Showing 15001 words to 18000 words out of 28793 words
Chapter 6 - TAFARKIN TSIRA Book Complete by Sarkin Marubutan Yaki .pdf
daga kan kujerar da take zaune ta fita daga turakar ta nufi turakar mai gidanta,
Da yake a wannan lokaci safiya ce ko wane waje a gidan sarautar ya cika maƙil da barori,
Hadimai da bayi, Duk inda Rusayyat ta gifta sai ka ga bayi da barori na zubewa ƙasa suna
kwasar gai wawa cikin girmamawa, kai tsaye ɓangaren da ake dafa abinci ta kunna kai, sa'adda
da kuyangi dake hidima a wajen suka yi arba da ita sai suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa,
wata dattijuwa daga cikin kuyangin da ake kira da suna Ashrila ita ce ta yi gyaran murya ta ɗago
da kanta cikin ladabi ta ce "Ya shugabata lafiya mu ka gan ki a wannan lokaci da ba ki saba
zuwa ba ?
Ko da jin wannan batu daga bakin kuyanga Ashrila sai Rusayyat ta daka mata tsawa ta dube ta
ta ce "Ya ke Ashrila shin wane irin rashin hankali ne ya sanya ba a kai wa mai martaba uwan
wanka kewaye ba, kuma an shirya abin kalaci har hasken rana ya bayyana haka?
Sa'adda Ashrila ta ji wannan tambaya sai jkinta ya kama tsuma yana ƙyarma saboda matuƙar
tsoro bakinta na karkarwa ta ce " Ayi ma-ni afu-wa ya shu-gaba-ta"
"Ina so a kammala komai cikin daƙiƙa ashirin kacal!" Rusayyat ta faɗa sannan ta juya ta fice
daga madafar ta nufi wata ƙofa ta musamman domin ta isa turakar mai martaba.
Lokacin da ta iso sai dakarun dake tsaron ƙafa suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa
sannan suka wangame ƙofar ta kunna kai izuwa ciki, da shigarta ta tarar mai gidannata yana
kwance bisa gadon sarauta yana sharar barci har da minshari,
Sai kawai ta matsa izuwa gareshi ta zauna a gefen gadon ta sanya hannayenta biyu ta shafi
fuskar mai gidanta nan take ya farka ta hanyar buɗe idanuwanshi gami da yin miƙa ya zuba
fararen idanuwanshi masu haske gami da kwarjini akan uwar gidant asa.
Cikin wani tattausan murmushi mai ɗimauta zuciyar duk wani ɗa namiji mai hankali cikin
zazzaƙar murya mai daɗi tamkar sarƙewa ta ce "Barka da safiya SARKIN SADAUKAI ma'abocin
kyawun sura da annuri, lafiya yau barcinka ya yi nauyi haka ?
Ko da jin wannan batu sai fitinatul-Amir ya yi murmushi mai kama da yaƙe ya ce "Tabbas kam
yau na makara ya abar kaunata dare da rana kuma na yi mamakin hakan"
Rusayyat ta yi murmushi a karo na biyu sannan ta ce "Ya annurin rayuwata ai sai ka tashi ka
shiga izuwa kewaye domin tuni kuyangi sun tanadi ruwan wanka"
Tana gama faɗin hakan sai ta miƙe tsaye tsam ta kama hannun mai gidanta ta tashe shi tsaye
ta ja shi har izuwa inda kewayen ya ke sai da shigar da shi har ciki ta janyo Ƙofar ta rufe sannan
ta dawo izuwa turakar ta shiga gudanar da bincike domin ta gano inda garin maganin shirin
yake. Abu kamar wasa sai ga shi Rusayyat ta shafe tsawon daƙiƙa hamsin ta na bincike a turakar
amma ba ta gano inda garin maganin yake ba kuma a dai-dai a wannan lokaci ne ta jiyo alamun
takun sawaye yana kusanto turakar, al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin ta kenan
ta ta ji kamar ta saki fitsari a wando.
BABI NA SHA BIYU
A can Birnin Zainul-Ansar kuwa lokacin da aka cigaba da fafata azababban yaƙi tsakanin
dakarun haɗin gwiwa da dakarun musulunci sai yazamana an rincaɓe MUTUWAR MAZAJE
ihun dakaru gami da ƙarar karafniyar ƙarafa suka cika dodon kunne, sassan jikkunan bil'adama
suka dinga shawagi a sama suna zuba a ƙasa JINI DA ƘASA suka cakuɗe babu kyawun gani. A cikin gidan sarauta kuwa, sarki Nu'umanu da waziri Yazid sun wanzu suna kaiwa juna sara
da suka cikin baƙin zafin nama JURIYA DAa BAJINTA, duk sa'adda takubbansu suka haɗu da
juna sai ka ga tartsatsin wuta ya tashi haɗe da ƙara mara daɗin saurare,
Sai da suka shafe tsawon daƙiƙa hamsin a cikin wannan hali suna ɗauki-ba-daɗi amma
ɗayansu bai samu nasarar lakutar jikin ɗan uwansa da takobinshi ba har makamansu suka fara
dakushewa, yayin da sarki Nu'umanu ya ga abin da ke faruwa sai ya shiga neman taimakon
Ubangiji a cikin zuciyarshi yana mai cewa "Ya Ubangijin halitta ka taimaki bawanka mai rauni a
bisa maƙiyin addininka".
Tabbas! Ubangiji mai amsa roƙon bayinsa ne a duk lokacin da suka miƙa komai nasu
izuwa gare shi,
Ana cikin wannan yaƙi ne sarki Nu'umanu ya samu nasarar yiwa waziri Yazid wani lafcecen
sara a kafaɗarshi jini ya yi tsartuwa, kafin ya sake mayar da wani martanin waziri ya kaiwa
masa wani bahagon sara a kafaɗarshi, duk da irin zafin naman da waziri ya yi wajen kaucewa
saran sai da takobin ta yi masa rauni jini ya yi tsartuwa,
Kafin shudewar daƙiƙa talatin kowannensu ya yiwa abokin faɗanshi rauni fiye da guda goma
layi na ɗibarsu tamkar waɗanda suka sha barasa suka bugu,
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa Nu'umanu kai kenan kuma ba shi mamki bisa ganin cewa
duk da yana neman taimakon Ubangiji amma ya gaza samun nasara akan abokin gabarshi,
Abin da sarki Nu'umanu bai sani ba shi ne, kamar yadda yake neman taimakon Ubangijin
Musulmi haka shi ma waziri ya ke yi.
Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce "makashin ka yana nan tare da kai"
kuma da zama da munafiki gwara zama da ɓarawo, domin shi dai munafiki yana tare da kai ne
kuma yana cutar da kai ba tare da ka sani ba, shi kuwa ɓarawo sai ya ga kayanka zai ɗauka,
yanzu dai ga shi Sarki Nu'umanu yana artabu da wazirinshi amma bai sani cewa shi ne abokin
gabar shi ba,
Ana cikin wannan yaƙi ne sarki Nu'umanu da waziri Yazid suka cakawa junansu tsinin
takubbansu a cinyoyinsu na hagu take wajen ya dare jini ya yi tsartuwa, a lokaci guda suka
zube ƙasa magashiyan suna masu nishin wahala, a cikin wannan hali ne waziri ya shafi wani
gurun tsafi a damtsenshi na dama ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa wanzuwa ba, A lokacinne waɗansu likitoci suka rugo izuwa wajen ɗauke da gado na ɗaukar mara sa lafiya
aka shigar da shi izuwa cikin gidan sarauta domin ba shi taimakon gaggawa.
***
Al'amarin aljani Lattul-kifas kuwa, wato hadimin boka kaddadul-Gurub da ya tura domin
farauto mashi yaro mai hatimin takobi domin ya yanka shi ya sha jinin shi,
Tun sa'adda ya kammala fafata yaƙi da dakarun dake gadin gidan shugaban 'yan fashin duniya
ya kwanta barci, bai kwanta ba har sai da gari ya waye rana da ƙwalle sannan ya farka ya yi
miƙa gami da hamma,
Sannan ya miƙe tsaye yana nazarin Ƙofar da zai shiga gidan ko da kammala nazarin sai ya
kaɗa fuka-fukanshi ya tunkari wani sashi, lokacin da ya rage saura taku goma ya isa ba sai
kawai ya ji an ɗamƙe shi an shaƙama shi wani sinadari a hanci barci mai nauyi ya ɗauke shi,
Bai tsinci kanshi a ko ina ba sai a cikin ƙasaitaccen kurkuku mai matuƙar kwarjini, duk inda ya
kai dubanshi a kurkukun babu abin da zai gani face bayi, da barori na jinsin mutum da aljan
suna ta kai komo suna aiyukan wahala waɗansu kuwa ana gana masu ukuba nau'i
daban-daban. Sa'adda aljani Lattul-kifas ya tsinci kanshi a cikin wannan kurkuku sai ya firgita ainun
jikinshi ya kama tsuma bai sa'adda ya saki fitsari a wando ba, kawai sai ya yunƙura da nufin ya
tashi sama, amma sai ya ji shi ɗaure cikin sasari na baƙin ƙarfe hannu da ƙafa,
Yana cikin wannan hali ne waɗansu irin samudawan dakarun aljanu biyu suka tusa ƙeyarshi
izuwa wani ɗaki na musamman a kurkukun wanda aka gina shi da zallar duwatsun wuta masu
ƙwarin gaske,
A tsawon rayuwar Lattul-kifas bai taɓa gani ko jin labarin kurkuku mai ɗauke da musibu da
annoba tamkar wannan kurkuku ba,
Shi dai wannan kurkuku ana yi masa laƙabi da Sarirul-Maut, ma'ana matattarar dukkan musibun
duniya, bokaye da masu hasashe sun tabbatar da cewa tun bayan rushewar kurkukun Sarkin
bokayen duniya na farko wato boka shuyuɗan mai mallakin ANNOBA ƊARI ba a samu kurkuku
mai ɗauke da musibu da nau'ikan azaba tamkar kurkukun Sarirul-Maut ba.
Ba wani ba ne ke ɗauke da mallakin kurkukun ba face sadauki fitinatul-Amir shugaban'yan
fashin duniya, fiye da kaso hamsin na musibun dake kurkukun ya sana'anta su da ƙarfin shirin
tsafi, kuma babu wata nau'in dabbar daji mai cutarwa da babu ita a cikin kurkukun, kuma a
tarihin kurkukun ba a taɓa samun wani mahaluki da ya shiga kuma ya fito a raye ba.
***
Al'amarin sadauki ukaiza kuwa wato shugaban dakarun sarki Lamsarul-Azlam da ya tura
domin farauto ma shi yaro mai hatimin takobi, sai da dare ya tsala sannan ya durfafi hanyar da
zata sada shi da birnin Baitul-Ashmar, lokacin da ya zamana saura bai huce taku talatin
tsakanin shi da birnin sai kawai ya yage wani yanki a tufafinshi ya rufe fuskarshi da shi ta yadda
babu wanda zai iya gane shi, sannan ya durfafi ƙofar birnin,
Lokacin da dakarun dake tsaron ƙofa suka hango shi sai suka dafe kuben takubbansu domin
jiran ko ta kwana,
Yayin da ya iso sai wani basamuden ƙato daga cikin dakarun wanda da alamu shi ne
shugabansu ya dube shi da 'yan mini-minin idanuwanshi masu kama da garwashi saboda ja da
suka yi ya dakama shi tsawa mai firgitarwa sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an
aiko mashi da WASIKAR MUTUWA cikin kakkausar murya ya ce "Shin wane ne kai? Kuma
mene ne ke tafe da kai izuwa wannan birni namu mai albarka?
Ko da jin waɗannan tambayoyi sai ukaiza yayi shiru yana zurfafa cikin kogin tunani,
Abu na farko da ya faɗo mashi a rai shi ne shin yanzu zai miƙa wuya ne ga sarki
Lamsarul-Azlam bayan cewa bai san halin da iyalanshi ke ciki ba?
Baka da wata mafita da huce ka yaƙi waɗannan dakaru domin ka isa inda iyalanka suke, ina
amfanin ma miƙa wuya bayan baka da tabbacin ya lafiyarsu take.
Lokacin da Ukaiza ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya kame bakinshi ya yi tsit! Ba tare da
ya amsa tambayoyi da shugaban ƙafa ya yi masa ba,
Al'amarin da ya fusata sarkin ƙofar kenan ya dakawa yaransa tsawa dake nuna ba su umarnin
su afkawa mashi,
Cikin hanzari suka zare makamansu suna ihu da kururuwa mai firgitarwa su ka yi ɗauki kanshi
kafin da isa gare shi sai suka cika da matuƙar mamaki, abin da basu mamaki shi ne yadda
tsananin yawan su bai firgita baƙon ba tabbas wani sirri game da shi domin Ruwa baya tsami
banza! Kuma idan ka ji makaho ya ce ayi wasan jifa to yaji ya taka dutse! Lokacin da ya rage saura taku uku tsakaninsu sai Ukaiza ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a
damtsenshi ya yi wata irin katan-tanwa a ƙasan dakarun take ya sare mutum goma ƙafafu suka
zube ƙasa guragu suna masu kurma wawan ihu,
Sannan ya afkawa sauran aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni ban tsoro
daban al'ajabi.
Mu haɗu a TAFARKIN TSIRA littafi na 7 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaki
08137237071
TAFARKIN TSIRA 7
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan yaƙi
Wthapp Number
08137237071
ELEGANT ONLINE WRITER'S
Littafan Marubucin
Kogon Annoba
Sarautar Mutuwa
Kangin Bauta
Jaruman Duniya
Takobin Ɗaukaka
Ƙarshen Zalunci
Fataucin Bayi
Sarkin Sadaukai
Goga Sha Fama
Tafarkin Tsira
Gasar Sarauta
Kundin Al'ajabi
BABI NA SHA UKU
Sa'adda muridi Zabratul-ukub ya samu nasarar ɗaukar wannan kyakkyawar dudurwar da ta
fafata yaƙi da dakarun sarki Lamsarul-Azlam, kuma ya ɓace ɓat! Cikin alƙalumman sihiri, yana
cikin wannan hali ne sai ya ji jikin shi ya ɗauki zafi, ba shiri ya bayyana ba a tsakiyar wani
makeken fili mai ɗauke da rairayi, yana sauka sai ya duba tafin hannunshi aikuwa sai ya gan shi
wayam babu wannan kyakkyawar dudurwa, cikin hanzari ya ɗaga kanshi izuwa sararin
samaniya nan take ya yi arba da wani kyakkyawan aljani ɗauke wannan kyakkyawar dudurwa
wato gimbiya NUWAIRAT yana tsala gudu a sararin samaniya, kafin ƙiftawar idanu ya ɓace ɓat
tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Cikin matuƙar takaici Zabratul-ukub ya ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu, a lokaci guda kuma
ya turɓune fuska, sannan ya sake ɓacewa a karo na biyu bai bayyana a ko ina ba sai a tsakiyar
fadar sarki Lamsarul-Azlam ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa kanshi a sunkuye,
Lamsarul-Azlam ya daka ma shi tsawa wacce ta sanya hantar cikin kowa dake fadar ta kaɗa
saboda matuƙar tsoro, a lokaci guda ya turɓune fuska tamkar an aiko ma shi da WASIƘAR
MUTUWA cikin kakkausar murya ya ce "Ya kai Zabratul-ukub shin wane irin rashin hankali ya
sanya har ka yi sake gimbiya Nuwairat ta suɓuce daga hannunka ? Tabbas ka aikata babban
kuskure a gare ni, na rantse da girman halarar tsafina sai na gana maka nau'ikan ANNOBA
ƊARI wacce ba a taɓa yiwa wani mahaluki ita ba.
Ko da gama faɗin hakan sai ya nuna Zabratul-ukub da ɗan yatsanshi na hagu take nan take
waɗansu irin sarƙoƙin wuta suka ɗaure shi hannu da ƙafa, nan fa ya shiga yin kururuwa da
neman agaji saboda yadda sarƙoƙin ƙe ƙona sassan jikinshi,
Al'amarin da ya firgita Al'ummar fadar kenan kuma cikin ya ɗuru ruwa, waɗansu har suna sakin
fitsari a wando,
Sa'adda Zabratul-ukub ya ga cewa a koda yaushe zai iya rasa rayuwarshi sai ya shiga yin
magiya yana roƙon sarki akan ya cewa idan har ya ƙyale shi zai kirawo dukkan jinsinsu na
muridai su je su yaƙi gaba ɗaya jama'ar birnin MADINATUL-AFNAN ko da kiyashi ba za su bar
shi a raye ba, Ko da jin wannan magajiya sai sai sarki ya yi nuni gare shi a karo na biyu take sarƙoƙin suka
ɓace ɓat! Daga jikinshi tamkar ba su taɓa wanzuwa ba,
Sannan ya dube shi ya ce "Ka sani cewa kwanaki uku kacal na ɗaukar maka idan har aka samu
matsala kafi kowa sanin abin da zai biyo baya,"
Cikin ladabi da ƙasƙantar da kai Zabratul-ukub ya ce muryarshi na rawa "Godi-ya na-ke ya ma-i
du-ni-ya",
Yana gama faɗin hakan ya shafi shimfiɗar fadar ya sake ɓacewa a karo uku tamkar bai taɓa
wanzuwa ba.
A sannanne jama'a suka dawo cikin hayyacin su, shiru ne ya wanzu a fadar tamkar an yi
ruwa an ɗauke, daga can sai sarki ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar buɗar baki ya dubi
sarkin yaƙi ya ce "Ya kai dirkar birnina ka yi sani cewa ina so ka fara shirye-shiryen fita yaƙi ina
so alfijir ɗin kwana biyu masu zuwa ya keto a lokacin da muke tsaye a Ƙofar birnin
MADINATUL-AFNAN, domin wannan yaƙi da zamu fita ya bambanta da sauran yaƙoƙi, domin
dole ka haɗa mana rundunar ƘARE DANGI,
Ko da sarkin yaƙi Huzmal ya ji wannan batu sai ya risina ya ce "An gama ya shugabana yaba
gama faɗin hakan ya miƙe tsaye tsam! Daga kan kujerarshi ya durfafi ƙofar fita daga fadar,
Kallo ɗaya zaka yiwa Sarkin yaƙi ka fahimci cewa ya cika gwarzon Jiya, domin ya tara ƙwanji,
kwarji da Haruna, komai dakewar zuciyar jarumi idan ya yi arba da shi sai hantar cikinshi ta
kaɗai,
Ko da ficewar shi sai sarki Lamsarul-Azlam ya tafi ya shiga izuwa gidan sarauta dakaru na take
masa baya, nan take fadar ta watse kowa ya kama gabanshi tamkar wata halitta bata taɓa
wanzuwa ba.
***
Lokacin da Rusayyat ta ci gaba da gudanar da bincike a turakar maigidanta sadauki
fitinatul-Amir domin ta gano wannan garin magani na sihiri don tseratar da rayuwar yaro Usaiba
mai hatimin takobi, lokacin da ta ji alamun takun sawaye na tunkaro turakar, sai kawai ta miƙe
tsaye zumbur! Ta ruga izuwa bakin ƙofar shigowa ta sanya idanuwanta a tsakiyar wata 'yar
siririyar ƙofa dake jikin ƙofar, nan take ta hango cewa ashe wata kuyanga ce ɗauke da wani
ruwa a cikin kasko, nan take ta cika da matuƙar farin ciki, jim kaɗan ƙofar ta buɗe, Rusayyat ta
dakawa kuyangar tsawa cikin matuƙar fushi ta dube ta ta ce "Ya ke Hulaifa shin mene ne ya
kawo ki nan ? Bayan cewa an kawo dukkan abin da na buƙata ?
Ko da jin wannan tambaya sai jikin Hulaifa ya kama kyarma ta buɗi baki cikin ladabi ta ce "Ki
gafarce ni ya shugabata na manta ne ba a kawo ruwan ɗauraye hannu ba ne, shi ne yanzu na
kawo",
"Bama buƙatar komai yanzu".
Rusayyat ta bata amsa.
Hulaifa ta risina sannan ta juya ta fice daga turakar, dakarun dake tsaron ƙofar suka sake
kulleta,
Kawai sai Rusayyat ta koma izuwa cikin turakar ta cigaba da binciken cikin hanzari, cikin sa'a ta
samu nasarar gano garin maganin, cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ta sanya shi a cikin
aljihun rigarta na hagu, sannan ta sanya hannunta a aljihun na dama ta ɗauko hodar banju ta
taka da ƙafafuwanta izuwa wajen da teburin abinci yake ta buɗe kofin dake ɗauke da taceccen
ruwan inibi ta zuba a banjun a ciki, sannan ta mayar ta rufe ta zauna a ɗaya daga cikin
ƙayatattun kujerun dake wajen.
Jim kaɗan da aiwatar da hakan sai ƙofar da ke ɓangaren yamma a turakar ta buɗe sai
Fitinatul-Amir ya bayyana sanye cikin tufafin alfarma irin na hamshaƙan