Showing 21001 words to 24000 words out of 30696 words
Chapter 8 - GOGA SHA FAMA Book by Mansur Usman Sufi .pdf
da alamar
SADAUKANTAKA,
Kuma fuskar ta rufe take da rawani Nan fa daya wa daga cikin jihar jama'a suka kama yi mata
dariya wasu kuma tausayin ta ne ya kamu bisa ganin cewa ita da bata kasance Basadaukiya ba
amma ta shiga gasar mai haɗarin gaske da zata iya rasa rayuwar ta.
Bayan dukkanin jaruman gasa sun zauna a bisa kujerun da aka tanadar musu,
Sai sarkin yaƙi abu-Damraz ya cigaba dacewa
"Kafin mu kai ga shiga cikin shagalin yana dakyau dukkan jarumai su san da wadannan dokoki
na gasar jarumtaka,
Doka farko ita ce Ba'a yarda ayi amfani da sihirin tsafi ba
Wajen samun nasara, koda mutum ya aikata acikin alƙalan gasa akwai bokaye dasu gane cewa
yayi tsafin,
Dukkan jaruman da aka haɗa ku faɗa dashi babu damar a canza.
Kuma kamar yadda aka sani cewa dukkanin jaruman zasu dunga gwagwarmaya a tsakanin su
har sai an fitar da gwarzo wanda shi ne babu wanda yakasance a saman shi.
Dukkan wanda yayi kisa za'a haramta masa shiga gasa na tsawon shekaru goma tare da tara
mai tsauri,
Idan kuwa ya lashe gasar to za'a bawa yan uwan wanda ya kashe dukkan kyautuka da za'a ba
shi,
Lokacin da sarkin yaƙi abu-Damraz yazo nan a jawabin sa sai ya koma kan kujerar sa a ya
zauna,
Kawai sai wani garjejen kato mai sanye da jajayen tufafi masu yalwa ma'abocin tarin ƙasumba
da gemu baƙaƙe siɗik
Ya miƙe daga cikin alƙalan gasar ya buɗi baki cikin kakkausar murya yace
"Yanzu dukkan jaruman gasa zasu hallara a Filin fafatawa dake tsakiya bayan ambaci sunayen
su,
Da farko akwai mai girma gimbiya haya'ul-nur yar mai girma shaibat
Tare da gimbiya Rumaisat yar sarki shuraih
Sannan sadaukai Hibairu ibn Shabbaru
Tare da jaruma Amirat bintu Hamza ta birnin madinatul-barnawiy
Sadauki lazwas ibn shaslam na birnin Laufas
Da Jarumi nazwar ibn gaurus na birnin shasrad.
Koda kammala karanto sunayen sai filin gasar ya sake kaurewa da shewa da ihu fiye da ko
yaushe,
Ɗaya bayan ɗaya jaruman suka dunga tashi suna isa zuwa filin,
Jim kaɗan sun kammala hallara.
Nan take kowa ya shiga kallon abokin gwamin sa kuma suna masu gazaye juna,
Dai dai lokacin da waɗansu dakaru ke buga waɗansu tambura da ganguna dake ziga dukkan
mazaje da tsuma zukatan su a filin fama,
A bangaren gimbiya haya'ul-nur tsananin takaici ya turnuƙe zuciyar ta da a karon farko na gasar
ba'a haɗa ta da hubairu sarkin sadaukai ba,
Ita kuwa gimbiya Rumaisat tsananin farin ciki ne ya kamata bisa ganin cewa ba'a haɗa saurayin
da ta kamu da kaunar sa da abokiyar gabar ta gimbiya haya'ul-nur ba.
Daga can sai wani garjejen kato na daban ya ɗauki wani zunguren ƙaho a jikin sa ya kafa a
bakinsa ya busa shi da ƙarfi,
Tamkar haɗin baki a lokaci guda jaruman kowanne bangare suka yi ɗauki kan abokanan
gwamin su,
Suna masu ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAKA a filin daga,
In da a ce mutum yana tsaye a wannan waje zai ga yadda jaruman takwas suka yi ɗauki kan
junan su dole abin ya firgita shi domin yasan ko ba'a ce komai ba haƙiƙa za'ayi KARON
MAZA,Kuma za'a sha ɗauki ba daɗi.
Yayin da aka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini
muni,tashin hankali da ban tsoro,
Wohoho haƙiƙa idan kaji ƙidan farauta sai GWARAZAN JIYA ke amsa gayyata,
Idan garken zakuna suna fito fagen artabu babu masu tarar su ayi gaba da gaba face manyan
giwaye,
Nan fa ɓangarorin suka shiga kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da
bajinta tagaban kwatance tamkar jikkunan su basu kasance na jini da tsoka ba
Abangaren mahalarta taron gasa kuwa, lokacin da jaruma Nihla, Sunaila,saurayi Hizmal,
sarauniya Abidatul-auliya,Nuwairat da yaro Humair makaho suka ga an kacame da azababban
yaƙi tsakanin sarkin sadaukai Hibairu tare da jaruma Amirat bintu Hamza sai hankalin su ya
dugunzuma ainun,
Duk da cewa a zahiri sun san cewa HUBAIRU ya nunka Amirat fiye da arba'in a
SADAUKANTAKA da ƙirar jarumtaka,
Amma bisa ganin yadda Amirat ɗin ke yakar Hibairu cikin zafin nama juriya na ɓacin tsiya
tamkar wata shaiɗaniya sai hankulansu suka dugunzuma ainun,
Domin dai matsawar Hibairu ya faɗi wannan gasa,
Tamkar rushewar cikar burikan su na duniya ne baki ɗaya,
Abangaren sarki Baddadul-ulƙas kuwa zuciyarsa babu yabo babu fallasa,
Domin yana ganin cewa tamkar Hibairu ya samu nasara ne akan jaruma Amirat,
Sai dai inda kizo ke saƙar shi ne don HUBAIRU ya samu nasara akan Amirat to lalle bane yakai
ga nasara akan sauran jaruman,
Wani ɓangare a zuciyar kuma a zuciyar sa kuma yace dashi kada ka manta cewa nasara da
Sa'a a jinin Hibairu take haƙiƙa sai ya samu nasara a wannan gasa,
Domin a halin yanzu babu gwarzon mayaƙi kamar shi a faɗin duniya,
Koda sarki Baddadul-ulƙas yazo nan a tunanin sa sai ya bushe da dariyar farin ciki,
Al'amarin da ya sanya sarki shuraih dake zaune daf dashi ya murtuke fuska tamkar an aiko
masa da SAƘON MUTUWA,
ya dubi Baddadul-ulƙas da wani irin kallo mai ɗauke da alamar tamabaya,
A bangaren mai girma shaibat kuwa ya zuba idanu ya kallon yadda gasar ke gudana,
Zuciyar sa na dukan uku-uku,
Domin yana ganin cewa haƙiƙa koda yar sa gimbiya haya'ul-nur ta samu nasara gimbiya
Rumaisat bai zama tilas ta samu nasara akan Hibairu ɗan Barde Shabbaru ba,
Abangaren teburin alƙalan gasa, al'marin sarkin yaƙi abu-Damraz kuwa ana fara wannan
fafatawa tsananin jaruman sai hankalin sa ya dugunzuma ainun ya kasa samun nutsuwa, domin
a halin yanzu yana cikin tsaka mai wuya,
Idan sarkin sadaukai Hibairu ya cinye wannan gasa,
Gimbiya haya'ul-nur ta faɗi, dai dai yake da ya rasa rayuwar sa,
A Ɓangaren dabbobin dajin da suka yi Hibairu rakiya izuwa Filin gasa,
Sa'adda suka ga yadda shugaban su Hibairu ya kacame da azababban yaƙi da jaruma Amirat
sai suka dunga yin gurnani suna hargagi,
Dake nuna fatan nasara ga sarkin sadaukai Hibairu,
Nan fa mamaki Yakamata jama'ar dake filin gasar bisa ganin yadda dabbobin ke nuna alamun
fatan alkairi ga Hibairu,
Abin tambaya anan shine mene ne alaƙar HUBAIRU da waɗannan miyagun dabbobi,
Me ne ne alaƙar dake tsakanin HUBAIRU da Barde Shabbaru tabbas a yadda alamu suka nuna
lokacin da aka ambaci sunayen jaruman ya tabbatar dace wa Hibairu ɗan Barde Shabbaru.
Tabbas kyan ɗa ya gaji uban sa,. Nanfa jama'a suka dunga yiwa gwanayen su jinjina,
Amma sai ya zamana fiye da rabin jama'a hubairu suke ɗagawa hannu suna yi masa kirari,
masu wake nayi masu shewa nayi.
Nan fa zuciyar sarki shaibat ta kama tafarfasa tamkar zasu ƙone,
Bisa ganin yadda jama'a ke nuna goyon baya ga Hibairu,
A tsakiyar filin gasar kuwa jaruman sun wanzu suna kaiwa junan su sara da suka cikin ɓakin
zafin nama juriya da jarumtaka irin ta JARUMAN DUNIYA,
Duk wanda ya gaɓzawa ɗan uwan sa nashi sai kaga shi ma ya mayar da martani Cikin zafin
nama tamkar suna casar hatsi.
Kai kace wata na'ura ce ke sarrafa su ba da jini da tsoka ke gudana a jikkunan su ba.
Lokacin da zaratan Jaruman gasar GOGA SHA FAMA suka wanzu suna kaiwa Juna naushi da
bugu cikin matukar zafin nama juriya da jarumtaka ta gaban kwatance,
Sai aka shafe tsawon daƙiƙa arba'in ana wannan fafatawa babu sassauci,
Nan fa wani abun mamaki ya fara wakana,
Domin bangarorin jaruman ana samu ragas ma'ana karfi yazo ɗaya,
Duk sa'adda ɗayan su ya gaɓzawa abokin faɗa sa naushi sai kaga ya shanye dukan,
Shi ma ya taƙarkare ya mayar da martani Cikin gwanin ta da zafin nama.
Nan fa jama'a suka shiga yin shewa da tafi bisa ganin cewa har yanzu babu alamun nasara ga
dukkan bangarorin jaruman,
Wannan fa shine abinda masu iya magana ke cewa kyan faɗa akwana ana yi.
A ɓangaren Jarumi Hibairu da jaruma Amirat kuwa sun wanzu suna bawa hammata iska,
Suna kai wa juna hari ta ƙasa da sama,
Wasu lokutan har daka tsalle sama suna kaiwa juna harin.
Lokacin da Hibairu sarkin sadaukai yaga cewa an shafe tsawon Sa'a sittin batare da ya samu
nasarar kai Amirat ƙasa ba,
Sai ya cika da matukar al'ajabi da mamaki, kuma hankalinshi ya dugunzuma ainun,
Abin da ya bashi mamaki shine yadda akayi ya kasa samun nasara akan Amirat bayan cewa a
zahiri ya nunka a karfin damtse da ƙirar jarumtaka,
Abin da Ya dugunzuma hankalin sa kuwa shine matsawar ya faɗi wannan gasa shi kenan bazai
taɓa samun nasarar fansar rayuwar mahaifinshi daga hannun sarki Baddadul-ulƙas ba,
Sa'adda sarkin sadaukai yazo dai-dai nan sai kawai ya sake zage damtse yana cigaba da
kaiwa Amirat naushi da bugu da wani irin salo na musamman.
A ɓangaren gimbiya haya'ul-nur yar mai girma shaibat da gimbiya Rumaisat yar sarki shuraih
kuwa
Labari yasha bambam domin sun fara haɗawa junan su jini da majina suna rangaji jiri na ɗibar
su amma saboda juriya da bajinta irin ta JARUMAN DUNIYA sai suka ƙi yarda su faɗi ƙasa,
Su ka cigaba da faɗan a haka kawai,
Abangaren sadauki lazwas ibn shaslam da Jarumi nazwar kuwa,
Sun tara zufa sun jiƙe sharkaf saboda yadda suke naushi da bugun juna cikin gwaninta da
salon yaƙi mai matukar kwarjini,
Domin idan lazwas ya gabzawa nazwar naushi a fuska ya kife ƙasa,
Sai ya ɗan huta na yan daƙiƙa sannan ya taso sama ya mayar da martani,
Lokacin da Sa'a ɗaya ta cika da fara wannan artabu sai salon yaƙin ya canza salo,
Kasancewar rana tayi tsananin zafi ainun sai sadaukan suka fara galabaitar da juna,
Ana cikin wannan artabu ne sadauki lazwas ya kaiwa jarumi nazwar naushi a wuya a lokacin da
shi ma yakai mishi harin a kirji,
Cikin nasara kowanne su ya samu nasarar samun ɗan uwan sa nan take suka kurma wawan
ihu suka sulale ƙasa
Babu alamun rai a tare dasu,
Al'amarin da ya sanya fadar ta kaure da shewa da tafi kenan kuma ya dugunzuma hankalin
attajiran da su ke ɗauke da alhakin sanya jaruman a cikin gasar
Shin yanzu jaruman nasu sun rasa rayukansu ne ko kuwa doguwar suma su kayi
Cikin hanzari waɗansu zaratan dakaru suka shigo filin Ɗauke da keken doki suka ɗauki jaruman
biyu suka ɗora su akai,
Suka fice daga filin gasar domin basu taimakon gaggawa a ceto rayuwar su,
Ana cikin wannan fafatawa sarkin sadaukai Hibairu tare da jaruma Amirat suka kaiwa juna
naushi a fuska,
A lokacin da suka Daka tsalle izuwa sama,
Cikin Sa'a kowanne ya gabzawa ɗan uwan sa naushi a fuska,
Take suka hantsilo suka rikoto ƙasa, amma saboda gwanin ta kafin su kai ƙasan sai kowanne
su ya ware kafafunsa biyu ya turje a cikin ƙasa,
Sannan suka kaiwa juna karo da kawunan su jika ke gau,
Amma a wannan karon sai suka kife a ƙasa suna haki tamkar waɗansu zakaru,
Koda ganin irin gwanintar da sadaukan ke yi sai filin fadar ya kaure da shewa da jinjina haɗe da
ihu,
Al'amarin gimbiya haya'ul-nur da Rumaisat kuwa,
An cigaba da yin kare jini biri jini babu alamu dake nuna cewa ga gwanar dake da nasara a cikin
su,
Lokacin da alƙalan gasa suka cewa an shafe tsawon Sa'a uku ana wannan artabu babu alamun
nasara ga dukkan bangarorin sai wannan badakare daya busa ƙahon yaƙi ya sake ɗauko
wannan ƙaho ya busa da karfi,
Take kowanne jarumi yaja ya tsaya cak yana haki da hararar abokin gwamin sa.
Sarkin yaƙi abu-Damraz ya sake miƙewa tsaye a karo na biyu yayi gyaran murya ya fuskanci
jama'a yace"yaku mahalarta wannan gasa mai albarka kuyi sani cewa duba da yadda har sa'o'i
uku suka shuɗe babu alamun nasara ga dukkan bangarorin,
Bisa tsarin wannan gasa za'a tafi hutu na rabin Sa'a domin jarumai su sake kimtsa wa suyi
sabon shiri domin yin karon batta ta biyu wacce a cikin ta ne muke sa ran za'a ƙarƙare wannan
gasa domin fitar da gwarzon mayaƙi,
Koda jin wannan jawabi daga bakin Sarkin yaƙi abu-Damraz sai fadar ta sake ruɗewa da shewa
cikin Hanzari dukkan jaruman huɗu suka fice daga filin gasar,
Kai tsaye sarki Baddadul-ulƙas ya sanya hadiamn sa suka shiga duba lafiyar jarumi Hibairu
domin ya samu wartsakewa kafin a koma zagayen gasa ta biyu,
Shi kuwa sarki shuraih cikin tashin hankali ya tari yarsa gimbiya Rumaisat tare da duba halin da
take ciki koda yaga cewa ta galabaita ainun sai hankalinsa ya dugunzuma ya umarci wadansu
kwararrun likitoci suka shiga duba lafiyar ta,
Abangaren mai girma shaibat kuwa da kansa ya a shiga gasawa yarsa gimbiya haya'ul-nur
fuskan ta ta ruwan ɗumi domin kumburin dake fuskantar ya sabe,
Sakamakon jinin da ya taru a fuskar saboda naushin da gimbiya Rumaisat yar sarki shuraih tayi
mata,
Kuma duk bayan daƙiƙa uku ya tambaye ta shin ya a bar alfaharina a wane hali kike jin jikin ki
yana sauƙi kuwa,
Al'amarin jaruma nihla, sunaila, Hizmal,yaro Humair makaho, sarauniya Abidatul-auliya,
Nuwairat da matsafi shubairu kuwa,
Lokacin da suka ga yadda sarkin sadaukai Hibairu ya jigata ainun,
Sai hankulan suka dugunzuma ainun, suka dunga kai komo a bakin ɗakin da ake duba lafiyar
Hibairu.
Kamar yadda sarkin yaƙi abu-Damraz ya faɗa haka al'amarin yakasance,
Wato rabin Sa'a na kammala cika sai dukkan jaruman gasa gami da sauran jama'a suka sake
hallara a karo na biyu,
A lokaci guda jaruman gasa suka shiga izuwa Filin fama suna masu zagaye juna,
Amma a wannan karon babu jarumai biyu, wato sadauki lazwas da jarumi shazwas,
Har a wannan lokaci fuskar jaruma Amirat na sanye cikin rawani idanuwan ta kaɗai ake gani,
Koda ganin cewa Jaruman suna shirin fafatawa,
Sai wannan badakare ya sake ɗauko wannan gabgegen ƙaho ya kafa a bakinshi ya busa da
karfi
Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan babu ƙasa nanne ake
gardamar kokawa.
Kuma ranar bikin sarakai babu e fitowa ya taka rawa face wacce da wane,
Kafin sautin ƙahon ya kammala mamaye fadar
Sarkin sadaukai Hibairu yayi ɗauki izuwa kan jaruma Amirat,
Gimbiya haya'ul-nur kuwa ya ruga izuwa kan gimbiya Rumaisat,
Su dukan ukun suna ihu da kururuwa mai firgitar wa,
Jaruma Amirat na ambaton sunayen Ubangiji a cikin ran ta,
Lokacin da aka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini
daban sha'awa,
Jaruman huɗu suka wanzu suna kaiwa juna naushi da bugu hannu da ƙafa,
Cikin matukar zafin nama juriya da jarumtaka irin ta zaratan Jarumai
Nan fa ƙura ta turnuƙe, sautin naushi da ihun mazaje ya cika filin baki ɗaya
Ana fara wannan artabu ne wani abin mamaki ya fara gudana domin kuwa a wannan karon
jarumi Hibairu da jaruma Amirat na tashi izuwa sararin samaniya suna yaƙar junan su,
Tamkar sun kasance masu fuka-fukai,
Nan fa filin gasar ya ruɗe da shewa masoyan Hibairu da jaruma Amirat nayi musu tafi,ihu da
jinjina,
Al'amarin da ya harzuƙa zuciyar mai girma shaibat kenan,
Zuciyar ta kama tafarfasa tamkar zata faso kirjinshi ta fito waje,
Ya dubi Sarkin matsafan masarauta yace dashi a cikin raɗa a fusace "shin mene ne amfanin
alƙalancin da aka baku,
Shin bakwa ganin anyi amfani da karfin sihirin tsafi ga wadancan jarumai biyu,
Koda jin wannan tuhuma sai sarkin matsafa ya risina ya dubi sarki cikin ladabi da girmamawa
yace"ya shugabana ai tuni dukkan tawagar alƙalanci sun gudanar da bincike bisa abinda ke
wakana tsakanin jarumi Hibairu da jaruma Amirat,
Kuka kuma abin da Binciken ya tabbatar mana cewa sam wannan tashin saman da suke yi
babu aikin sihiri a cikin shi.
Ni kaina al'marin ya firgita ni kuma ya ɗimauta domin ko da a tarihi ban taɓa ganin wanda yayi
wannnan aikin almara ba batare da yayi amfani da sihiri ba,
Sai dai irin mutanen nan da ake wa lakabi da ma'abota addinin Musulunci,
Ka da jin wannan bayani daga bakin Sarkin matsafa,
Sai takaici ya sake turnuƙe sarki shaibat yaji tamkar ya zare takobin sa ya afkawa hubairu
sarkin sadaukai ya hallaka shi,
Kuma ya tambayi kanshi a cikin ranshi yana mai cewa
Shin tsakanin HUBAIRU da Amirat wane ne yakasance ma'abocin addinin musulunci?
Amma kuma yadda sunan ya nuna Amirat suna ne Musulmi,
Amma shi hubairu ya ƙarbi addinin ne ko kuwa,
Taya ya yake yin wannan abin bajinta batare da yayi amfani da sihiri ba,
Haƙiƙa idan har ɗaya daga cikin su yakasance
Musulmi abune mai matukar wahala bazasu samu nasarar lashe wannan gasa ba,
Koda ya sake zuwa Nan a tunaninshi sai yaji tamkar ya kwala ihu
Abangaren sarki Baddadul-ulƙas kuwa sa'adda yaga yadda jaruma Amirat take yaƙar hubairu
cikin gwanin ta da kwarewar yaƙi,
Kuma babu alamun dake nuna cewa HUBAIRU zai samu nasara akan ta.
Sai hankalin sa ya dugunzuma ainun kuma ya fusata
Abinda ya dugunzuma hankalin shi shi ne yadda alamu ke nuna cewa abu ne mai matukar
wahala hubairu ya lashe wannan gasar jarumtaka,
Shin ko kuwa hubairu baya tare da zoben sihirin sa ne,
Abin da ya fusata shi shine shin wace wannan boyayyen jaruma Amirat dake ƙoƙarin ganin ta
tozarta shi,
A wannan gasa ta sanya yayi muguwar