Showing 3001 words to 6000 words out of 28793 words

Chapter 2 - TAFARKIN TSIRA Book Complete by Sarkin Marubutan Yaki .pdf

dubi waziri ya ce "Ya amintacen waziri ga Sarkin
Musulimci Nu'umanu ibnu Abbas shin wane mummunan al'amari ne ke shirin faruwa gare ni?
Ina so ka gaggauta sanar da ni domin samun mafita".
Ya ƙare furucin na shi hankalin shi a tashe.
Ko da jin wannan batu sai waziri ya bushe da dariyar mugunta sai da ya yi dariyar ta ishe
shi sannan ya tsuke bakin shi, kawai sai ya tunatar Idanuwanshi ya shiga karanta ɗalasiman
tsafi, a lokaci guda ya tsuke bakinshi tare da yin nuni da hannunshi na hagu ga bangon turakar.
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa Sarki Rakibu kai kenan kuma ya ba shi mamaki bisa jin
waziri ya na karanta ɗalasiman tsafi a matsayin shi na musulmi wanda aikata fita daga addinin
Musulunci ne baki ɗaya.
Ko da waziri ya ɗauke hannun shi daga bangon sai taswirar ɗakin taro ya bayyana, Nan
take Rakibu ya ga dukkan tattaunawar da sarki Nu'umanu ya yi da 'yan majalissar shi tun daga
farko har ƙarshe, Sannan waziri ya sake nuna bangon a karo na biyu taswirar ta ɗauke tamkar
bai taɓa wanzuwa ba. Sa'adda Sarki Rakibu ya ga Wannan taswirar sai hankalinshi ya dugunzuma ainun fiye da ko
yaushe.
Waziri Yazid ya yi gyaran murya a karo na biyu ya ce " Ya kai Rakibu ka yi sani cewa
wannan tattaunawar an yi ta ne domin a juyar da al'ada da addinin ku da ku ka gada tun iyaye
da kakanni, kuma ina mai tabbatar maka da cewa dole a kwabza yaƙi tsakanin mu da kai,
Sanin kanka ne cewa ko ba a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza, ko na ce SARKIN YAWA
yafi SARKIN ƘARFI, ma'ana dakarun mu ba sa'anni ba ne da na ka,
Na sani cewa a halin yanzu hankali ya shiga tararrabi da ɗimauta amma idan har zaka haɗa kai
da ni za mu samu nasarar murƙushe Sarki Nu'umanu daga kan KARAGAR MULKI,
Da yake masu iya magana na cewa "Da ɗangari akan ci gari" to mu haɗa ƙarfi da ƙarfe da
sarkin yaƙi lauzar tare da waɗansu fitattun MAYAƘA na birnin Baitul-Hazwar,
Kawai za mu afkawa birnin ne da rana tsaka domin mu ci su da yaƙi da zarar mun samu nasara
zan ɗare bisa KARAGAR MULKI ta sarki Nu'umanu, sarkin yaƙi lauzar zai cigaba da riƙe
muƙamin waziri, kai da jama'ar ka kuma za ku cigaba da tafiyar al'ada da addinin ku batare da
wata matsala ba". Ko da jin wannan dogon bayani bakin waziri sai hankalin sarki Rakibu ya ɗugunzuma ainun
fiye da Kowa ne lokaci ya ji tamkar ya kurma ihu cikin ƙankanin lokaci zufa ta fara tsattsafo
mashi,
Ya shiga juya al'amarin a cikin ran shi ya ƙulla wannan ya warware wancan.
Abu na farko da ya dugunzuma hankalin shi ne ya tabbatar da cewa idan ya fafata yaƙi da
sarki Nu'umanu ba zai taɓa samun nasara ba domin idanu ba nufi ba ne amma sun kima"
Abu na biyu shi ne yanzu zai karɓi addinin Musulunci ne wanda tabbas shi ne addinin gaskiya
da ke bisa TAFARKIN TSIRA, haƙiƙa yin hakan zai tserar da sarki Nu'umanu daga mugun
tanadi da ɓakin makircin waziri Yazid,
Shin yanzu ta ya ya zan ƙyale addini na da na gada tun iyaye da kakanni tabbas wannan
babban abin kunya ne a gare ni.

Haka dai Rakibu ya dinga nazari akan al'amuran har daga ƙarshe ya yanke shawarar ya yi
biyayya ga waziri Yazid domin ba zai taɓa barin turbar shi ta gado ba wacce ya tabbatar da
cewa bakomai ba ce face TURBAR AJALI.
Rakibu ya tattara hankalin shi ga waziri ya dube shi ya ce "Ya kai Yazid haƙiƙa tabbas na
amince da shawarar ka yanzu batare da ɓata lokaci ba a cikin dare kafin ketowar alfijir zai
kammala haɗa rundunar MAYAƘA na".
Da jin wannan batu sai waziri Yazid ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa domin
yana ganin cewa yana kusa da cika burin shi na ɗarewa bisa KARAGAR MULKI ta birnin
Zainul-Ansar.

Gudu suke yi tamkar diga-digansu za su karairaye saboda matsanancin gudun tsira da
rayukansu.
Ƙananan yara ne mace da namiji da shekarun su ba zasu haura goma da haihuwa ba,
Suna gudun ne a cikin wani ƙasaitaccen daji ma'abocin dogayen bishiyu, duwatsu da ƙoramu,
Suna cikin gudun ne kwatsam bazato babu tsammani sai suka ga wani murgujejen zaki ya yi
fitar burgu daga duhuwar bishiyun dajin ya bayyana a gare su yana gurnani da ɗaga
ƙafafuwanshi sama, kawai sai suka ja suka tsaya cak! tamkar waɗansu gumaka dukkanin su
sun sallama cewa a halin yanzu rayuwar ta zo ƙarshe, Lokacin da ya rage saura taku uku zakin ya cimma su kwatsam sai kawai suka ga ya yi sama
tamkar an janye shi da ƙugiya sannan daga bisani ya faɗo ƙasa tim a matuƙar galabaice, kafin
ya yi yunƙurin miƙe tsaye ta dunƙuke hannayen ta biyu ta gabza ma shi naushi a wuya take ya
karye jikake ruƙus! Ƙas ya faɗi ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba, Cike da matuƙar mamaki suka ƙura mata idanu suna al'ajabin irin sadaukantakar ta da kuma
ƙoƙarin ceto rayuwar su da ta yi,
Ita kuma ta na mamaki bisa ganin su a cikin wannan mugun daji mai cike da haɗari a matsayin
su na yara ƙanana da ya kamata ace suna zaune a gaban mahaifansu.
Suna cikin wannan hali ne rundunar sarki Lamsarul-Azlam ta tunkaro wajen a sukwane bisa
dawakai,
Sa'adda yaran biyu suka arba da su nan take suka fara zubar da hawaye,
Al'amarin da ya sanya wacce ta ceci rayuwar ta su ta fahimci cewa dakarun ne suke yunƙurin
cutar da su saboda haka ne suka shigo cikin dajin yin gudun tsira,
Ko da fahimtar hakan sai kawai ta tuntse idanuwnta ta karanta waɗansu ɗalasiman tsafi, tana
gama rufe bakinta take ta ɓace ɓat tare da yaron tamkar ba su taɓa wanzu ba.
Cikin matuƙar takaici da baƙin ciki shugaba Hukaiza da sauran dakarun suka ja linzamin
dawakan su suka tsaya cak,
Kawai sai Hukaiza ya ɗauko madubin tsafin shi ya shafe shi da hannunshi na hagu da nufin
gudanar da bincike amma sai kawai ya ji an ja shi sama daga kan dokinshi an fyaɗa shi da
ƙasa,
Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankulan dakarun kenan domin tun da suke da
shugaban na su hakan bai taɓa faruwa ba.

BABI NA HUƊU

Tun sa'adda sarki Nu'umanu ya baro ɗakin tattaunawa da 'yan majalissar shi sai ya kasa
zaune ya kasa tsaye ya wanzu yana kai komo a cikin turakarshi ya saƙa wannan ya kunce
wannan,
Tsawon daƙiƙa hamsin yana nazarin shawarar 'yan majalissar a cikin ran shi,
Inda daga bisani dai ya yanke shawarar ya yi amfani da maganar magatakarda na aikawa sarki
Rakibu da WASIKAR gayyata zuwa addinin Musulunci.
Ko da gama yanke shawarar sai kawai ya fice daga turakar domin zuwa masallaci
Waɗansu ZARATAN MAYAƘA suka mara mashi baya, duk inda ya huce a gidan sarautar sai dai
kaga dakaru, hadimai, barori, kuyangi da bayi na zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa a haka har
ya iso zuwa masallacin dake wajen gidan sarauta.
Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Nu'umanu na birnin Zainul-Ansar.
Al'amarin waziri Yazid kuwa, bayan sarki Rakibu ya aminta da shawarar da ya zo masa da ita
kuma ya ɓace cikin alƙalumman sihiri,
Domin zuwa birnin Zainul-Ansar bai bayyana a ko ina ba sai a cikin sai a cikin turakarshi,
Turakar ta ƙawatu ainun da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya har da abin
da idanu ba su taɓa gani ba,
Batare wani jinkiri ba ya tura wata kuyangar shi izuwa gidan Sarkin yaƙi lauzar da wasiƙa mai
ɗauke da dukkan tattaunawar da suka yi da sarki Rakibu da kuma shirye-shiryen da zasu
gudanar,
Sarkin yaƙi ya yi matuƙar farin ciki da samun wannan sako,
Don haka cikin hanzari ya shiga tara rundunar MAYAƘA su kimanin dubu goma cikin sirri suka
nufi daga ɓoyayyar hanyar suka fice daga birnin domin saduwa da inda dakarun sarki Rakibu
suke batare da wani ya gane su ba.




TAFARKIN TSIRA
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
SARKIN MARUBUTAN YAƘI
Wthapp Number
08137237071




BABI NA BIYR

Boka kaddad ya dubi aljani Lattul-kifas ya ce da shi " Ya kai Lattul-kifas ka yi sani cewa
bakomai ne ya sanya na kira ko nan ba sai domin ina so ka tafi gabas maso arewacin duniya ka
ɗauko Mani wani yaro mai ɗauke da hatimin takobin Saiful-zayyad a gadon bayanshi".
Ko da jin wannan batu sai Lattul-kifas ya buɗe baki cikin ladabi cikin wata irin kakkausar
murya mai kama da saukar aradu ya ce "An gama ya shugabana wannan aiki ai cire silin gashi

daga cikin tandun mai ya fi shi wahala a waje na, amma kafin haka ya shugabana ina da
tambaya shin mene ne ya sanya ake kiran takobin da suna Saiful-zayyad?.
Boka kaddad ya murtuke fuska ya ce "Ai Wannan tambaya ta ka bayani mai zurfi wanda ko
da zamu kwana ɗari ina baka ba zai yiwu mu zo ƙarshen shi ba,
Amma a jawabi a takaice anan shi ne
Sadauki zayyad wani gawutaccen mayaƙi ne da a ka yi wanda bokaye da masu hasashe suka
tabbatar da cewa a wannan ƘARSHEN ƘARNI babu gwarzon mayaƙi tamkar shi tsakanin
duniyar MUTUM DA ALJAN a wannan lokaci ya zame wa sarakunan duniya da bokaye
ANNOBA ƊARI, ko da sunan shi aka ambata sai ka ga boka ya ɗimauce saboda matuƙar tsoro, Asalin Sadauki zayyad yakasance mutum birnin biladul-tukrur dake yammacin duniya
Kuma yakasance ma'abocin wani addini da ake yiwa lakabi da musulunci.
Kawai dai yanzu abin da nake so ka sani shi ne mallako wannan yaro shi ne zai kawo
kwanciyar hankali a wannan duniya ta bil'adama, sabanin hakan kuwa na iya haddasa ɓarkewar
ANNOBA ƊARI.
Sa'adda Aljani Lattul-kifas ya ji wannan batu daga mai gidan shi sai ya risina ya ce "An
gama ya shugabana",
Yana gama faɗin hakan ya juya ya kaɗa manyan FukaFukanshi ya tashi zuwa sararin samaniya
ya ɓace ɓat a cikin gijimare.
Bakomai ne ya sanya boka Kaddad ya ke so a farauto mashi yaro mai hatimin takobin
Saiful-zayyad ba, sai domin bisa binciken da ya gudanar halarar tsafin shi ta tabbatar nashi da
cewa matsawar yana so yafi kowa ne bil'adama ƙarfin damtse da sihirin tsafi sai ya yanka yaro
mai hatimin takobin ya shanye jinin shi, Bisa dalilin hakan ne ya umarci aljani Lattul-kifas ya ɗauko yaron.

BABI NA SHIDA

Al'amarin wannan baƙuwar jaruma kuwa tun sa'adda da ta ɓace cikin alƙalumman sihiri tare
da ƙananan yara biyu bayan ta ceci rayukan su daga hannun dakarun Sarki Lamsarul-Azlam,
Ba su bayyana a ko ina ba sai a cikin wata ƙasaitacciyar turaka da aka ƙawata ta da nau'ikan
kayan alatu daban-daban, komai ƙasaitar BASARAKE ko attajiri idan ya tsinci kanshi a cikin
wannan turaka dole ya raina kanshi ya tabbatar da cewa GABA DA GABANTA aljani ya taka
wuta. Masana tarihin duniya da masu hasashe na wannan SABON ƘARNI sun tabbatar da cewa a
wannan zamani babu wani attajiri fiye da mai mallakin wannan gida, wato shugaban 'yan fashin
duniya Sadauki Fitinatul-Amir,
An ambace shi da Fitinatul-Amir ne saboda ya zamowa sarakunan duniya ƙadangaren bakin
tulu kuma ciwon idanu,
Amma asalin sunan shi shi ne Huraisu ibn Dazwan.
Huraisu yakasance MASHAHURIN SADAUKI mai tarwatsa DANDAZON MAYAƘA a filin
fama, Gawutaccen matsafi ne kuma fitaccen ɗan fashi da makami da ya zamowa duniya
ANNOBA ƊARI,
Bincike ya tabbatar da cewa a kaf sarakunan bil'adama babu attajiri tamkar shi haɗe da ilimin
tsafi,

Wanda yake kunnen doki da su a fagen sihiri su ne Sarkin dake mulkin bakaken aljanu sarki
Sulusainul-layal tare da sarki Lamsarul-Azlam na birnin Darul-Ashmar.
Duk sarkin da Sarkin 'yan fashin duniya ya sanya a gaba sai ya ga bayan shi komai irin
matuƙar yawan rundunar mayaƙan shi da dukiyar shi,
Bisa wannan dalili yasanya sarakunan duniya ke aika mashi da harajin mai tarin yawa a kowace
shekara domin ganin sun tsira da rayukansu da biranensu.
Ta wannan hanya ne Fitinatul-Amir ya tara dukiya mai yawan da babu kamar ta,
Sai dai duk tarin dukiyar shi da ya tara ta tashi a banza domin ba shi da magaji da zai zamo
halifan shi bayan rasuwar shi,
Duk sa'adda ya ga Wannan al'amari a cikin alƙalumman sihirin shi sai ya cika da matuƙar baƙin
ciki maral-musaltuwa,
Bisa binciken da ya gudanar bisa halarar tsafin shi ya gano cewa har abada ba zai taɓa samun
haihuwa ba face ya hallaka wani yaro mai hatimin takobin Saiful-zayyad a gadon bayanshi,
Domin shi ne zai kawo ƘARSHEN ZALUNCI shi, bisa wannan dalili ne ya sanya dare da rana
Fitinatul-Amir ba shi da wani aiki face farautar yaro mai hatimin takobin,
Babban abin da ya fi dugunzuma hankalin shi shi ne, Duk sa'adda ya tsananta bincike domin ya
gano inda yaron yake zaune a duniya sai madubin tsafin na shi ya yi bindiga ya tarwatse,
Amma duk da faruwar hakan bai sanya gwiwoyin shi sun yi sanyi ba wajen farautar yaron domin
ya cire kan shi barcin dare kawai saboda binciken yaron a cikin alƙalumman sihiri.

***
Bayan Jarumar ta sauke waɗannan yara biyu a cikin ƙasaitacciyar turakar sai ta umarci
waɗansu irin tsala-tsalan kyawawan kuyangi suka suka ɗauki yaran suka shiga da su izuwa
kewaye suka yi masu wanka suka sanya masu tufafi masu tsadar gaske irin na hamshaƙan
sarakai sannan suka dawo da su izuwa cikin turakar, A sannanne baƙuwar jarumar ta shiga ba su abinci da abin sha gami da nau'ikan kayan
marmari suna ci sai da suka ƙoshi suka samu nutsuwa.
"Ya ku waɗannan yara ina so ku sanar da ku labarin rayuwar ku kuma mene ne ya sanya
waɗannan dakarun ke farautar ku domin su hallaka ku?.
Ko da jin wannan tambaya sai sai yaran suka fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya
daban tausayi,
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa Rusayyat mamaki kenan kuma ya sanya ta kamu da matuƙar
tausayin su ta janyo su ta rungume a kirjinta ta shiga rarrashin su har da suka yi shiru sannan ta
janye jikinta daga na su,
A karo na farko Namijin wanda ake kira da suna Usaiba ya ce " Ya ke wannan jaruma
ma'abociyar tausayi da jin ƙai ki yi sani cewa bakomai ne ya sanya mu gudun tsira da
rayukanmu a cikin wannan daji ba sai domin tsira daga sharrin dakarun sarki Lamsarul-Azlam
wanda ya rabu da mahaifin mu da muka fi so fiye da komai a duniya, A lokacin da muka baro birnin mu mun kasance ayarin 'yan gudun hijira fiye da mutum dubu,
Azaton mu mun samu kuɓuta daga TSANANI DA UKUBA ashe dakarun sarki Lamsarul-Azlam
suna biye da sahun mu, sai da suka tabbatar mun saki jiki a cikin daji sannan suka afka mana
suka hallaka dukkan ayarin mu har ta ƙananan yara da mata ba su ƙyale ba,
A halin yanzu mu kaɗai ne mu ka rage daga cikin al'ummar birnin mu mu kan mu na domin ke
ba da tuni mun daɗe da baƙuntar barzahu,

A halin yanzu rayuwar mu bata da wani amfani, domin mun rasa duk wani farin cikin rayuwar
mu".
Lokacin da yaro usaiba yazo nan azancen shi sai suka sake fashewa da matsanancin kuka
mai tsuma zuciya a karo na biyu,
Rusayyat bata san sa'adda hawaye suka kwaranyo daga idanuwanta ba ta sake ruguntsume su
Usaiba a karo na biyu ba, tsawon daƙiƙa ashirin suna cikin wannan hali sai daga bisani ne ta
yanye jikinta daga na su suka fuskanci juna a lokacin da Idanuwanta suka ciki da ƙwalla kuma
suka kaɗai suka yi jajur ta dafa kafaɗunsu sannan ta buɗi baki cikin murya mai taushi da ban
tausayi ta ce "Ya ku waɗannan yara ku yi sani cewa wannan na ku ya sanya ni na kamu da
soyayyar ku kuma ya tuna mani da nawa labarin da nake da tabbacin ya huce na ku ban
tausayi da tsantsar zalunci,
Ina so ku zauna tare da ni a wannan gida zan baku dukkan wata kulawa da uwa ke bawa
'ya'yan ta,
Ku shiga duk inda kuke so a wannan gida ku ɗauka tamkar a masarautar ku ne,
Zan baku horon yaƙi har izuwa lokacin da za ku iya ɗaukar fansa akan sarki Lamsarul-Azlam,
Ina so ku riƙe ni a matsayin tamkar mahaifiyar ku ni kuma zan riƙe ku tamkar 'ya'yan da na
haifa".
Ko da Usaiba da 'yar uwar shi suka ji wannan batu daga bakin Rusayyat sai suka cika da
matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
Usaiba ya yi gyaran murya ya ce "Ya ummina shin ko mene dalilin da sanya kika ce labarin
rayuwar ki ya fi namu ban tausayi?.
Da jin wannan tambaya sai Rusayyat ta cika da matuƙar farin ciki bisa jin usaiba ya
ambace ta da suna ummina, cikin matuƙar farin ciki ta dube shi ta ce "Ya farin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login