Showing 24001 words to 27000 words out of 30696 words
Chapter 9 - GOGA SHA FAMA Book by Mansur Usman Sufi .pdf
asarar dukiya mai tarin yawa wacce ban taɓa yin
kamar ta ba.
Me ne ne dalilin daya sanya halarar tsafi na bata bayyana mini jaruma Amirat ba,
Haƙiƙa matsawar jaruma Amirat ta lashe wannan gasa sai na shafe Birnin su daga doran ƙasa
koda kuwa kiyashin birnin su bazan bari a raye ba.
Lokacin da sarki Baddadul-ulƙas yazo nan a tunaninshi sai ya sake murtuke fuska tamkar an
aiko masa da SAƘON MUTUWA.
A binda sarki shaibat da sauran jama'a basu sani ba shine
Bakomai yasanya Amirat take samun nasarar tashi sama batare da fuska fukai ba.
Sai domin ta na yin hakan ne bisa iko da karfin buwayar Ubangiji
Shi kuwa jarumi Hibairu yana samun nasarar tashi saman ne bisa sirrin tsafin dake jikin
ZOBEN SHIRIN sa,
Abinda yasanya alƙalan gasar basu gane sihirin tsafin ba,
Sai domin bisa tsarin sirrikan tsafin dake jikin ZOBEN sune makarin dukkan sirrikan tsafin
duniya,
Duk wani sirrin tsafi da ya haɗu da na jikin ZOBEN SHIRIN
Sai ya lalata sirrikan tsafin gaba ɗaya koda kuwa sun kai guda miliyan guda,
A tsakiyar filin fama kuwa an cigaba da yin ɗauki ba daɗi,
Jaruman sun wanzu suna kaiwa juna naushi da bugu cikin matukar zafin nama juriya da bajinta
tagaban kwatance,
Ana cikin wannan fafatawa ne Hibairu da jaruma Amirat suka kaiwa juna wawan naushi a ciki,
A lokaci guda bisa Sa'a sai kowannen su ya samu ɗan uwan sa nan take su duka biyun suka
sulale ƙasa,
Babu alamun rai a tare dasu har idanuwan su sun fara ƙafewa.
Lokacin da jama'a suka ga halin da manyan gwanayen biyun ke ciki,
Sai hankulan su suka dugunzuma ainun.
Har wasu daga cikinsu suka fara zubar da hawayen baƙin ciki.
Domin fargabar kada ace gwanayen su sun rasa rayukansu a wannan gumurzu.
A wannan karon ne gimbiya haya'ul-nur da Rumaisat suka baje a ƙasa suna haki, gami da
hararar juna tamkar waɗansu zakaru,
Abangaren tawagar sarki Baddadul-ulƙas kuwa,
Wato dukkan sarakuna da jaruman da sukayi masa rakiya su ka ga halin da gwanin su SARKIN
SADAUKAI Hibairu ke ciki sai kwallar takaici ta
A dai dai wannan lokaci shugaban alƙalan gasa wato sarkin yaƙi abu-Damraz ya lura cewa
lokacin da aka ɗibarwa gasar ya kusa ƙarewa gashi babu alamun nasara ga dukkan bangarorin,
Sai kawai ya miƙe tsaye tsam daga kan karagar sa da nufin yace wani abu sai kawai ya jiyo
gimbiya haya'ul-nur da Rumaisat daga filin gasar,
Ai kuwa yana dubawa sai ya ga ashe dukkan su san sake zubewa ƙasa ne babu alamun
nasara,
Daga can sai kawai akaga HUBAIRU da Amirat sun miƙe tsaye zumbur tamkar haɗin baki gami
da kaiwa juna bugu da naushi,
Tamkar babu wani abu da ya sameshi,
Koda ganin hakan sai gaba ɗaya jama'ar dake wajen suka ruɗe da shewar murna.
Jaruma nihla masoyiyar hubairu bata san sa'adda ta miƙe tsaye ba ta kama yiwa masoyin ta
jinjina,
Sarki Baddadul-ulƙas da dukkan tawagar murna ce ta kama su ainun,
Ana fara wannan sabon artabu ne sai Hibairu ya shiga ambaton waɗannan kalmomi da yaji
ameerat na ambata a duk lokacin da suka fara gumurzu wato Allahu Akbar!
Domin ya tabbatar dacewa tunda har nasara da jarumtakarsa bata sanya yayi galaba akan
Amirat ba,
To lallai kalmomin da amirat ke amfani dasu zasu iya bashi nasara,
Domin dai ya samu nasara akan Amirat ɗin,
Amma wani abu daya fahimta shine tabbas jaruma Amirat Bata niyyar taga ta cinye shi a
wannan gasa,
Domin sau arba'in tana samun damar da zata illatashi kada yayi nasara amma taƙi aiwatar da
hakan,
Faruwar hakan keda wuya sai hubairu yaga cewa a halin yanzu yana samun nasarar kai Amirat
ƙasa,
Har takai bata iya mayar da martani, ana cikin wannan hali ne hubairu ya shammaci ta ya
gabza mata wawan naushi a gadon bayan ta.
Saboda da karfin naushi,
Sai da amirat tayi sama tamakar an janye ta da ƙugiya,
Sannan daga bisani ta faɗo ƙasa tim! Hancinta da bakinta na yoyon jini,
Numfashin ta na fita sama-sama, adai dai lokacin ne gimbiya haya'ul-nur da Rumaisat suka
suka bajewa a ƙasa wanwar sakamakon naushin juna da sukayi a cikin su,
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa hamsin acikin wannan hali batare da an ga ɗaya daga cikin
jaruman uku ya miƙa tsaye ba domin cigaba da artabu,
Har sai da badakaren dake busa ƙahon gasa ya ɗauko ƙahon ya busa sau uku amma babu
wanda yayi yunkurin miƙewa.
Nan fa magoya bayan jaruma Amirat, gimbiya haya'ul-nur,da gimbiya Rumaisat suka shiga kiran
sunayen gwanayen su domin su miƙe kafin wa'adin busa ƙahon ya cika.
Shi kansa sarki shaibat bai sa'adda ya shiga kwallawa yar shi gimbiya haya'ul-nur kira amma
shiru kake ji.
Amma sai badakaren a kammala busa ƙahon gasar,
Abin da ya tabbatar dacewa sarkin sadaukai Hibairu shine ya zamo gwarzon daya lashe gasar
GOGA SHA FAMA,
Nan fa fadar ta ruɗe da shewa, kide-kide da raye-raye kamar za'ayi shagalin nadin sarautar,
Saboda da murna,
Jaruma sunaila, Hizmal, Abidatul-auliya, Nuwairat,yaro Humair, matsafi shubairu,sarki shazwan
da tawagar sa, aljani Marhutul-Azab da sauran dabbobi tawagar sarkin sadaukai basu san
sa'adda suka shiga tiƙar rawa ba suna shewa da murna tamkar waɗanda suka zautu.
Sarki Baddadul-ulƙas kuwa kururuwar murna ya shiga yi tamkar wani tsohon mahaukaci,
Bisa ganin jarumin sa ya lashe gasar GOGA SHA FAMA ta sabuwar Shekara,.
Cikin hanzari dakaru na musamman suka shiga izuwa Filin yakin suka ɗauki
Jaruma Amirat, gimbiya haya'ul-nur da gimbiya Rumaisat abisa keken doki aka fice dasu daga
filin gasar, domin duba lafiyar su,
Mu haɗu a littafi na 5 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga Alkalamin
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan yaki
08137237071
GOGA SHA FAMA
End book
Writing by
MANSUR USMAN SUFI
Cikin kaɗuwa da matukar fushi da sarki shaibat bai taɓa yin kamar sa ba,
A wannan lokaci in da ace mutum yana tsaye a wannan waje sai ya rantse yace "garwashin
wuta aka watsa masa akan fuskar tashi saboda yadda ya murtuke ta tamkar bai taɓa dariya ba.
Kawai ya miƙa tsaye zumbur daga kan karagar shi ya yabi bayan keken dokin da gimbiya
haya'ul-nur ke ciki da sauri,
Dakarun shi na biye dashi cikin tashin hankali,
Sarkin yaƙi abu-Damraz kuwa saboda tashin hankali dakyar ya samu dama yayi wa mutane
bayanin cewa
A gobe ne za'a gabatar da bikin naɗin Jarumi Hibairu a matsayin GOGA SHA FAMA,
Tare miƙa kyautuka gareshi da bawa wakilin daya sakashi a cikin gasar dukkanin dukiyar
sauran sarakunan da jaruman su sukayi rashin nasara a cikin gasar.
Yana kammala jawabin ya miƙe zumbur yaja tawagar dakarun shi suka fiye daga fadar,
Shi kuwa jarumi Hibairu koda yaga an fice da jaruma Amirat cikin halin dake tsakanin Rayuwa
da mutuwa sai ya tsinci kanshi cikin alamun tsananin damuwa da tausayin halin da take ciki,
Nan fa jama'a suka fara darewa suna ficewa daga filin gasar,
Gaba ɗaya tawagar sarki Baddadul-ulƙas suka dunguma suka tari sarkin sadaukai Hibairu suna
masu yi masa jinjina.
Kai tsaye suka dunguma suka fice daga filin gasar domin komawa izuwa masaukin su.
Lokacin da tawagar sarakuna da jarumai suka yiwa da suka yiwa Sarkin sadaukai Hibairu
rakiya izuwa Filin Garsar goga sha fama,
Sai suka ci-gaba da tafiya acikin saƙo da lungu na birnin madinatul-shaja'a.
Duk inda suka zo giftawa sai kaga jama'a suna yiwa Hibairu jinjina suna ɗaga mashi hannu.
Haka dai suka shiga da tafiya acikin birin har suka iso izuwa masaukin su.
Kai tsaye aka dunguma izuwa ciki, bayan dakarun dake tsaron kofa sun wangame kofar shiga
masaukin.
Da yake a wannan lokaci duhun magari ba ya kawo kai sai sarki Baddadul-ulƙas yayi Umarni
aka kunna dukkan fitulun dake gidan ya kaure da haske ɗau!.
Lokacin da hubairu ya shiga izuwa masaukin shi sai ya kasa zaune ya kasa tsaye ya wanzu
yana kai komo.
Bakomai na sanya shi a cikin wannan hali ba sai tunanin halin da jaruma Amirat ke ciki.
Nan take ya raya a ranshi cewa haƙiƙa komai tsananin duhun dare kafin wayewar gari sai
ya ziyarci jaruma Amirat a sirran ce batare da wani ya sani ba.
Yana cikin wannan hali ne yaji an kwankwasa kofar turakar.
Kawai sai yayi gyaran murya da nuna bayar da umarnin shigowa.
Kofar tayi ƙara tana kammala buɗe wa sai yayi arba da ita ba wata bace face jaruma
Nihla,
Sannu a hankali ta iso daf dashi, tana sakarmashi ƙaytaccen murmushi,
Shima martanin murmushin ya shiga mayarta.
Fuskar ta cike da annuri ta dubeshi
tace "ya masoyiyina ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, hankali yakasa kwanciya, shi yasa ya
yanke shawarar cewa dole sai nayi arba dakai sannan zan iya samun runtsawa.
Murmushi ya sakar mata bisa jin daɗin furucin nata, ya buɗi baki yayi gyaran murya.
Yace "ina matuƙar alfahari dake ya farin cikin zuciyata, haƙiƙa ina cikin ƙoshin lafiya.
Nihla cikin mamaki.
"Amma ina dalilin rashin barcinka a lokacin daya kamata ace ka kwanta domin warware
gajiyar dake tare dakai, domin a gobe da safe ka tashi da kwarin jiki, a lokacin da za'a baka
lambar girmamawa ta Zakaran GOGA SHA FAMA.
Koda jin wannan batu daga bakin masoyiyarshi sai hankalin shi ya dugunzuma bisa tsoron
kada ta fahımcı akwai wata damuwa a tare dashi.
Sai yayi gyaran murya yace "ya rabin raina haƙika bakomai ne ya hanani rintsawa ba sai
bisa ga dalilai guda biyu.
Na farko shine tunanin a wane hali mahaifina yake ciki a hannun sarki Baddadul-ulƙas.
Dalili na biyu tsaron kada sarki Baddadul-ulƙas yaci amanata ya yaudareni, a kowa ne hali
dakarun sumame zasu iya kawo mini farmaki akoda yaushe.
Koda dai na mai girma shaibat ko na sarki shuraihu domin su hallakani.bisa jin haushi da
baƙin cikin faɗuwar su gasar GOGA SHA FAMA.
Da jin wannan bayani sai Nihla ta gyaɗa kai alamar gamsuwa gami da tausaya wa.
Tace "tabbas maganar ka gaskiya ce amma baka ganin cewa duka gidan nan cike yake da
dakarun tsaro, bana tunanin akwai hanyar da wani zai kawo farmaki.
Hibairu yayi murmushi yace "Zancen ki dutse ne amma kada ki manta masu iya magana na
cewa.
"Komai sammakonka wani a hanaya ya kwana ".
"Kuma idan kana dakyau ka ƙara da wanka".
"Zance ka dutse ya sarkin sadaukai.
Nihla ta faɗa tana mai juyawa domin ficewa daga turakar gami da sakar mashi ƙayataccen
murmushi.
Koda ficewar ta daga turakar sai ya shiga sanya waɗansu kayatattun tufafi baƙaƙ, ya rufe
fuskar sa da rawani ya rataya wata zabgegiyar takobi a gadon bayanshi.
Yana kammala hakan sai ya kawai ya murza zoben sihirin dake hannunshi, take ya ɓace ɓat
tamkar bai taɓa wanzuwa ba.
Ko da ɓacewarshi da kamar daƙiƙa goma ba sai ga waɗansu miyagun halittu ya ketowa
daga jikin bangwayen turkar, tamkar yadda danshi ke tsattsafowa daga ƙasa.
Sannu a hankali suka dunga bayyana suna fitar da wani irin gurnani mai ban tsoro.
Yayin da suka kammala bayyana sai suka bincike turakar saƙo da lungu.
Al'amarin jarumai Hibairu kuwa, lokacin da ya ɓace daga turakarshi bai bayyana a ko ina ba,
sai a nesa ƙaɗan da masaukin su.
Sannan ya cigaba da tafiya cikin ɗarɗar yana mai waige-waige, domin yana ganin cewa a
kowa ne lokaci za'a iya kawo mashi farmaki.
Yana cikin wannan tafiya ne kwatsam bazato babu tsammani sai yaga waɗansu irin
zaratan dakaru marasa adadi na fitowa daga cikin kowace kusurwar dake unguwar.
Kafin yayi wani yunkuri sunyi mashi ƙawanya suna gurnani da hargagi tamkar zasu ci babu.
Dakarun suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro, suna
ɗauke da makamai na ƙare dangi.
Komai dakewar zuciyar mutum idan yayi arba dasu dole ya ɗimauce saboda kwarjininsu.
Cikin matuƙar zafin nama HUBAIRU ya zare takobinshi aka fara kallon-kallo tsakanin su, na
tsawon daƙiƙa arba'in.
Daga bisani wani garjejen ƙato,wanda da alama shine shugaban su ya buɗi baki cikin
kakkausar murya tamkar saukar aradu yace.
"Yakai Hubairu ina so yanzu take ka miƙo mini zoben sihirin dake hannunka cikin ruwan
sanyi,domin na yanke maka kisa mafi sauƙi ta hanyar tsinke maka wuya.
Idan kuwa kayi taurin kai, yanzu zan umarci tawagata ta gididdiba sassan jikinka, ta yadda
kowa tsuntsaye basu damar tsatstsagar namanka ba.
Koda jin wannan batu daga bakin katon, sai hubairu ya bushe da dariyar mugunta, daga
bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa wasikar ajali, ya dube sa yace "yakai wannan
katon banza kayi sani cewa ka tafka babban kuskure da kake bani umarni.
Nine yafi cancanta na baku umarnin, yanzu kafin na zare ruhikan ku daga gangar jikkunan
ku ina so ku sanar dani shin wane mai ɓatar basirar ne ya turoku domin ku hallakani?.
Kafin Hubairu ya gama rufe bakinshi, ƙaton ya tari numfashin shi yana mai daka masa
tsawa yace"tabbas yanzu zan ganar dakai kuren ka zan hallaka kuma na tafi da ZOBEN SHIRI,
domin sanin wane ne ya aiko mu gareka ya huce tunanin ka.
Kafin ya gama furucinshi, dakarun sun zare makamansu sunyi ɗauki izuwa kan hubairu, suna
ihu da kururuwa mai firgitar DANDAZON MAYAKA a filin daga,
Shi kuwa ya tare su aka fara ɗauki badaɗi, duka ɓangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa
juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta tagaban kwatance.
Wohoho! Maza gumbar dutse, haƙika inda babu ƙasa nan ne ake gardamar komowa.
Nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, ihun mazaje haɗe hargagi ya cika dodon kunne.
Sai da aka shafe tsawon rabin Sa'a da daƙiƙa talatin ana wannan artabu babu sassauci.
Nanfa dukkan bangarorin biyu suka fara gane kuren su, shi hubairu ya cika da mamakin
yadda dakarun ke da zafin naman sa yakasa samun nasarar hallaka su.
Su kuwa suna al'ajabi ne bisa ganin cewa duk yawan su ya tashi a banza, halitta ɗaya ta
zamemusu alaƙaƙai.
Lokacin da Sa'a ɗaya ta shuɗe ne ana wannan fafatawa,wani daga cikin mayakan ya sulala
ta bayan hubairu ya makashi ƙoatar takobin sa, saboda raɗaɗin da hubairu yaji, bai san sa'adda
ya kurma ihu ba.
Kafin yayi wani yunƙuri badakaren ya sake dankara mashi wawan sara a gadon bayan
shi,take in da ya sareshin ya haddasa wani lafcecen rauni jini ya kama feshi yana tsartuwa.
Hubairu ya sake kurma ihu karo na biyu ya sulale ƙasa magashiyan yana nishin wahala,
Kawai sai wannan garjejen kato ya zare wani zabgeegen al'amudi a damtsen shi ya taka da
kafafunshi har izuwa in da yake kwance, sannan ya ɗaya ɗaga al'amudin domin ya tarwatsa
ƙoƙon kan Hubairu.
Kwatsam bazato babu tsammani sai sauran dakarun suka ji shugaban su ya tsandara ihu,
ya sulale ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba.
Al'amarin daya firgita su kenan suka ja da baya domin suga wane ne yayi kisan, ai kuwa sai
suka akayi arba da wata bakuwar jaruma
Sanye da fararen tufafi masu yalwa, ta rufe fuskar ta da siɗin rawani, hannunta rike da wata
ƙasaitacciyar kwari da baka.
A sannanne dakarun suka fahimci cewa Jarumar tayi amfani da kibiyoyin ta wajen hallaka
shugaban nasu, don Allah sai jikinsu Yakama tsuma yana kyarma saboda matuƙar fushi sukayi
jarumar ƙawanya,
Wani daga cikin jaruman ya kurma wawan ihu yayi ɗauki kan jarumar yakaimata wani wawan
sara a wuya, Cikin wani irin baƙin zafin nama ta sanya bakanta ta kare harin sannan ta daki
badakaren a kirji.
Take ya faɗi ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba, cikin zafin nama jarumar ta buɗe