Showing 27001 words to 30000 words out of 30696 words

Chapter 10 - GOGA SHA FAMA Book by Mansur Usman Sufi .pdf

07 Aug 2025

607

baki ta
karanti waɗansu kalmomi da ita kaɗai tasan me take furtawa , ta tsugunna ƙasa ta tofa a bisa
raunin dake gadon bayan Jarumi Hibairu,

Take raunin ya warke sumul, adai dai lokacin da hubairu ya miƙe tsaye cikin ƙoshin lafiya,
yana mai ƙura wa ɓakuwar jarumar idanu ko ƙiftawa ba yayi.

Yana mai tambayar kansa a cikin ranshi yana cewa shin wacece wannan bakuwar jaruma,
kuma mene ne dalilin daya sanya ta ceci rayuwata, shin ko kuwa jaruma Amirat ce tayi
badda-kama, amma kuma ai Amirat na cikin jinyar rashin lafiya yaushe ta samu lafiya.

Amsar tambayar da hubairu yakasa bawa kanshi kenan, adai-dai da dakarun suka kammala
yi musu ƙawanya.

A na cikin wannan hali ne kwatsam sai aka hango wadansu dakaru na daban kuma
mabanbanta na fitowa daga kowace kusurwa a birnin,waɗansu akan dakwai wasu a ƙafa.

Lokacin da suka kammala bayyana asannanne hubairu ya lura dacewa ba wasu bane ke
jagorancin mayaƙan ba face Sarki shaibat da sarkin yaƙi abu-Damraz.

Yayin da dakarun suka yi arba da mai girma shaibat sai suka dare a tsakiyarsu suka bayar da
wata hanya da mutum zai iya hucewa.

Sannu a hankali Sarki shaibat na ratsa tsakanin kafaɗun dakarun har ya bayyana daf inda
Hibairu da baƙuwar jaruma take.

Tsawon daƙiƙa hamsin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne sarki shaibat ya dubi hubairu
yayi gyaran murya cikin matukar fushi fuskar shi har gyatsine take yi yace"yakai Babban abokin
gaba na har abada hubairu ibn Shabbaru kayi sani cewa haƙiƙa kana da tsanin sa'a da rabo da
har ka iya tsalle ke tarkona, ka sani cewa a halin yanzu bazaka tsira da rayuwarka ba, domin ka
maimaita laifin da mahaifinka Barde Shabbaru yayi mini.

Yanzu abinda nake bukata kawai shine ka miƙo mini zoben sihirin cikin ruwan sanyi, kafin
sarki shaibat ya gama rufe bakin shi sai akaji wata murya taɓa cewa "Haƙika nine nafi cancanta
daya mallaki zoben sihiri face domin kuwa sai a yanzu ne na gano cewa ashe ma aikin banza
nake yi dana ɓata lokaci wajen mallakar dukiyar gasar GOGA SHA FAMA.
Cike da matuƙar al'ajabi sarki shaibat, hubairu,baƙuwar jaruma suka waiga domin suga
wanda yake wannan furuci, yayin da suka yi arba dashi sai suka yi turus!.

Ba wani ne bane face Sarki Baddadul-ulƙas shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar
kwarjini daban tsoro tamkar wani ifritu,hannun shi na hagu rike da wani irin makami na haske,
na hagun kuwa rike da sarƙa ta wuta, wani dattijo ne ɗauke da jikin sarƙar ta ɗaure sassan
jikinshi, ba wani ba ne dattijon ba face Barde Shabbaru mahaifin sarkin sadaukai Hibairu.
Sa'adda hubairu yayi arba da halin da mahaifishi ke ciki, bai san sa'adda kwalla ta cika Mashi
idanu.

Sarki Baddadul-ulƙas ya bushe da dariyar mugunta sannan ya murtuke fuska ya ɗorawa
dacewa "Binciken dana gudanar bisa halarar tsafina ya tabbatar mini dacewa duk wanda yake
tare da zoben sihiri zai mulki duniya, domin, zai iya lalata dukkan sirrikan tsafin dake duniya,
domin dukkan makarin tsafin dake duniya na jikinshi, yakai Hubairu kayi sani cewa, a halin
yanzu mallaka mini zoben sihiri domin kuwa hakan ne zai sanya na cire mahaifin ka daga
wannan kangin bauta, idan kuwa kayi kunnen uwar shegu dani yanzu zan hallakashi a gaban
idanun ka kuma na kashe na mallaki zoben cikin ruwan sanyi.

Koda jin wannan batu daga bakin sarki Baddadul-ulƙas sai hawaye suka zubo daga idanun
hubairu yaji tausayin mahaifin shi ya sake kama shi, kawai sai ya sanya hannu na dama akwai
na hagu zai cire zoben sihiri ya

Da nufin ya miƙa wa Baddadul-ulƙas, amma sai baƙuwar jarumar ya dakatar dashi ta hanyar
buɗar baki ta fara magana a karo na farko cikin Daddaɗar Murya tace"yakai sarkin sadaukai
kayi sani cewa a yau ne zaka tabbata jarumi Ɗan baiwa, amma hakan bazai cika ba face ka
rushe zaluncin wadannan sarakuna biyu, Baddadul-ulƙas da shaibat
Da ma dukkan zaluncin dake ɗoran ƙasa,

Ta hanyar amfani da wannan zobe.

Ka sani cewa damƙa shi ga sarki Baddadul-ulƙas tamakar ka damƙa rayuwarka da sauran
al'ummar duniya cikin rayuwa da mutuwa, shin yanzu kana da tabbacin cewa sarki
Baddadul-ulƙas bazai ci amanar ka ba idan ka mallaka ma shi zoben?.

Koda jin wannan jawabi haɗi da tambaya daga bakin baƙuwar budurwar sai Hibairu ya
mayar da zoben bisa ɗan yatsanshi,

Shi kuwa sarki Baddadul-ulƙas sai ya bushe da dariyar mugunta ya dubi baƙuwar jarumar
cikin tsakanin fushi yace"yake wannan jarumar ɓoye haƙiƙa kin tafka babban kuskure da kika
shiga gonar da ba taki ba.

Yanzu nan zan ganar dake kuren ki, yana gama faɗin hakan sai kawai cilla sarƙar da dake
hannun sa izuwa sama,take Barde Shabbaru dake ɗaure da sarƙar yayi sama tamkar an janye
shi da ƙugiya ya tsaya a cikin iska, sannan Baddadul-ulƙas ya ɗaga wannan makami na haske
dake hannun shi ya ruga izuwa kan baƙuwar jarumar yana ihu da kururuwar mai firgitarwa
Koda ganin hakan sai mai girma shaibat ya zare wata sharbebiyar takobi a damtsen shi ya
kurma Wawan ihu yayi ɗauki kan Hubairu sarkin sadaukai.

Ana haɗuwa akayi karon batta ƙarfe, nan fa GWARAZAN JIYAn suka wanzu suna kaiwa juna
sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da jarumtaka irin ta zaratan Jarumai.

Lokacin da GWARAZAN JIYA huɗu, sarkin sadaukai,mai girma shaibat, Baddadul-ulƙas da
baƙuwar jaruma suka ruguntsume da azababban yaƙi.

Sai suka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare- hare cikin matuƙar zafin nama juriya da
jarumtaka irin ta zaratan Jarumai.

Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan Manyan giwaye suka fito
filin daga, dole kananan dabbobi su zamo yan kallo, hakan ya faru ga sauran dakarun koda
sukaga shuwagabannin su sun kacame da azababban yaƙi sai suka zamo yan kallo.

Kyan faɗa akwana ana yi inji masu iya magana, sai ɓangarorin huɗu suka shafe tsawon
rabin Sa'a da daƙiƙa talatin Suna ɗauki ba daɗi ta hanyar kaiwa juna miyagun hare-hare tamkar
waɗansu ifritai.

Duk sa'adda sarki Baddadul-ulƙas ya kaiwa naƙuwar jaruma sara da makamin dake hannun
sa idan ya haɗu da takobin ta sai kaji sun fitar da sautin ƙara ƙal! Ƙal, kuma tartsatsin wuta ya
tashi,

Sa'adda Baddadul-ulƙas yaga cewa ya kasa samun nasara akan baƙiwar jaruma sai ya fusata
ainun kuma ya faɗa izuwa kogin tunani,

Abu na farko daya faɗo mashi a rai shine, shin mene ne dalilin da yasa sanya ya kasa samun
nasara akan jarumar duk da cewar a zahiri ya fita karfin damtse da salon yaƙi, abu na biyu
shine haƙiƙa idan yayi jinkirin kawar da ita sarki shaibat ya samu nasara akan Hibairu to zai riga
shi mallakar zoben sihiri
Lokacin da Baddadul-ulƙas yazo nan a tunanin shi sai kawai ya zage damtse yana cigaba da
kaiwa naƙuwar jaruma sara da suka cikin ɓakin zafin nama, amma sai wani tunanin da ya faɗo
mashi shine anya kuwa wannan ba jaruma Amirat ba da ta fafata yaƙi da hubairu a gasar
GOGA SHA FAMA ba, amma idan kuwa har ita ce ɗin akwai babbar damuwa domin kuwa
komai zai iya kasance, domin binciken da na gudanar bisa halarar tsafina ya tabbatar mini
dacewa da sani Amirat ta faɗi wannan gasa domin hubairu ya samu nasara.

Lokacin da ya sake zuwa nan azancenshi sai zuciyar shi ta buga da karfi, amma saboda ƙi
faɗi irin ta hamshakan sarakai sai ya bar abin a ranshi.

Abangaren mai girma shaibat da sarkin sadaukai kuwa sun wanzu suna kaiwa juna sara da
suka babu sassauci. Ga duk wanda ke kallon yadda artabun ke wakana zai fahimci cewa mai
girma shaibat ya nunkashi a karfin damtse sau huɗu.

Abinda ke ceton hubairu shine naci da zafin nama, amma badan hakan ba da tuni shaibat ya
samu nasara akan shi.

Lokacin da kowannen su yaga cewa yakasa samun nasara sai ya faɗa izuwa kogin tunani
domin samun mafita.

Abu na farko daya faɗo sarki shaibat shin yaza'ayi ace gwarzon mayaƙi kamar shi ya kasa
samun nasara akan Hibairu, yaushe aka samu wani hatsabibin jarumi a wannan nahiya dazai
fishi karfin damtse, ko kuwa zarginshi ya tabbata na cewa hubairu ya ƙarɓi addinin Musulunci
ne ,haƙiƙa idan kuwa haka ne akwai baban matsala akoda yaushe zan iya kunyata domin
ma'abota addinin Musulunci hatsabiban mutane ne da babu su a wannan duniya baki ɗaya,
haƙiƙa wajibi ne na ƙara zage damtse.

Aɓangaren hubairu kuwa abinda ya faɗo mashi a rai shine shin ya akayi yana tare da zoben
sihirin shi amma ya gaza samun nasara akan shaibat, abu na biyu daya faɗo mashi a rai ne
matsawar kana son kayi nasara, wajibi ne ka kayi amfani da waɗannan kalmomi na jaruma
Amirat waɗanda ka karanta su har ka samu nasarar lashe gasar GOGA SHA FAMA.
Lokacin da dukkan suka zo nan a tunanin su sai suka canza salon faɗansu, sarki shaibat na
karanta muhimman sirrikan tsafi a ranshi,

Hubairu kuma ambaton sunayen Ubangijin jaruma Amirat a cikin ranshi.

Gaskiyar masu iya magana da suka ce idan kiɗa ya canza dole rawa ma ta canza, faruwar
hakan keda wuya sai hubairu ya fara samun nasara akan shaibat, duk sa'adda sarki shaibat ya
kai mashi hari idan ya kare kafin ya sake mayar da martani, hubairu ya soka mashi mashinshi a
wani ɓari a jikinshi jini ya kwatanta.
Abinda shaibat bai sani ba shine bakomai ya sanya sihirin shi yaƙi yin tasiri ba sai domin
zoben sihirin hubairu bazai bari nashi na yayi tasiri ba.

Kamar yadda ya wakana abangaren su hubairu,haka al'amarin yakasance ga su
Baddadul-ulƙas, a inda baƙuwar jaruma ta fara samun nasara akan shi har takai ga cewa baya
iya mayar da martani ya shiga yin amfani da sihiri amma sai ya zamana ya tashi abanza domin
kuwa duk sihirin daya turawa jarumar da ya doshi inda take sai su zama hayaƙi su ɓace ɓat.
Ana cikin wannan yaƙi ne mai girma shaibat ya shammaci hubairu ya gabza mashi naushi a
ciki, saboda karfin naushin sai da ya yayi sama tamkar an jashi da ƙugiya amma ya daɗo ƙasa
yana mai amai na jini lokacin daya dunga birgima aƙasa yana mai dafe cikinshi saboda yadda
yake murɗamshi.
Koda samun wannan nasara sai shaibat ya suri mashin hubairu daya faɗi can gefe guda ya
taka dakyar har izuwa inda yake ya ɗaga Mashin domin ya caka akan saitin zuciyar hubairu,
yana mai yi mashi murmushin mugunta.

Al'amarin daya sanya hankalin baƙuwar jaruma ya dugunzuma ainun kenan ta juya domin
kaiwa hubairu ɗauki, kafin tayi taku biyu Baddadul-ulƙas ya sammace ta ya maka mata wani
makami a tsakiyar kanta, take ta sulale ƙasa sumammiya babu alamun numfashi a tare da ita.

Kwatsam bazato babu tsammani sai a kaga waɗansu zaratan kibbau sun dira akan gadon
bayan sarki shaibat sun faso ta ƙirjinshi jini ya dunga kwaranya yana tsartuwa tamkar an buɗe
kan fanfo.

Al'amarin daya sanya shaibat ya saki makamin dake hannun shi kenan, ya kurma wawan
ihu yana mai durkushewa ƙasa domin yaga wanda ya harbeshin.

Ai kuwa sai ya yi arba da ita ba wata bace face jaruma Amirat zaune a bisa kan wani
matashin aljani,zaune a gefen ta na dama wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa tagaban
kwatance, waɗansu tawagar aljanu marasa adadi na biye da ita cikin shigar yaƙi tamkar masu
shirin yaƙar duniya, suna saukowa daga sararin samaniya.
Nan fa kowa dake wajen ya shiga da matukar al'ajabi, musamman jarumi Hibairu SARKIN
SADAUKAI dake kwance a ƙasa magashiyan

Shi kuwa sarki Baddadul-ulƙas saboda ya matuƙar al'ajabin ya manta da baƙuwar jaruma da
ya sumar ya ɗaga kanshi sama yana ƙarewa Jaruma Amira kallo cikin tashin hankali,yana mai

tambayar kanshi a cikin ranshi yana mai cewa "shin kenan baƙuwar jarumar da nake fafatawa
da ita ba ita ce Amirat ba, yaushe Amirat ta samu lafiya, sannan a ina ta ɗauko wannan tawagar
aljanu da idanu basu taɓa ganin irin su ba.

Amsar tambayayin daya kasa bawa kanshi kenan.

Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga sarkin sadaukai Hibairu ya miƙe tsaye zumbur
cikin koshin lafiya ya suri waɗansu takubba biyu ya ɗora akan wuyan sarkin shaibat ya tsinke
mashi kai, kan yayi fitar burgu,jini ya dunga feshi yana kwaranya, ganagar jikin ta faɗi ƙasa
rikici! .
Kaico! Haƙiƙa kafirci rayuwar banza ce, ina da ace mutum yana tsaye a wannan waje zai ga
yadda gawar mai girma shaibat ta wulakanta kwance a ƙasa, dole yayiwa Allah godiya bisa
ganin yadda Allah ya kawo karshen azzalumi.

Cikin wani irin baƙin zafin nama HUBAIRU ya daga tsalle sama, sai gashi yana taka
kawunan dakarun dake tsaye a wajen tamkar yana tafiya a turba, cikin abinda bai gaza daƙiƙa
goma ya dira a dai-dai saitin in da sarki Baddadul-ulƙas ke tsaye tun a saman ya kai mashi wani
wawan sara a kafaɗar shi.
Bisa sa'a sai gashi ya sare hannun shi ɗaya, Baddadul-ulƙas ya kurma ihu lokacin da jini ke
feshi daga dungulmin hanuun.

Cikin ɓakar zuciya Baddadul-ulƙas ya sanya hannun sa ɗayan ya kaiwa hubairu naushi a
fuska.

Cikin zafin nama HUBAIRU ya wurƙila ya zamewa harin ya sake sanya takobin shi ya sare
ɗayan hannun, Baddadul-ulƙas ya sake kurma ihu ya durkusa kasa bisa gwiwoyinshi, haka dai
hubairu ya shiga sare gaɓoɓin Baddadul-ulƙas ɗaya bayan ɗaya, duk sa'adda ya sarewa wata
gaɓar sai sarkar tsafin data ɗaure mahaifinshi Barde Shabbaru ta ɓace ɓat.
Lokacin da yazamana cewa kai ne kawai ya rage da gangar jiki a tare da Baddadul-ulƙas
sai Barde Shabbaru ya faɗo ƙasa daga sararin samaniya babu komai na sarkar tsafin a tare
dashi, kuma a dai-dai wannan lokaci ne tawagar su saurayi Hizmal suka iso wajen filin fafatawar
tare da dabbobin hubairu, kuma jaruma Amirat da tawagar aljanun dake biye da ita suka sauka
a turba.

Sa'adda su Hizmal suka ga gawar mai girma shaibat a ƙasa, kuma suka yi arba da sarki
Baddadul-ulƙas cikin mummunan yanayin dake tsakanin Rayuwa da mutuwa, sai suka cika da
matukar mamaki da farin ciki.

A bangaren Dabbobin hubairu kuwa koda sukayi arbda da Baddadul-ulƙas sai kawai suka
afka masa suka shiga yaga sassan jikin shi kafin wani lokaci babu wani abu na jikinshi da basu
cinye ba face kans hi.

Kaico! Haƙiƙa mutuwar azzalumai ba ta da daɗin kallo, yanzu dai gashi duk kasaita da
dukiya, sihiri gami da jarumtaka da sarki Baddadul-ulƙas ke takama dashi sun zamo a banza
yayi mutuwar wulakanci, wacce dabbobi ne ma marasa daraja suka kashe shi wanda shi bai
ɗauki rai na ɗan adam a bakin komai ba.
Cikin matukar kwaɗuwa hubairu ya durƙusa a gaban baƙuwar jaruma domin yaga a wane hali
take ciki, amma sai yaji taja dogon Gwauron numfashi ta miƙe tsaye cikin koshin lafiya, dai dai
lokacin da jaruma Amirat ta iso inda take tsaye suka rungume juna cikin matuƙar farin ciki, koda
ganin sai hubairu ya riga izuwa inda mahaifinshi yake tsaye suka rungume juna suna masu
fashewa da kukan farin ciki.

A sannanne gumbiya Zarifa dake tare Amirat ta hango mahaifinta sarki uslaim don haka sai
ta ruga gareshi suka rungume juna suna masu zubar da hawayen farin cikin sake saduwa da
juna,

Ashe shi ma aljani Marhutul-Azab ya lura cewa wanɗannan tawagar aljanu da ke tare da
Amirat ba wasu ba ne face zuri'arshi dake bukatar jarumi Hibairu ya ceto su daga fadar sarkin
bokayen Duniya, kawai sai ya ruga garesu cikin farin cikin saduwa da juna.

Bayan komai ya samu lafawa kuma jama'ar gari sun taru a wajen lokacin alfijir ya keto sai
jaruma Amirat ta shiga yiwa jama'a bayanin yadda akayi ta samu nasarar zuwa fadar sarkin
bokayen Duniya a cikin sa'o'i kaɗan har ta ceto rayuwar gimbiya Zarifa yar sarki uslaim tare da
zuri'ar aljani Marhutul-Azab da ruhukansu dake ajiye a cikin akwatun shiri, tun daga farko har
ƙarshe ta zayyanewa jama'a.

Sa'adda jama'a suka ji wannan bajinta gami da karfin Ubangijin halitta sai suka kara cika da
mamaki da imani da Allah (SWT).

Jarumi Hibairu da mahaifinshi Shabbaru ne suka fara ƙarbar kalmar shahada a hannun
Amirat, sannan jaruma sunaila, Hizmal, Abidatul-auliya,Nuwairat,yaro Humair makaho, matsafi
shubairu, budurwa Nihla,sarki shazwan da tawagar bokayen shi,gimbiya, boka ƙarzum, aljani
Darmanu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login