Duk wanda ke sanye da hular zai iya shafe tsawon sa'o'i yana ARTABU ba tare da ya ci ko ya
sha ba,
Babu wani makami da zai yi tasiri akan shi, duk tsawon shekarun da mutum ya shafe yana jinya
inda aka sanya mishi ita nan take zai warke sumul tamkar bai taɓa jinya ba,
Sirri na ƙarshe shi ne mutum na iya sanya hular izuwa kowa ne nau'in makami kuma ya aikata
zuwa inda yake so ta aiwatar da dukkan abin da ya nufa,
A halin yanzu hular Lauhul-Sihir tana ajiye a wani kogon dutse mafi haɗari a duniya, kafin
mutum ya isa inda yake sai ya ƙetare waɗansu miyagun dazuka guda sha biyu,
Babu wani mahaluki da doran ƙasa da zai iya shiga kogon face ya mallaki wani ALLON SIHIRI,
Allon yana ajiye a cikin wani masifaffen kada dake zaune a ƙarƙashin tekun Baharul-Saljir,
kadan ya haɗiye Allon ne a lokacin da waɗansu manyan matsafan duniya suka fafata yaƙi a
saman tekun domin ɗayan su